Showing 30001 words to 33000 words out of 108975 words
Chapter 11 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf
ne sosai dayamafi na Mom girma, zaka
dauka dakin wani president ne ko gwamna sunji kujeru da kayan gayu, wata Babbar mace ce
mai kiba sosai a falon, kana ganinta you don’t even need to ask twice kaga Hajiya irin cash
HajiyUoyin nan.
2️⃣2️⃣
Free page
Fara ce tass kana ganinta kaga bafulatana dan tanada mark na fulani a gefen fuskanta taci
gayu na alfarma tana sanye dawani stone gown na exclusive mai pattern, kunenta zinare
wuyanta ma haka yatsun hannunwanta guda biyu ne kawai babu zoben zinare ajiki manyan
yatsun hannunta sune babu but sauran 4 4 fingers nata duka da zinare tana zaune akan kujera
ta hakimce gawani iPad na Apple agabanta tadaura kan wani very very fine stool tana video call
dabata iya ganin kowaye a screen din tunda ita daga waje take, hannunta matan rikeda wani
white transparent bowl da ita kanta Khairy basuda irinshi agidansu an yanyanka strawberries da
kiwi fruits kanana tanaci da fork, kokai waye kaga matan saika shiga taitayinka like duk rawan
kanka irin matan nan ne da they don’t even needs to show u su waye kana ganinsu kasan
they’re no nonsense powerful woman saisa haryau itadai Khairy bazata iya cewa ta tsani matan
bane but kawai bata sonta, hasalima ita tsoronta ma takeji ko haukanta take agidan dazaran
Ammi tazo wajen natsuwa take kaman ba itaba kodako da Baffa take magana, kuma agaban
kowa ko agaban Baffa ne Ammi zata iya rufe kowa da fada baruwanta saidai in bakayi ba daidai
ba.
Kallo daya tama Khairy ta dauke kai, ahankali Khairy tajawo kofan falon ta maida tarufe sanan
takaraso cikin falon ta nemi waje ahankali akasa tazauna kanta akasa tana sauraron maganan
datakeji na namiji daga iPad din ashagwabe data rasa na waye dan tasan muryan duka yaran
gidan nan banda Babban yayansu da akace yana UK.
Ashagwabe yace “Ammi please niki kyaleni I will get the food nafita jibi fa yanda kitchen dina
yadawo” hararanshi Ammi tayi tana kallon screen din tace “My friend dauki egg din break it
ingani” cikeda gajiya kaman zai fashe da kuka yace “I don’t even know why I called u ki koyamin
yanda ake soya egg ma” dan dariya Ammi tayi da saida Khairy dake zaune tadan saci kallonta
dan bata taba ganin Ammi ko taji Ammi tai dariya haka ba lallai waye wanan itakuwa.
“Good boy Zayn, tom add a pinch of salt” Zayn! Zayn Zayn! Itako a inama ta tabajin sunan nan
Ohhkay kaman shine sunan yayan nasu dake kasan waje ko yayan su Hafiz, tatabaji Baba da
Baffa suna maganan.
Maganan Ammi ne yadawo da ita daga tunanin datake tace “bagashi nan ba kagama soya egg
din amman da u are being lazy” dariya yayi sosai yace “Ammi nataba gayamiki u are the world
best Mommy? No not just best you are the bestest Mom in this world Ammi na” dan murmushi
Khairy tayi dan maganan yasa ta tuna da Mama haka take cema Mama world best, kiss taji
yasakin ma Ammi ta wayan yace “love you Ammi bye” murmushi sosai Ammi tayi tace “I love
you too Son, speak later, make sure u put on jacket kafin kafita dan u are having cold” “who am
I to say no to this fine woman, Ammi this egg taste delicious bye” dasauri Ammi tace “kaci
ahankali karka kwar…..” kafin takarasa maganan ya katse wayan murmushi tayi sosai kafin
takalli bowl don fruits din hannunta ganin tacinye yasa ta kwalama mai aikinta kira. “Karima” da
gudu mai aikin tafito daga kitchen jikinta har yana bari dan inhar Ammi takiraka sau biyu to kora
ne, cikeda girmamawa tace “Hajiya gani” bowl din Ammi tamika mata tsugunnawa tayi sanan ta
karba tace “akawo miki wani abune Hajiya”? Girgiza mata kai tayi tamata alamu da hannu ta
tafi, wucewa tayi tawuce kitchen falon yarage daga Khairy dake zaune akasa ta takure waje
daya saikuma Ammi data dauki wayanta Z-flip tana daddannawa kaman batasan da mutum
awajen ba.
