Showing 21001 words to 24000 words out of 108975 words
Chapter 8 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf
har jibi Ice cream dai
saika kaini nasaiwa jikoki na ja’irin yaro kawai” ko kala baice mata ba da taimakonshi ya daurata
akan keken sanan yamaida kofan bayan yarufe da karfi tace “kama balla motan baban karfi,
ubanka zai sayamin wata Alhamdulilah Allah yamai arziki rufin asiri danasha takaici” cikeda
masifa yace “wlh Goggo in baki shiru ba anan zan barki na shiga ciki nasayo” wani kalan
murmushi tayi tamaka bakinta tace “yo ai nadauka gaba kake dani to muje nadena” dan
murmushi kadan kawai yayi sanan yashiga turata zuwa gaban entrace din dakenan divided into
3, staircase ne gefe da gefe sai tsakiya a bit sloppy floor dazaka haura ka shiga cikin shagon,
daidai lokacin security na budewa Khairy kofa tana fitowa rikeda paper bag na ice cream din
dakuma handbag dinta rataye a shoulder dinta, saiga wasu yara su biyu maza dabazasu wuce
8yrs ba suna guje guje kowanne rikeda ice cream dinshi dayan kawai ya mamayi brother shi ya
fizge ice cream din hakan yasa brother yay ihu yabi dan uwanshi da gudu Khairy dabude mata
kofa kenan tasa kafa tafito zata fara sauka daga staircase din kawai yaran suka fito suka mugun
bangajeta dayasa ita kanta tasaki wani irin ihu kafanta ya gicce abunku da tiles kawai ta kifo
zata fadi da mugun sauri Gwaggo tace “Subhanallahi” dawani irin sauri yasaki wheelchair
Gwaggo daidai kanta zai daki dakaIUlin stairs din…
ALKAWARIN ZUCIYA
✍ M SHAKUR
Dan magana da M shakur
wa.me/+2347012181461
1️⃣5️⃣
Yasa hannunshi daya awajen kanta ya daki tafin hannunshi bayan hannunshi yadaki stairs din
sanan yakai dayan hannunshi yakama waist dinta yajuyo da ita hakan yasa ta mirgino side
tafado jikinshi.
Daga yaran, security, iyayensu dasuka biyosu da sauri, Gwoggo dakekan wheelchair duk
sandarewa sukai danba karamin faduwa zatayi ba inda Allah bai kiyaye ba, yanda yakeji yanda
take nishi a hannunshi yasa ahankali yazare hannunshi daga waist dinta gently yakai hannun
kan fuskanta yadago fuskanta yana kallon face dinta yanda ta kankame idanunta gam gam
cikeda tsoro pink lips dinta nawani irin shaking dayasa dimples dinta na lotsawa tana nishi sama
sama dayake jinshi akan hannunshi, murya chan kasan makoshi while looking into her face
yace “are you okay”? Muryan dataji yadaki dodon kunnenta yasa kadan kadan tashiga bude
idanunta danta gasgata abinda taji kafin tabude su tass tadaura white fararen idanun nan nata
manya manya dasukenan kaman an wanke da madara tadaura su akan fuskanshi, jitayi
numfashinta ya makale somewhere in her throat ganin fuskanta dab da nashi yana kallonta as if
he’s trying to check something, yatsanshi yakai saitin nose nata jin bata numfashi kawai
takafeshi da manyan white eyes nata yasa dasauri yakalli security man din yanunamai jakanta
dake kasa chan yace “give me her bag” dasauri yakawo jakanta yamikamai juye jakan yayi kasa
inhaler ta yafado dasauri ya dauka yacire marfin yakai bakinta ahankali yace “breathe in
Ummulkhair!” Wani irin bugawa zuciyanta yayi jin yanda yakira sunanta kaman sunanta
dayakira ne yay reviving nata batasan lokacin datawani saki numfashinta data rikeshi
amakogoronta ba yafito mai kara sanan taja inhaler, zagayesu mutane sukayi barinma parent
din yaran da jikinsu yay sanyi ganin Yarinyar da yaranta suka ture is even asmatic, ganin yanda
mutane suka cika kansu duk ana kallonta yasa ahankali takai hannunta batare data kalle
fuskanshi ba tana kokarin karban inhaler daya rikemata abaki, ganin haka yasa gently yasakin
mata ahankali yaran dasuke tsaye sukace “Anty sorry” dan murmushi tayi tana cire inhaler daga
bakinta duk dasauri tana kokarin tashi tsaye, tsugunnawa Maman yaran tayi tace “rest a bit
