Showing 1 words to 3000 words out of 108975 words
Chapter 1 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf
ALKAWARIN ZUCIYA
PROMISE OF THE HEART
✍M SHAKUR
1️⃣
~UK~
Tundaga nesa take leke babban building din datake dumfara tana bin uban tulin cars din wajen
da kallo kaman akwai abinda take nema kafin daga bisani idanuwanta su sauka kan wata white
Bentley car, gashinan kar kar ko alamun a single dust babu ajikin motan, ajiyan zuciya tasauke
ahankali murya chan kasa tace “Alhamdulillah he’s still around” sanan tashiga sauri takarasa
gaban wajen da ake kira da Cozy, harzata saka hannu tabude kofan tashiga tadanyi jim tsaya
kafin ahankali tabi jikin ta da kallo tana sanye dawani white jeans daya kamata tsam dawata yar
dark blue top mai shegen kyau wacce da kadan tasauka daga kan cibiyanta, saidan gyalen data
yana kanta white shima dayamata kyau sai gashin kanshi dakenan kusan rabi awaje anmata
kalaba da attachment kanana dayamata kyau shima, hannunta rikeda wasu books guda biyu
dakuma phone nata kirar iPhone 13, sai wata yar karaman jakan datake rataye da ita, ajiyan
zuciya takara saukewa kana ganinta kasan she’s nervous sanan ahankali tasa hannu tabude
kofan wajen tashiga ciki.
Hadaden eatery ne and bar mai shegen kyau, babu wasu mutane dayawa awajen wayanda
suke wajen yawancinsu turawa ne fararen fata maaikatan wajenma fararen fatane hakan yasa
zaka gane wajen na bature ne, ahankali take tafiya tanabin wajen gabaki daya da kallo da gefen
idanunta, kafin takarasa gaban kanta taja kujeran wajen ta zauna sanan tasauke books dinta
agabanta da wayanta, daidai baturen Bar attendant din yakaraso yana kallonta yace “what can I
get you miss” dan waigawa tayi kaman tana neman abu awurin tace “Pierre Zēro Rosé please,
two shot” ganin duk tana maganan ne batare datama kalleshi ba yasa yace “gotcha” sanan
yajuya yakoma yadauko wine din datai order yazuba mata a cups guda biyu sanan yadawo
gabanta ya ijiye yace “here we go” dan juyowa tayi da sauri takallai sanan tasauke jakanta da
sauri tadauko kudi taba shi tace “keep the change” kafin ma yay magana tasake juyarda kanta
tana bin mutanen wajen da kallo one after d other…..
“Kai Zayn look” wani hadadden chocolate guy daga tachan karshen babban falon wajen da aka
cikada kujeru ne kowa na zaune yana abinda yake yataba wani kyakkywan thick farin guy dake
zaune kan kujera ya lumshe idanu pipe din shisha na bakinshi yana zuka yana fitarda hayakin
ta hanci, yana sanye da riga da wando both black na LV, farine shi kal yanada cikan jiki dayake
rigan dayasa short sleeve ne hakan yafito da kakkauran murdadden hannunshi, irin guys dinan
ne masu manyan gabobi dakuma murdadden jiki, dudda idanunshi a lunshe but idan ka kalleshi
bazaka so kadauke idanunka ba dan yanada wani irin kyau kaman mace, lips dinshi sunyi wani
kalan masifan ja kodan shishan dayake shane oho, yanada dogon hanci siriri dayazauna akan
fuskanshi gwanin ban sha’awa, sai gashin giranshi baki sidik kuma acike yanada tabon salla
agoshi sai gashin kanshi baki sidik shima dake kyalli sun nannade kaman na buzu sanan
gawani kwantaccen saje a fuskanshi Masha Allah, koda ace shiyay kanshi bazaiyi kanshi da
wanan kyau dinba ballema bashi yayba.
