Showing 42001 words to 45000 words out of 79746 words

Chapter 15 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

da yanayin maganarta kasan kuruciya ke
dawainiya da ita. Ta ce "Sabida mai ba kya sonshi Mairo?
Ga shi kyakkyawa, son kowa, kin wanda ya rasa. Ga shi da ilimi kamar Yaya Habibun da kike
cewa yana burge ki. Yana da mata Baturiya, amma ya tsallakota ya zo ya ce yana sonki. Zai iya
rabuwa da ita sabida ya aure ki. Ga shi da kirki, ga addini. Ke kuwa mai kike nema a da namiji
da ya wuce wannan?" Sai Mairo ta sa kuka. Ta kwantar da kai a cinyoyin Dina, tana kuka mai tsuma zuciya.
"Na kasa mance Uncle Junaidu ne Aunty Dina. Na kasa mance dumbin alherin da ya yi min a
rayuwa. Shi ne tsanin duk wani matsayi da matakin da nake kai a yau. Idan na auri wani ba shi
ba, na ci amanarsa…...."
Dina ta katse ta "Akwai hanyoyi da yawa da zaka saka wa mutum alherin da ya yi maka ba dole
sai ta hanyar aure ba. Misali shi ne, ka dinga binshi da kyakkyawar addu'a ba tare da shi din ya
sani ba. Wannan addu'ar Allah Ya yi alkawarin karbarta. Kada ki yi mamakin zuwa yanzu shi
Junaidun ya samu wata da yake so ya aura. Ni na kasa gane kan wannan soyayyar da kike yi wa Junaid, maras dalili. Kin ce bai taba cewa
yana sonki ba. Kin ce ba ku yi alkawarin aure ba, kin ce yasan gidan Baffa, amma bai neme ki
ba. To ki gaya min wacce hujja gare ki da zata tabbatar da cewa yana sonki?
Ba ki san akwai masu taimako sabida Allah ba, ba don a aure su ko a saka musu da soyayya
ba? Haba Mairo, ki yi tunani mana? Ki yi aiki da hankalinki. Ki so mai sonki a zahiri da badini. Ki
yi aure saboda Allah da raya sunnar ma'aiki, amma ba don abin da zuciyarki ta afu akai ba.
Mai yiwuwa ne shi wannan abun da kika kwallafawa ran ba alheri ba ne a gare ki, wanda ba kya
so din shi ne alherin. Idan kika fauwalawa Allah a hankali za ki so abun, tunda shi ma Junaid ba
lokaci daya kika fara sonshi ba, so na soyayya, kin ce sai da tafiya ta yi tafiya kika mallaki
hankalin kanki, sabida fahimtar halayenshi da kika yi. Shi ma Amiru a hankali za ki fahimce shi, kuma ki so shi wallahi fiye da son da kike wa Junaid
ma. Ba ki ci amanar Junaid ba, ba ki yaudare shi ba tunda ba alkawari kuka yi ba. Iyakar
soyayya ta gaskiya kin yi wa Junaidu, ko ba ki aure shi ba Allah Ya shaida ya yi alkawarin sanya
masoyan gaskiyan da suka mutu ba tare da sun auri juna ba a aljanna. Ina tunanin Junaid ya yi
abin nan ne da Hausawa ke cewa, "A BARI YA HUCE... SHI KE KAWO DA RABON WANI".

Ta dubi Dina sosai, ta ce "Idan haka ne Aunty Dina, kema kin yarda Uncle Junaid yana sona?
Furtawa ce bai yi ba, kamar yadda Inna da Nabilah ke cewa?"
Gyada kai Dina ta yi, ta ce "Eh, yana sonki, amma ya bari YA HUCE... Don babu wata mu'amala
ta mutumci da tausayi tsakanin mace da namiji sai SOYAYYAH!
Idan ma mutumcin ne da farko, to daga baya rikidewa ya ke ya koma soyayya. Kuma dama ita
irin wannan dadaddiyar soyayyar ba a fiya auren juna ba. Wasu ma har su mutu, ba sa kara
ganin juna.
Wasu kuma daya ne yake mutuwa ya bar dayan cikin soyayyar, kuma babu yadda dayan zai yi,
a karshe dole zai hakura ya auri wani, wasu kuma hakura suke da auren har zuwa sanda nasu
ajalin zai riske su.
Amma Ubangiji ba ya son hakan, don haka bana son ki zamo daga cikin wadanda za su

