Showing 63001 words to 66000 words out of 79746 words

Chapter 22 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

mazauni ba ne, sannan ko da wasa Hajiya
ba ta yi gigin sanar da shi abin da ta yi ba, don tasan bazai goyi bayanta ba. Sai su Khalisa da
Nina wadda ke aure a Lagos sune 'yan abi yarima a sha kida, duk suka yi ta tsalle.
Nina ta ce
"Mun gama da wannan, saura 'yar kauyen Gurin-Gawa, don Allah Hajiyarmu ki yi mana
waje-road da ita".
Hajiya ta ce
"Ku barni da su, duk na ishe su, ko ba ta yi waje ba, ai ta yi zaman boranci idan na aura mishi
wadda zata cika min gida da 'ya'ya".
*****÷
8/6/21, 5:15 PM - Kawata: F
An debi watanni biyu kwarara, Hajiya na tarairayar danta don dai ta wanke dattin ta dake

idanunshi, tana kuma nuna kulawarta akan Mairo, wadda ita kuma ba ta san tana yi ba,
karatunta kawai ta sa a gaba.
An yi bikin su Sabah tun shekarar da ta gabata, bayan sun kare karatunsu. Don haka yanzu
sassan Hajiya babu kowa, daga ita sai 'yan aiki. Watakila hakan ne ya sa ta kwallafa ranta ga
son ganin 'ya'yan Amirun, tunda sauran jikokinta iyayensu maza ba za su ba ta ba.

Yau da ya shigo gaishe ta da safe, cikin sakin fuska ta amsa. Bayan sun gaisa ta janyo wata
dirkekiyar jarka irin wadda ake zuwa da zam-zam daga Saudiyyah din nan, cike ta ke taf da
ruwan rubutu bakikirin da shi ta girgiza ta tsiyayo a kofi ta mika mishi.
"Ungo shanye ka ba ni kofin".
Ya ce
"Na mene ne Hajiya?"
"Maganin sammu da tsarin jiki ne, ko ba zaka sha ba? Idan ka shanye shi duk wani makaru da
ke jikinka zai karye, don haka shanye ka ba ni kofin".
Bai yi musu ba ya karba ya soma sha a kyankyame, don kam shi Amiru tun fil'azal mutum ne
mai kyankyami matuka, ko (spring water) ba kowanne ya ke sha ba.
Tun yana kyankyami har ya zamo masa jiki. Don ka'ida ne kullum ta Allah ya zo gaishe ta, sai ta
cika kofi ta ba shi tsawon sati biyu suna hakan. Ya ji ya fara jin wasu sauye-sauye a zuciyarshi
akan Mairo, sai dai ko kusa bai alakanta hakan da cewa rubutun da Hajiya ta ke daddaka masa
ba ne. Yau da yamma da ya dawo daga ofishin Daddy inda ya koma zuwa yana taya shi da wasu
ayyukan, sabida nauyin Habibu da yake ji ya sanya alakarsu yanzu ta ja baya.
Duk da cewa shi Habibun a nashi bangaren, ya maida komi ba komi ba, amma Amirun gani
yake Hajiya ta riga ta gama tozarta shi a idon Habibu, ta yadda har abada ba zasu koma kamar
da ba.
Ya yi sallama Hajiya da ke harde cikin kushin tana sauraron labaran Al-Jazeera ta amsa mishi.
Ya samu kujera mai fuskantarta ya zauna. Ya dan zamo daga cikin kujerar yana gaishe ta.
Ta amsa mishi da sakakkiyar murya, can kuma ta ce.
"Anya Amiru, rayuwa zata yiwu da hakan? Ace mutum ya yi ta zama, ba ya tunanin samun dan
kansa, duk tsararrakinka daga masu 'ya'ya uku sai masu hudu amma kai ba abin da ya dame
ka, sabida idonka ya rufe da son matarka. Alhalin kuma ba zata iya ba ka sanyin idanu ba, sai
dai a cika maka masai da kashi, to wallahi bazan yarda da wannan ba". Ya dago idanunshi a kankance ya dubeta.
"Hajiya mun isa mu ba wa kanmu abin da Allah bai ba mu ba ne? Sannan ba ki san matsalar
nan daga gare ni take, ko daga gare ta ba? Don haka bai kamata ki dau zafi akan al'amarin ba,
don Allah Hajiyata".
Ta ja dogon tsaki tsiiit!
"To ku je asibiti mana? Ko haka za mu yi ta zama cikin jiran gawon shanu? Ai gara a banbance,
don a san matakin dauka".
Da wannan tunanin na maganganun Hajiya ya kwana, har ya soma jin kamshin gaskiya a
cikinsu. A shekarunshi ya ci ace shi ma ya aje masu yi mishi addu'a. Har ya soma zargin Mairo
ko tana amfani da 'contraception'. Tunda dama ai tun farko ba sonshi ta ke yi ba.
Ya yi gaggawar kwabar zuciyarshi daga wannan mummunan zargin da ta darsa mishi. Ya yarda