Ganin baida niyyan amsashi yasa Mamu ya fizge pipe din shisha dake bakinshi yace “kafara ko
ina maka magana kamin banza” ahankali yabude idanunshi dasuka wani lumshe sukai yaushi
da idanda zai kalli mace dasu sai lissafinta yarikice sanan yazubasu kan Mamu kaman ance
yay magana dan dole yace “what”? Dan murmushi Mamu yayi da hannu yamai alamu yace
“look over to the counter ga budurwanka chan, stalker dinka tazo sai kallon ka take wlh, haba
Zayn kaiko bazakaji tsoron Allah ka kula yarinyar nan koda sau daya bane tunda dai ta kasa
maka magana for morethan 2months yarinyar nan kullum binka take tana stalking naka tana
kallonka u know she really really likes u waikai maisa kacika wulakanta mata ne eh? Anyway I
don’t blame you ni wlh in mace ne banmaga abin so ajikinka ba mutum dukgaka nan kalan
asibiti farin fata kalan cuta, duk baku da karfi” dan murmushi yayi dan yasan Mamu so kawai
yake yajashi suyita surutu this afternoon shikuma baida time dinan, hannunshi yamikamai
alamun yabashi shishi shi, ijiye pipe din shishan Mamu yayi kan table din gabansu yace “Ya
isheka hakanan gashinan duk idanunka sun chanza launi, munada lectures yanzun nan fa I
think in the next 5min” dan tsaki yaja yasa hannu yadauki pipe din shisha yacigaba dasha
abinshi yana daddanna wayanshi yana hura hayakin ta hancinshi batare dayama daga kai ya
kalli inda Mamu yacemai yarinyar nan takeba Mamu nabinshi da kallo yarasa yanda zaiyi
yaraba Zayn da shisha, shima bawai bayasha bane no but occasionally yakesha, shiko Zayn zai
iya wuni yanashan shisha hakanma yasa baya iyacin abinci sosai, ganin yasake lumshe idanu
yasa Mamu yaja tsaki yamike tsaye yace “dalla Malam wuce mutafi” bude idanunshi yayi
dasuka dan kankance sukaija sanan ya watsama Mamu harara kafin ahankali ya ijiye pipe din
yamike tsaye dogon namiji ne nagaske, budadde sanan kuma cikakke irin mazan nanne da ake
kira da burin mata, car key dake kan table din yadauka yana rikeda wayanshi yay gaba abinshi
batare daya cema Mamu komi ba yay hanyar kanta.
Tundaga nesa ta hangoshi ya dumfaro gaban kanta, duk taku daya dazaiyi saita jishi har kirjinta
yana amsawa, tun kafin ya iso wajen wani kalan kamshin dayakeyi dayake neman sata ta
haukace sabida sonshi ya lullube mata hanci ganin ko’ina najikinta yadau kyarma yasa ahankali
tasa hannu tadauki cup na drink dinta takai bakinta still tana kallonshi ta gefen idanunta daidai
ya iso ya tsaya dab da ita dasauri bartender din yazo yace “u done sir” bai amsashi ba yasa
hannunshi a wandonshi yaciro wallet dinshi yabude yana kokarin zaro kudi ko kadan batasan
drink din yamakai saman hancinta ba tsabagen yanda take kallonshi kawai numfashin dazata
shaka ta shaki wine din wani irin mahaukacin shakewa tayi dabama tasan lokacin data saki cup
din akasa ba tana wani kalan mahaukacin tari wine nabin hancinta suna fita idanunta sunyi ja
kwalla yacikasu dawani kalan sauri daga Bartender din harshi suka juyo suna kallonta dasauri
Bartender din yataho ta saitin gabanta yace “sorry Miss” dudda tarin datake kokarin danne tarin
take tana kakalo murmushi dan wanan kwafsin haka har ina baki tabude zatai magana wani
tarin yakara sarkaketa wine din na fitowa daga bakinta yana diddiga akan white wandonta duk
yay staining sabida Jan wine ne, kaman daga sama taga wani clean white handky agabanta
kamshin da ajikin mutum daya tall a duniyan nan takejin kamshi taji yana fitowa daga hanky
ahankali tadago kanta sama tanabin Tundaga handkerchief din dakallo harzuwa white hannun
dake rikeda shi zuwa kan fuskan Zayn dake kallonta in the eyes, wani sabon bugawa zuciyanta
yashiga yi hannunta har rawa yake tasa takarba zatakai kan fuskanta dan sharewa shikuma
yajuya ya ijiye kudaden dayariga yaciro daga wallet dinshi yadaura kan kantan yajuya yawuce
batare daya kara bata second look ba, ahankali ta janye handky dagakan bakinta tabishi da
kallo harsaida yabace ma ganinta sanan tasauke ijiyan zuciya kafin ahankali tasauke kanta tana
kallon handky din ko kadan tama manta inda take rungume handky tayi akirjinta tana murmushi
sosai.
