Showing 3001 words to 6000 words out of 108975 words
Chapter 2 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf
ginin zamani, tana sanye dawata doguwan rigan Atampa mai kyan bala’i ga kallabi daure
akanta da kana gani kasan daura dankwalin kawai tayi amman hakan baihana kwantaccen
black gashinta dake gauraye da farare lekowa ba, tana tsaye agaban wani hadadden babban
gas a kitchen tanama wata yar aiki dake juya basmati rice a tukunya dawani wood spoon
magana sukaji wata zazzakan murya dake ratsa zuciya na y’a mace ta kwala ma matar uban
kira. “Mama nadawo, nakawo miki wasu kawayena ki gansu” wani irin kwashewa da dariya yar
aikin dake juya abinci a tukunya tayi takalli Matar da aka kira da Mama datai tsaye kawai tama
rasa ta cewa tace “Hajiya wlh tun ina iya kirga yawan kawayen Khairy harna bace a kirgan”
kwafa kawai Matar da aka kira da Mama tayi tace “karasa juya abincin sai ki kwashe a warmer
Ladid…..” bata idasa maganan ba aka kara rangadamata kira da wanan zakakkiyar muryan
kaman ana busa sarewa. “Mamaaaa kina ina zoki gansu” dafa goshinta Matar tayi cikeda
takaici tace “Allah nagode maka dakabani wanan yarinya, ina ganin Ummulkhairy ce zata bani
hawan jini aduniyan nan” tai maganan tana fitadaga kitchen din ta hanyar bude kofa tafice, tana
fitowa dining tai kicibus da yammata kusan su tara a zazzaune kan lafiyayyun kujerun falon
suna maganganu suna hira suna kallon lafiyayyen hadaden falon dayaji Cubana furnitures,
ganin Matar da kallo daya suka mata suka gane itace mahaifiyar Khairy yasa duk suka zubo
daga kan kujerun cikeda girmamawa duk suka gaidata. “Mama ina yini, Mama barka da rana,
Mama ina gajiya” lafiyayyen murmushi ta sakin musu tana karasowa tsakiyan falon tana bindi
da kallo daidai tace “Masha Allah sassannunku da zuwa yammata yakaratu”? Kafin subata
amsa wata kyakkyawan budurwa yarinya chocolate skin color, yar doguwa bachan sosai ba
dabazata wuce 20yrs, skin dinta nawani kalan glowing fuskanta babu ko kuraje guda, tanada
dan dogon hanci yet kuma dan karami dan diss afuskanta but fitacce, tanada manya manyan
pure white eyes, idanunta are very big sunada wani kalan adorable spherical shape that is just
damn gorgeous, dan kana kallonta the first thing dazasu fara daukan maka hankali a fuskanta
are her big white eyes, ga eyelash dinta dogaye bakake cikakku, hakama gashin giranta,
tanada goshi wanda kusan yarabu biyu ne rabi duk gashi ne dayake nan baki sidik sun kwanta
daya karama fuskanta wani kalan kyau dan zaka dauka buzuwa ce sai dayan rabin kuma fatarta
ne dayataho har gira, tana sanye da dogon rigan atampa itama da dan kwalinta akanta, tawani
buga uban ihu da saida falon ya amsa gabadaya. “Mamaaaa” yanda ta kwala mata uban kiran
nan yasa mahaifiyar nata tadago da kanta tareda juyowa ta zuba mata idanuwanta kurii irin na
jama’a yaya zanyi da wanan yarinyar ne? Wani irin washe baki Khairy tayi cute saitin white
teeth dinta suka bayyana tashiga saukowa daga stairs din dagudu kaman ba ita Mamar kema
kallon zaki ganeba kawai tawani irin fada jikin Maman nata tana ihu sosai tana rawa ta kankame
Maman kamkam. “Wayyooo Mama wlh nai missing naki, inata nemanki nadauka kin fita ne har
hankalina yatashi ashe kina kitchen, Mama tun safe yau banganki ba awa nawa yanzu bansaki
