Showing 18001 words to 21000 words out of 79746 words

Chapter 7 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

kalla guda biyar tana yagawa. Lokacin da ta shiga aji biyar na babbar
sakandire aka ba ta kallabin 'AMIRA' sabida hidimarta ga masallaci da kungiyar dalibai
musulmai da Uncle Junaid ya sa ta. Haka nan ita ce ja gaba a club din Uncle, watau English
club.

Kowa yasan Uncle Junaid a Minjibir, yasan shi tare da Maryam Bedi. Mairo ce mai rubutawa
club din DRAMA Uncle ya yi gyara a gabatar da ita. Wannan wata hikima ce da Allah Ya yi mata
wadda ke bai wa kowa mamaki. Sai dai iyaka kwakkwafinka da sa ido, haka nan so kulla karya
da sharri, ba zaka ce akwai soyayya tsakanin Junaid da Mairo ba, sai mutunta juna.
A wannan hutun na zangonsu na biyun karshe a sakandire da Mairo ta zo gida. Ta tarar da
ciwon kafar Inna ya yi tsanani. Ko bayan gida ba ta iya takawa sai dai ta ajiye (foo) a kusa da
ita. Don haka Mairo ta kara kadewa ta rame, ta kuma soma tunanin jingine makaranta domin
Innarta, tun tana tunanin Habibu har ta watsar ta hakura da shi, shi da ya ce shekaru shidda
kacal zai yi.
Ta tabbata inda duk Habibu ya ke tunda ya iya ya yi shekaru takwas bai neme su ba, to babu
shakka ya manta da su, ya samu sabuwar rayuwa a gaba. Ba zata taba amincewa da cewa
wani mugun al'amari ne ya faru da shi ba, tunda kuwa lafiya ita ke buya, amma ba rashinta ba.
Cikin watan January ne sanyi ya yi tsanani, hazo ya mamaye sararin samaniya, wanda duk ya
yi kuskuren fita babu shakka gashin ido dana girarsa fari fat za su koma. Mairo ta dawo daga
wani chemist inda ta amsowa Inna maganin mura tana tafe yafe da mayafin gyauton atamfa, ta
dunkule hannuwanta wuri guda.Tana ta sauri domin ta daura dafa-dukar taliya akan wuta,
wadda zata bai wa Innar, kasancewar ba komi ta ke iya ci ba, sai abu mai laushi, kuma mai dan
ruwa-ruwa, duka Mairo na kokari a kai. Ta kada ta raya da Innar ta kai ta asibiti, amma Innar ta
ki, ta ce, ciwon kafa ba a kanta tsoffi suka fara shi ba.
Ta doso zauren gidansu ke nan ta hange shi, tsaye a kofar gidansu. Sanye yake da farar shirt
(Armani) da dogon bakin wandon jeans ya daura jibgegiyar rigar sanyi mai hade da hula bisa.
Duk hazo ya ba ta tsararren gashin idonsa, girarsa da sajensa. Mairo ta ce a ranta, Allah Sarki
Uncle! Cikin wannan sanyin ya taho tun daga Minjibir sabida rashin komawata makaranta. Tun daga nesa ta ke yi masa murmushi amma shi fushi yake sosai. Ta kariso cikin nutsuwa,
tana karasowa ta russuna tana gayas da shi ya ce "Ni bana son wata gaisuwarki, kawai shiga
ciki ki hado kayanki ki zo mu tafi".
Ta girgiza kai kamin ta wuce cikin gidan ya bi ta a baya. Ta fara da sauke tukunyar daga kan
wuta, kana suka karasa dakin Innan da sallama. Shi kansa ya girgiza da ganin ramar da Innar
ta yi, tana kwance bisa katifar auduga ta amsa sallamar su. Nan ya gano amsarsa ta rashin
komowar Mairo makaranta. Jikinsa ya yi sanyi, ya daga manyan idanunsa ya dube ta suka yi wa juna kuri da ido.

