Showing 39001 words to 42000 words out of 108975 words
Chapter 14 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf
Batool kasan bata hayyacinta don ahankali tace “ina Mama”? Danne kukan
datakeji tayi zatai mata magana taji kukan yatokare mata wuya hawaye yazubamata dasauri
tashare daidai Mom tashigo hararanta Mom tayi tadauki tea tace “tashi kibani waje” da kyar
Mom tasamu ta kurbi tea sau biyu sanan takara kwanciya dagata Mom tayi takaita bayi alwala
tamata tasata a dadduma salla tajirata tayi Allah dai ya karba sanan tadagata, wani sabon
kayan bacci na Batool Mom ta dauka tasamata bayan tacire mata atampan jikinta spaghetti
hand ne dan kaman shimi yake iya guwiwanta ya tsaya mata pink color dan itama Batool nasan
komi pink, dawowa tayi kaman wata Yar baby roba akayan looking damn cute, kaita Gado Mom
tayi ta kwantar da ita tarufa mata bargo itama kaman abinda takeso kenan rufe idanu tayi
dasauri, Mom tazauna abakin gadon tana tofamata addu’a bude kofa akayi Baffa ne yashigo
yana sanye da jallabiya ganin Mom namata addu’a yasa ya tsaya yana kallonsu saida tagama
sanan yace “tai salla”? “Eh tayi” “what about abinci” Baffa yatambaya anatse, ahankali Mom
tace “tasha tea kadan ba laifi, shine na chanza mata kaya nakwantar da ita, karka damu she will
be fine nan bada jimawa ba” murmushi Baffa yayi yana kallon Mom ahankali yace “thank you
mace tagari” yakalli Batool dake bayanshi tai zuru zuru yace “dama kuka zaki dingayi kika
dameni nadawo da ita nan kisami Yar uwa” dasauri ta girgiza kai tace “Bazan karaba Abba”
murmushi yayi yashafa kanta yace “jeki kwanta” sanan yakalli Mom yace “jeki kwanta kihuta
wife muje narakaki” murmushi tayi ta tashi, itakuma Batool taje gefen Khairy ta kwanta itama
tashiga bargon Baffa yakashe musu wuta tareda jawo musu kofa sanan yaraka Mom zuwa
dakinta kafin yafito yasauka kasa yakashe wutan falo sanan yaja kofan yawuce side din Ammi.
Wuraren karfe biyun dare tabude idanunta tass jin muryan Mama nakiran sunanta.
“Ummulkhairy!” Hakan yasa tabi dakin da kallo ganin Mama tsaye jikin kofa tana sanye da
Atampa mai kyau tai lullubi yasa ta yaye bargon data rufa dashi tawani tashi tsaye tai wajen
kofan bakinta na motsi, gani tayi Mama tabi ta kofan tafice bude kofan tayi dasauri tafita ko’ina
duhu but she could see Mama natafiya akan stairs dan fararen kayane ajikinta, hanyar stairs din
tayi itama dasauri ganin Mama tai kofa tafice yasa itama tai kofan, hannu tasa tabude kofan
tafice batare data rufe kofan ba, tsakar gidansu kaman rana sabida ko’ina hasken lantarki
tashiga sauka daga stairs din gaban kofan tana mika hannu ganin Mama tamata nisa tai hanyar
gate murya chan dake cikeda nuna alamun bacci tace “Mama jirani!”
Zaune yake kan daya daga cikin wasu hadadun kujerun dayake nan barandan flat dinshi, irin
hadadun kujerun basket dinan da ake sawa a garden, dagashi sai wani gajeren wando
dayakaimai guiwa da farin singlet tass yadaura kafafunshi kan class table din wajen yana shan
shishi, tunda yadawo naija saiyau yasamu yakeshan shisha, yama fito waje ne yanasha sabida
kar dakinshi yakama kamshin gashi Abba nashigowa dakin dakannenshi duka, jin karan kofa an
bude flat din Mom dan daga flat din Mom sainashi at this hour of night yasa yasaki pipe din
shishan kasa dasauri yana mika hannu yana sauke shisha pot din daga kan table din at the
same time yana kallon kofan yaga wanda zai fito daga dakin.