a idona ba karfe biyar fa, nai kewanki Maman mu, Mamana, I miss you Mommy Ummulkhaiyr”
tai maganan tana kara kankamet Mama cikeda tsananin murna, dudda yanda Mama ke mugun
kule da ita saida tai murmushi har cikin ranta duk cikin yaranta babu wanda ke sonta kaman
yanda Khairy ke sonta, idan Khairy tadawo gida batanan wani zubin har zazzabi takeyi, Son da
Khairy ke mata dabanne, gabaki dayan kawayenta baki suka sake suna kallon Khairy yanda ta
kankame mamanta cikeda murna tana rawa kaman wata yar karaman yarinya, murmushi kawai
Maman takeyi ganin yanda kawayen ke kallon Khairy sabida wayan nan wasu new set ne basu
saba ganin haukanta agidaba yasa Mama tace “ke dalla cikani kije kitchen kitaya Ladidi ku
kwaso abinci kiyi serving friends naki kuci” sakin Mama tayi ahankali tana murmushi dake
bala’in kara mata kyau tana kallon Mama tace “tom Mama” sanan tawuce kitchen da ihunta ta
shiga kitchen din. “Ladi kwas kwas!” Tsabagen yanda Ladidi tafirgita batasan lokacin data saki
cokali data rike a hannunta kasa ba, kwashewa da dariya Khairy tayi ganin yanda Ladidi
tafirgita, Ladidi ta watsa mata harara tana dafa kirjinta da hannu jin yanda yake bugawa tace
“aniyarki tabiki Khairy bani zaki sawa bugawan zuciya ba wlh” dariya Khairy tayi tadauki spoon
tazo kusa da ita tana kallon tukunyar tana murmushi tace “uhmm smells good, let’s have a
taste” abincin tadeba takai baki tana lumshe ido, harara Ladidi tabita dashi tana kallon long full
lushy eyelash dinta dazakaji kaman ka cire kasama naka sabida kyau, dan murmushi tayi tace
“yayi dadi Khairy? Kinga nasa coconut milk dakikace nadinga sawa” bude idanu Khairy tayi ta
kalleta sanan ta yatsine fuska tace “yayi dadi ba laifi amman ba kaman nawa ba” batarai Ladidi
tayi hakan yasa Khairy tafashe da dariya tace “ki zubamana nida kawayena kizo ku gaisa”
hararanta Ladidi tayi tace “Malama ki tsaya ki dauki abincinku ki kaimusu ba inda zani nagaji da
gaisawa da kawayenki, nibansan ko kamfani gareki na kawaye ba” turobaki Khairy tayi tace
“bakinciki kikemin kinga inada kawaye masu sona ke bakida kawa ko daya” dasauri Ladidi
tanuna kanta tace “ni Khairy bakin ciki ana zaune lafiya, kawayenki sunfi dari, ni idan Allah
yabani kawaye ko sama da biyu ne bansan yanda zanyi dasu ba” hararanta Khairy tayi tadauki
Baban tray da Ladidi tajera musu different abinci akai a different plate guda 5 tafita dasu taje
takai musu sanan tadawo ladidi na kallonta tace “yanaga kin dawo” akufule tace “su tara ne plus
ni goma, kuma is just 5 plate of food nafita dashi” kasa magana Ladidi tayi kawai tashiga zuba
wasu sababbi tass abincin yakare Ladidi tace “yayyinki suka dawo maizasuci” “oho” ta amsata
akufule tafice abinta takaimusu abinci suka shiga ci suna hira shaaaa kakeji sun cika falon da
hayaniya kadauka biki ake kowani liyafa aka hada, lekosu Ladidi tayi daga kitchen kwafa tayi
tace “yo wlh ban kara daura wani girkin barima kiga tafiyata zanyi, masu gida nakema aiki ba
kawayenki ba, yarinya kowani kare da doki kawayenki ne, mijinki zai sha fama Khairy” tai
maganan tana komawa ciki, hada yan kayanta tayi a handbag dinan sanan tabi takofar kitchen
tafice abinta daman inhar tagama aikin yamma indai Hajiya na sama tafiyanta take saidai in
tana kasa ne saitaje tamata sallama tawuce.
