Showing 36001 words to 39000 words out of 79746 words
Chapter 13 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf
ne, sai dai duk duniya babu wanda nake jin zan iya
aure sai shi…...."
Ta shiga baiwa Habibu labarin tun bayan tafiyarsa, yadda akai ta je FGGC, haduwarta da
Junaid, Kausar da su Nabilah, saran da maciji ya yi mata, ba da jininsa da ya yi gare ta, karfafa
mata gwiwa da kwarin gwiwar da yake ba ta a karatunta, amanar da Malam Bedi ya ba shi a
kanta, tsayawa da ya yi akan lafiyar iyayensu, har zuwa gama makaranta da nemansa da ta yi
ranar candy ba ta ganshi ba. Ta kare labarinta da ba shi labarin zuwansu karbo sakamakonsu a
makarantar inda aka gaya musu ya tafi karo karatu Russia. Ta dakata ta share hawaye, ta
cigaba da ba shi labarin zuwanta gidansu wajen mahaifiyarsa, amma ba ta gaya mata ko ita
wace ce ba.
Habibu ya yi shiru, cikin zuzzurfan tunani na ma'abota hankali. Ya rasa ta inda zai bullowa
al'amarin Mairo. Tabbas soyayya ke dawainiya da kanwarshi tilo, ba tareda ita din ta sani ba.
Dole ya tsamota, ya ba ta (hope) na yadda zata manta, ta fuskanci sabuwar rayuwar da ke
gabanta. Neman Junaid agareshi ba wahala ba ne, zai iya kai ta kasar Russia, to amma ba zai iya cewa
da Junaid don Allah ya aureta ba, tunda shi din ba sonta ya ke yi ba.
Da yana sonta da ya nemeta, tunda ta ce yasan da Alhaji Abbas. A ganinshi ma, a wannan
sabon zamanin da muka shigo. Mairo ta yi kankanta da aure, yana sonta da ilimi mai zurfi ba
soyayya ba. To amma shi kansa ya kasa yanke hukuncin cewa Junaidun yana son Mairo ne ko
ba ya sonta? Idan ba sonta yake ba haka kawai ba zai yi ta dawainiya da rayuwarta har haka ba. Allah ne
kadai Ya san wane ne mijinta. Don haka ya kada harshe ya ce "Za ki yi min wata alfarma,
Mairo?"
Ta dago a hankali ta dube shi "Ta mece ce Yaya Habibu?"
"So nake ki manta da Uncle Junaidu. Ba wai ki manta da alherinsa gare ki ba, a'ah, ki manta da
soyayyar da zuciyarki ke yi masa, da tunaninki na ba zaki iya auren kowa ba sai shi. Amma
kullum kika yi sallah ki dinga yi masa addu'ar budi da nasarar rayuwa kamar yadda ya zama
sanadin da kika samu ingantaccen ilimi.
Ni ma zan tayaki, zan dinga yi wa Junaid addu'a, wannan shi ne kawai alherin da za ki yi ki
rama mishi, ba lallai sai kin aure shi ba. Da yana sonki da ya zo neman aurenki. Ko bai zo
neman aurenki ba, da ya zo ya yi miki sallama a lokacin da zai tafi, ya gaya miki wata
kwakkwarar magana, mai nuni da yana son aurenki a nan gaba. Ko ya ce ku yi alkawarin aure, don haka ki manta da soyayyarsa, ki tsaya ki yi karatu irin na
Junaidu, ke ma ki taimaki mutane kamar yadda Junaid ya taimake ki. Ki zama malamar
makaranta, mai nagarta irin Junaidu. Idan Junaid mijinki ne, wata rana ni na gaya miki zai zo
inda ki ke, Allah Zai hada ku, amma hakan ba yana nufin za ki zauna zaman jiransa ba ne, a'ah,
matar mutum kabarinsa.