kyamaci sunnar Ma'aiki sabida soyayya. Manzon Allah (S.A.W) cewa ya yi "Ku yi aure don ku
hayayyafa... Bai ce ku yi aure don soyayya ba. Karewama, duka matan ma'aiki da dalilin da ya
yi sanadin da ya aure su, ba soyayya ba.
Soyayyarsu tana kafuwa ne a hankali cikin gidan aurensu. Ki yi koyi da Nana Khadijah wadda
halayen amana na Ma'aiki ya kwadaitar da ita ga son aurensa, shi ma kuma ya aure ta don
dukiyarta, addininta da nasabarta. Ki auri Amiru don yana da nasaba, addini, ilmi da arzikin ma,
ku raya sunnah ku haifi 'ya'ya ku yi musu tarbiyyar musulunci in gaya miki karshen soyayya ke
nan.
Ke nan har wata soyayya kika sani ko halarci? Wallahi HALACCI kike yi mawa ba SOYAYYA ba.
Amirun shi kike so da gaske, na gani a kwayar idonki, na gani a gangar jikinki. Kina jin
abubuwan da kike ji kan Amiru a Uncle Junaidun? Kina neman Junaid ya aure ki ne don ya
tallafi rayuwarki a lokacin da kike neman matallafi, amma ba don kin san hakikanin me aure ya
kunsa ba.
Kina so ki ramawa Junaid halaccin da ya yi miki ne ta hanyar 'aure' don da shi kika saba, ya
sanki, kin sanshi, a tunaninki wannan shi ne karshen soyayya, to ba shi ba ne, soyayyar aure
daban ta ke, Allah ke hadata, kuma bata fassaruwa.
Haka ita ma kauna daban ta ke, sai kin auri Junaidun za ki ji kamar kin auri Babanki. A sa ma
shi din ya ce yana son naki, balle bai ce ba. Tsayin shekara biyun nan wallahi da duk inda kike
ya neme ki, da fa ya damu da ke.
Ita zuciya an halicce ta ne da son mai kyautata mata, wannan shi ne tsakaninki da Junaid ba
soyayyar aure ba. Idan kuma mata sun fara zuwa neman aure ne, to sai mu je gidansu mu
neme shi mu kai kudin aure, mu gaya mishi yadda kike sonshi har kina gayawa masu sonki da
auren, ke ba kya sonsu, sabida kar ki ci amanar soyayyar sa da ya ba ki…..." 8/2/21, 10:31 PM - Kawata: G
Ala dole ta murmusa, don tasan zambo ne take mata. Duka wannan bata lokacin da Dina ta yi
tana bayani, ba duka abin da ta ce ne ta yarda da su ba.
Ta dauki Dina a matsayin mai campaign ga Amiru, sabida shi ta sani, shi ne mai irin tsarinm
rayuwarsu. Ita kudin Yaya Habibu ma tsoro ya ke bata, balle na Amirun da ta sha jin suna cewa
yana world bank, karewar Barclays.
Ta yarda ta hakura da Junaid sabida kwararan hujjoji masu karfi da kowa yake gaya mata, hatta
Nabilah. Ta ce da ita lokaci ya yi da ya kamata ta manta da soyayyar da ta ke wa Uncle Junaid
ta yi aure. Ta dubi irin auren da ita ta yi, amma ga shi ya zame mata ALHERI, don yanzu ba
abin da ta ke so a duniya sama da mijinta, kuma shi ma hakan har ga albarkar haihuwa. Ta sauke ajiyar zuciya, ta koma ta kwanta a gadonta, ta ja bargo har kanta. Barci ta ke so ya zo
ya dauke ta, amma ya ki zuwa. Al'amarin na neman tarwatsa mata kwakwalwa, tareda wargaza
mata tunani. Tana son ta yarda da Dina, halaccin da ke zuciyarta na karyatawa. Amma
abubuwan da ta zana ai duk haka suke, zata je neman auren Uncle Junaid ne? Ko haka zata
kare da zaman jiran tsammanin warabbuka?
Zata iya ci gaba da zaman jiran ranar da Junaid zai neme ta, ya bayyana mata soyayyarshi, ya
ba ta uzurin da ya hana shi yin hakan har nan gaba da abada. Amma ba zata iya jure bukatar
gangar jikinta da zuciyarta ba, kamar kowanne lafiyayyen dan Adam. Idan haka ne tana bukatar
aure, domin kare kanta daga ZINA, da sauran ayyukan ALFASHA, cikar mutunci a idon duniya,
da karuwar matsayi a fadar Ubangiji.