Sai wuraren 6 sanan kawayen nata suka fito bayan takaisu sama sunma Mama sallama har
compound tarakosu inda sukai parking motocin su duk suka shishiga, daya daga cikinsu taleko
bayan tama motarta benz key tace “wai Khairy yaushe zaki farajan mota kine eh? Gamu duk
mu munaja ke kadaine kullum driver ke kawowa” kaman zatai kuka tace “ba su Mama bane da
Baba wai tsoro suke su barni nafara tuki wai nacika rawan kai kumafa na iya wlh Paddy” dariya
dukansu sukayi wacce ta kira da Paddy tace “ke da karfin hali zakisa su barki kifara tuki wlh
daukan mota kawai zakiyi wataran ki fice, Babe magrib tayi bari muwuce see you tomorrow at
school” hannu tadaga musu tace “see yah girls” gateman dinsu yabude musu gate suka fice
motoci biyar daidai kuma motocin yayinta na shigowa gida na Baban su biyeda su, washe baki
tayi tana tafi ahankali tana kallon motar Baban su dake shigowa last tace “oyoyo Baba” motan
na parking tai wajen motan da gudu batare databi na yayyinta da kallo bama.
ALKAWARIN ZUCIYA
PROMISE OF THE HEART
✍M SHAKUR
4️⃣
Kafin ma Baba yabude kofa tasa hannu tabudemai kofan jikinta har rawa yake tanajin dadi.
“Baba oyoyo, Baba sannu da zuwa” wani magidancin mutum ne babba sosai yana sanye da
babban riga yanada gemu dayacika da furfura, ga kuma katon ciki irin na manya wayanda suka
manyanta dinan, exactly idanunsu iri daya da ita manya saidai nashi daya soma kankancewa
sabida tsufa, wani kalan kyayataccen murmushi yasakin mata, cikin kamilallen muryanshi irin na
magidantan nan yace “yarinyar Babanta” yay maganan yanajan dan hancinta, murmushi tayi
sosai tace “sannu da zuwa Baba” fitowa daga motan yayi yace “to akwasomin kaya akai ciki”
gyadamai kai tayi tace “to Baba” yawuce yana kallon yaranshi maza su uku da duk suke tsaye
suna jiran fitowanshi, Manaf wanda yake Babba yanada 27yrs, sai Mu’az shima 27yrs twins ne
shida Manaf saidai ba identical twins ba ko kadan ma basuyi kamaba idan baa gayamaka yan
biyu bane bazama ka yardaba, Manaf na kama da Mama, Mu’az na kama da Baba, sai Maheer
dakenan 24yrs, dukansu sun gama makaranta duk a company Baba suke aiki yanzu.
Gaida Mahaifin nasu sukayi cikeda girmamawa kana ganinsu kaga yaran dakeda tarbiya
dakuma natsuwa. Cikin so da kauna ya amsasu yana tambayan kowa ya aiki sanan suka wuce
masallaci, itakuma kayan Baba su files da wasu yan tarkace tafito dasu daga motan sanan tai
cikin gida.
Sama tayi direct zuwa lafiyayyen hadadden falon Baba, ijiye kayan tayi sanan tajuyo tabude
kofa ahankali, ganin Mama tsaye abakin kofan kaman ita take jira daman yasa takarasa fitowa
tareda maida kofan tana rufewa tana kallon fuskan Mama dake kallonta tana murmushi, harara
Mama ta watsa mata tace “ba murmushi nace kimin ba, quietly go to that kitchen kidafa sabon
abinci wanda za’aci agidan nan this night tunda wanda aka dafa dake da kawayenki kun
cinyeshi tatas” dan turobaki tayi dan wlh tagaji ahankali kaman zata rushe da kuka tace “Mama
maisa Ladidi bata dafa wani ba wlh nagaji school fa naje” cikin fushi sosai Mama tace “are you
stupid Umma? Inba so kike na makeki ba kiwuce yanzun nan kafin raina yabaci kije ki daura
abincin daza’aci this night, I am talking to you kina gayamin Ladidi tadafa, kin zaci sabida ke
nadauki Ladidi aiki kokin dauka jakace ita batasan ciwon kanta ba dazata zake tai girkin gida
keda kawayenki kuzo kutasa abincin agaba ku cinye tas, yanzu ina gayamiki kije ki daura wani
kina neman kawomin gabli da ba’adi, to the kitchen my friend!” Mama tadaka mata tsawa
kaman zata kurma ihu tawuce hawaye sun cika idanunta tass tai kasa, harara Mama tabita
dashi sanan takada kai kawai tawuce tashiga dakinta.
Kitchen din tashiga tamaida kofan da mugun karfi tarufe kaman zata Balla kofan sanan ta
jingina da kofan tana maida numfashi takai kusan 5min sanan tawuce ta kwaso kayayyaki
tashiga shirin hada girki.
