Showing 27001 words to 30000 words out of 108975 words
Chapter 10 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf
yayi yafita cikin yayyafin da akeyi yakoma gaba
kunna motan yayi yaja motan har gaban motansu yakaita sanan yay parking jacket dinshi tacire
ta linkemai ta ijiye ahankali tace “thank you” sanan tabude kofan zata fita kaman daga sama taji
yakirata. “Ummulkhair!” Faduwa gabanta yayi batasan mesaba duk idan yakirata sai gabanta
yafadi, juyoda kanta tayi takalleshi shima ita yake kallo, ahankali yace “I am a very very jealous
Man! Be mine only Khairy! I am in luv with you! Good night!” Dawani irin sauri har hannunta
narawa tamaida kofar tarufe sanan tajuya tabude bayan motarsu ta shige kafin yaja motar nashi
yawuce.
2️⃣0️⃣
Free page
Wucewa yayi daidai lokacin wayanshi na ringing ganin Meena ce ke kiranshi yasa yamaida
kanshi kan tukin inda yasan zai gansu chan yawuce, atsaye ya gansu da alamu shi suke jira,
kashe motan yayi yafito yana kallon Gwaggo dake binshi da kallo ganin ya wartsake sosai yace
“lpy” hararanshi tayi tace “munafuki nidai sani a mota” sata yayi a mota yana murmushi kasa
kasa sanan yamaida kujeran boot su Meena suka saka ledojin abubuwan dasuka siya a boot
sanan yarufe kowa yakoma yashiga motan yaja motan zuwa gida yana parking yafito baima
tsaya bi takansu ba masallaci yawuce dan yasan zasu tafi da Gwaggo ciki.
Tareda Abba suka shigo gidan daga masallaci magidancin mutum ne yana sanye da suit baki
dan daga wajen aiki yake, falo suka wuce, duk su Mami da yaran na falo gaida Abba duk
sukayi, ganinshi yasa Mami tace “akawo abincin yanzu Alhaji” girgiza matakai yayi yay hanyar
stairs yace “I am coming tukunna muje Aliyu” binshi Hydar yayi har zuwa sama wani babban
falo suka shiga wanda kana gani kasan na Baban shine, zama yayi akan kujera Abba yazauna
kusada shi yakai hannunshi yabude idanunshi yana haskawa dawani dan tocula dankarami
yana dubashi, dan jim yayi sanan yace “you have typhoid Aliyu, I think zan saka on injections
tunda bakason magani” yatsine fuska yayi ahankali yace “Abba wlh naji sauki, kainafa kadai ke
ciwo kuma yadena” “yimin shiru my friend” Abba yay maganan yana tashi wani babban first aid
box yadauko yabude sanan yahada wani allura Aliyu naji yana gani Abba yamai allura, sanan
Abba yace “Aliyu this work is draining you, akan me u are a Barrister kawani kama kashiga aikin
police with just mukamin ASP eh, why will you choose a police man job Son common talk to me”
yay maganan yana kallon Aliyun cikeda damuwa, Aliyu ne kadai danshi namiji, yaranshi duka
takwas aduniya, Aliyu ne nafarko he’s 32yrs sai kannenshi mata guda bakwai hudu sunyi aure
dukansu baa Nigeria suke aure ba Saura 3 agida suna school, ganin yay shiru yakasa cewa
komi yasa ahankali Abba yace “tashi katafi, but make sure kaci abinci kafin ka kwanta kaji”
gyadamai kai yayi sanan yatashi yawuce yabude kofa shikuma Abba yashiga cire kaya dan yay
wanka duk bayajin dadi.
Yana fitowa da Mami yaci karo anan falon sama tana zagaye, kallo daya yamata yadauke kai
yashiga sauka kasa itakuma tawuce tashiga falon Abban da sauri tanabin ko’ina da kallo dan
Abba yariga yashiga bayi, ganin allura da first aid box abude yasa tasauke ijiyan zuciya taje
gaban wardrobe tana budewa dan samoma Abba kayan dazai sa….