please” tai maganan tana maida mata kayan jakanta back aciki tareda daukan mata jakan ice
cream dinta da sauri ta mike tsaye tana karban abubuwan ta daga hannun matan tace “I am
okay thank u” Gwaggo dake kallonta tace “sannu kinji inane gidanku mukaiki nida jikana”
dasauri tace “direbana na nan nagode Ma” sanan tawuce da sauri hartana tuntube tai wajen
motansu da Adamu ya kwantar da kujera yanata hira awaya abinshi batare dayamasan meke
faruwaba, saida yaga tabude motan ta shiga sanan yakoma wajen Gwaggo yatura keken sukai
ciki tace “ohh yara da rashin wayau Hydar, inda badadan kaiba da sunja Yar yarinyar nan tafasa
goshi wlh, itama yarinyar uwa batacin abinci yoo nakema wanan maganan haka rainon indomie
ce daga ganinta, ace daga yan yara sun bangaje budurwan yarinya haka kawai sai faduwa uwa
lagwani, ace yara suci tuwo suki duk irinku ne ai gashinan kaga yara sun taso basu da karfi ko
kadan, kai Allah dai ya wadaran naka subaci, Allah dai yasa kai aure ka haihu, wlh tun yaranka
na wata biyu zan fara basu lafiyayyen tuwo da miyan kuka dataji daddawa” hararanta yayi
baima cemata komiba ya sassayi ice cream din sanan suka fito tace “minene Wanan abin
danaga kanata matsamata abaki” kin kulata yayi yasa ta amota ya maidata gida sanan yafito
yatafi aiki.
Har suka shigo anguwan su badaidai takeba yau sau uku kenan tana ganin mutumin nan, saida
suka shigo gida tukunna sanan taji wani kalan dadi, parking sukayi sanan tafito dasauri tana
kwaso kayayyakin ta tana kwalama Mama kira. “Mamaaaa! Mama nadawo” daga Mama, Baba,
Baffa da yayyinta da Hafiz duk suna zaune a falo dan basu dade da dawowa daga asibiti ba
babu wanda yama iya wani kwakkwaran motsi, ita tsabagen murna batama lura da Karin mota
kan tagidansu ba tai hanyar flat dinsu tana shouting Mama. “Mama nayomiki tsaraba yau
nasayo miki ice cream kuma best flavor naki mint ban miki adding any thing ba ayanda kike
sonshi plane” tai maganan tana bude kofan falo tana shiga tana kiran Mama. “Maaaam……”
kasa karasa kiran Mama tayi ganin mutane a falon ga Mama zaune kusada Baba tana kallonta
tana murmushi, hararanta Hafiz yayi yayi yace “inda ace ke kadai keda Mama aduniyan nan
Khairy da munsha takaici” cikeda wasa Baffa yace “kagamin d’a kai kanama namiji ka more
taka Maman balle ita mace kuma auta, ina tsaraban dakika kawoma Maman bazaki zo kibata
ba kin wani tsaya awajen” akunyace takaraso cikin dakin wani irin rungume Mama tayi tana
murmushi akunyace ganin duk ana kallonta yasa tadaurama Mama paper bag na ice cream din
akan jikinta akunyace ta sauko dagakan jikinta tace “Baffa ina wuni” murmushi yayi yace “diyar
Mamanta ya makaranta” ahankali tace “fine” sanan takalli Hafiz tace “Ya Hafiz ina yini ya baby
kuma, dan Allah ya Hafiz kasa mata sunana” dasauri yazaro idanu yace “waaaa niii rufamin
asiri Khairy sokike y’ata tazama fitinanna irinki” dariya aka hauyi adakin ahankali Khairy tace
“Baffa kaga Ya Hafiz ko” kafin Baffa yay magana Baba yace “karya yayi to Khairiya” turo baki
tayi kaman zatai kuka Baffa yace “sharesu Yar albarka, sun lashe basusan baiwan dake tattare
da sunan ki bane saisa suke magana ahaka” wani kalan murmushi tayi tace “yauwa Baffa”
sanan tajuyo takalli Mama tace “Mama kin sha maganin kan yadena miki ciwo muji” takai
hannunta tana taba goshin Mama with so much care, gyadamata kai Mama tayi tace “yadena,
cikani maza tashi kai ice cream din kisa a fridge kije kiyi wanka kiyi salla idan bakiyi a school ba
saiki sauko kici abinshi” gyadama Mama kai tayi sanan ta tashi tana kallon yayyinta dataga
sunyi wani iri harzata wuce tace “Ya Manaf kungaji ne haka naga kunyi wani iri, Ya Maheer
idanunka sunyi ja kaman kayi kuka” hararanta yayi hakan yasa ta murgudamai baki tawuce
abinta sama itama, dayake yana takanshi dayaji ciwon Mama yatashi yau baima biyemata ba.