2️⃣9️⃣
Free page
Ganin yarinyar nan da Mamanta tarasu dayaga antaho da ita gidansu dazu dazasu dawo dan
he can’t even remember her name yasa yadan ware idanu yana binta da kallo yanda take
sauka daga kan staircase din gaban flat din Mom, babu takalmi akafanta babu dan kwali akanta
kalaban kanta na lilo atsakiyan bayanta, daga ita saidan rigan bacci pink mai hannun taliya
daya tsaya a guiwanta, ganin yanda take tafiya one one as if she’s trying to hold something
yasa yadanja karamin tsaki yace “God am I a baby sitter now” jin tace Mama kijirani tai hanyar
gate yasa yadanja tsaki yatashi dasauri ganin tai hanyar gate, dawani irin sauri yasha gabanta
batare dayace kalaba yay folding hannunshi a chest dan ihu yaso yamata but to his biggest
suprise gani yayi gabaki daya idanunta are close is she sleeping walking or what? Yatambayi
kanshi daidai ta iso gabanshi babu any tazara tsakanin shi da ita tsayawa yayi yana kallonta
just to feed his curiosity yaga mezatayi, wani kalan heart melting murmushi tasaki daya bala’in
lobar da dimples dinta all the 2 yabayyana set na white teeth dinta, pink lips dinta nawani kalan
shinning kafin ahankali takai duka hannayenta biyun tadaura kan hannunshi daya rungume a
kirji takama cikin muryanta kaman na baby tace “Mama kinjirani, Mama I miss u, karki kara
tafiya ki barni kinji Mama” tai maganan tana warware hannunshi daya rungume a kirji tasaukar
da hannun kasa sanan gently takara tako one more step ta shige cikin jikinshi tai wrapping two
hands nata around his back tawani kalan kankameshi tana sauke ijiyan zuciya dahar cikin brain
dinshi saida yaji ahankali tace “Mama bacci” tunda yake in his life what he just felt now baitaba
jinshi ba, sandarewa yayi hannunshi sauke akasan batare daya iya komiba yanajin saukan
ijiyan zuciyanta akirjinshi yana kallon tsakiyan kanta da yanda gashinta ke lilo sabida iskan dake
kadawa da yanda heart dinta ke biting each beat yana jinshi anashi heart din, yakai kusan 2min
ahaka she’s still holding him tight batare data kara magana ba, ahankali yadaga hannayenshi
dayaji sunyi sanyi kaman basa functioning kuma yakai saitin hannunta abayanshi zai kwance
yanda tadaure hannun abayanshi, kankame hannun tasakeyi saikuma yaji tasaki kuka dabaida
kara ko kadan. “Baran sakeki ba Mama, ina sakinki cemin zasuyi kin mutu, Mama nakusan
haukacewa da suka fadamin haka ni nasan baki mutu ba, ni ajikinki zanyi bacci anan dakinki
zanyi bacci, I will not allow u to leave me ever again and go” yanda hawayenta kebin kirjinshi
yasa yaji zuciyanshi ta tsinke shifa baicika tausayin mutane ba but for the first time jiyayi
yarinyar nan tabashi tausayi sosai ahankali yakomar da hannunshi batare daya rabata dashi ba,
yadan dade ahaka sanan gently yadan duka tareda ita yasa hannayenshi the two yadauketa
ajikinshi kankameshi tasake yi gamgan tana kara gyara zaman kanta akirjinshi yana kallon
fuskanta saida tagama sanan ahankali kaman yadauki Kwai yafara tafiya har zuwa flat din
Mom, shiga ciki yayi daman kofan abude yake yay stairs da ita yana mamakin yanda batada
nauyi kaman yadauki paper, dakin Batool dayagani a bude ya tabbatar mai daganan tafito,
shiga cikin dakin yayi dudda ko’ina da duhu but he could see sabida hasken window dake nuno
compound nasu gently ya tsugunnawa kaman yanda ake kwantar da baby haka ya kwantar da
ita kan gadon zai zame hannunshi yaji ta chapke hannunshi da sauri tana sheshekan kuka
kaman yanda jarirai kema mamansu takai hannunshi kirjinta ta kankame sosai kaman idan
tasaki hannunshi something will happen to her, wani dauuuu yaji a brain dinshi kaman an watsa
acid a alkaline environment, dan gabaki daya a boobs nata ta kankame hannun nashi, he could
basically feel sign na her sleeping nippy, karya fizge hannun tahau kuka ne this is middle of
night a ganshi adakin nan saisa yakeyi ahankali, gently ya tsugunna jikin gado, wani kalan zufa
yaji yana ketomai shi kanshi baisan mesa ba this is not the first time yake feeling boobs na
mace why is hers different, why so much effect, ahankali yakai dayan hannunshi yadaura akan
fuskanta yana shafa kumatunta he don’t even know what to do samin kanshi yayi da hura mata
iskan bakinshi a fuskan wani irin ijiyan zuciya ta sauke tasaki hannun nashi kadan bakaman
yanda ta kankame hannun a kirjinta da farko ba, ganin haka yasa yacigaba da hura mata iskan
yana shafa kumatun nata dayaji yamafi na jariri taushi sanan gently yashiga janye hannunshi
kafin yay nasaran janye hannun duka sanan ya dauke hannun kan fuskan nata dawani irin sauri
yatashi yafice yaja kofan nasu ahankali sanan yasauka kasa yafice waje abinshi.