Wayarta da ke karkashin filo ta soma dan kidi mai sanyi, alamar shigowar sako (text). Cike da
mamakin wanda ya yo mata sako a dai-dai wannan lokacin, karfe biyu na sulusin dare
agogonsu na can. Ta mika hannu ta lalubo wayar ta danna, ba tasan lambar ba, don bakuwa
ce. Ga abin da ke rubuce.
'... When life change, and we go our separate ways, U will still be in my heart till my dying
days... My world has never meet a person like U……...!
(A yayin da rayuwa ta canza , ni da ke muka bi hanyoyin mu mabambanta (muka rabu), za ki
cigaba da zama a xuciyata har karewar numfashi na. Duniyata bata taba haduwa da mutum irin
ki ba).

Haka ta sa sakon a gaba, tana ta karantawa. Har aka yi kiran assalatu. Don ta tabbatar ba kowa
ba ne, Amiru ne, duk da bai sa suna ba. Allah sarki ko YA HUCE ne? Ta fada a fili. Tana so ta
ba shi amsa, ba ta san me zata ce masa ba.

Da safe ta ke nunawa Dina, ta karanta, ta yi dan miskilin murmushinnan nata, ta ce.
"Ke kuma kika ce mene?"
Ta zumburi baki. "Ni ko kulasa ma na yi?"
Ta yi dariya, ta na kwaikwayon ‘yar muryar ta tace, "Haba Mairo? Yi hakuri ki dan kula sa. Kinga
shi ya yi fushin amma ya sauko, saboda ya gane ba son sa ne ba kya yi ba, kawai ke mai
aminta amana da alkawari ce!".
Ta yi dariya har kumatun ya lotsa, Dina kam akwai shegen wayo, kanwa ce uwar gami.. Ta ce
"To me zan rubuta?"
"Ki ce kawai ya zo yayi joining dinmu break fast…..".
Ta rubuta ta tura, amsar da ya ba ta ta sata yin murmushi. Domin ya ambato rabin-ranta (uncle
Junaidu).

"...A'ah kirawo Junaid….".

"He is far-away...!!"(Amsar Mairo )

"And am not closer too... am far-away either, and I'll not come back...!!! On my way to Detroit
Metro…...".

Hankalin Mairo yayi mummunan tashi, da sauri ta jefar da wayar, da gudu ta yi daki ta dauko
mukullinta, Dina na kira amma ba ta juyo ba, cikin rishin kuka ta ce.

"Shi ma zai tafi ya barni, kamar yadda Junaid ya gudu ya barni. Bayan sun kimsa min
soyayyarsu. Bana son in samu wannan heart break (karyewar zuciyar) a karo na biyu".

Dina ta ce "Bishi Mairo, shi ne ZABIN ALLAH!!"

Gudu ta ke shararawa akan titin da zai kai ta airport din Detroit. Cikin kankanuwar motarta GMC
Terrain. Hawaye na sauka akan kundukukinta. Da gaske Dina ta ke, Wannan ita ce soyayyah!
Da gaske Dina ta ke, Amiru shine zabin Allah!! Da gaske Dina ta ke da ta ce ta kama mai sonta,
ta rabu da JIRAN TSAMMANIN WARABBUKA. Ta karbi 'Soyayyah' a hankali zata rikide ta
zama 'Kauna'. To gashi soyayyar ma zata tafi ta barta da tsammanin warabbukanta wanda bata
fata…….…

Koda ta iso airport din ko kulle motar ba ta yi ba, a jikin motar ta bar mukullin. Da gudu ta sheka
cikin reception tana dube-dube, babu Amiru, babu ko mai kama da AMIRU. Ta karasa terminal
bayan ta hankade ma'aikacin da ke kokarin hanata shiga. Dai-dai sanda aka rufe kofar jirgin
(Lufthansa), wanda zai tashi zuwa kasarmu mai dumbin albarka. Ba da jimawa ba kuma ya
soma ruguginsa mai gigitarwa bisa kwaltarshi. Kafin ya dai-daita sosai, a sararin samaniya.