1️⃣6️⃣
Free page
enjoy
Kofan dakinta tabude ahankali ta shiga tanabin dakin da kallo yanda ko’ina tsaf tsaf an
gyaramata sai kamshi dakin yake, shiga ciki tayi sanan tamaida kofan tarufe kafin awani irin
gajiye cikeda sanyin jiki tasaki handbag dinta akasan dakin tafada kan gadon batare data cire
takalmin kafanta ba tawani kalan kankame jikinta tanajin wani irin sanyi na shiga jikinta, she
don’t even know why amman hakanan fuskan police man dinan take gani a idanunta muryan shi
namata yawo a kunne da kanta gabaki daya yana kiran sunanta Ummulkhair breathe in, runtse
idanunta tayi gam gam tana feeling yanda bones nata ke cringing to each other tana ganin
fuskanshi namata yawo a idanu kafin idanunta suna hasko lips dinshi wani kalan ihu tayi.
“Ahhhh stop!” dasauri ta tashi zaune tana wurwurga kafafunta cikeda damuwa tace “Stopppp
noooo what’s wrong with me”? Wani irin zabura tayi ta tashi tsaye kawai tawuce dasauri tafada
bathroom, wanka tayo sanan tafito daure da towel tana tunanin yaushe Mama zatasa amata
Kitso dan gashin ya isheta daga tsifemata jiya, wani simple dogon Riga tasaka sanan tasaka
hijabi tai salla tana idarwa tafito falo tawuce ganin duk basu tasan sun tafi masallaci sallan
magrib, dinning tawuce zama tayi tana bubbude kula rice tazuba kadan sanan tasa nama
tafaraci saida tacinye sanan takai plate din kitchen kafin tafito ahankali tai stairs, knocking dakin
Mama tayi sanan tabude kofan ganin Mama akan gado ta lullube da bargo yasa tashigo da
sauri tace “Mama menene” wani kalan kallo Mama tamata tace “bacci zanyi nagaji” hawa gadon
tayi tana kallon fuskan Mama tace “Mama kibari ayi isha’i tukunna nima bacci nakeji”
gyadamata kai Mama tayi tana kallon gashinta tace “weekend zakiyi kitso tunda ke kin dawo
yarinya daga tsife miki kai kanki yadawo kaman na mahaukaciya” gyadama Mama kai tayi tana
hamma, ganin haka yasa Mama tace “Oya tashi kije kiyi sallan to gashinan ana kira saiki
kwanta tunda kin gaji, kinmasha ice cream din” girgizakai tayi agajiye tace “gobe zan sha Mama
nagaji, gud night world best” night my baby girl, Mama tai maganan tana binta da kallo wucewa
tayi tafice daga dakin tana salla ta kallabi tahau gado sai bacci.
Da asuba tana tashi salla tafarayi sanan takoma bacci dan yau batada lectures sai 10 and she
wants to sleep sosai cus kanta yay clearing tadena all this banzayen tunanin nan datakeyi.