**
Tana komawa gida kayan jikinta tacire tayo wanka sanan tai salla tasauko kasa gabaki dayansu
duk suna zaune a falo suna dinner gaida kowa tayi sanan tazo kusada Mama tazauna tana
kallon Mama dataga tasaka sweater turtleneck black daya rufe har wuyanta tasaka hulan sanyi
shima baki kafanta da bakin safa, kallonta Mama tayi jin ajikinta ana kallonta hannu tasa taja
hancin tace “ke abinci zakici ko kallona kikazo yi” dan dariya kadan tayi tace “Mama sanyi kikeji
ne AC akashe” gyadamata kai Mama tayi batare data bata amsan tambayan ba tace “mezan
zubamiki” kallon abincin tayi sanan takalli madaran da Baba kesha tace “Mama madara zansha
banson naci abinci” Madaran da Baba Kesha a cup da zafinshi ma yamika mata da sauri ta
karba tana murmushi tace “thank you Baba” hararanta Mama tayi tace “kwadayi Khairy, aikin ki
kenan tun kina Yar kankanuwan ki sabida babban ki kullum yanashan dafaffen milk kema
kikesha” mikewa tsaye Baba yayi yace “bagashi nan saisa she’s so bright ba ga kwanya, milk is
good for children barin ma Wanan na Shanu damuke sha dababu mix, bari naje nai salla” yakalli
su Manaf da duk suka tashi suma sukawuce suka tafi masallaci, madaran ta shanye tass sanan
ta tashi ta tattara kayayyakin dasukaci abinci takai kitchen sanan tadawo tana kallon Mama
dahar lokacin take zaune inda tabarta tace “Mama tashi mutafi sama” ahankali Mama tace
“wuce kitafi akwai wani program na wa’azi dazan kalla yanzu za’a fara” sanin Mama da kallon
tashoshin wa’azi yasa tawuce stairs abinta tace “Mama gobe zani saloon kitso good night”
ahankali Mama tace “Allah yakaimu Khairy” saida taji bude kofanta tashiga daki sanan gently
tasa hannunta tadaura kan kujeran dake gefenta tana kokarin tashi tsaye amman takasa
idanunta sunyi jazur kana ganinta kasan tana wahala ita kadai tasan metakeji, komawa tayi
tazauna ahankali sanan tasauke ijiyan zuciya, hawayen daya zubomata takai hannunta tashare
tanajan hancinta jin majina ya tsinke mata kafin tasauko da hannun ta share majinan, sanan
ahankali tasauke hannunta kasa tana kallon tafin hannayen nata dasukai jajir kaman wanda yaji
ciwo, ajiyan zuciya tasauke majina na gangarowa daga hancinta sanan tadaura hannunta kan
hannun rigan tajashi sama tana kallon fatan jikin hannunta dasukai jaaa wasu kalan kuraje
dasuka fitomata sunyi dabbare dabbare sunyi chaaaaa wanda is not just hannu ko’ina ajiki suka
fesomata har wuya saisa tasaka Riga turtle neck dankar Khairy tagani, hannu takai tashare
majinan dataji yana gangaromata yakai mata baki sanan tadaura hannunta kan baki tana kuka
mai bala’in tabarai, she don’t even know why she’s crying, tana zaune a inda take aka turo
kofan falon aka shigo dago kanta tayi takalli kofan Baba ne yashigo, kallo daya yamata yagane
kuka take maida kofan yayi yarufe sanan yakaraso ciki ahankali yazo gabanta tsugunnawa yayi
sanan yakai hannunshi yakama nata yakai kan kafadarshi kafin ahankali yadagata tashi tsaye
tayi da taimakonshi dan ayanzu sai an dagata an kuma kwantar she can’t really do anything da
kanta sabida, har yakaita daki bai iya cemata uppan ba, zaunar da ita yayi akan gado sanan
yashiga bayi yadauko baho da buta da kanshi yamata alwala sanan yasamata hijabi kwantar da
ita kan gado yayi sanan yace “pray” gyadamai kai tayi da idanunta dasukai jajir sanan tashiga
yin sallan isha’i yana zaune gefenta harta idar sanan yacire mata hijabin.