Wuraren 6 tafarka daga bacci daga Mom har Baffa daya shigo dubasu da asuba saida sukaji
dadi ganin yanda tai bacci sosai yau dan this last few days dudda ana mata allura bata tabakai
war haka bata tashi ba 4 ta tashi ko 3 nadare ma.
Kalle kallen data shigayi yasa Mom data shigo dubata tace “Khairy ya akayi me kike nema? Kin
tashi” Dasauri zuciyanta na bugawa fast fast tace “Mama ina take?” Shiru Mom tayi tana
kallonta hakan yasa tafashe dawani irin kuka tace “wlh ba karya nake ba Mom naga Mama
adakin nan takwana tareda ni I was even holding hannunta sabida idan kuka tashi kugani, kuma
tace bazata kara tafiya tabarni ba” hannu Mom tasa tadafa cinyanta ahankali tace “Khairy idan
aka rasu an rasu kenan mutum baya dawowa, sabida rasuwan Mama na ranki saisa kike
mafarke mafarke, Mama tarasu, you had a dream about her, tashi kije ki dauro alwala kiyi salla”
tashi tayi ahankali tana goge hawayen dasuke zubomata tai bayi, fitowa tayi daure da alwala tai
salla, da kyar tasha kunun da Mom tabata shima kadan sanan Mom tabarta da su Batool da
Zara’u daketa musu surutu Khairy na kallonsu kuri kaman tazare itakuma Mom ta sauka kasa.
Knocking akayi tareda shigowa dakin, Zayn ne yana sanye da kananun kaya yay kyau yana
zuba wani uban kamshi, ganinshi yasa Mom tace “Zayn shigo mana zoka zauna” karasowa yayi
cikin falon cikeda girmamawa yace “Mom zan tafi” dasauri Mom tace “harzaka koma” ahankali
yace “eh something come up dole nakoma dama 1week naso nayi amman bazai yuba”
murmushi Mum tayi tace “Allah sarki to Allah kiyaye hanya, Aida nasan yau zaka tafi dana maka
su dambun nama wlh yanzu sai yaushe kenan” dan shiru yayi yana tunani sanan yace “let’s just
say 2month intotal nagama komi” ahankali Mom tace “Alhamdulilah Alhamdulillah komi yay
farko zaiyi karshe Allah bada sa’a Allah ya kiyaye hanya” Ameen yace yana tashi har waje Mom
tarakashi Baffa dasu Hafiz suka daukeshi a mota har zuwa airpDort.
3️⃣0️⃣
This book is 1k pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank. Saiki turomin evidence of
payment ta watsapp number na 07012181461.
LAST FREE PAGE
Bayan 3 weeks!
Yau 3 weeks kenan chip chip da rasuwan Mama, an dage sosai da addu’a akanta she’s very
very much better yanzu, tadena koke koken nan she’s doing everything dakanta saidai she
hardly speak, kome aka cemata saidai ta gyadakai tariga ta yarda Mama tarasu and babu
abinda zata iyayi dazai dawo da ita, har yau bata iyacin abinci at all, saidai kadan kadan kuma
shima liquid, once in a while Besty nazuwa har gidan Baffa dubata dan su Ya Manaf nema suka
kawota gidan tasani, sanan Baba yabata number shi yanzu ma haka ance gobe zata koma
school danta kira Baba next week zasu fara first semester 400 level exam sauran ta one
semester tagama school hakan yasa aketa shiryamata har sababbin dinki Baffa yamata
hadadun gaske Mom ma haka, just to cheer her up amman ina bin kowa take da ido dakuma
kalman godiya shikenan.