Ahankali kaman ba Khairy ba tsabagen yanda ta natsu tace “Ammi ina yini” batare da Ammi
takalleta ba kota daina abinda takeyi da wayaba tace “yanzu kikaga daman shigowa gaida ni
Ummulkhairy” girgiza mata kai dasauri Khairy tayi gabanta nafaduwa da kyar tace “Ammi
kiyakuri bansan kin…..” “stand up and get out of this room!” Ammi tadaka mata tsawa dan she
finds it insultive ace itace Babba agidan nan ko kare yashigo gidan nan yasan itane Babba an
dole ne abata wanan girman balle Wanan Yar karaman yarinyan nan da aka haifa agabanta
tashigo gidan nan saita fara zuwa ta gaida kishiyanta sanan zatazo nan, itafa Ammi is like that
bata daukan raini kona waye gatada fada, komin girmanka zata iya daga hannu ta kwasama
mari.
Tashi tayi jikinta har rawa yake itafa adai rayuwanta yanzu this woman is the only woman
datake shakka aduniyan nan, duk iskancin ka baka iya kallon fuskan Ammi kace zaka mata
rashin kunya kozaka maida mata da magana wlh bazaka iyaba Allah yariga yabata Wanan
haiba da kwarjinin nanne, gabanta nafaduwa sosai idanunta sunyi ja tace “Ammi I am so……”
“out!” Ammi tai maganan tana nuna mata kofa dasauri tai kofa zata bude aka turo kofan hakan
yasa kofan yabuge mata hannu, baya tayi tana yarfe hannun dasauri idanunta sunyi ja Hafiz ne
yana sanye da jeans da riga ganin Khairy yasa yace “Khairy kene agidan” hannunta yabi da
kallo yace “ohh no sorry nabuge miki hannu ne” murmushi takakalo tana maida hannun baya
tace “Ya Hafiz welcome ina yini” sanan tabi tagefenshi tafice dasauri yabita da kallo kafin ya kalli
Ammi dake danna wayanta abinta, maida kofan yayi yarufe yazo kusa da Ammi ya zaune yace
“Ammi yaushe Khairy tazo” batare data kalleshi ba tace “maiya hanaka tambayanta kake
tambayana” shiru yayi baice komi ba, saida tagama abinda zatayi sanan ta ijiye wayan
takalleshi tace “how’s my granddaughter”? Murmushi yayi yace “she’s fine” “tafara shan
nonon”? Gyadamata kai yayi yace “tafara Ammi, bata barin mu bacci, koda yaushe shan Nono
take bata barin Moon tahuta” dan dariya Ammi tayi taharareshi tace “idan naga granddaughter
na tarame dagakai har matarka will have to answer me I am very very serious Hafiz, anyway
anjima idan yan suna sun watse akwai kayan dazaka tafi musu dashi” Gyadamata kai yayi yace
“Ammi kinsan irin uban kudi da Ya Zayn yaturomin wai nabama Moon da Little niko sule biyar
bai baniba bayan ni namafi mai jegon wahala” dariya Ammi tadanyi saikuma tai shiru kaman
mai tunani ahankali tace “I can’t wait to see yaran Zayn shima” dasauri Hafiz yace “Ammi ai
nagayamiki Zayn nadawowa kurikeshi kumai aure dan wlh Ammi Ya Zayn bai shirya yayi aure
ba” shiru Ammi tayi batace komi ba, kallon fuskanta Hafiz yayi ganin tai nisa a tunani yace
“Ammi kema u believe what I am saying ko” “stop talking about ur brother Hafiz” shiru yayi
saikuma chan yatashi yace “ina zuwa Ammi” baijira amsanta ba yawuce yatafi, awaje yaga
Khairy gaban tap na wajen flower tana wanke fuskan ta da ruwa, bamata lurada shi ba yana
zuwa ya tsaya agefenta yace “after all this years haryau baki gane halin Ammi ba kullum kikazo
sai kinyi kuka common my friend, je daki ki dauko gyalenki keda Batool na kaiku gidan suna
kowa nachan banda ku” murmushi tayi tajuya da dan gudunta tashiga dakin Mum, basu wani
jimaba itada Batool suka fito datai wanka taci gayu motanshi suka shiga sai gidaUnshi.