Kashe wutan dakin yayi sanan ya kwanta gefenta yarufa mata bargo kafin yadaura kanta kan
kirjinshi yanajin yanda jikinta yay zafi sosai, murya chan kasa tana kara kankameshi tace
“nagode Baban su Manaf” gyadamata kai yayi yakasa magana har lokacin, hannunshi takama
takai kan kirjinta ta manna sabida yaji yanda zuciyanta ke bugawa ahankali tace “kaji yanda
zuciyana ke bugawa ko, tunanin yarana yasa haka, dan Allah ka kara aure banso daidai da
sakan daya yarana suyi maraici kaji Baban Manaf” wata kalan huci kai zafi Baba yasaki
ahankali yace “Maryam at this junction danake in my life banma da natsuwan dazan iya neman
aure, yarana bazasu taba maraici ba, I am here, Baffan su nada mata har biyu they are
sounded with mata they can call mom, please tunane tunanin nan will keep on eating u harsai
kin daina, please concentrate on your health kinji, gobe zan kira Dr” girgizamai kai tayi tace
“please no kabarshi yaje yay saving those that still have chance not me nariga naji ajikina my
end is nea…..” Kankameta sosai yayi ajikinshi yana huci mai zafi wasu thick tears na neman
fitomai daga idanu ya hadiye su ahankali yana jijjigata ahaka bacci yay awon gaba da ita saida
ya tabbatar tai baccin sanan yatashi ahankali gyaramata bargo yayi sanan yawuce yashiga bayi
alwala yadauro yazo yahau kan dadduma shafai da wuturi yayi yamata addu’a sanan yakoma
gado kusada ita ya kwDanta.
2️⃣1️⃣
Free page
Saida tai sallan isha’i sanan tacire hijabi kayan bacci taciro tasaka tana tunanin abinda yafaru
dazu itada Aliyu, dan murmushi tayi sanan ta kashe wutan dakin ta kwanta.
Batasan mesaba tadade kwance rikeda wayanta tana kallon wayan every minute deep down
she wish to hear his voice amman kuma bamataso tana tunanin what she wish for din akanshi
abin is so so new for her she’s not just use to it, ahaka bacci yay awon gaba da ita wayan nakan
kirjinta this is the first ever time in her life da waya ke bacci akan kirjinta.
Wuraren 12 nadare wayan nata yahau ringing afirgice tafarka tana daukan wayan daga kan
kirjinta tana danna gefe dan yadena ringing yay silent, sanan takalli screen din da kyau ganin
Aliyu Hydar batasan mesaba faduwa gabanta yayi, ahankali takai yatsanta dake dan rawa ta
danna wayan na gab da katsewa takai kunnenta, murya chan kasa dake nuna alamun bacci
tace “Hello” shiru yayi yana sauraron muryanta da bazaiyi karyaba tunda yake baitabajin macen
da muryanta yamai dadi kaman nata ba, dan gyaran murya kadan yayi cikin wata kalan murya
dashi kanshi baisan yanada itaba yace “Khairy” ahankali kaman wata Yar karaman baby tace
“Uhm yajiki? Kasha magani?” dan murmushi yayi jikinshi namai wani iri jin muryanta like that so
naked sabida baccin data fara, sanan har ranshi yaji dadin yanda ta tambayeshi yajiki koyasha
magani, ahankali yace “yeah, Abba yamin allura” kaman zatai kuka dan ita harga Allah tanada
tausayin mara lafiya tace “auuch that must have hurts, I hate niddles, sorry ko!” murmushi yayi
ya gyadamata kai yace “thanks, you are sleepy”? Gyadamai kai tayi tace “Uhm” ahankali yace
“alright good night, make sure you plug in your phone sabida yasami chaji, and say your prayer
before sleeping okay” gyadamai kai tayi ahankali tanajin wani iri azuciyanta kaman tacemai
sucigaba da magana karya tafi tadenajin baccin tace “okay night” tai maganan batare data cire
wayan daga kunnenta ba shima bai katse wayanba sunkai kusan 10min ahaka sanan murya
chan kasan kasan makoshi yace “I love you Ummulkhair okay” gyadamai kai tayi ahankali tanaji
hawaye nazuwan mata dabama tasan na meyeba but ko Allah yasani she just feel damn
connected to him and vulnerable around him kaman ba itaba, katse wayan yayi hakan yasa
taciro wayan daga kunnenta tarungume wayan hawayen na gangaro mata daga idanu, karan
message dataji yasa taciro wayan daga kirjinta dasauri tabude wayan ganin message from Aliyu
Hydar, bude messege din tayi da sauri. “Maisa nake sonki Ummulkhair? Well who am I to
question faith? All I feel right now is I wanna spend my eternity with you, gud night Khairy”
Takaranta message din kusan sau biyar sanan ta danna reply tai shiru tana kallon blank space
din bamatasan mezata rubuta maiba, saikuma chan tashiga typing .