Wani irin tausayinta ke ratsa zuciyarshi, wani sabon feelings ya shiga ratsa kowannensu. A
yanzu kam ji ta ke ba ta da kowa sai Uncle, babu wanda ya damu da rayuwarta sai shi. Duk da
Alhaji Abbas na iya kokarinshi akansu. Ta sauke kwayar idonta kasa a hankali, hawaye na disa
bisa tafukanta. Ya sauke nasa idon akan Innan cikin matsananciyar damuwa, ya ce "Sannunku
da jiki Inna, amma ya dace ki daure yanzun nan mu tafi asibiti".
Ta ce "Kayya Junaidu, wadannan kafafun bana jin za su kuma takawa a doron kasa. Akwai
likitan da ya isa ya raba tsoho da ciwon kafa? Sai Allah!"
Ya ce "Inna ku daina fidda rai da rahmar Ubangiji, babu ciwon da Allah Ya saukar, ba tare da ya
saukar dashi tare da maganinsa ba".
Ta ce "Ai ana shan maganin Junaidu. Watakila abin da nake gudu ne, dole sai ya faru…….."

Cikin matsananciyar damuwa ya ce "Wane abu ne kike gudu Inna?"
Ta ce
"Zaman Mairo da Iyalan Abbas". Daga haka ta yi shiru.

Daga shi har Mairo su ma shirun suka yi. Mairo ta rasa dalilin da ya sa Inna ta tsani iyalan Alhaji
Abbas, abin kam ya wuce na cewa wai don sun so su dauke ta ne. Watakila dai akwai wani
boyayyen abun don yadda ba ta sonsu ba ta shiga shirginsu, haka su ma.
Tun tasowarta ba ta taba ganin wata cikin matan Alhaji Abbas a gidansu ba, haka ita ma Innar
ba ta taba zuwa ba. Ita duk ba wannan ya dame ta ba, illa samun lafiyar Innarta. Ba ta son jin
irin maganganun da Innan ke yi a kullum suna kara tayar mata da hankali.
Junaid ya yi musu sallama ya tafi, washegari sai ga shi ya zo da likita har kauyen wanda likitan
gidan su ne. Ya dade yana duba kafafun Innar, ya rubuta magunguna masu inganci da allurai ya
ba Junaidu.
Ranar litinin ya dawo da magungunan ya nunawa Mairo tsarin shan su dalla-dalla. Ya je babban
dakin shan magani na kauyen ya tattauna da nurse da kullum zata zo har gida ta dinga yi wa
Innan allura.
Cikin sati guda kafafun Inna sun yi kyau, har tana iya zagayawa bayan gida. Ranar wata
alhamis da daddare suna kwance ta ce "Mairo”, tace “Na’am Inna” “ ni ko ba don wani abu ba,
da na ce Junaidu YA AURE KI".

Gaban Mairo ya fadi damm! Ta dade bata saisaita tunaninta ba, cikin dabarbarcewa ta ce "Inna
ke ko mai yasa kika yi wannan tunanin?
Uncle Junaidu Yayana ne, yadda na dauki Yaya Habibu haka na dauki Uncle, babu wani tunani
na daban ko ya ya game da shi a zuciyata.
Allah ne Ya hada mu, Ya hada zumunci mai karfi a zuciyoyinmu. Babu wani abu makamancin
wannan, sai mutunta juna".
Inna ta yi murmushi ta ce "Wannan zuciyar Mairo ce kike gaya mini, ba ta Junaid ba. Kin taba
ganin inda namiji zai yi ta wahala da mace da iyayenta babu gaira babu dalili? Idan kin ga kare
na sunsunar takalmi, wallahi dauka zai yi. Har yanzu ke yarinya ce da sauranki. In gaya miki
gaskiya na hango miki abin da ke ba ki hango ba, cikin kwayar idon Junaidu. Na hango miki abubuwa da dama, wadanda a shekarunki bazaki iya hango su ba. Babu komai
cikin kwayar idanunsa sai sonki da kaunarki, ke ma sai dai ki karyata zuciyarki da gan-gan,
amma kina son Junaidu. Adadin soyayyarka da mutum, yana da nasaba da yawan ambatonsa.
To gaya min tun haduwarki da shi, wace rana ce ba ki ambace shi ba? Ni ba wani abu na ce ba, kawai ina gano miki dacewar hakan. Ina gano miki mutumin da zai rike
ki da kauna ta gaskiya, har zuwa karshen rayuwarki. Wanda kuma shi ne wannan Junaidun.
Duk runtsi, duk wahala da tsanani kada ki bari a rabaku. Zan iya rantsuwa in fada miki Junaidu
sonki yake yi, idan kuma ba ki yarda ba, ki jira LOKACI ya fada miki……." Cikin gundura da zancen ta ce "Na ji Inna, amma don Allah don Annabi ki rufa min asiri kada ki
ce wai ya aure ni, ai kin zubar min da aji, sai ka ce wata wadda kike neman yadda za ki yi da
ita? Ni kam gare ni har gobe Uncle Junaidu Yayana ne".
Inna ta yi murmushi ta ce "Neman yarda zan alkinta rayuwarki nake yi mana, ga shi kuma ina
hango inda za a alkinta min ke".