2️⃣3️⃣
Free page
Gidan Ya Hafiz yacika makil da mutane sabida suna, duka yaran Baffa na wajen, Yaran Baffa
takwas, Ammi ta haifi hudu duka maza, Zayn ne babba, sai Hafiz, sai yan biyun da Ammi ta
haifa maza da Hassan da Hussain, dukansu manya duk sun gama makaranta suma aure yau
ko gobe, dan Ammi da Baffa sunyi aure tun suna yara, haihuwan yan biyun yazo mata da
complication da dole aka cire mahaifanta gabaki daya data haifi sama da haka, itakuma Mom
yara hudu ta haifan ma Baffa, mata biyu Batool da Zara’u wacce itace auta dan maza biyu kebin
Batool kafin Zara’u, Abdulhamid da Abdullahi sai Zara’u, Zara’u ce kadai ke primary school su
Abdulhamid yanzu suke SS1 boarding school, Batool itace ke university, dayake ana hutu
dukansu suna gidan ga mamakinta harda su Ya Manaf da Maheer, dukansu sun hadu dasu Ya
Hassan suna gaggasa raguna, mantawa ma tayi tayi kuka suka shiga shagalin suna ga Matan
Ya Hafiz badai kirki ba sunan Moon yabita hakan yasa kowa Anty Moon yake cemata.
Sai Bayan sallan isha’i sanan suka baro gidan itadasu Ya Manaf, tagaji iya gajiya bacci ma
tasoma abayan motan tadaura kanta kan kafadan Ya Maheer, bai tadata ba ganin tagaji
yacigaba da danna wayanshi abinshi.
Bude musu gate akayi ganin motocin su Baffa yasa daga Ya Manaf har Mu’az din kowa yasha
jinin jikinshi, parking sukayi hakan yasa tabude idanunta jin tsayuwan mota ta tashi zaune tana
kallon compound dinsu sanan tabude kofa suka fito zata wuce Ya Manaf yace “ke ina zaki”?
Dasauri tajuyo takalleshi kafin ma tabashi amsa yace “kibi Maheer kuje flat dinmu su Baffa
sunzo magana akeyi” batai musu ba danta gaji tabi Maheer sukai flat dinsu shikuma da Mu’az
sukai flat dinsu Mama da saurin su, bude kofa sukayi suka shiga sunabin kowa na falon da
kallo, Baffa ne da Baba zaune kan kujera daya, sai Ammi da Mom zaune tareda Ammi akasa da
fuskanta ya kukkumbura kaman ba ita suka Bari this morning fuskanta looking normal ba, Mom
na rikeda handky tana share idanunta dan takasa rike kuka itakuma Ammi idanunta sunyi ja dan
ciwo is something dako enemy naka don’t wish it on him, duk wanda yaga Mama saiya koka
mata, kallonsu Mama tayi lurada kaman magana takeso tayi yasa Manaf yakaraso inda take
hannunta yakama yarike yace “na tura Maheer da Khairy chan side dinmu Mama” ahankali yace
“Mama meke miki ciwo”? Kafin ma wani afalon ya iya magana aka bude kofa aka shigo Dr ne,
rikeda wata karaman Leda a hannu yana zuwa allura yahada yazo wajen hannun Mama
yakama yamata alluran a jijiya sanan yakalli Baba da Baffa dake kallonshi yace “can I talk to
you sir in private”? Girgiza mai kai Baba yayi yace “likita duk duniya banda family daya wuce
Wanan circle din dakake gani anan u can say anything, I think we are ready to hear kome
zakace right wife” gyadamai kai Mama tayi kaman ba ita ke wahala ba, huci Dr yayi yakalli
Mama yace “alluran nan zai saukar da kumburin fuskan nan da wuyanta, but at this point all I
can say is make ur wife as comfortable as possible dan koda ankawota asibiti babu abinda
zamu iyayi kuma, daga yanzu kome zaku gani kawai hakuri zakuyi har Allah yayi ikon shi dan
komi na hannunshi, just make her comfortable and happy, please kudena kuka agabanta
kowani abu dan Allah, that’s all bari nakoma hospital” tashi yayi yafita babu wanda ya iya cemai
kala, Manaf yayi yayi yarike kukan nashi but yakalli Mama yaga yanda tadawo but dudda haka
she’s still faking smile musu kawai yaji zuciyanshi yay breaking, fuskanshi yakifa akan kujera
kusada Mama sai kuka yake da Mu’az dahar lokacin shi yama kasa shigowa cikin falon yana
wajajen kofa, ahankali Mama tasa hannu takamoshi wani irin rungumeta yayi sanan tamikama
Mu’az hannu alamun yazo zuwa yayi shima kuka wiwi ajikinta babu wanda ke iya magana
cikinsu har Maman dan kumburin da fuskanta da wuyanta yayi yasa bata iya magana.