da matarsa 100% (Azzannu zambun, wa lau kana hakkun), sai dai rashin damuwarta akan
al'amarin ma ai abin dubawa ne, bokonta kawai ta sa a gaba, da son ganin kwalayen ilimi, tare
da son hango kololuwar biro da takarda.

Ta murda kofar ta shigo cikin sallama cikin sassalkar doguwar riga baka sid, kirar Dammam,
fararen duwarwatsu na ta walwali a jikinta, sannan ni'imtaccen kamshinta na din-din-din ya doki
hancinsa.
A kwance yake 'flat' bisa makeken gadonsu ya lumshe ido kamar mai barci. Har ta zauna gefen
kafafunshi ta soma ja mishi yatsu bai juyo ba. Haka nan ya samu kanshi da jin haushinta babu
gaira babu dalili. Ta yi kiranshi cikin tattausar murya, amma bai bude idonshi ya dubeta ba.
Karewa ma kara runtse idonshi ya yi, tareda janye kafarshi dake ciin hannunta, don ba ya son
ganinta, ba ya son kamshin turarenta.
Ta yi wa kanta kyakkyawan matsugunni a kirjinshi, ji ya yi kamar ta dosana masa wuta. Ya yi
azamar angijita ya ce
"Leave me alone, please!"
Cikin mamaki ta ke dubanshi, idanuwanshi sun hargitse kamar ba Amirun nata ba. Ta ja gefe ta
zauna jikinta yana rawa, don ko kadan bai taba yi mata magana cikin tsawa irin haka ba,
sannan ita a rayuwarta ba ta iya tashin hankali ba.
Zuwa can kuma ya mike ya soma shiri, ya dan juyo a kai-kaice ya kalle ta.
"Ki shirya, asibiti za mu".
Ta yi ta maza cikin sanyi ta ce.
"Waye ba lafiya?"
"Idon matambayi ne".
Abin da ya ce da ita ke nan.
Kamar ta ce, 'to ba zani ba', amma kwarjinin Amirun da kimarshi dake cikin idanunta ya hana.
Soyayyar da ta ke mishi wata kaddara ce daga Allah da ita kanta bata san adadin ta ba. Ta
yadda ba ta iya fushi da duk abin da ya yi mata. To balle ma bai taba yin ba. Idan haka ne ya
dace ta yi mishi uzuri, ba kullum ne mutum yake kasancewa cikin dadin rai ba.
Suna tafe a motar amma ba mai ce da dan uwansa uffan, kowanne abin da yake sakawa a
zuciyarsa daban ne da na dan uwansa.
Tunanin Mairo shi ne, shin laifin me ta yi wa Amiru haka da zafi, da har ba zai iya budar baki ya
fada mata ba don ta gyara?
Shi kansa Amirun ya rasa laifin da ta yi mishi ya ke ganinta bakikkirin da jin zafinta babu gaira
babu dalili. Amma ransa na gaya masa rashin haihuwar tane, yazo wani limit na kasa jurewa.
Har suka iso babban asibitin Abuja, kalma daya ba ta hada su ba.
Kai tsaye ofishin Dr. Fredrick suka nufa, Amiru ya ce da shi.
"Doctor mun zo ne yau ka duba mana dalilin rashin haihuwarmu, al'amarin ya fara damuna.
Sannan Hajiya ta tada hankalinta, idan ba asibitin nan muka zo ba, ba zata barni na zaun lafiya
ba".
Sai a sannan ne Mairo ta cira ido ta dube shi. Yanzu ne ta gano dalilin bacin ranshi. Wato sun
fara damuwa da rashin haihuwarta, wanda ita ba ta isa ta bai wa kanta ba.
Dr. Fredrick ya hada su da Gynaec Doctor da za su gani, wato Dr. Ma'u. Bincike iri-iri Dr. Ma'u ta