Yau tun safe Mom dakanta ta shigo dakin ganinta zaune kan dadduma yasa tace “laaaa yar nan
Oya maza tashi ki shirya yau kinada lectures 8 kika zauna yanzu har 7 yi maza tashi ki shiga
bayi” batai musu ba tashi tayi tai bayi wanka tayi tafito, gani tayi Mom tamata arranging kayan
dazata saka akan gado, wasu Riga da skirt ne na atampa cikin sababbin da aka dinka mata
orange color ne atampa yanada flowers yan kanana brown, sai brown gyale tahada mata jakan
makarantan ta da book sai wayanta da tuntuni aka kawomata gidan bata taba tabawa ba shima
Mom dukta saka mata, shiryawa tayi tsaf, Mom tashigo dakin dauke da tea da chips tana kallon
yanda kayan suka mata kyau dudda tarame sosai takalli kitson kanta tace “satin nan zamu
kwance kan nan ayi wani kitso Khairy” takarasa ta ijiye abincin akan carpet sanan tadauki dan
kwalin kayan tamata dauri mai kyau kafin tadauki tea tabata, karba tayi da kyar ta iya shan dan
kadan sanan ta ijiye, ita kanta Mom batama iya tursasata taci abinci tashi tayi tadauki jakan a
hannu da gyalen ahankali tace “natafi” binta Mom tayi tace “dan Allah Khairy kiyi karatu da kyau
kinga jarabawa zaku fara next week karki fadi” Baffa suka gani afalo shima wa’azi yamata
sanan yakaita har mota saida tashiga sanan yama Adamu alamun yatada motan yatada suka
tafi, titi kawai takebi da kallo, jitayi hawaye ya gangaro mata dasauri ta share, she use to kullum
saitaga Mama take tafiya school, school sukakai Adamu yay parking ganin taki tashi yasa
Adamu yace “tashi kije class Khairy” kukan datake rikewa taji yazo mata fashewa da kuka tayi
sosai tasa gyalenta akan fuska tana kuka shiru Adamu yayi takai kusan 20min sanan ta share
fuskan nata da gyalen idanunta sunyi jazur tabude kofa tafita tana tafiya kaman iska ya kadata
tafadi tarame babu abinda yarage ajikinta sai nono da hips, su kadai ne basu rame ba but
wuyanta duk kashi idanunta sun fada ciki sosai, ahankali take tafiya yan makaranta su natareta
suna mata gaisuwa gyadamusu kai kawai take tana wucewa dasauri dan bataso taita kuka ta
tarama kanta mutane ahaka hartakai aji da lecturer ma aciki, baa hanata shiga ba hakan yasa
tashiga taje tasami chan baya karshe chan tazauna ko abu daya bata ganewa ahaka aka gama
lectures din lecturer tafita by 10, basuda wani lectures kuma sai 2, zagayeta yan ajin sukayi ana
mata gaisuwa gyadamusu kai take tana danne zuciyanta, ganin yanda takeyi yasa class
governor dinsu yace “dan Allah kubar Khairy tahuta let’s go guys” fiffita daga ajin suka shiga yi,
su Amal sukace “tashi muje cafe Khairy” ahankali tace “kuje ina zuwa” dan jim sukayi suna
kallonta babu maison yatakurata hakan yasa duk suka tafi ajin aka watse ita kadai tarage aciki
hakan yasa takifa kanta akan desk tahau kuka ita kanta she wants to stop the cry amman bata
iyawa tadade ahaka ita kadai a class kaman aljana kanta akife akan table, kaman daga sama
taji ance “Ummulkhair!!” Awani irin hankali take dago kanta daga table kafin tadaura jajayen
rinannun idanunta kan Aliyu dake tsaye agaban ajin yana sanye da uniform na yan sanda yana
kallonta, yarame shima idanunshi sunyi wani kala yana mata kallonda only heart dinshi zai iya
sanar da mai kallon ke nufi, jitayi duniyan ya tsayamata chak duk wani bakin ciki emotions,
tausayin kanta da sauransu sun taso mata sun tsayamata awuya, jikinta harwani rawa yake