PROMISE OF THE HEART
ALKAWARIN ZUCIYA
✍M SHAKUR
2️⃣
Murmushi Bartender din yayi inda sabo yasaba yasan yanda yarinyar nan ke crushing on that
guy like hell, not just her da many other ladies ma, sabida guy dinan cinikin dasukeyi yanzu a
eatery dinan is mind blowing, dazaran ansan yana ciki yammata zasu fara tururuwa suna
shigowa from no where so koshima he’s happy for her at least yau yakulata, he hope suyi
relationship dudda guy din dumping yammata yake anyhow kaman trash kuma ko ajikinshi dan
yasan yanda suke binshi, he just hopes wanan will not be one of his victims, dan yana using
babes kaman yanda yake using pen na rubutu idan yagaji da wanan ya yar yadauki sabo.
Tadade awajen ita kadai sai murmushi take tana daddaura handkerchief din akan fuskanta
tanajin dadi daga bisani wayanta yashiga kara, dasauri ta kalli wayan ganin Juliana Munari ke
kiranta yasa dasauri tadauka tana murmushi sosai tace “Hi Babe ya” daga tachan bangaren
wata yarinya tace “ina apartment dinki amman bakinan Ayshu where are you? Ba tundazu muka
gama lectures ba” murmushi tayi sosai tace “ina Cozy” dan jim Jully tayi tace “for Godsake
Aisha when will u get sense? Eh, look at the way Kabeer ke binki Ayshu yaron nan loves you
like a mad man amman kina nan kina stalking wanan heartbreaker da the worst part baimasan
kina existing ba” dasauri Aysha tai fari da ido tace “says who, wayace miki baisan ina existing
ba? Wlh yasani infect right now ma yanzu haka handkerchief dinshi nake kallo a hannuna it
feels warm and smells succulent, OMG it smells just like him wlh, I feel kaman Zayn dina ne
anan wajen” shiru Jully tayi saikuma chan tace “Ayshu I am ur friend and I will always tell you
the truth, forget that guy he’s nothing but a dream and face the reality face wanda ke sonki ba
wanan ba da kowa in our university sunsanshi ba wajen using yammata yay dumping nasu,
Ayshu enough of this stalking, sabida yaron nan kin chanza gida kin dawo apartment din
dayake, kin biya kudi double of the normal amout sabida acire tenant din dake zaune adakin
dakenan directly opposite nashi kinyi parking kin koma compund din, Aysha sabida yanda kike
stalking guy dinan kinsan karfe nawa yake tashi, karfe nawa yake fita gym, karfe nawa yake
shiga school, sau nake yake da lectures kinsan all his spots, grades dinki kullum low suke
karayi sabida soyayyan wanda baisan dakeba ke gabanki kum…” “Jully please enough, allow
me to leave my life, ana so by force ne banson KB ki rabudani da maganan shi, kuma zaki gani
Zayn will notice me and I will date him” dasauri Jully tace “dating Ayshu bakince min Islam
dating babu kyau ba” dan yatsine fuska tayi tace “Jully is because bakisan guy dinan bane
saisa, irinsu idan kika basu kanki ne kawai zasu zauna dake, dan gayu ne nafitina kaman ba
muslim ba, boko tashigeshi, I want him to be addicted to me kaman yanda yakenan addicted to
shisha, I am ready to give him anything, wlh Ina bala’in sonshi, just wait for me, ki dafa mana
abinci gani nan zuwa”
tana maganan ta katse waya shiru Jully tayi, at this point zubama Ayshu ido zatayi dan Allah
yama Ayshu taurin kai batajin shawara, kuma yaron nan will only break her heart, she will only
chop breakfast a hannunshi a nothing will happen yaron da har lecturorin su mata crushing suke
akanshi, anyway she just hope for the best.
