Showing 48001 words to 51000 words out of 108975 words

Chapter 17 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf

M Shakur   

09 Oct 2025

2848

paper tommorow”
Dudda message din baiyi acknowledge na calls nata but tadanji nauyi yasauka daga mind
dinta, kasa hakura tayi tamai reply.
“Ya Aliyu I am sorry, please kayakuri” jin shiru baimata reply ba yasa tasake turamai wani
sakon.
“I know him, class governor namu ne saisa nama amsa maganan shi, but I will not do it again I
promise”

Almost 5min but bataga reply ba, sosai taji ta bala’in damu sake turamai wani sakon tayi.

“Ya Aliyu I am sorry”
Tana turawa yamata reply.
“I said kije kiyi karatu” gyadamai kai tayi kawai ta ijiye wayan book dinta tadauka ta tashi taje
tazauna kan dadduma dudda karatun rabi tunanin shine but hakanan ta tursasa kanta tayi.

Yau rabonta dajin muryan Aliyu sati daya chur kenan dan gashi nan wata asabar din ta zagayo,
exam ma adaddafe take tabashi hakuri harta gaji yaki hakura dudda kullum saiya mata text
yasata tayi karatu but other than that shiru kakeji, har dan ramewa tayi dayake ansan exam take
babu wanda yabama abin attention, yau tunda gari yawaye Mom tasata ta shirya taje tagaida
matan Baba da tuni akai biki harta tare, bataso taje amman bazata iya cewa no ba hakan yasa
ta shirya dan yau at the same time zaa raba gadon Mama abinda yasama bataso taje kenan.


Parking direba yayi acikin gidansu gani tayi gidansu ya chanza an sake penti, Baba tagani
akujera a tsakar gidan da alamu shan iska yake yasa farin jallabiya ga flask don shayi
agabanshi dawasu papers yarame sosai ganinta yawani fadada murmushin fuskanta yabude
mata hannu dawani irin gudu tazo batai wata wata ba tawani rungume shi she miss baba so
much, sun dade ahaka sanan tasakeshi yazauna kan kujeran dake kusada shi tace “Baba ina
yini” murmushi yamata yana tana kumatunta yace “Khairy na ya jarabawa next week zaki gama
ko” gyadamai kai tayi yace “yaushe zaki dawo gida” gidan tabi da kallo sanan ahankali tace
“bayan jarabawa Baba” Gyadamata kai yayi sanan yadauki papers dake gabanshi yabata yace
“ga gadon Maman ki nan dakika samu na filaye biyu dakuma gidan kifinta guda daya, sai
kayayyakin ta, duk wani abu na Maman ki daidai da cokali an raba, duk suna store, su Manaf
duk sunkai nasu gidan marayu sunyi sadaka dasu naki kome kikace ayi dasu haka zaayi”
ahankali tace “Baba akai gidan marayu, kayanta na sawa zan cire wanda nakeso sauran sai
akai” Gyadamata mata kai yayi sanan ahankali yakama hannunta yace “I am here for you
Khairy okay, hope bakida any damuwa” dan murmushi tayi tace “Baba I am fine Allah kuwan,
ina su Ya Manaf” “sun tafi office” gyadamai kai tayi ahankali tace “ina new Mom”? Yadade yana
kallonta sabida yanda tafadi sunan kafin ahankali yace “tana ciki” tashi tayi tace “bari naje
nagaidata” tawuce ciki Baba yabita da kallo, ahankali tabude kofar falonsu wani sanyi yamata
sallama tadade tsaye kafin ta shiga cikin falon daidai da foot mat nabakin kofa an chanza har tv
bango an chanza komi tatas kaman ba gidansu ba kaman ba falon Mama ba, abin was so
strange, mutuwa mutuwa wlh karshe ne! yanzu shikenan this falo is not for Mama again na wata
ne, Anya zata iya cigaba da zama agidan nan kuwa Anya bazata koma da zama gidan Baffa
gabaki dayaba Dan what she is feeling right now jitayi kaman ta kurma ihu hatta labule duka
bana Mama bane jin kuka yazo mata sosai dawani irin sauri tajuya zata fita taji ankirata.
“Ummulkhairy” chak ta tsaya, sanan takai hannuwanta ta goge hawayen dasuka zubomata
daga idanunta tass kafin ahankali tajuyo, sabuwar matan Baba tagani batada wani makusa
Babba ce itama amman daga gani Mama ta girmeta sosai, doguwa da ita kana ganinta kaga
natsassiyar mace, murmushin dole Khairy ta kakalo ahankali tace “ina yini uhnnn” tama rasa
sunan dazata kirata dashi murmushi matan tayi daidai takaraso gabanta hannunta tasa ahankali
takama hannun Khairy tace “sunana Mariya, maisa kika tsaya anan bakin kofa keda falonku
shigo mu gaisa” taja Khairy cikin falon danne kukanta Khairy tayi sosai sanan ta zauna akan