Ta ce (kamar ta yi kuka), "Ni dai don Allah Inna ki bari……..".
Ta ce "Na bari, amma wata rana idan kina shayar da jaririn Junaidu, ki tuna na gaya miki
Junaidu na sonki, tun ba ki mallaki hankalin kanki ba".
Ta yi narai-narai da fuska, ta ce "Yanzu don Allah Inna ba zaki bar zancen nan ba?"
Ta ce "Na bari".

Ashe karshen hirar tasu ke nan. Inna Hure ta tako da asubahi cikin dafa bango domin yin
alwala, ta zo gittawa ta gefen da rijiyarsu ta ke, santsin cabalbalin gindin rijiyar ya kwashe ta ga
kafafun babu karfi, ta zame ta baya sai ji kake cindummmm….! Ta fada rijiyar ita da butar da ke
hannunta. Mairo wadda ba ta yi barci ba tun daren jiya, tana tunanin zancen Inna akan Uncle Junaidu, ta
kasa yakice al'amarin a zuciyarta. Haka kawai ta samu kanta da fatan ina ma ace zancen Inna
ya tabbata gaskiya? Uncle Junaidu ya so ta? Ita kuwa da wace irin sa'a zata yi a rayuwarta?
A farkon shekatun karatunta ba ta tantance wane ne Junaid ba, sai da girma da hankali suka
fara game mata jiki.
Uncle Junaidu na daya daga cikin irin mazan da suka yi karanci a wannan zamanin. Ta fannin
sura, halayya da kyawawan dabi'u.
Ta kasance ma'abociyar karance-karancen littattafan nobels' na Turanci. Littattafan Shakespear,
Wole Soyinka, Zainab Alkali, Abubakar Gimba, Ama Ata Aidoo da mabiyansu babu wanda bata
karanta ba. A duk lokacin da ta ke karatun, takan rasa dalilin da yasa ta ke danganta al'amarin
jaruman littafin da Uncle da ita kanta. Ba tasan dalilin da yasa a duk lokacin da aka ambaci
managarcin mutum mai kyawun sura ta ke cewa cikin ranta, "Kaman Uncle Junaidu".
Eh, Junaidu kyakkyawa ne, ma'abocin kwarjini, zati da kamala, wanda kwata-kwata bai dace da
matsayin da yake kai ba, wato malamin makaranta. Saidai da yake ance (ra’ayi riga ne)
Mutum ne da yasan mene ne 'dressing' wanda kuma kowanne irin kaya ke karbarsa, su dace da
da zubin halittarsa. Kai kace don shikadai aka kirkiresu. Junaidu idan ya shigo waje dole kasan
ya shigo, sabida kwarjininsa da cikar zati. Yana da fara'a amma yana da zucciya, abu kadan sai
ya bata mishi rai, haka abu kadan zaka yi ya wanke laifinka nan take daga zuciyar shi. Ba ta
san me yasa ba, komai Uncle ya yi burge ta yake koda kuwa ace fada ne yake mata. Ta sha
tambayar kanta, anya za a samu mutum mai kirkin Junaidu? Ta taba ce da Nabilah matar duk
da Uncle ya aura ta caba.
Nabilah ta ce "Dalili?"
Sai ta dauko mata littafin da ke boye a bayanta, GENDER STUDIES (wani bangare ne na
sociology mai banbance jinsin maza da mata). Shafin da aka fasalta halittar maza masu gamsar
da diya mace a shimfida, kuma irin mazan da matansu ba sa iya rabuwa da su komi wulakancin
da zasu yi masu. Tana jan layi-bayan-layi tana fassarawa Nabilah. Ta kare tana murmushi, ta ce "Edactly Uncle ko?"
Nabilah ta kama baki cikin mamaki, ita karance-karancen Maryam ya fara ba ta tsoro. Yadda ta
nakalci harshen Turanci ko goyon Birtaniya dole ya sara mata. Ta ce "Ke dai wallahi shegen
karance-karancenki sai ya lalataki. Yanzu ina ke ina littafin 'yan jami'a? Tukunna ma ina kika
samo shi?" Ta yi dariya cikin nishadi ta ce "A wurin Uncle na dauke rannan daya aikeni in kai mishi littattafi
staff-room na ganshi cikin lokarsa shi ma bai sani ba na dauke".