Karan wayanta yatadata by 9, da kyar ta iya bude idanunta ta kalli wayan rabon data danna
wayanta hartama manta one thing dabai dameta aduniya kenan ba waya, she’s not just a phone
person, itadai barta da physical surutu, yawo rawa haaba anan ake samin Khairy, hannunta
tamika da kyar tadauko wayan ganin Besty yasa taji duk wani kalan bacci datakeji yafice daga
idanunta dasauri tai picking call din tace “Iyye su Besty Amarya ai nadauka kin manta dani yar
rainin hankali saisa na shareki banma nemekiba” kuka Besty tasaki awaya dayasa dasauri ta
tashi zaune adan tsorace tace “ke menene Besty, what happen? Kinasa inajin tsoro why are u
crying?” Cikin wani kalan muryan ban tausayi Besty tace “Khairy wlh nafasa auren mutumin nan
kasheni zaiyi tun ranan da aka kawoni abu daya ake har yau nagaji” dan ware idanu Khairy tayi
tanajin maganan wani banbaram itadai barta da rashin ji but duk wani harka na maganan banza
da Iskanci bata aciki, adan kunyace cikedajin nauyin magannan tace “to ba ance ana sabawa
ba” tai dan shiru saikuma ta turo baki tace “idan yaki kihadashi da Maman ku” wani gajeren
tsaki Besty taja cikeda masifa kaman tabugama Khairy dundu tace “I don’t even know why I
called u you are crazy Khairy, da zancen party ake da yanzu kingama tsara komi, lemme call
Amal” tana maganan ta katse wayan, hararan wayan Khairy tayi ta ijiye saikuma chan kaman ta
tuna wani abu wayan ta dauka dailing number Besty tayi back ringing daya tadaga, ahankali
tace “sorry Besty kinji I seriously don’t know what to tell u or how to advice u” cikin muryan
damuwa Besty tace “wai Khairy when will you learn all this stuff eh, u are just hella wired Umma,
u are just leaving life kaman bamace ba gashi duk munata aure Khairy keko saurayi bakida shi
sai wanan Wizzy dake binki” hararanta Khairy tayi tace “nacemiki kidena hadani da wanan
yaron” dan dariya Besty tayi kaman ba itane mai kuka yanzun nan ba tace “naji nadena, yanzu
dai kinyi wani saurayin”? Dan shiru tayi kaman mai tunani harta bude baki zatai magana
saikuma tai shiru hakan yasa Besty tace “ohhh wowww, Khairy this is something new, tell me
who is he? Dan tunda nake dake duk aka miki tambayan saurayi direct kike cema mutum baki
dashi wanan dakika kasa magana tell me wayeshi” dan murmushi tayi tayi dan juyi akan gado
tana dan lumshe ido saikuma ahankali tace “wlh Besty banda kowa kawaidai wani Police man
ne naketa haduwa dashi this days amman ko magana bamayi kawai dai he always saves me
from trouble ne I don’t know if that means anything amma dai ba soyayya muke ba ko magana
ma bamayi” ahankali akuma natse Besty tace “ohh my Goddd! Khairy kinji yanda harwani
natsuwa kikayi kina bani labarin police man dinnan kuwa, My world Khairy you love me! Wlh….”
Dan yatsine fuska Khairy tayi dasauri tace “stop it! Mutumin dabanma sanshi ba, yaushe zaki
dawo school nidai” dariya Besty tayi sosai tace “tunda u are avoiding maganan ai ba matsala,
this weekend zai dawo dani but every weekend zai dinga zuwa” gyadamata kai Khairy tayi tace
“sai kinzo bye” tai maganan tana katse wayan da sauri dan tasan Besty bazata taba hakura da
topic dinan ba, ijiye wayan tayi ahankali sanan ta mirgina zuwa dayan gefen gadon tana tunani.
Ajiyan zuciya tasauke sanan ta tashi tasauka daga kan gadon zatai bathroom wayanta yashiga
kuka cikeda masifa tadawo tace “mekuma kike sake kirana eh” wayan tadauka ganin Glory
yasa tai picking wayan takai kunne kafinma tai magana Glory tace “hello fine girl, melanin
goddest, pop skin with those sexy milky eyes” dan dariya tayi, Glory is her friend masters ita
take a school nasu ta girmeta far far amman tana bala’in son kawance da Khairy, dan murmushi
Khairy tayi tace “Hey! Where have u been i haven’t seen u in school this days” dan dariya tayi
tace “I travel naje PH chan gida, Khairy u don’t know I am angry with u ba” dasauri Khairy tace
“what happen? Why” kaman zatai kuka tace “today is my birthday Khairy” Adan kunyace Khairy
tace “ohhh Glory, sorryy happy birthday darling” dasauri Glory tace “come to my party and wish
me there, zamuyi a jabi lake mall a cikin jirgin ruwa, dress code is red 4pm sharp” wani kalan
juya idanu Khairy tayi tace “ohh okay then bye see u later” ta katse wayan sanan tawuce bayi
da gudu wanka tayi agurguje sanan tafito cikin wata doguwan rigan atampa ta shirya tafito tana
tunanin yanda zatai planning zuwa party zata dawo gida by 2 wuraren 5 saita tafi tadawo 6.