kujeran da Mariya ta zaunar da ita sanan tace “ina zuwa” dasaurinta ta wuce kitchen tafito da
drinks a tray takawoma Khairy ta ijiye sanan tasake zama kusada Khairy data kasa kallonta dan
wani iri takeji, ahankali takai hannunta tadaura kan cinyan Khairy cikeda tausayawa tace “ina
tunamiki da mahaifiyanki ko” dauke kai Khairy tayi da sauri tana kokarin danne hawayen dake
gab da zubowa tace “uhn uhn” ahankali Mariya tace “Khairy I am so sorry about your mother’s
death, Allah ubangiji ya haskaka makwancinta, Allah yasaka mata da gidan aljanna” ahankali
Khairy tace “Ameen” murya chan kasa tace “Khairy mijina na farko nima yarasu so I understand
pains dinki sabida yarana suma sunma mahaifinsu kuka, at first da akazo nemama babanki
aurena nariga nai alkawari bazan kara aure ba but danaji matarshi tarasu tabar yara abinda
yasa na aure mahaifinki kenan sabida inaso nazama uwa ga yaranshi dan ni bansami chance
dinan nama yarana hakaba” dasauri Khairy takalleta tana share hawayen daya zubomata,
Gyadamata kai tayi tace “bayan rasuwanshi iyayenshi suka karbe yaran, kafin naga yarana
yanzu sai Hutu Hutu akawosu sumin kwana biyu, tuntuni naso nazo dakaina ma har gidan
Baffan naku ko Baban ki ko yayyinki sukawoni nadawo dake gidan mahaifinki, Khairy just know
this, nasan ba lallai ki daukeni ko ki kalleni a matsayin mahaifiyanki yanzu ba saidai a matsayin
kishiyaneuwa, I want to assure u ke y’ata ce Khairy, u can come to me for everything and
anything, zan rikeki da yayyinki amana kaman yaran da na haifa, bazan taba cutar daku ba
kinji” Gyadamata kai Khairy tayi sanan ahankali tace “thank u” hannu Mariya tasa tashare mata
hawayen sanan tace tashi muje sama binta Khairy yayi Baba dake kofa yaji komi baitaba jin
sonta aranshiba sai yau, tunda akai auren basuma taba kwana daki daya ba dan gani yake
kaman yacuci Mama amman yau yakudiri aniya komi zai chanza zai saki ranshi da ita.


Khairy bata bar gidan ba sai bayan sallan magrib shima saida matan Baba tasa tamata alkawari
dazaran tagama jarabawa zata daCwo gida.



3️⃣6️⃣



Yauma hartai bacci Aliyu bai kirata ba ita at this junction tama fara tsoro haka Aliyu keda fushi,
abinma haduwa yayi yataru yamata yawa hakan yasa ta tashi da zazzabi jikinta zafi gashi
hancinta yatoshe mura, wuraren 7:30 tafito kasa, ganinta wani iri yasa Mom tace “meke
damunki idanunki sundan kumbura da hancinki” ahankali tace “mura ne” jin yanda take magana
da hanci yasa Mom tace “Ayyah sannu zoki breakfast bari nakowa miki maganin mura” kunu
tadeba tafara sha bata wani dade ba Mom tasauko rikeda maganin mura karba tayi tasha sanan
takarasa shanye kunun ta tashi tama Mom sallama ta tafi.

Tun kafin sukarasa wajen parking space din ta hango Aliyu tsaye yay wani irin bala’in kyau
yakara haske kaman wani balarabe, yana sanye da uniform din yan sanda jingine da motanshi
yay folding hannunshi a kirji yana kallon motansu tunda ta doso, idanunshi sun fada ciki kadan

kana ganinshi kasan shima yawahala yan kwanakin nan kaman yanda itama ta wahala.