yi amma ba ta gano wata matsala a tare da Amiru ba. Da ta zo kan Mairo, sakamako ya nuna
cewa, ita ce bakin mahaifarta yake a tsuke sosai. Idan har tana son haihuwa, dole sai an yi
mata aiki, an bude bakin mahaifar.
Ya roki Dr. Fredrick da Dr. Ma'u lokacin da Mairo ta nufi mota cewa su taimake shi su bar
wannan sirrin a tsakaninsu, ba ya son Hajiya ta ji.
Dr. Ma'u ta ce da shi.
"Ai ko ba ka ce ba, amana ce tsakanin likita da 'patient' dinsa, insha Allahu ba za a fada mata
ba".
Ya yi godiya ya barsu da alkawarin idan sun dai-daita ranar da za a yi mata aikin za su dawo.

Mairo ta shiga cikin tsananin damuwa. Tashin hankali da rudani. Yadda farat daya Ameeru ya
sauya mata. Kamar ba shi ba. Babu wannan murmushin, babu wannan soyayyar tashi mai
kidimata. Kullum daga fada sai hantara. Duk ta bi ta kare a tsaye, ta soma samun tangarda a
karatunta. Amma don zurfin ciki irin nata, ko Dina ba ta taba tunanin fadawa ba. Hajiya ta samu yadda ta ke so, domin ta janye hankalin tilon danta kanta. Duk abin da ta ce da
shi dashi ya ke amfani, jikin shi har rawa yake wajen bin umarnin ta, ta himmatu da yi wa
surukarta karfar baka, mai wuyar magani, wadda ta fi kiyayyar zahiri lahani a zuciyar wanda ake
mawa. Duk yadda ya so ya lallame ta su koma asibiti a yi mata aikin amma Mairon ta ki. Idan ya takura
mata da nacin maganar sai ta sa kuka. Ga shi shi kuma ba abin da ya tsana irin kukanta da ke
soya zuciyarshi.
Ta dage akan cewa, ita Allah ne kawai bai nufe ta da samun cikin ba. Ranar da ya nufa Ya ga
damar ba ta zata samu ne.
"Amma Shi Ya ce 'tashi in taimake ka. Sannan babu cutar da Ya saukar ba tare da ya saukar da
ita tare da maganinta ba.
Idan ke ba ki damu ba, ni ina son ganin dan kaina. Tun da rayuwar ba jiranmu ta ke ba, mu
muke jiranta".
Tana so ta yi tsaki, amma kimarshi da martabarshi sun wuce hakan a idanunta. Dole ta maida
tsakinta.
"Ni fa babu inda zan je".

Duk inda ranshi yake idan ya yi dubu, to ya baci. Ba ta taba yi mishi musu a rayuwarshi irin na
wannan lokacin ba. Ya rasa abin da zai mata YA HUCE... Gaba daya ya soma tunanin bokon da
ya barta tana yi ne ya sanya ta raina shi... Wannan ne karo na farko da ya kai kararta wajen
Habibu tun bayan aurensu. Habibun ya ce, ya kawo mishi ita.
Daga ita sai Yaya Habibun a babban falonshi, don Amirun da ya kawota bai zauna ba ya wuce
ofis wajen Daddy. Dina na kicin tana kacaniyar shirya abinci.
Habibu ya ce
"Mairo me nake ji haka? Wai mijinki bai isa ya sa ki abu ki yi ba?
Idan ke ba kya son 'ya'yan, to shi yana so. Muma muna so, me kike nufi da ba zaki yarda a yi
miki aikin ba?"
Ta fashe da kuka, ta ce

"Da da ne ya ce na yi abin da yake so, ai zan yi ne, ba tare da kowa ya ji ba. Amma ni ma
yanzu ban san me yake nufi da ni ba. Babu magana mai dadi tsakanina da shi sai hantara.
Kuma yadda ya ke nunawa kamar ta karfi yake so na haifo mishi dan, sannan ni gaskiya tsoro
nake ji, lafiyata kalau inje a jagwalgwala min mahaifa". Habibu ya ce
"Likitoci ba za su yi miki karya ba Mairo. Maganar canzawarshi sai ki yi mishi uzuri, yanayin
rayuwar kenan, wata rana a sha zuma, watarana a sha madaci! Ba kullum ne mutum yake
kasancewa cikin dadin rai ba!".