“I feel vulnerable and free around you, my heart beat whenever I hear your voice, duk sanda na
rufe idanuna kai kadai nake gani, is that love?“
Yana ganin message din yay mata reply.
“time will tell Khairy na❤️”
Wani kalan murmushi tayi ganin yakirata da Khairy na sanan ta tashi zaune USB takamo dake
jone da wall socket ta saka wayan nata kaman yanda yace tayi sanan takoma ta kwanta tadade
kafin bacci yay awon gaba da ita.
Da asuba Baba yashigo yatadata saida yaga tashinta dan Khairy nada nauyin bacci sanan
yawuce yatafi, bayi tashiga tadauro alawala tazo tai salla, koda tagama karatun Al Qur’ani tayi
yau sosai wuraren 6 ta tashi, hijabi tacire yau ita keson yimusu breakfast tunda bazata school
ba hakan yasa ta tashi tafice daga dakin tasauka kasa kitchen tashiga tana murmushi tace “idan
matarchan tazo yau zataga na hutashe ta” lafiyayyen breakfsat tahada musu dan sinasir tayi da
farfesu sai kunun Gyada dasu fried chips, saida tagama tsaf sanan tashiga fito da komi falo
ganin Mama zaune afalo kusada Baba yauma sanye da kayan sanyi yasa ta ijiye kulan a
tsakiyan falo ta tashi tana kallon Mama dataga tamata haske sosai Mama datake nan baka but
tai wani irin haske, kafinma Mama tai magana Baba yace “ke wuce ki kawo mana abinci ga
yayyinki nan zuwa” dasauri tajuya tana murmushi tace “Baba naga Mama tai haske ne takara
kyau” kitchen tashiga takarasa fito dakomi takawo lokacin su Manaf sun shigo suma zama duk
sukayi Baba da kanshi yadebo ma Mama Sinasir yana bata abaki, murmushi tayi tana kallonsu
tana taba Ya Manaf, hararanta yayi yace “dalla kauyus” cigaba dacin abinci duk sukayi kowa
yay shiru Baba da Mama ne suka fara gamawa sanan yakalli Khairy yace “Maman ki tace zaki
saloon ko” gyadama Baba kai tayi tace “eh Baba, gyadamata kai shima yayi yace “yau rabonki
da gidan Baffan ki kwana nawa” dan ajiyan zuciya tayi ganin yanda Baba ke kallonta sanan
ahankali tace “an dade Baba” jinjina kai yayi yace “kije ki shirya kitafi saloon yanzu ana gamawa
kije gidan Baffan ki ki gaidasu sanan kije gaida Matar Hafiz” ahankali tace “to Baba” “tashi kije”
tashi tayi tai sama Baba yacigaba dayima Mama hira yau yanaso yakaita asibiti kotaki kotaso
dan kwata kwata this days bata iya baccin dare ga kurajen nan kara fesowa suke ajikinta bana
wasaba.
Tana shiga dakinta zama tayi kan gado sanan tadauki wayanta dahar lokacin bata cire daga
chaji ba tabude message din Aliyu tagani around 5 na asuba.
“it’s time for subhi, wake up”. Murmushi tayi sosai sanan ta ijiye wayan tawuce bayi wanka tayo
tafito direct gaban wardrope dinta taje wani riga da skirt na wani paper lace dinta tafito dashi da
akamata dinkin jumper rigan yakai mata har gwuiwa sai skirt shikuma straight skirt daidai jikinta,
mustard color ne lace din sai aka ni kayan dawasu bakaken stone, murmushi tayi taje tadaurasu
kan gado sanan tazauna gaban mirror tadauki manta tana shafawa tana kallon fuskanta
amadubi tana tunanin Aliyu, saida tagama shafawa sanan ta saka kayan dasuka mata bala’in
kyau sosai, murmushi tayi black veil tadauka ta feffesa turare sanan tadauki handbag dinta ta
jefe wayanta aciki tasa flat slippers yau tafito, afalo taga Baba kan doguwan kujera yana duba
jarida Mama kwance tayi filo da kafanshi tana bacci yarufamata bargo, ganin Khairy yasa
yadaura hannunshi akan lips dinshi yace “karki tadamin da matata tana bacci” turo baki Khairy
tayi ashagwabe tace “Baba yanzu kafisun Mama dani Yar Autan ka” dan dariya tayi yamika
mata wasu kudade yace “gashi Adamu na jiranki kije saloon kina gamawa ki wuce gidan Baffa”
gyadamai kai tayi ta karbi kudin sanan takalli fuskan Mama dake bacci tace “Baba natafi” adawo
lpy.