Jitayi wani abu yazomata wuya amman ta danne, parking Adamu yayi hakan yasa tafito daga
motan ahankali kallonshi tayi kaman yanda yake kallonta, hawayen dataji yazo mata yasa
takauda kanta gefe dasauri taredakai bayan hannunta tashare sanan ahankali tadaga kafanta
tafara tafiya wuceshi tayi ahankali kaman bata ganshi ba dawani irin sauri yasha gabanta hakan
yasa chak ta tsaya batare data dagokai ta kalleshi ba dan dazaran ta kalleshi zata iya kuka
kuma bataso tayi, ahankali tace “excuse me please I have exam by 9” dan ijiyan zuciya yasauke
tareda lumshe idanunshi jin muryanta sanan ahankali yabude su yadaura akanta, murya chan
kasa yace “Ummulkhair!” Wani abune yataso mata tundaga cikinta harzuwa wuyanta dataji
inbata amayar dashiba zata iya mutuwa dago idanunta dasukai jaa tayi sun cikada kwala tace
“don’t call my name again Ya Aliyu, nadauka ai kadena daukan wayana, kadaina kirana,
kadaina texting dina? Why are you here then? Mekazo nema wajena”? Kallonta yake idanunshi
sundanyi ja, jiyayi zuciyanshi na tafarfasa, ko kadan baiso yanunama Khairy fushin shi that’s the
reason why he avoided her yamaki wayada ita, wani irin zuciya yakawomai wuya ciki wani irin
harsh tone that’s not loud yace “kinmin laifi and kina fushi dani? Why would you talk to anyman
har kina karban abinshi why?!” Yamata wani kalan ihu da saida tadan firgita tadan koma baya
tana kalle kalle tagodema Allah dababu kowa awajen, zuciyanshi yanuna mata yace “kinsan
what you did to me? To my heart haaa? Why will you talk to anyman why?? Akanme zaki tsaya
kinama wani namiji magana bayan kinsan I love you! My heart beats for you! You are my life! U
are my happiness! You are my everything Khairy haaa” yanda idanunshi taga sunyi jajir saida
abin yabata tsoro kaman zai daketa, jijiyoyin kanshi sun fito, bayan hannunta tasa tagoge
hawayen daya zubomata kafin ahankali tace “Ya Hydar akanme zakai tunanin wani abu bayan
nacemaka class governor dinmu ne, is it my fault we bumped into each other that day? Ya Aliyu
akanme zakai tunanin wani nakeso bayan nariga nama zuciyata alkawari cewa ita taka ce,
zuciyata, gangan jikina, ruhina duka nakane Ya Aliyu Wanan shine ALKAWARIN ZUCIYA na,
akan me zakai tunanin bana sonka uhmm”? Hawayen daya zubomata ta share, kawai tawuce
fuuuu hannu yamika zai kirata amman yakasa cikin wani irin fushi yadaki motanshi da kafa
shikanshi baisan mesa yake da mugun kishi nan ba.


Adaddafe tai exam din ranan, inda ace batai karatu ba dababu abinda zata iya rubutawa sabida
yanda babu abinda kemata dadin nan, bata taba sanin haka akeji idan akai fada da masoyi ba
sai yau, she miss Aliyu badly, she just miss him.
Tana gama paper tafito bata tsaya jiran su Besty da Amal ba sabida yanda batajin dadin komi
ga jikinta yakara zafi, fitowa tayi yanda takeji batajin zama ta iya jiran Adamu yazo daukanta ba
hakan yasa tafara tafiya tai hanyar gate, wani irin shan gabanta da mota Aliyu yayi tana ganin
motan tajuya zata chanza hanya da sauri yafito baima tsaya mata magana ba hannunta yaja
ganin mutane yasa tabishi dan ayanda yake zai iya cewa daukanta zaiyi gaban mutane idan
bata bishi ba, bude mata yayi tashiga batare data kalleshi ba sanan yamaida kofan yarufe
yazagaya yashiga mazaunin direba yaja motan, batare data kalleshi ba tace “kana fita daga
gate kasauke ni natare cab natafi gida” kallonta yayi da jajayen idanunshi cikin husky voice