Mairo ta durkushe a nan tana kuka, kukan da ta dade batayi irinsa ba tun bayan rashin
BABANTA da INNAR TA. Fita yake tun daga karkashin zuciyarta. Amiru ya tafi tareda dukkan
farin cikin da ta samu cikin Michigan wanda Habibu ya dade kafin ya assasa. Bai shigo
rayuwarta da sauki ba ashe! Ashe ya shigo ne don ya rusa komai . Ya tafiyar da sauran karfin
zuciyarta. Ya dawo da rayuwa unbearable kamar Uncle Junaidun? Meyasa ita ba ta da sa’a ko
kankani a soyayya ???.
Ji ta yi kamar an tsugunna a gabanta, kamin ta dago kuma, an kai hannu a hankali an dafa
kafadarta. Don haka ta dago idanunta jage-jage da hawaye... don ganin ko wane ne
wannan???

Masha Allahu La Kuwwata Illa Billah!
Mu biyo Mairo da Amiru da Junaidunta a littafi na uku. Kafin nan ina sauraron ra'ayoyinku kan
jaruman namu, AMIRUN ko JUNAIDUN???
Maman SAFAH da MARWA ce.

07030137870
8/3/21, 12:25 PM - Kawata: 444
Ta dago idanunta jage-jage da hawaye, don ganin ko wane ne wannan? Da haka kawai zai zo
ya dafata? Ko ta ce da wani tana neman taimako ne? Wa za ta gani? Yaya Habibu ne!
Cikin matsanancin mamaki ya ce, "Mairo?"
Ba ta amsa ba, illa ta bi shi da kallo, da jajayen, idanunta. Ya sake cewa
"Me ya kawo ki nan? Ina za ki je?"
Nan ma shiru ta yi masa, sai kallonsa ta ke kamar ta rufe shi da duka don haushi. Ya ishe ta da
tambaya, ya barta ta ji da kukan zuci, da takaicin da ya dame ta. Don ji take kamar Amiru ya
bula mata kura, ya ja motar rayuwarshi, ya barta.
A nashi bangaren, shima Habibun, haushi ne ya kama shi, ya ce
"Kina ji ina magana kin yi kunnen uwar shegu da ni? Na ce me ya kawo ki nan, kuma gurin wa
kika zo? Ina zaki je?"
Nan ma shiru ta yi masa, kamar da dutse yake magana, kuma ba ta dauke idanunta daga
kanshi ba. Ta kafe shi dasu kurrrrr! Kamar shi ne ya kori Amirun. Iyakar fusata Habibu ya fusata,