ganinshi dan she can’t believe shine, wani irin tashi tsaye tayi tana kallonshi kaman yanda yake
kallonta kallon dayana mata zuciyanta nafassaramata dawani irin gudu gyalenta na faduwa
akasa tai wajenshi kaman dama shitake jira batai wata wata ba kawai tawani kalan fada jikinshi
sai kuka sosai as if she ne dama asalin wanda takeso tama kukan, ahankali ya lumshe
idanunshi yana feeling kukan datake in every single bone of his flesh, hannayenshi yadaga
gently yay wrapping nasu around her back kafin yakai bakinshi saitin kunenta murya chan kasa
yace “I am here for you Pickle, I am here” sake kankameshi tayi sosai cikin kuka tace “Ya Aliyu
Mama…..” murya chan kasa dake nuna he’s with her, he’s feeling what she’s feeling yace “I
know Pickle” takai almost 3min tana kuka ajikinshi sanan ahankali yacirota daga jikinshi yana
kallon yanda take kuka hannunta yakama zuwa first kujeran dake ajin zaunar da ita yayi sanan
ya tsugunna agabanta still yana kallonta, jikinta ko’ina rawa yake na kuka, hannunshi yasa a
aljihu yaciro clean handkerchief dinshi yakai kan fuskanta yafara share mata hawayen murya
chan kasa yace “shiiiiiii” shiru tayi tana kallonshi still, tass yashare mata fuskan harda hancin
sanan yamike tsaye yay inda take zaune a ajin da, tsugunnawa yayi yadauki gyalenta daya fadi
a tsakar class din sanan yakarasa yadauki handbag dinta sanan yadawo har zuwa inda take a
zaune, gyalenta ya yafa mata aka yasauka har kan kirjinta sanan yamika mata hannunshi yace
“let’s go” kallon fuskanshi tayi kafin ahankali tasa soft hannunta cikin nashi yariketa gam sanan
suka fito daga class din suna tafiya ahankali sai kallonsu ake amman ko ajikinshi har zuwa
parking space, gaban motan yabude mata zama tayi tana kallonshi da jajayen idanunta sanan
ya maida kofan yarufe kafin yazagayo yazauna wajen mazaunin direba yarufe motan yatada
motan yafice daga school din da ita, sunyi tafiya mai nisa sannan taga ya tsaya gaban wani
eatry ya shiga batasan meya siyoba yadai bude bayan motan ya ijiye komi sanan yadawo
yatada motan, wani waje yakaita ita kanta duk zamanta a Abuja batasan wajen ba, duwatsu ne
masu kyau ga kamshin ruwa awajen da alamun akwai water fall ciki, parking yayi sanan
yakalleta yace “I am coming” fitowa yayi yabude baya yadauki ledan daya siyo musu dawani
babban dadduman dayake dashi mai taushi sanan yashiga wajen baiwani dade ba yadawo,
bude inda take yayi yasake saka hannu yadauki jakanta sanan yamika mata hannu ahankali
tasaka nata ciki, saukowa tayi yamaida motan yarufe sanan suka shiga wajen, cikin dutse ne
kaman cave sanan ga ruwa atsakiyan wajen yana gangarowa daga dutse babu kowa wajen,
wajen is so serene and peaceful bakajin karan komi saina tauntaye dana karan ruwan dakuma
kamshin ruwan dutse dakakeji.
Zaunar da ita yayi kan dadduman sanan shima yazauna yana facing nata, ledan yabude yaciro
take away na biryani rice da rosted lamb sai ruwa mai sanyi daya siya yabude, ahankali yasa
spoon din aciki sanan yadebo abincin a spoon yakai bakinta yana kallonta jitayi zuciyanta
yawani tsinke wani sabon kuka yazo mata ahankali tashiga reramai kukan, jaaa idanunshi yayi
sanan gently ya girgiza mata kai bude baki tayi yasamata abincin taci saiyau tasan ashe tanajin
yunwa, kadan tarage abincin all through harta koshi kuka take, yanabata abaki tanaci tanamai
kuka sanan yadauki ruwa yabata shima sha tayi sanan ya ijiye.
Ijiye komi gefe yayi sanan