Showing 51001 words to 54000 words out of 108975 words
Chapter 18 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf
sanan tafito tashiga mota
suka tafi wuraren 5:15 sukakai wajen, tana rikeda abin tashiga wajen bayan tanuna IV dinta
daya turamata awaya, wajen yacika makil baya tasamu tazauna tana kallon stage lokacin ana
decorating Aliyu ana karamai stars a uniform nashi murmushi tayi tahau tafi, yayi wani irin kyau
kaman bashiba, bata wani dade da zama ba aka gama abin Dj yasa waka, gani tayi Aliyu ya
sauko daga stage din yafara tafiya dudda ana tareshi ana gaisawa dashi but idanunshi nakanta
chass, ita bama tasan yaganta ba sai yanzu dataga yana kallonta dauke kai tayi daga kallonshi
ganin yanda mutane ke kallon inda yake kallo tahau wasa da yatsunta chan kuma taciro wayan
ta daga jaka tana daddannawa. “U look beautiful Pickle Anya zan iya jira kigama school kuwa”?
Taji muryanshi akanta, dan turobaki kadan tayi sanan takalleshi ganin yanda yake kallonta yasa
akunyace tadau bag dinshi tamikamai murya chan kasa tace “congratulations” wani irin kallon
cute bag din yayi sanan yay murmushi yasa hannu yakarba yace “Pickle got me gift, I promise
dazaran nakoma gida shi zan fara budewa thank yo….” Bai karasa maganan ba jin wayanshi na
ringing zaro wayan daga aljihu yayi yakalli screen din sanan yamaida kafin yakalleta yace
“come muje lemme introduce u to some people” makemai kafada tayi ahankali tace “ni kunya
nakeji kabari natafi” dan hararanta yayi yace “kokizo muje Kona daukeki wlh” dasauri ta tashi
daga kan kujeran tana turomai baki, murmushi yayi yace “muje gimbiyar Aliyu” jerawa sukayi
atare yana kallonta ganin yanda take bin wajen da kallo tayi kyau ba kadan ba kaman amarya,
wajen dasu Gwaggo ke zaune yakaita, Gwaggo da Mami sai Meena da Khadija da Amal ke
zaune Abba ne kadai bashi awajen shima bai dade da tafiya ba sabida emergency da aka
kirashi for a hospital, ita binshi kawai take har gabansu Gwaggo dabatasan suwaye ba,
dukansu kallonsu suke sanan yadan juyo yakalleta ahankali yace “meet my family Pickle”
Innalillahi! Tafadi dasauri jitayi zata nitse akasa dawani irin sauri tajuya zata gudu dan bama
tasan mema zatayi ba, hannunta ya chapke yanadan dariya cikeda wani irin mugun sonta yace
“come back here” wani rin boyewa abayanshi tayi tana jan gyalenta trying to cover her face,
sanan Aliyun yakalle su Gwaggo kafin ma yay magana Meena tace “Ya Hydar Anty Khairy
ce”?Gyadamata kai yayi sanan yakalli Gwaggo hararanta yayi yace “ga Ummulkhairy nakawo
miki kiganta” wani irin washe baki Gwaggo tayi itakuma Meena tashi tayi tazo har bayan Aliyu
tawani irin rungume Khairy tace “Anty Khairy oyoyooo please kibari inga fuskanki dan Allah”
kafinma Khairy tai magana tashi Gwaggo tayi ta dakama Meena duka abaya tace “ke dalla tashi
kibama mutane waje da rawan kai zakija yarinya tafadi bakiga kunya takeji ba, angayamiki
irinku ce ita fitsararru muna kallonku kuna kallonmu kuri, Khairiya ta yaki kinji” Gwaggo tai
maganan tana kamo hannun Khairy, sakin hannunta Aliyu yayi yana binta da kallo ahankali
Khairy tabita still tana rikeda hannun Aliyu dake murmushi dudda shi yasaketa, sosai Mami tabi
tundaga hannun nata data rike Aliyu dashi da kallo harzuwa fuskan Aliyu dazata iya cewa bata