Nabilah ta ce "To wallahi ki bar karanta sociology za ki hauka ce".
Maryam ta ce "Da Uncle bai hauka ce ba? Ya gaya mini digirinsa ya yi shi ne kan sociology.
(With first-class honour) Nima insha Allahu abin da zan karanta kenan".
Nabilah ta ce "Sai ki yi azama, me ake da abin da zai juyawa mutum tunaninsa zuwa na Yahudu
da Nasara?"
Ta ce "Eh, idan kin amince da abin da suke fada ba? Ni dai ina so tunda Uncle shi ya karanta".
Nabilah ta kyabe baki ta ce "Kya karaci gulmarki dai, kina son mai abin kina cewa abin kike so".
Ta bude baki cikin mamakin Nabilah, ta suri bokiti ta yi waje tana yi mata dariya, tana cewa, "Ku
gama kumbiya-kumbiyar taku a yi candy mu zo Galadanchi mu kawo amarya….".
Ta bi ta da duka ita kuwa ta falla da gudu.

To sai ga shi yau Inna ta fadi wani abu kwatankwacin na Nabilah. Ta yi ajiyar zuciya, ta ce a
ranta "Shin ko dai Nabila da Inna gaskiya suka fada ne? I fall in lobe with Uncle Junaidu?
Neman tabbacin hakan abu ne mai matukar wahala a kwawalwarta".
Ta mike ta fito ganin shiru-shiru Inna ba ta dawo ba daga fita alwala har gari ya waye, gabanta
ya soma bugawa da sauri da sauri, cikin matsananciyar faduwar gaba. Ta duba gabas da
yamma, kudu da arewa, babu Inna babu alamarta.
Ta matsa kofar bayin ta kasa kunne babu motsin Inna. Cikin karfin hali da matsanancin firgici ta
ce, "Inna kina ciki ne?"
Shiru babu amsa, ta ce "Inna ki yi min gyaran murya idan ba za ki magana ba".
Nan ma shiru, sai amsa kuwwar raunanniyar muryarta da ginin kasa ya dauka, ya dawo mata
da abinta cikin kunnuwanta. A lokacin ne ta ankara da zanin da ke daure a jikin Inna wanda
karfen guga ya makale ya yage. Ba ta son gasgata abin da kwakwalwarta ke son ankarar da ita.
Ta matsa ga rijiyar ta leka jikinta babu inda ba ya kyarma. Kafafuwan Inna ta gani a sama,
maganar motsi kuwa babu shi a tare da su.
Sai ta yiwo waje da gudu tana ihu tana kururuwa a kawo mata agaji, kanta ko kallabi babu,
kafarta babu takalmi, hawaye shabe-shabe a idanunta. Abinki da jama'ar kauye, ma'abota
hadin kai da taimakon junansu, nan da nan gidan ya cika makil da dan Adam, makotansu da
abokan arziki kowa yana ta Allahu Akbar! Hure Allah Sarki!! Nan da nan wasu samari majiya karfi suka hada doguwar igiya suka cilla, biyu suka kama
hancin suka rike, daya ya bi ya dauko Hure suka fiddo su.
Mairo ta daga ido ta ga wai yau Innarta ce wannan babu numfashi, ta tafi har abada ta barta.
Innan da ta rage mata a duk fadin duniya, ita ma ta tafi. Sai ta fadi, wuni guda cur ba tasan inda
kanta yake ba.
***

F
arkawa ta yi ta samu kanta a gidan makociyarsu Karime. A lokacin har an yi wa Innar sallah, an
kai ta makwancinta. Mairo ta ja jiki ta takure wuri guda sai a lokacin kuka ya zo mata. Ta yi ta
kuka kamar ranta zai fita. Karime na ba ta baki tana rarrashinta. Ta ce, "Wannan ba shi ne
karshen rayuwarki ba Mairo. 'Ya'ya nawa ne iyayensu suka mutu tun a wurin haihuwarsu, kuma
sun rayu? Ki godewa Allah da Ya nufe ki da tashi tare da su, kika san dadinsu. Ni kin ganni nan
ban taba sanin uwata da ubana ba, cikina da wata biyar Babana ya rasu, lokacin haihuwata
uwata ta rasu, amma gani nan da nawa 'ya'yan goma sha uku. Ina yi miki ta'aziyya Allah Ya
jikan Hure, mutumiyar kirki, mai alheri".