Da kyar Habibun ya rarrashe ta, ta yarda za su je ayi aikin. Ranar litinin Dr. Ma'u ta yi mata
aikin.

***








Tsawon shekara guda har da doriya, babu wani bayani, wato ba abin da ya sauya bayan yin
aikin. Babu ciki ba alamarsa.
Dai-dai lokacin da ta kammala rubutun 'project' dinta na kwalin master, sabida kwazon da ta
nuna kai tsaye suka ba ta gurbin zama daya daga cikin malamansu, wato 'lecturing' a jami'ar
Abuja.
Mairo ta debi kudi masu yawa, ta dankawa Yaya Habibu aka soma ginin makarantar firamare da
sakandire a kauyen Gurin-Gawa. Sannan ta dauki sauran gaba daya ta mallaka mishi
halak-malak, bayan ta warewa Baffa nashi kason.
Habibu ya saida gidanshi na kasar America da wasu manyan kadarorinsa ya tada kafadar
(Habib Bank) wanda ke gaf da durkushewa. Cikin taimakon Allah sai al'amuran suka soma
dai-daita. Amma a ranshi ya dai karbi kudin Mairo ne kawai bai ce mata komi ba, sai dai cikin
ranshi ya kudurce juya mata zai yi.
***
Hanan Abdulwahab, diyar kanin Hajiya ce, wato Uncle din Amiru da ke garin Gaya. 'Yar kimanin
shekaru ashirin da hudu, kyakkyawa ce matuka, kuma tana da irin tsagin su Amiru a gefen hagu
da dama na fuskarsu.
'Yan asalin garin Gaya ne su ma, don da Babanta da Hajiya ubansu daya. Mahaifinta tsohon
soja ne, wanda ya rike manya-manyan mukamai a aikin soji, har zuwa matsayin da yake kai a
yau, wato Major Genaral Abdulwahab Gaya.
Gaba dayan karatun Hanan tun daga firamare har jami'a ta yi shi ne a garin Lagos, inda
mahaifinsu ya yi aiki a wancan lokacin. Daga baya da ya yi 'retire' suka dawo garin Kaduna da

zama, inda suke zaune a halin yanzu.
Direban Hajiya Mr. Kademi ne ya je ya dauko Hanan daga filin jirgi, wadda ta sauka karfe hudu
dai-dai na yammacin ranar ta Laraba.
Hajiya ta yi mata kyakkyawar tarba bayan ta rungumeta tana lale da diyarta. Kamar yadda
Hajiyar ta nemi izinin mahaifin Hanan di n kan ya barta ta zo ta yi mata kwana biyu.