taba sanin yanama murmushi hakaba sai yau, wani irin kallon yarinyar yakema yarinyar kaman
zai hadiyeta, zama Gwaggo tayi akan kujera Khairy kuma tadan tsugunna agabanta sanan
ahankali taja gyalen Khairy baya sunnar da kai Khairy tayi kasa murya chan kasa tace “ina yini
Gwaggo” wani irin washe baki Gwaggo tayi tace “Allah nagode maka Aliyu wayyo Allah na,
yarinya ga ladabi ga biyayya gakuma kunya kagama biyana Hydar, Allah ya tabbatar da
Alkhairi, inane gidanku gobe zanzo na nemama jikana aurenki” dagota Aliyu yayi dasauri yana
hararan Gwaggo yace “ni bazakije neman mini aure ba hakanan kisa ahanani” Mami yadan
kalla sanan yadauke kai yace “ga Mami Pickle” ahankali batare data dagakai takalli Mami ba
tace “ina yini Mami” kan Mami nakan waya batare data kalleta ba tace “lpy sannu” Khadija da
Amal ne duk suka gaidata suna murmushi sanan yakalli Gwaggo yace “bari narakata sai indawo
mutafi” dasauri Gwaggo takara tashi tana warware kullin zaninta tace “bari nabata kudin mota”
dariya Aliyu yayi yace “direbanta na waje Gwaggo” “kai wlh makirin yaro ne Aliyu bakin ciki kake
zan bata kudi kai bani baka, katon banza kawai andaiji kunya” dariya Khairy tayi kanta akasa,
sanan Gwaggo takawo dubu daya tasamata a hannu tace “gashi asaiwa kanne tsaraba ki
gaidamin da mamanki kinji” Gyadamata kai Khairy tayi tace “nagode Gwaggo” Aliyu ya harareta
irin hararan makwaduwa dinan yace “muje” Meena tace “bye Anty Khairy” bye tamata sanan
suka wuce Mami tabi Khairy da kallo tundaga kasa har sama daya tabbatar mata da Yar masu
kudi ce, ga zinare a hannunta da kunne atampan jikinta kadai is worth 260k gashi kuma taji
Aliyu nacewa direban ta na jiranta awaje, a ina Aliyu yasamo Yar masu kudi haka, iska tadan
fuzar ahankali takara kallonsu yanda Aliyu ke kappa kappa da ita kaman Yar Kwai, jitayi
zuciyanta namata zafi, “kinga Zainabu kiramin mijinki awayanki bani da kati atawa in gayamai
danshi yasami mata ohhh ashedai zanga Auren Aliyu kafin na mutu iyye, kai Allah nagode
maka Allah, kiramin imaza” akufule tace “nima banda katin” dasauri Meena tazo wajen tace
“Gwaggo inada shi bari nakira” wai Gwaggo kaman zata zare, sabida murDna.
DUK WACCE TAKARANTA MIN LITTAFIN NAN BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA
Dakin Ammin shi yawuce, tana zaune as usual cikin shiga na alfarma kaman matan shugaban
kasan Nigeria waya a kunnenta tana waya, kan stool na gabanta kuma fruits ne yankakku da
spoon aciki da alamu sha take sai wayan ya tsayar da ita, zama yayi kusada ita sanan yadauki
bowl na fruit din nata yafara sha abinshi wayanshi yaciro yana dubawa miss calls yagani like 9
daga number daya shiru yayi yanaji ranshi na baci baisan ya akayi Faisal yabama that Aisha girl
number shi ba, bayan yabar Abuja lokacin da Mama tarasu daya koma baima sauka agidan ba
hotel yakoma da zama dan he’s tired of yanda yarinyar keep stalking him school gida kaman
zata haukace akanshi, he just had sex with once which he paid which infact ma bashi yama
nemeta ba, Wanan halin datakeyi yasa kwata kwata bayama neman yaran naija, all babes
dinshi achan turawa ne cus sunsan menene sex for fun not sex for attachment, dan tsaki yaja