Ranan dukansu suna zaune a falon nan babu wanda ya iya motsi har asuba sanan tai bacci,
daki suka Kaita suka keantar da ita sanan Baffa ya kwashi iyalinshi suka tafi gida, suna shiga
alwala yadauro kawai yawuce masallaci.
Wuraren karfe 8 nasafe yafito daga masallacin, gida yawuce dayake yana dakin Ammi ne nan
yayi bata falo yasan ta kwana hakan yasa yay sama zuwa dakinshi, zama yayi kan wata kujera
ta musamman dayake da ita adakin nashi datake nan kaman gado shiru yayi yana tunani,
ahankali yamika hannunshi yadauki wayanshi yay dailing number dayay saving da Zayn dayake
nan international number, wayan na gab da katsewa yadauka anatse yace “Abba” dan ajiyan
zuciya ABBA yasauke anatse shima yace “Zayn nasan is late ko wajenku” gyadamai kai Zayn
yayi yana ture shishan dake gabanshi yatashi daga wajen yay bedroom dinshi zama yayi kan
study chair nashi jin muryan ABBA somehow couple with the fact Abba baima Saba kiranshi da
night ba most time da safe ABBA ke kiranshi ko darana, ahankali yace “Abba what is it are u
okay”? Ajiyan zuciya Abba yasauke yace “Zayn Maryam matan Baffan ku batada lafiya, she’s
seriously ill, inaso kome kakeyi yanzu kabarshi find any available flight dazaka samu dazai taho
naija gobe be it PJ ko normal flight ne kadawo gida” tunda yafara school that’s tun lokacin
dayake degree Abba baitaba demanding yadawo gida ba sai this time hakan yasa ahankali
yace “okay Abba, but meke damun Mama”? Zayn yay tambayan ahankali dan yanason Mama
she’s one humble woman da he admires alot dudda he’s not that close to her shi aduniyan nan
ma only Ammin shi ne he’s close too. Ahankali Abba yace “she has blood cancer! Just few days
takeda shi left inji Doctors, anyway just come home kayi few days Saika koma tunda baka fara
finals dinka ba, good night son” “night Abba” yay maganan ahankali feeling down, yadade
ahaka sanan yatashi.