Sun baje a falon Hajiya suna labari, Hanan ta ce.
"Ina labarin brother, yanzu yaran shi nawa ne Hajiya?"
Hajiya ta kyabe baki, ta ce.
"Babu ko daya".
Hanan ta yi murmushi, ta ce.
"To ai kin san Turawa ne, watakila ba su shirya fara tarbar 'ya'yan ba".
Cikin rashin walwala Hajiyar ta ce.
"Ke raba ni da abin haushi, kada ke ma ki bata min rai yanzun nan. Turancin yaci abu kazan
ubansa. Ba wani tsarin iyali, juya kawai ya je ya auro".
Kwanan Hanan biyu a gidan, amma ba su hadu da Amiru ba, sabida sanda yake shigowa gaida
Hajiyar da safe ita ba ta tashi daga barci ba, sabida dai Hanan 'yar hutu ce ta karshe.
A rana ta uku ne da ya shigo Hajiya ta je har dakin da ta sauka wanda ya kasance dakin su
Rayyah ne kamin su yi aure, ta tasota ta ce ta zo su gaisa da Yayanta. Ta ba ta wani farin kwalli
ta ce, ta zizara a idonta, ta yi duk kokarin da zata yi ta tabbatar sun hada ido.
Hanan ta cika da mamakin mene ne dalilin Hajiya na yin hakan? Sai dai kuma ba ta jin zata iya
kin bin umarnin Hajiyar.
Tsaye ya ke a baranda yana amsa kiran Habib cikin wayarshi, a lokacin da Hanan ta fito falon.
Ya juya baya hannunshi daya dafe a bayanshi, yayin da ya yi amfani da dayan wajen rike
wayar.
Hanan ta tsura mishi idanu, wani al'amari mai karfi na fizgarta. Rabonta da Amiru tun wani zuwa
da ya yi Kaduna gaida mahaifinta a lokacin yana Washington. Zuwa yanzu ya kara girma da
haiba. Duk wasu kamanni na ingarman namiji ya mallake su, kuma kyakkyawa na
karshen-karshe. Ya zama 'giant' mai wani irin kyawun halitta na burgewa da ban mamaki. Irin
mazan da ba kowacce lafiyayyar mace ce zata iya dauke ido a kansu ba.
Gwiyoyinta suka yi sanyi, kuzarin jikinta ya kare, wata irin soyayyar Amirun na tsirga zuciyarta.
Ba ta iya ta dauke ido a bayanshi ba har ya juyo.
Da farko kallo daya ya yi mata, amma ya rasa dalilin da ya sanya ya kasa dauke idonshi a
kanta. Don sai ya ganta kamar Mairo, idanunta, bakinta da karan hancinta duk sun rikide sun
koma na Maironshi sak! Har ya ke jin yafi son wannan Mairon, akan wadda ya baro a gida.
Sakon Hajiya ya yi aiki sosai, ya hada wata matsiyaciyar soyayya, mai wuyar fassarawa.
8/8/21, 1:23 PM - Kawata: 55



Tsayin watanni biyu Alh. Abdurrahman na jinyar tilon dansa, ya na kwantar masa da hankali ta
hanyar bashi misalai da al’amuran rayuwa kala-kala. Don ya yaye wa kanshi damuwar daya
sanyawa zuciyar shi. Yana kuma karantar abubuwanda ke faruwa a cikin gidanshi musamman

Hajiya A’isha daya digawa gundumemiyar ayar tambaya. Sabida yadda ta fita hayyacinta da
rashin lafiyar Amiru, sai surutai take mai tonawa kai asiri, wani zubin ta hada da su Nina tace su
suka angizata, ta zazzagesu tayi musu mugun kalami tana cewa sun cuce ta.
Bai tambayeta komai ba, kuma bai tambayi Amiru mai yasa ya saki Mairo ba. Wanda rayuwar
sa ke hannun Allah. Dr. Fred yana zuwa gida akai-akai yana kula dashi. Ya ki yarda a maida shi
New-York. Yace da Daddy in ma mutuwarce, to yafi so ta dauke shi a dakin da yayi rayuwa da
Mairo.
A yau Ambasadan Malaysia yazo ganin sa, ta dalilin Habibu da Amiru Daddyn Dina da Alhaji
Abdurrahman suka kulla abota. Alh. Abdurrahman yayi masa kyakkyawar tarba, shikansa saida
ya zubda hawaye ganin halin da Amirun ke ciki. Ya koma Malaysia cike da alhini inda ya tarar
da Mairo da tata sabuwar matsalar har yau ba sauyi. A wannan satin da surutan Hajiya suka ishi Alh. Abdurrahman, yayiwa ‘ya’yan shi mata
gabadaya waya, na ciki dana waje, yace yana so su hallara a ‘family meeting’ ranar asabar mai
zuwa. Sannan ya kira Alh. Abdulwahab Baban Hanan shima yace yana so Hanan tazo ranar
asabar. Alhaji Abdulwahab wanda ke cike taf da fushin sakin da Amiru yayiwa Hanan sati daya
da aure ya gintse fuska yace
“ince ko lafiya? Bayan an riga an saketa?”
Daddy yace lafiya kalau, ‘meeting’ zasu yi tare da ita. Ya gaya mishi bai san abubuwanda suke
faruwa a gidan ba, yana so ya sani ne, inda halin gyara ayi gyara. Yace Hanan zata zo
albarkacin ka, amma babu batun gyara. Don dama Hanan tana da mai sonta tuni, mutunci da
‘yan uwantaka aka diba aka bawa Amiru. Tunda kuma yace baiyi, to Allah ya hada kowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login