dinshi yace “idan naki fa” hannunta tadaura akan fuska tafashe da kuka sosai cikin kuka tace “I
said I am sorry, I don’t have anything to do with class governor munhadu ne by accident, he said
yazo wajen da sister shine, and he insisted saina karbi candy hannunshi, I don’t wanna be rude
koyaga namai wulakanci saisa na amsa, nabaka hakuri kaki hakura what do you want from me,
what do you want from me?” Wani irin fizgota taji anyi da bala’in karfi, dawani irin sauri tabude
idanunta jikinta na rawa, tuki Aliyu yake da hannu daya akan titi amman ya fizgota da karfi tana
jikin kafadanshi yakai hannunshi ta waist nata yariketa gam ajikinshi takasa kwace kanta yana
kallon hanya, dasauri takalli hanyan jikinta narawa tace “Ya Aliyu dan Allah zamuyi accident kayi
parking” gangarawa gefen hanya yayi yawani kalan taka burki kaman motan zai kife
kankameshi tayi tareda runtse ido gam gam jikinta narawa still, habanta dataji ankama yasa
tabude idanunta ahankali, hada idanu sukai da Aliyu da idanunshi sukai ja faduwa taji gabanta
nayi, cikin wani irin murya yace “you ask wat do I want from you” gyadamai kai tayi tana wani
irin shakkan shi, wani kallon fuskanta yake ahankali yace “I want you Ummulkhair! I want you so
bad saisa my heart can not stand yaga kinama any namiji magana, zuciyana yakusan bugawa
ranan I had an accident” dan zaro idanu tayi cikeda mamaki, lumshe idanu yayi sanan ahankali
yakai fuskanshi dab da nata yana kallonta dawani irin sauri ta lumshe idanunta gabanta
nafaduwa dasauri dasauri yadade yana kallon fuskanta ahaka kafin ahankali yadaura goshinshi
kan nata yanajin saukan numfashinta akan fuskanshi, cikin wani whispering voice dake nuna so
yace “I am sorry for hurting you, I couldn’t help it, Ummulkhair ina sonki da yawa and Aliyu is a
very very jealous man bayin kaina bane, can you put up with me? I can’t help it bazan iya
magance kishina akanki ba, zaki iya rayuwa dani eh Ummulkhair?” Jitayi zuciyan ta gabaki daya
yasaki gyadamai kai tayi ahankali tace “but don’t ever hurt me the way you did by not answering
and responding to my calls, Ya Aliyu I….Love yhuu” this is the first time tafadimai kalman daya
dade yakeso yaji daga bakinta, ahankali yace “you are the PROMISE OF MY HEART Khairy”
ahankali tace “Ya Aliyu nima kaine ALKAWARIN ZUCIYA ta” ahankali yamata peck a forehead
sanan yakai hannunshi yashare mata fuska tass sanan gently yasake ta yamaidata kujeran
datake kafin ahankali yatada motan zuwa pharmacy, magunguna yasayo mata da ruwa da
kanshi yabata sai kallonta yake sanan yadawo motan yatada har anguwan su Baffa yakawota
nesa da gida yay parking sanan yakalleta, kallonshi tayi sanan ahankali tabude motan tasauka
tawuce saida yaga shi ganta gida sanan yatada motan yabar anguwCan.




3️⃣7️⃣

Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp

number na 07012181461
Thank u❤️


Wuraren 10 yau taga kiranshi wayan na gabda katsewa tadauka ahankali tace “Ya Aliyu”
ahankali shima yace “Ya muran? Jikinki yadena zafi” gyadamai kai tayi tace “eh yadena naji
sauki” dan ijiyan zuciya yasauke kafin ahankali yace “I am sorry for hurting you Pickle, will you
forgive me” gyadamai kai tayi tace “bakomi yawuce” dan ijiyan zuciya yakara saukewa ahankali
yace “kinada paper ranan Monday” gyadamai kai tayi tace “yes but in the morning” ahankali
yace “good, I want to invite you to my promotion stuff zakizo” wani irin murmushi tayi tace
“za’ayi promoting naka awajen aiki”? Dan yatsine fuska yayi yace “kind of and I want you to be
there for me, ina stage ina ganinki ina murmushi” dan murmushi tayi sosai tace “to baranzo ba”
Dasauri kaman dan yaro yace “pleaseeee Khairirin Baba” dan dariya tayi ganin yanda yake
tsokanta ahankali tace “okay shikenan zanzo but kaizaka daukamin jakana” dasauri yace
“zanma goyaki like my baby idan kinas..…..” katse wayan yayi dasauri jin alamun mutum tsaye
adakinshi, dago kanshi yayi ganin Abba tsaye yana sanye da jallabiya ya rungume hannunshi
yana murmushi yasa yaji wani kalan kunya, daman abinda yasa baije wajen Abba ba sabida
yay wasu manyan baki ne, patient dinshi saisa baije ba.