Wuraren 6 ta shigo gidan, kana ganin gidan kasan na mugun yaran masu kudi ne, elevator ta
shiga zuwa floor dinsu sanan tawuce Dakinsu tana kallon nashi dakin datana gani tasan
baidawo ba daman baya dawo da wuri kullum sai 11 ko 12 nadare kuma kullu yaumin bata iya
bacci saitaga dawowanshi wata rana tai kuka duk randa zai dawo da mace wata tana kuma tai
murmushi, the truth is baifiye neman mata ba, wani zubin zaiyi 2month baidawo dakowace
mace ba wani zubin kuma saiya dawo da mace zasuyi kusan kwana uku ko hudu tare saikuma
shikenan bata kara ganinta dudda batasan dalili ba but kawai haka take gani, kuma baka taba
ganinshi da babe din dabataci sunanta babe ba, duk tana tunanin nan tana tafiya ne tana kaiwa
gaban Dakinsu tabude kofa tashige ciki tana ihu kitchen tafada tawani irin rungume Jully tana
nuna mata handky tace “Jully look” murmushi Jully tayi tana kallon handky sanan tace “Ya akayi
yabaki handky shi” nan tabata labarin from A to Z tana murna, murmushi Jully tayi tace “nidai
jeki wanka kizo muci abinci dan Jerry zaizo yadauken” gira daya Aysha tadaga mata tace “Iyye
love birds” tai maganan tana wucewa bedroom nata tashiga sanan ahankali ta ijiye handky kan
pillow dinta tareda shafawa sanan tawuce ta shiga wanka agurguje tana fitowa tazo sukaci
abincin tare sanan Jully ta shirya ta wuce abinta, komawa tayi ta kwanta kan gado tadauki
handky tana kallon shi kafin ahankali tace “Zayn! I love you so very much Zayn” rungume
handky tayi akirjinta tsamtsam tanaji kaman shita rungume, ahaka bacci ya kwasheta 11 dot na
bugawa ta bude idanunta tsam shi kanshi gangar jikinta yasaba da stalking nashi, fitowa falonta
tayi tai hanyar window ta ta tsaya dayake wutan dakin akashe ne ta tsaya tana kallon kofarshi
tana tsaye awajen kam wajejen 11:30 saigashi ya shigo yana tafiya nan cikeda isa akuma
hankali tundaga wajen saida kamshin dayake yadaki hancinta bude kofanshi yayi ya shiga
sanan ya maida yarufe kafin ya kashe wutan falon, murya chan kasa tace “good night My love,
asuba tagari” sanan ahankali tasauke window blind din tajuya takoma daki ta kwanta saikuma
kaman wani abu yafado ranta dasauri ta tashi tadauki handky tafada bayi ta wan ke shi tsaf
sanan ta shanya tafito tazo ta kwanta, shida dot tabude idanuwanta agurguje tafada bayi
tadauro alwala tafito sallan ma agurguje tayi bama ta tsaya cire hijabin ba tafito ta daga window
blind ta tsaya jikin window dan 6:30 dot yake fitowa tafiya gym, tana tsaye saigashi yafito cikin
kayan workout gajeren wando da singiletin Riga da safa da canvas, cinyanshi tabi da kallo
amunmurde kaman na yan wrestling sanan yaja kofan dayake da pin suke bude kofan yawuce
yana jogging yatafi abinshi murmushi tayi ahankali sanan tace “good morning baby na” sanan
tajuya handkerchief din tadauka tai ironing nashi, sanan ta shiga wanka tadade sosai abayin
sanan tafito tana ganin 8 saura da sauri tawuce wajen window Wuraren 8 yashigo yana zufa
murmushi tayi dasauri tajuya tashiga ciki wani hadaden short gown ta saka daya sauka daga
guwiwabta da kadan pink yamata kyau Wanan Karan batasa dankwali ba sai turaren data
feffesa sanan tai parking gashin ta in a stylish way sanan ahankali tadauki handky tana kallon
kanta agaban madubi ahankali tace “Ya Allah kadaurani akanshi” sanan ta zura slippers dinta
tawuce tafita falo ahankali tabude kofa tafito daga flat dinshi sanan kaman wacce abi yafashewa