Tea kawai tasha sanan tawuce school dan tayCi latti sosai.
1️⃣7️⃣
Free page
Ahankali yake tuki ganin ya shigo cikin estate dinsu, saida yakarasa gaban wani dankareren
gate sanan ya danna horn, budemai gate da akayi yasa yaja motan zuwa cikin gidan dakeda
bala’in kyau kuma babban gaske ga flowers dasuka karama gidan kyau sosai, parking yayi
abangaren parking sanan yakashe motan yana kallon cikin gidan dababu kowa sai gardener
dinsu daketa yayyanke flowers yana gyara su, yakai kusan 1min cikakke zaune a motan yay
shiru sanan ahankali yabude kofar motan yafito yamaida kofan yarufe sanan yafara tafiya dai
dai yawuce zuwa babban flat dakenan shine first flat a gidan, bude kofa yayi ahankali tareda
sallama chan ciki sanan yashiga babban falon da babu kowa ciki, falon ya bala’in hadu yaji
furnitures, saikuma dan kara dayakeji a kitchen da alamu mai aikice ke wanke wanke, juyawa
yayi zai fice kaman daga sama yaji ankirashi. “Aliyu” dan juyoda kanshi yayi ya waigo, wata
matace doguwa mai jiki fara kal da ita taci gayu da sarkan gwal a wuyanta wacce bazata wuce
40 ba tana sanye da lace ja da baki ke saukowa daga benen, kallo daya yamata yadauke kai
yace “barka da rana Mami” dan murmushi matan tayi sanan takalli agogo bangon falon ganin is
just 11 yasa tace “Lafiya kadawo gida ware haka Aliyu”? Batare daya kalletaba ahankali yace
“lpy lau Mami” gyadamai kai tayi tana kallonshi still tace “tom shikenan, mezakaci a aiko maka
dashi”? Batare daya kalleta ba har lokacin yajuya yace “zanci abinci wajen Gwaggo” yana
maganan yajuya yafice tareda rufo kofan binshi da kallo tayi ta jikin window falon har saida yay
side din Kaka yabace mata daga gani sanan tasami kujera ta zauna tanadan karkada kafa
tunda take bata taba ganin wanda uniform na police kemai kyau kaman Aliyu ba, haryau tarasa
maisa Aliyu yawani zama police ba yaron dayay lafiyayyen karatu yakuma gama da good result,
kwanciya ahankali tayi tana kwalama Yar aikinta kira dan tazo ta danne mata kafa.
Bangaren Gwaggo shima yanada girma sosai, da sallaman nan nashi chan kasan makoshi
yadaga labule ya shiga dakin ko kadan Gwaggo dake zaune tana kada lagwani bataji alamun
shigowan mutum ba kawai karan kwas kwas na takalmin dake kafanshi taji akan tile din dakinta
afirgice takalleshi tana “Innailaihi wa innailaihi raji’un, waikai Aliyu wani irin murdadden yaro ne
eh, bama wanan ba dan ubanka koma ka cire shegen takalmin nan naka dazaka shigomin
dashi falo ina salla a ko’ina afalona dan tsarki ne dashi wlh” ko kallonta baiyiba saima hawa kan
dogon kujeran ta dayayi yay kwanciya abinshi yanadan lumshe idanu, ijiye komi Gwaggo tayi
tamike tana gyara zani tazo kanshi zatahau mai bala’in idanunshi daya lumshe tabi da kallo
ganin sundanyi ja yasa tace “kai yaron nan zazzabi kake yine”? Dan bude idanunshi kadan yayi
yakalleta dauke kanshi yayi yaki kulata, dasauri ta kalli agogo ganin ko shabiyu batayiba yaron
da dazun nan dasafe yafita aiki yasa tace “wlh bakada lafiya Hydar zo meke damunka”? takai
hannunta da duk audugan lagwani yake kai zata tabamai fuska dasauri yatashi zaune yace
“karki tabani da hannun dattin nan Gwaggo” dan sassauta murya tayi kaman ba ita kemai ihu ba
cikeda damuwa