ganin tasake kiranshi ya ijiye wayan Ammi datagama call tace “kai lafiya kana neman fasa
wayanka” ahankali yace “Ammi damuna wata mayyan yarinya take ne wlh” dan murmushi Ammi
tayi tace “kai haka kakema yammata wulakanci ahaka zaka sami matan kayi aure, danni wlh
tasaka zanyi agaba Kwanan nan zakai aure dan bazan barka hakama yaro kanada 36 kana
neman 37 ace ba mata ina, akwai ma wata yarinyar kawata danakeso kaje kadubo bakaga
yarinyar ba kaman baturiya” ijiye bowl na fruits din yayi yace “Ammi please don’t start niba yaro
bane dazaki dinga nemomin mata ba I will get married but lemme take my time baaa rushing ayi
aure, I still young bawai tsufa nayiba” tunda yake maganan Ammi ke kallonshi tace “wai kai Son
na lura bamaka son Auren nan gabaki daya” murmushi yayi ya kwanta akan kujeran yana daura
kanshi kan cinyanta ashagwabe yace “Ammi kaina kaikayi sosamin” hannu tasa cikin soft
gashin nashi tana sosamai scalp tace “daga ina kake dan na aika dakinka bakanan” ahankali
yana lumshe idanu yace “dakin Mom” tsayarda susan tayi tace “akanme zakaje gaida matan
nan ita yaran datake zama dasu bata taba turosu sun shigo sun gaidani ba barinma Wanan mai
idanun mujiyan Khairy” shiru yayi yana jinta baice komiba yace “ita tanaso yarana sudinga
girmamata ita batasa nata sunyi hakaba” murya chan kasa yace “common Ammi nowww, yaran
gidan nan waye baya tsoronki masifanki yasa babu wanda keso yashigo side dinki ya gaidake”
ture kanshi tayi dagakan cinyanta tace “ni uwarka kake kira masifaffiya eh” maida kanshi yayi
kan cinyanta yace “Ammi ok bazan kara zuwa ba cigaba damin bacci nakeji wlh” yanda takeson
Zayn yasa shi kadaine bata iyawa masifa da wanine yau daya shiga uku, cigaba da sosamai
kan tayi baidauki cikakken 4min ba yay bacci ahaka, ta tasashi gaba tana kallo ahaka Baffa
yashigo side din yana kallonsu murmushi yayi yace “kin sangarta yaron nan dayawa wife”
murmushi tayi tace “wai nan lallabashi nake yaje yadubo yar kawata idan tamai mu musu aure
koya kagani dan wlh Alhaji na lura Zayn bayason yau aure at all” tunda tafara maganan Baffa
yay gim yana kallonta, ganin yanda yayi yasa Ammi tace “tunanin me kake bakace komi ba”
dan murmushi yayi yawuce sama sanan yace “idan bayaso karki takuramai” binshi da kallo tayi
dan reply din Baffa seems strange, dan tabe baki tayi tace “zaimaje kuma zai sota atoh”.
Wuraren 4 tana zaune adakinta tana waya da Aliyu da this is the third time yake kiranta tun
bayan text datamishi dazu kan ta yanke duk yadamu harda cemata zai dawo tahanashi karya
dawo dudda haka yaki yarda, turo kofa Batool tayi tawani fado gadon tace “Malama Ya Zayn
yace kifito kuje” ahankali tace “kije kicemai nafasa zuwa” hararanta Batool tayi tace “wacece Yar
aikenki ni kinga tafiyata wajen Mom bye” Aliyu dakejin maganan su yace “waye Zayn? Ina
zaku”? Dan yatsine fuska tayi tace “gidan mu zani wajen Baba, Ya Zayn kamanta Babban
yayanmu dandan Baffan mune” dan ijiyan zuciya taji yasauke kafin ahankali yace “go and tell
him u are not going, gobe Adamu yakaiki” gyadamai kai tayi tace “tom bari naje” katse wayan
tayi ta ijiye kan gado sanan taja wani gyalen Batool data jefar kan gado tadaura akanta dababu
dan kwali tazura silipas tawuce tafita”.