ya fizgi hannunta suka fito harabar adana motoci na airport din, yana baza ido don gano inda ta
yi fakin.
Daga can ya hango motar ta yi mata wani banzan fakin a inda aka rubuta no parking, Security
ne cikin fararen kayan ma'ikatan gurin tsaye jikin motar, wato sun kamata.
Ya yi tsaki, tsut…, suka doshi wajen, har yanzu yana rike da hannunta, sai janta yake kamar
kayan wanki. Ya mika hannu ya zare makullin ya soma ba su hakuri ya nuna musu Mairo ya ce
ga dukkan alamu ba cikin nutsuwarta ta ke ba, su yi mishi uzuri su ba shi motar.
Abinka da malam bature da bai san cin hanci da rashawa ba, gami da bin ka'ida da dokar duk
da aka shimfida masa, kememe sun ki yarda, sun dage dole su dangana da ofishinsu in har
suna son motar su, don a ka'ida mai matsala a kwakwalwa, ba a yarda ya tuka abin hawa ba,
ya ce lafiyarta kalau, tension ne kawai, suka ce idan haka ne ke nan tana sane ta karya musu
doka? Don haka dole su dangana da ofishinsu, amma ba zasu bada motar ba.
Cikin matsanancin fushi, Habibu ya dubi Mairo
"Kin kyauta, kin ga abin da kika jawo min ko?
Yau shekaruna goma cur cikin kasar America, ban taba zuwa ofishin 'yan sanda ba, don haka
sai ki bi su ku je, ki yi musu bayanin dalilinki na karya dokarsu, tunda ni kin yi min banza, sai ki
je ku karata.......”
Ya cika hannunta zai tafi, ta riko bayan rigarsa tana kuka. Ya ce
"Wallahi bazan je ofishin 'yan sanda ba, sai dai ki hakura da motar, ki bar musu mu tafi, kuma
wallahi-wallahi ba zan sake siyan wata ba".
Ta ce ta yarda, don haka suka bar motar a nan, suka nufi motar Habibun.

Allah Sarki, dan uwa rabin jiki! Sun yi nisa sosai danja ta tsaida su, ya saci kallon Mairo da ke
kujerar gefensa, ya ga har yanzu kuka ta ke mara sauti, ta rufe fuska da mayafinta. Sai ya
hadiye fushinsa, ya soma lallashinta cikin dabara.
"Ni dai idan don na tambaye ki inda za ki ne kike min wannan kukan, to ki yi hakuri. Mantawa na
yi, ashe fa Amiru ya fada min ba kya son tambaya.
Ban da abinki Mairo, idan wajen Junaid kike son zuwa, jirgi ya tashi ya barki, ai sai ki fada mini,
na yi miki booking din wani, amma ba ki sunkuya cikin dubban mutane kina rafka kuka ba,
kamar wata mai tabin hankali. Yana ina Junaid din? Nigeria ko Russia?"
Cikin kuka ta ce
"Ni fa tunda na yi maka wancan alkawarin, ban sake tuna zancen Uncle Junaid ba".
Ya ce "To ina za ki? Ko AMIRU kika biyo?"

Hantar cikinta ta karta, ta rasa me zata ce masa, don haka ta ja bakinta ta yi shiru. Habibu ya
kuta ya ce
"Hakan da kike yi, kina ganin mutumci za ki sayawa kanki?
Shi wancan bai ce yana sonki ba, sabida neman gindin zama kika kwashi jiki kika je gidansu
don rashin hankali da rashin mafadi. Shi wannan da ya ce yana sonki, kin ce ba kya sonshi,
sabida kar ki ci amanar wanda bai ce yana sonki ba. Ya hakura ya bar miki kasar ma baki daya
ba garin ba. To uban me kika biyo shi ki mishi? Da kin same shin me za ki ce masa? Yi hakuri na tuba, ka zo
ka aure ni ko me? To ni bana son rashin hankali da rashin mutunta kai, aikin zubar da kima, da

wulakanta kai. Kin riga kin ce ba kya sonshi, to a barshi a hakan. Allah Ya kawo miki wanda kike
so.
Don wanda ya ce ba ya sonka tun farko, daga baya ya dawo ya ce yana sonka, to akwai
dalilinshi na yin hakan. Wato za ki yi A RASHIN UWA... akan yi UWAR DAKI...? To ba da
abokina ba!
Idan auren kike so ki yi, ki je ki nemo Junaidun, tunda ba kya son karatun da nake sonki da shi.
Abu na dan lokaci kalilan, ba zaki maida hankali akai ba, mazan nan da kike gani, dukkansu
matsala ne, shi kansa auren idan ba a tsaya anyi shi cikin nutsuwa ba, babu inda ya ke zuwa.
Don haka yarinya, kama kanki. Wayar ma daga yau ba zaki sake rikewa ba, kamar yadda babu
ke babu tukin mota. To kin ji".
Dai-dai lokacin da ya yi fakin a harabar gidansu, ya juya bayan motar ya dauko falmaran din
suit' dinshi da wayoyinshi ya fito, ita ma ta fita, ba tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login