Mairo ba ta fasa kukanta ba, addu'a ta ke Allah Ya dauki ranta ita ma ta huta, maraici na uwa da
uba ba karamin abu ba ne. Tunaninta shi ne, ina zata kuma samun mai kaunarta a duniya
kamar iyayenta? Ina zata je? Da wa zata zauna? Mene ne amfanin sauran rayuwarta? Ba ta da
kowa ba ta da komi sai Allah, domin ta fidda lissafin Habibu a zuciyarta. Ta samu kanta cikin
kullatar Yaya Habibu, kullata mai tsanani. Ba ta ga ranar da haihuwarsa tai wa iyayensu ba.
Karime ta shigo da dambun masara a kwano da ruwa a kofi, ta sa ta gaba lallai sai ta ci. Ta
dauki loma ta kai bakinta tamkar mai taunar madaci, haka ta ke taunar abincin. Ta tsame
hannunta tana sharce wasu dunkulallun hawaye da suka zubo mata. A lokacin ta tuna babban
kuskurenta a rayuwa, ba ta yi wa Inna addu'a ba. Ta mike ta je ta dauro alwala ta zo waje mai tsabta a dakin Karime ta shimfida sallaya, ta
suturce jikinta ta tayar da sallah. Tana sallah hawayenta ba su bar ambaliya ba. Da ta idar ta
bude Alkur'ani mai Tsarki ta shiga karantawa Inna suratul Yasin da suratul Rahman ta rufe da
(du'a'ul mutawaffa) tana addu'ar Ubangiji Ya yi mata masauki da aljannah. Ranar kwana uku da rasuwar Inna Hure ta tattaro duk ajiyarta kudin mota kawai ta barwa kanta,
ta ba wa Karime aka yiwa Inna sadakar gumba, waina da kosai. Mijin Karime da Dagacin
Gurin-Gawa suka zo suka same ta har dakin Karime suka fara da yi mata ta'aziyyah, sanan
Dagaci ya ce sun zo ne su kai ta gidan kanin mahaifinta su damkata a hannunsa, wannan ita ce
amanar da za su sauke.
Hankalin Mairo ya tashi, zancen Inna ya dawo mata sabo tar! A kwanyarta, "Wata kila abin da
nake gudu ne dole sai ya faru... Zaman Mairo da iyalan Abbas".
Ta sunkuyar da kai tana kuka, ta ki ba su amsa, Malam Tanimu ya ce "Hakuri za ki yi Mairo,
mutuwa riga ce akan kowa, tafiyarki birni ya zama dole, domin ba ki da wanda ya fi shi. Sannan
Abbas mutum ne mai ZUMUNCI ki dubi yadda ya rayu yana kyautatawa mahaifinki. Ina da
yakinin zai rike ki da amana tamkar mahaifinki, har zuwa sanda zai miki aure". Sai ta mike cikin karfin zuciya, ta yafa mayafinta ta sa takalminta. Karime ta rakata gidansu tana
hada kayanta tana kuka.
Ta tattara zannuwan Inna da kayayyakinta ta sa a wata tsohuwar akwatun karfe ta rufe, ta tura

karkashin gadon bononta. Ta tattara 'yan kudaden Innar irin wanda Junaidu ke ba ta ne a duk
zuwan da ya yi, da kudin motar da ta warewa kanta duka ta zuba cikin jakarta ta makaranta.
Suka fito Karime ta datse dakin da kwado, tana tafe tana waiwayen dakunansu da madafinsu
da ta ke jin tana yi masu kallon karshe ne, wasu hawayen suka zubo. Tana bayan motar Dagaci wata (mitsubishi) mai hayaniyar tsiya, in banda karar injina da
salansa ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login