Saloon suka wuce direct baa wani bata lokaci ba wanke mata kan akayi sanan aka mata kalaba
yan manya manya within one hour tagama tafito tashiga mota Adamu yatada motan zuwa gidan
Baffa, dan tsaki tayi ahankali kawai dan babu yanda zatayi ne dabataje ba bata wani don zuwa
gidan Baffa dudda tana bala’in don Baffa da duka yaran gidan, da Mum amman Ammi kwata
kwata jininsu bai hadu ba batasan mesaba, tana cikin yan tunane tunanen ta ta iso gidan,
Babban gida ne katoto, gidansu Babba ne but Gidan Baffan su is X2 nasu, mai gadi na ganinsu
yahau murmushi yace “oyoyooo Khairy” murmushi itama tayi Adamu na parking tabude tafito
dasauri mai gadon yazo wanda yake bayaro ba yace “munyi fushi wlh” dariya tayi tace “Baba
Bala wlh school yaboyeni” tai maganan tana ciro kudi a jaka tamikamai 5k cikin kudin da Baba
yabata karba yayi yace “nagode Yar albarka, Khairy mutuniyan kirki” murmushi tayi tajuya tana
kallon cikin gidan, dankara dankaran flat ne guda uku agidan haka ajere, na farko wanda
shizaka fara isa kafin kaje sauran yafi sauran biyun girma saina biyun dana ukun girmansu
daya, da sauri saurin ta gudu gudu take tafiya wuce flat na farkon tayi tayi na biyun bude kofa
tayi tana ihu. “Mummmmmm Mum” bin falon tayi da kallo daya hadu sai kamshin turaren wuta
yakeyi stairs tayi da gudu tai sama daidai wata mata dazata kai 45 kefitowa daga wani daki cikin
shiga na alfarma ta harari Khairy tace “ai nayi fushi wlh Khairy” wani murmushi Khairy tayi
batayi wata wata ba taje dagudu tafada jikin Mum tana juyida ita cikeda murna tace “Mum I am
sorry kinji, wlh school yahanani zuwa, Mum kinyi kyau iyyeee, ina Batool” turata Mum tayi tana
nishi tana dafa kujera dan jiri taji tanaji tace “jama’a na shiga uku yarinyar nan zata kassarani”
dariya Khairy tayi tajuya tai hanyar wani daki tace “nasan yarinyar nan tana bacci to baki isaba
nazo” binta da kallo Mom tayi ganin kullum kara girma Khairy keyi, tana bude dakin taga wata
yarinya da atleast zasu iya zuwa mate kokuma yarinyar tabama Khairy 1 zuwa 2yrs haka ta
tashi zaune sanye da kayan bacci tana hamma tana hararan Khairy, yarinyar kamansu daya da
Mom, wani tsalle Khairy tayi tafada kanta akan gadon yarinyar ta kwasa ihu tace “Mum kinga
Khairy ko ni dagani ai wlh fushi nake dake konai chatting naki up baki dubawa kuma baki
daukan calls” sakinta Khairy tayi tace “wlh Batool ni taba waya ma wahala yakemin balle
responding to calls or chat har gwarama kamin text message ina gani zan reply, but rabona ma
dana shiga watsapp harna manta wlh” baki Batool tabude zatai magana Mom ta turo kofan
dakin tashigo hakan yasa duk suka kalleta, Khairy takalla tace “kinje kin gaida Ammi Khairy”?
Dan zaro idanu Khairy tayi sanan ta girgiza mata kai ahankali, daure fuska Mum tayi babu
alamu kan fuskanta tace “Oya tashi kije ki gaidata, fast” tashi tayi kaman ruwan jikinta ya
shanye, jakanta ta ijiye kan gadon Batool sanan tawuce tafito Mum tace “duk idan kin shigo
gidan nan always ki shiga flat nata ki gaidata kafin kizo nan” gyadamata kai Khairy tayi sanan
tawuce ta sauka kasa kafin tabude kofa tafice.
Ajiyan zuciya tasauke tana kallon kofan sanan gently tasa hannu tabude kofan wani lafiyayyen
kamshin turare namata sallama ahanci, Babban falo