Wuraren 8:00 na safe tabude idanunta ganinta adakin yayyinta saida abin yabata mamaki,
murmushi tayi ta tashi zaune sanan ahankali ta sauko daga gadon lallai tagaji ko lace din jikinta
bata chanza ba tai bacci, jakanta tadauka tawuce tafita daga dakin tana tafiya ahankali, flat
dinsu tashiga babu kowa a falo sama tayi dakinta tashiga alwala tayi tai salla tukunna sanan
tacire kayan wata doguwan rigan bacci ta tasaka sanan tafito direct hanyar dakin Mama tayi
bude kofan tayi tace “Mama tun jiya nan ganki ba adakin su Ya Manaf na kwana” akan gado
taga Mama ta jingina da hango ta sanya sweater tai fayau da ita da hulan sanyi akanta batasan
mesa ba but gani tayi Mama tamata wani iri a idanu, karasowa tayi gaban gadon saikuma ta
tsugunna takai hannunta tai tagumi tana kallon Mama, hararanta Mama tayi da kyar ta iya
dagewa tabude bakinta tace “me haka”? Ahankali tana kallonta still tace “Mama wlh kin chanza,
lips dinki are so dry, Mama wai bakida lafiyane kike boyemin kinyi wani iri eh sabida kinsan zan
damu, bazan damu bafa Mama ai yanzu na girma saima na kula dake” dan shiru tayi tana
kallon Maman dake kallonta tanaso tai magana amman azaban datakeji awuyanta yasa takasa,
dasauri Khairy tace “zan damu kadan but zan kulada ke bakid lafiyane Mama” tai maganan
idanunta na rau rau dan she’s really believing Mama bata da lafiya, ganin haka yasa Mama
tamikamata hannu sanan tahadiye duk wani azaban datakeji tace “lafiyana kalau kawai gani
nayi my little Khairy has grown so sooo big, yarinya na tai girma she can even take care of her
Mama come here” dasauri ta tashi hannun Mama takama sai kawai tasaki hannun tafada jikin
Mama ta kankameta sosai ahankali tace “Mama wlh ina bala’in sonki, without you bansan ya
zan kasance ba, Mama ko idan na kalli wasu yaran ko sai inga they are not lucky sabida
bakene Maman su ba, Mama u are the best Mama I the world, u are the coolest Mom, the
softest, the sweetest, bakida fada, gashi kina sonmu, we are ur everything Mama, Mama kinsan
menene” girgiza mata kai Mamantayi, Khairy tace “all mothers are mothers, but not all mothers
are like Mamana, cus Mamana tafi takowa dadi, Mama kinga duk girman dazanyi I will always
be ur baby, Yar autan ki, kinga na gama school nafara aiki zan dinga miki komi, Mama nasan
kinje makka but zan kaiki makka da kudina da aka biyani albashi wajen aiki” dariya Mama
tahauyi sosai dayasa Khairy wani kalan murna, sanan tace “Mama yauma ni zan miki breakfast
mezaki ci na dafa miki” ahankali tace “fate nakeso” wani tashi tayi tasauka daga gadon sanan
tai juyi tace “then fate it is bari naje” tajuya dasauri tai hanyar kofa hartasa hannu zata bude
kofan ahankali Mama tace “Ummulkhair” faduwa taji gabanta yayi hakan yasa ahankali tajuyo
takalli Mama tace “naam” dakai Mama tamata alamu tazo dasauri taje gaban gadon, hannu biyu
Mama tasa tai cupping face nata tana kallonta kafin ahankali takai goshinta saitin bakinta sanan
ahankali ta manna mata kiss a goshin, murya chan kasa tace “I love you Ummulkhairy, Allah
yamiki Albarka, Allah ya haskaka rayuwanki, Allah ya tsaremin ke” ahankali tana kallon fuskan
Mama tace “Ameen Mama” takasa tashi, ganin kaman she’s trying to read something from
Mamas face yasa Mama tace “Oya tashi kije kimin fate na yunwa nikeji Madam kokin fasane
tunda kin tasani gaba kaman kin sami talavijin” da sauri ta tashi tana dariya tafice daga dakin.
Bana tagani agaban dakin murmushi tayi tace “good morning Bana natafi yima MaUma fate”.
2️⃣4️⃣
Free page
This book is 1k to join my group pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo
evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Chat me up directly by clicking on this link
wa.me/+2347012181461
Wuraren 11 tagama faten daya cika gidan da kamshi, fito da kulan falo tayi Mama tagani da
Baba zaune afalo saisu Ya Manaf sunama Mama hira, tashi Maheer yayi yatayata suka fito da
komi tsakar falo sanan suka zazzauna karban na Mama Baba yayi da kanshi yadinga bama
Mama faten bashi kadai ba harsu Manaf sunyi mamakin yanda tasha faten dan tadena cin
abinci, tass ta shanye sai dadi Khairy keji saida kowa yagama sanan ta kwashe komi itada
Maheer sukakai kitchen tarema sukai wanke wanken tace “lallai yau mutanen mutuncin ka na
nan kusa Maheer” hararanta yayi