Saida akai Isha’i sanan Baba da su Manaf suka shigo gida, afalo suka tarda Mama zaune
gaidata duk sukayi, Mama ta gaida mijin nata zama duk sukayi, Maheer yace “Mama me aka
dafa yunwa nakeji” ahankali Mama tace “Khairy na kitchen tana girki, itada kawayenta suka
cinye duka abincin da aka dafa tass shine yanzu dannace taje tadafa wani abincin take
kumbure kumbure” dan murmushi Baba yayi yana duba wayanshi ganin yanada miss call,
cikeda kufulewa Maheer yace “wlh Mama Allah zan zane yarinyar nan, duk randa takawo
kuchakun kawayenta tashiga kitchen tamusu girki da kanta ba abincin muba” cikin fushi shima
Mu’az yace “ni I don’t even know wani kalan brain Khairy keda shi, ni tunda nake bantaba ganin
wacce takai Khairy yawan kawaye ba, kawayenta sunfi dari biyu, tamaida mana da gida nanne
majallisar kawayenta ai gobe Saturday Allah sa takawo mana wata gidan nan wlh daga ita har
kawar saina kakkaryasu” Baba daduk ke jinsu yana taba wayanshi wayan ya ijiye yakalli Mama
yana murmushi sanan yakalli su Maheer yace “ku kyale yarinyar nan she’s just a small girl, idan
making friends makes her happy so be it, abincin gidan banike siyaba taita kawo kawayenta
sunaci is no big deal, and you wife” yajuyo yakalli Mama yace “idan abincin gida da kawayenta
keciki ki kara yawan abinci since kinsan yarki mai mutane ce, ta yanda zasuzo suci su koshi
sanan muma muzo muci okay” tabe baki Mama tayi tace “daman babu wanda ke bata yarinyar
nan saikai kacigaba” Mama tai maganan da fushi dan murmushi Manaf da tuntuni baice komiba
yayi ganin yanda ran Mama yabaci yace “Mama kudena making issue out of this small thing
please bagashi yanzu tana kitchen tana dafa mana wani ba, is just friends ta tara bawai wani
bad hali ko dabi’a takeyi wanda yaran yanzu sukeyi ba Mama, please ku kyaleta, she’s still a
small girl, inda ace bata gama secondary school dawuri ba da har yanzu bamata shiga
university ba ballema tazo hartana final year, ku barta please Mama ahankali zata gyara”
murmushi sosai Baba yayi yanajin maganan da Manaf keyi, Manaf nada dabi’unshi sak, ga
hakuri ga iya tafiyar da gida gashi da halin manyanta halin Baba, amman Mu’az da Maheer jin
kansu suke kaman sa’onnin Ummul Khairy. Baki Mama tabude zatai magana aka bude kofan
kitchen din aka fito Khairy ce tadauko wani hadaden warmer, ko kallonsu batayi ba sai uban
turo baki take tawuce zatakai warmer dinning Baba yace “zo kawo kulan nan Umma anan falo
zamuci” ahankali tajuyo tazo Mu’az da Maheer sai uban ballamata harara suke tana karasowa
ta ijiye kulan Baba na kallonta yace “yauwa sannu da aiki Yanmata na” Maheer dake kallonta
yace “yi sauri kije ki kawomin plate dina da fork” dasauri ta kalleshi da manya manyan idanunta
harara ta watsamai wani irin mikewa tsaye yayi kaman zaiyo kanta dasauri tai baya tareda dan
sakin ihu. “Wayyo Ya Manaf kaganshi ko” hararanshi Manaf yayi batare dayay magana ba
hakan yasa Maheer yakoma yazauna yana kwafa, Manaf yakalleta yace “go and bring the plate
and serve us” gyadamai kai tayi tajuya tana turo baki daga Baba har Mama suka bitada kallo,
bata wani dade ba tafito dauke dawani babban tray da plates spoons, bottle water da drinks ke
kai sanan takawo tsakiyan falon, sanan tabude kulan wani kamshi ne yadaki hancinsu tadafa
wani lafiyayyen taliya da nama, zuzzubama kowa tayi sanan ta tashi, Baba yace “ina zaki zauna
kici naki” ahankali tace “nakoshi naci shinkafa dazu, wanka zanje nayi Baba nagaji” “jikiyi
yarinyar kirki” wucewa tayi sama sukuma sukahau ci, saida Maheer yajuya ganin hartama shiga
dakinta yasa yajuyo yace “at least she’s good in one good aspect, wato girki” murmushi Baba
yayi yakalli Mama yace “akwai wacce zata zauna da Wife bata iya girki ba ballema yarta”
murmushi kawai Mama tayi batacemai komiba, saida suka gamacin abincin tsaf sanan Maheer
ya kwashe komi yakai kitchen kafin su tashi suma iyayensu sallama suka wuce side dinsu.