Ahankali Aliyu yatashi zaune daga gadon kasa kallon Abba yayi dan murmushin da Abba keyi
kadai ya tabbatarmai da yaji all maganan dayake da Ummulkhair, akunyace yace “Abba bakin
sun tafi” dan murmushi Abba yayi yamaida kofan yarufe sanan yashigo dakin har zuwa inda
Aliyu yake zaunen sanan yazauna agefenshi, ahankali yace “Aliyu so kanada yarinyar dakakeso
haka baka sanar dani ba” kunya yasakeji ganin yakasa magana yasa cikeda kulawa Abba yace
“what’s her name”? Ahankali murya chan kasa Aliyu yace “Ummulkhair” dan murmushi Abba
yayi yadade yanaso yaga Aliyu yayi aure amman ko budurwa Aliyu baidashi, daurewa yayi yay
hiding farin cikin shi karya nunamai yace “yaushe zamuje mu nemamaka aurenta”? Dan
murmushi yayi dashi kanshi Abba saida yaga murmushi hakan yakara tabbatarmai da yanda
Aliyu ke sonta sanan yace “inaso dama takarasa gama school ne Abba” ahankali Abba yace
“nan da kaman yaushe kenan” ”sauran mata just one semester, Accounting takeyi” gyadamai
kai Abba yayi saikuma yatashi tsaye yana kallonshi ganin yanda har yanzu yakasa hada idanu
dashi, cikeda tsokana yace “bari natafi nabarku kucigaba da soyayyan ku, anyway greet my
daughter in law for me” dan dariya yayi Abba yawuce yafita ranshi fess. Kiran Khairy yakarayi
sai after 1 sanan sukai sallama.



Yau Monday wuraren 12 tadawo gida dan 11 tagama paper ta na yau, tanacin abinci tai bacci
dan 4 zata wajen ceremony na karin girman Aliyu.


4 ta tashi agurguje tashiga bayi wanka tayo tana fitowa tai salla sanan tashiga shiryawa cikin
wani embroidery exclusive atampa, gold and red, an mata dinkin doguwan riga A-shape dayay

mata kyau, dan kwalinshi ta daura dayay kyau akanta sanan tadauki wani simple red veil tasa
kafin tadauki wani warwaron zinare ta tasaka da dankunnen zinare mai kyau sanan takalli kanta
a madubi kwalli tadauka tasaka ma manyan idanunta kafin tashafa man baki, wani takalmi mai
tudu tasaka red, sanan tadauki gold jaka tahada sake kallon kanta tayi amadubi tai wani irin
kyau kaman amarya, dan murmushi tayi sanan tafito tana kallon agogo 4:40, sallama tama
Mom da sunan zata gidansu sanan tawuce Adamu yadauketa she wants to get a gift for him is
his promotion and banda hakama bata taba bashi anything ba, hakan yasa tacema Adamu
yakaita wani Men’s boutique.

Shigatayi ciki tana kalle kalle kayan maza ne awajen babu abinda babu gaban wani Jaguar
special edition watch tana kallo, yanda take kallonshi yasa mai shagon yadauko yabata
murmushi tayi tace “how much is it”? 359k, gyadamai kai tayi sanan tazabi wani bakin
sunglasses dayamata kyau shima designers product na police shikuma 156k sanan taciro ATM
card dinta tabiya, indai kudi ne tanada shi, every month tun suna yara Baba nabasu monthly
allowance, yayyinta nabata kudi just like that, Mama ma nabata kudi, Baffa shima every month
saiya bata kudin break dan haka yake kiran kudin, banda random kudin datake samu every now
and then bata kashe kudi tanada komi, wrapping everything aka mata sanan tasa aka
rubutamata congratulations a paper tag aka makala jikin cute bag din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login