Yana zaune cikin mota yakafa black sun glasses a idanunshi kaman wani makaho yana kallon
kofar flat din Mom, sai uban kamshi yake yasaka wani gizna mai ruwan toka ajikinshi kaman
wani ango, bude kofan flat din Mom da akayi yasa ya gyara zama yana kallon flat din da kyau,
fitowa tayi babu komi a hannunta sanye dawani pink bathroom slippers da kumbunan kafanta
sukai Zara zara sukai kyau aciki, har lokacin tana sanye da gown din dake jikinta dazu,
hannunta dataji ciwo saiwani kaffa kaffa take dashi kaman Yar yarinya daga ganinta kasan bata
sabajin ciwo ba and she hates getting injured, fuskanta looks so innocent and so beautiful tana
wani irin glowing idanunta subyi fari kal kaman tana wankesu da hypo, pink lips dinta ko
daganan zaune amota da bakin glass dinan a idanunshi yana iya ganinsu, gani yayi ta tsaya
takalli waya nan tsuntsayen dayagani anan barandan Mom acikin cage dinsu masu kyau
dankoshi dazu dazai shigo saida ta tsaya ya kalli tsuntsayen dan sunyi kyau, murmushi tayi
sosai da he could see all side dimples nata na lotsawa jerin gajejjerun white baby teeth nata sun
fito tana kallonsu sanan ta tashi tajuyo tana saukowa daga staircase din, ahankali yakai
hannunshi yadaura kan kirjinshi dayaji every step datai taking yana jinshi a heart dinshi, tunda
yake shi he never baitaba jin haka on anygirl ba, shi baima taba tsayawa yakalli any girl kaman
yanda yakalli Khairy yauba, he don’t know mesa kawai he just like how innocent she is, dan iska
always know dan uwanshi idan yaganshi but anytime yakalli Khairy he sees yarinya that doesn’t
know anything, yayi nisa acikin tunanin yaji tai knocking glass din motarshi wani irin daure fuska
yayi batare daya saukarda glass din kasa ba yay unlocking car din hakan yasa tabude kofar
motan kallo daya tamai sanan tadan sunnar da kai ahankali tace “Ya Zayn baranj…..” “you don’t
talk to me daga waje get in kafin nabata miki rai” jitayi ranta yabaci ahankali tashigo motan
tazauna zata fara magana yace “rufemin kofan mota” rufe kofan motan tayi ahankali kafin tai
magana yatada motan yaja ana budemai kofa dasauri tace “Ya Zayn bazani ba shine abinda
nazo nafadama” batare daya kalleta ba yace “idan munkai kidawo” dan jim tayi ranta nabaci,
batare daya kalleta ba yace “sit belt Miss” jan sit belt din tayi tasaka sanan ahankali tamaida
kanta tana kallon hanya.
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.
wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp
number na 07012181461
Thank u❤️
Sakin hannunta yayi dawani irin sauri tajuya gabanta nafaduwa dum dum Batool sai hadiye
dariyanta take ganin yanda duk Khairy ta birkice sanan suka wuce suka shiga flat dinsu, suna
shiga Batool tafada kan kujera tana dariya tana kallon Khairy datai kuriii jikinta har lokacin bai
dawo daidai ba, kallonsu Mom data fito daga kitchen tayi tace “ya akayi” cikeda dariya Batool
tace “Mom Khairy taje takankame Ya Zayn tadauka nine saura kiris yamaketa bakiga yanda
dukta rude” hararan Batool Mom tayi tace “wlh daya makemin mu danama mai godiya, yara
daga tashinku kunbi gida kuna guje guje ko kayan bacci baku cireba ku wuce kuje kuyi wanka
kuchanza kaya kafin na sassaba muku” Khairy tafara gaba kafin Batool tabita abaya, hartahau
stairs sanan tajuyo takalli Mom tace “Mom yaushe Ya Zayn yadawo”? Batare da Mom takalleta
ba tace “around 2 nadare ya shigo gidan nan kuna bacci lokacin” wani irin tsalle Batool tayi tace
“yanzun nan bai wanka zanje nasame shi Mom yabani kudin ankon Na’ima” “kinfi kusa” Mom tai
maganan tana shiga kitchen abinta itakuma Batool tajuya tai dakinsu, shiga tayi ganin babu
Khairy afalon yasa tafada kan gado tana jiranta tafito daga wankan.