Tashi Baba yayi yana kallon Mama datai shiru yace “please kidena sa zancen shirmen Khairy
aranki, is just like what Manaf said at least friends kawai ta tara bawani mugun hali ba” dan
ijiyan zuciya ta sauke sanan ahankali tace “Alhaji still yawan kawaye basu da amfani wlh”
ahankali Baba yace “I promise duk randa nai sensing wani bad behavior kokuma wani abu nida
kaina zan rabata dasu, please this matter of her friends shouldn’t be an issue again ok”
Ahankali Mama tace “ai shikenan dama kaine ke bata Umma ai” Mama tai maganan tai gaba
abinta binta yay abaya yace “wifeyyy common” bata biyemishi ba tabude kofar dakinta ta shige,
murmushi yayi kawai aranshi yace “I will handle u later” sanan yay hanyar dakin Khairy,
knocking yayi ahankali tareda kiran sunanta. “Umma” jin shiru yasa ahankali yabude kofan
dakin, dakine nai kyau dakana gani kasan dakin Yar gata ne anyimai Fenti pink dakuma design
na flowers everywhere, tana kwance kan lafiyayyen gadonta mai kyau tana sanye da dogon
gown na bacci tana bacci hankali kwance ga dakin uban sanyin AC tachure alamun sanyi takeji,
karasowa gaban gadon yayi yace “Umma Umma, mamar ki dake fada ita batasan rashin jin
maganan ta kika daukoba” yay maganan yanajan bargon gadon yarufa mata sanan yadau
remote don AC yarage AC sosai kafin ahankali yajuya ya kashe wuta sanan yarufe mata kofan
yawuce dakin matarshi!!!!
PROMISE OF THE HEART
ALKAWARIN ZUCIYA
✍M SHAKUR
5️⃣
Da asuba kafin Baba yawuce masallaci yashigo yatadata wanda hakan yakeyi kullum.
Da farinciki ta tashi yau sosai kaman ba itane ta kwana da fushi jiyaba, murna take sosai sabida
yau zataje bikin kawarta Zainab.
Saida tai salla tai karatu sanan ta gyara dakinta tsaf tafito kasa ta sauka a kitchen ta tarda
Mama tsaye zata fara aiki dawani irin gudu taje ta rungume Mama. “Mama good morning”
murmushi Mama tasakeyi this is another aspect na halin Umma datakeso ko kadan batada riko,
tureta Mama tayi tace “waike karyani kikeso kiyi” dariya tayi tace “Mama dadi nakeji yau bikin
Zainab Kawata, Beaty wacce nai ankon ta kin tuna”? Baki Mama ta tabe tace “ina zan tuna wata
Besty Bestotin kin sunfi dari, keda kullum cikin bikin kawayenki ake, idan babanki ya shigo kije
ki tambayeshi izini baruwana da zuwa bikinki, bani tukunya nidai kiga” dasauri tadaukoma
Mama tukunyar nan suka shiga hada breakfast tanama Mama surutu wuraren 8 suka gama
komi suka jera a falo daidai nan su Baba suka shigo gidan duka zama sukai a falo suka shiga
kari sai bayan an gama ta kwashe komi takai kitchen sanan tadawo da saurinta tazauna kusa
da Baba, fuskanta kadai yagayamai dawani abu hakan yasa yace “Ya akayi Khairiyya?”
Murmushi tayi tace “Baba yau bikin Zainab kawata shine nakeso nagayamaka” idanu Baba
yazuba mata yace “amman kinsan yau yakamata kije gidan Baffan kiko” gyadamai kai tayi
dasauri ahankali tace “Baba gobe zanje gidan tunda yau inada biki please naje Baba”? shiru
yayi sai chan yace “ok kije, but by 4 kidawo gidan nan ban yarda kije kai Amarya ba” murmushi
tayi tace “Baba ai daman bazanje ba itada za’akai Kano, kumama ana daura aure wai zaa tafida
ita kaga kenan kafin 4 nadawo ma” jinjina