aciki tai hanyar dakin shi kirjinta na daukan uku uku tawuce gaban dakinshi tadade atsaye kafin
ahankali ta danna door bell, ankai kusan 5min kaman bazaa budewa farat aka bude kofan
gabadaya dasauri tadaga kanta suka hada ido wani irin faduwa gabanta yake tana kallonshi
yana daure da bathrobe ajikinshi kirjinshi duka abude gashin kirjinshi akwance ruwa nabi sai
karamin towel a hannunshi yana goge kanshi da alamu daga bayi yake, da mamaki yadan
kalleta batare datai magana ba, lips dinta har rawa yake sanan ahankali tadaga hannunta dake
rikeda handkerchief din murya chan kasa tace “ahhhhhmmm dama, dama, I brought your
handkerchief back ne” tai maganan tana wani irin nishi sama sama kaman numfashinta sai
dauke, kirjinta nawani irin racing, this is the first time take ganinshi ahaka, ganin still kallonta
yake ba yabo ba fallasa kuma bai fasa abinda yake ba wato sharekanshi da karamin towel din
dayake rikedashi, yasa taji wani bala’in fargabanshi na cikata jin baice komiba dakyar tadaga
hannunta tamai pointing kofan dakinta dake kallon nashi tace “actually that’s my flat, yanzun
nan naganka shine nace uhmmm bari nakawo ma” dan yatsine fuska yayi amugun wulakance
ya kalli handky datake mikamai tundazu har hannunta na neman sagewa yace “I don’t need it,
discard it” yaja kofan zai maida yarufe da sauri tace “uhmmm wait please” chak ya tsaya yana
kallon fuskanta da fuskanshi dababu alamun rahama akai face dinshi looking kaman zai
maketa, tagefenshi taleka tana kallon indomie da taga yafito dashi zai dafa yacika ruwa a
babban pot yazuba albasa aciki ya fasa kwai aciki ruwan na kumfa sosai, dan murmushi tayi
cikeda shakkanshi tace “are you trying to cook indomie”? Yana kallonta still a bala’in wulakance
yace “uhn” kaman dole akace yay maganan, murya chan kasa cikeda shakkan abinda zatace
tace “that’s not how to, lemme cook it for you p…..please” wani kalan wahalallan tsaki yaja ko
kunyanta baijiba yace “banso” sanan yay slamming door din on her face batare dayama jira
maitake shirin cewaba, kuka taji yazo mata wuya tadaure tahanashi fitowa tadade ahaka
awajen sanan ahankali tajuya tawuce takoma dakinta zama tayi tana kallon handkerchief din
tama rasa meke mata dadi, tunda take bata taba shakkan wani namiji ba sai wanan menene
shi? Jibeta fa tanada kyau babu namiji da bazata iya daukemai hankali ba shi waye, enough of
all this, tashi tayi fuu tai kofan tabude tafice sanan direct tai dakinshi ta danna door bell baa
wani dauki lokaci ba wanan karan tabude kofan koyana expecting wani ne oho, churus ya tsaya
ganin yarinyar dazu, wani irin faduwa gabanta yayi ganinshi dagashi sai dogon wando na Jean
da Riga a hannunshi dabai Riga yasaba yanada wani irin broad chest ga cikakken shoulder
parts garai, kasa magana tayi saiwani kalan kallon kirjinshi datake lips dinta na rawa tana kallon
dark aroelas dinshi, ahankali tace “l…..l….ove……you…..Z….Zayn” Tundaga sama har kasa
yake kalleta sanan yace “ke kikama kanki” wanan Karan wani slamming kofan yayi on her face
saida yataba goshinta ahankali tajuya kaman an kashe mata yaran ciki tawuce side nata ta
zauna dirshan akasa, tana zaune awajen taji fitowanshi yafice, kiri kiri kasa zuwa class din
datake dashi tayi sabida yanda komi baya mata dadi.
ALKAWARIN ZUCIYA
PROMISE OF THE HEART
✍M SHAKUR
3️⃣
~Nigeria~
Wata babbar mace ce doguwa chocolate skin tsaye cikin wani lafiyayyen hadadden kitchen