Fitowa Khairy tayi daure da towel dinta pink akirji ko kallon Batool din batayiba tawuce wajen
wardrobe dinsu, tashi Batool tayi zaune tana kallonta tace “towai fushi kikedani danna tadaki
daga bacci sorry to” juyowa tayi ta balla mata harara tace “ni gidanmu zan ma koma Wanan da
wanchan Yayan naku yafaramin gorin gida daga ganina bazan dauka ba” dasauri Batool ta tashi
dan idan akwai abinda ta tsana shine taji Khairy tace zata tafi gidansu, dasauri ta tsaya kusada
Khairy dake shafa mai ahankali tace “ke dalla don’t mind Ya Zayn, wlh Ya Zayn nada bala’in
kirki barshi dai da iyaji da kanshi amman yanada kirki kinga duk wulakanci Ammi baya biyemata
wlh, Bakiga yana shigowa nan ya gaida Mom ba dudda Ammi bataso shi baruwan shi kuma
yana sonmu, yana bani kudi koban tambayeshi ba hakama Zara’u, har dakinshi tana zuwa
taitamai surutu wlh baida wulakanci, dan Allah karki kara cewa zaki tafi” kwafa tayi tajuya mata
baya tanasa bra sanan tajuyo binta da kallo Batool tayi tace “ke Khairy ai wanan Bra yamiki
kadan, kinada nono wlh Khairy kaman muyi musanye” dan tsaki tayi tadau riganta tana sawa,
Batool cikeda tsokana tace “iyye su Ya Aliyu zai more” dawani irin sauri tajuyo zata dakamata
duka ihu Batool tayi tawuce dagudu tafada bayi, dan murmushi tayi tana kallon kanta a madubi
saikuma akunyace tamake kafada tace “ni bazan ma taba bari yaganni bama rigaba balle ma
yaganni” karasa shiryawa tayi abinta cikin wani plain dogon rigan atampa ja batare data daura
dan kwali ba tafito zuwa saukowa tayi kasa Mom ce kadai tanashan tea a dinning dayaji kayan
kamshi ganinta yasa tace “ko kefa jibi yanda kikai kyau” dan murmushi tayi Mom tace “oya zoki
zauna kiyi breakfast” karasowa wajen tayi tace “Mom ni indomie zandafa” baki Mom ta tabe tace
“Allah dai yay wadaran naka yabaci, nidai kinga tafiyata bari naje natado Baban ku daga bacci,
yadan kwanta shima yazo yay kari” kitchen tawuce itakuma Mom tai sama abinta.
Wani karamin tukunya tadauko sanan tashiga store dinsu tadauko indomie daya da kwai guda
daya tafito sanan ta tara ruwa tukunna gas don tadaura sanan tawanke kwan a tap tazo tasaka
a ruwan pot din tarufe pot din sanan takoma store, albasa tadauka awajen, wani black wukan
datagani ijiye tunkwal shikadai a store din tadauko tace “hala Mom ta manta da wukan nan a
store ne baga wajen wukake duk suna nan ba” takalli cabinet din wukansu wucewa gaban tap
tayi tadauraye wukan sanan tasa wukan ta yanke kan albasan sanan tabare albasan tass, kafin
tasa wukan taraba albasan biyu ta ijiye rabi akasa sanan tadauki rabi daya tasa wukan tafara
yankawa cirrrr wukan yawani irin yanketa a tafin hannu lafiyayyen yanka dayasa batasan
lokacin data saki wani azababben ihu ba daga wukan har albasan nafadi akasa daidai lokacin
Zayn na shigowa falon yana sanye da 3quater dawata faran riga, jin ihu acikin din Mom yasa
yay kitchen din dasauri ganin Khairy tana yarfe hannunta da jini ke tsayaya ya diddiga ko’ina a
kitchen din tana ihu tana kuka ga wuka da albasa akasan kitchen din yasa yay kitchen din da
sauri hannunshi yasa ya karbe hannun nata data yanke dasauri yay tap da ita kunna tap din
yayi ya tare hannun kasan ruwa wani kalan fashewa da kuka tayi zata kwace hannun amma
yaki yana wanke jinin daidai lokacin daga Mom har Baffa dasukaji ihunta sun shigo kitchen din
dasauri wukanda Mom tagani akasa yasa tai salati. “Innalillahi waya fito da wukan daga store”
cire hannunta Zayn yayi daga tap but still jini zuba yake ganin haka yasa Baffa yace “kawo first
aid kit dinan Wife” fita Mom tayi daga kitchen din, ahankali Zayn dake rikeda hannun yakalli
fuskanta yanda take kuka da yanda har gumi yafeso agoshinta dan ita anytime she’s stress or in
pain tuni zakaga gumi yaketo mata a goshi, yanda gumi yasa gashin gaban goshinta ya kwanta
ga hawaye na gangarowa daga idanunta datake gogewa da bayan dayan normal hannunta
idanunta duka suna kan hannun da jini kefitowa dagakai yasa yaji beat din heart dinshi na
raguwa, ahankali kaman wanda wani abu ke controlling yakai hannun saitin bakinshi kafin
ahankali yadaura bakinshi kan hannun wajen yankan yanashan jinin yana kallon fuskanta, wani
irin sanyi taji bakinshi yayi akan yankan kaman yadaura ice akai shiru yadena mata zafin
dayake dawani irin sauri takalleshi tana ware manyan idanunta duk wani hawaye datakeyi ya