Na ji dadi da ba ki gaya wa mahaifiyarsa ko ke wace ce ba, da ina nan ma, da ba zaki je ba,
koda yake ba wajenshi kika je ba, wajen wadda ta yi SANADIN kawo shi duniya ne, gaishe ta
da zuciya daya ba laifi ba ne. Ita darajar diya mace a wurin da namiji guda daya ce, don haka yi
min alkawarin mantawa da soyayyar Uncle Junaidu. Ki bude file ki sanyata a ciki, ki rufe, ki
adana. Ki fuskanci rayuwarki ta gaba, kin ji Mairona?"
Cikin shesshekar kuka ta ce "Na ji Yaya Habibu, na yi maka alkawari".
Ya tayar da motar suka harba kan titi. Mairo na addu'a cikin ranta, Allah Ya ba ta ikon rike
wannan muhimmin alkawari da ta yi wa Habibu, domin ba karamin nauyi ba ne ya azawa
zuciyarta ba, da ta ke fatan Allah Ya ba ta ikon saukewa.
******
"KUDI" Aka ce su ne 'KARE MAGANA'. Suna zuwa gida me zata gani? Ma'aikatan Julius
Berger. Sun sa katafila sun murkushe gidan Alhaji Abbas, sai fili fetal. Tuni har sun fara auna
rodi sun kakkafa matattakalar katako sun fara aikinsu. Su Habiba da yaransu duk suna gidajen
iyayensu, sai an gama ginin zasu dawo. Can gidan su Habiba suka je suka dauki yaran, Habibu
ya zuba su a mota suka wuce Dutsinma.
Mairo da takwararta da Muhammad da ta ke kira Abbana suna baya, Abbas yana gaba tare da
Habibu, wanda ke tuki cikin kwarewa da sukuni. Abba yana ta yi mata tambayoyi tana ba shi
amsa dai-dai yadda kwakwalwarshi zata dauka.
Sanyin A.C gauraye da ni'imtaccen kamshin turaren Yaya Habibu na 'Miyaki' ya gauraye motar.
Ya sanyawa Mairo wata irin nutsuwa cikin zuciyarta.
Habibu bai tsaya ba sai a garin Funtuwa, ya sai masu gasassun kaji da lemunan kwali da ruwan
Faro, suka mika. Bai kara tsayawa ba sai a kofar gidan kakannin matarshi da ke cikin garin na
Dutsinma.
Habibu ya fidda waya yana kiran Dina, ya ce "Ga mu nan mun iso".
Mairo na gefe, harde da hannuwanta a kirji. Idanunta kur, akan kofar fitowa gidan, tana zuba
idon ganin wace ce wannan Dina, da ta mamaye zuciyar Habibu haka?
Wace ce Allah Subhana Ya yiwa baiwar samun wannan Habibun? 'Yar Katsinawan sai ta fito,
kyakkyawar fuskar fal far'a. Sanye da doguwar bakar riga da mayafinta kirar Bahrain. Fara ce,
amma ba sol ba, ta ma fi dai-dai da a kirata choculate colour. Mai wadatar giran ido, gashin ido
da sumar kai. Ba ta taba ganin mace mai kyawun fata irin matar Habibu ba. Gayun ne ya hadu
da jin dadi, ya gauraya da hutu, ya cakude da wadataccen ilmi, sannan kwanciyar hankali da
zaman kasar sanyi ya biyo baya. Suka yi wa juna wani irin sassanyar kallo ita da Habibu,
sannan ta karaso ta rungume Mairo, tamkar ta tsaga kirjinta ta sanyata don kauna. Wani irin
matsiyacin kamshi da Mairo ba ta taba ji ba ya ziyarci hancinta.
"Lallai wasu tun a duniya Allah Ya ke ba su Hurul'eeni". Mairo ta ce a zuciyarta.
Da tana ganin Dinan ce mai sa'a da ta samu Yaya Habibu, ashe shi ma Habibun mai sa'ar ne,
don cikin mata dubu, da kyar zaka samu biyu irin Dina. Da tana ganin Nabilah 'yar gaye, ashe
Nabilah 'yar dukununu ce. Ba ta gama zancen zucinta ba, tattausan hannun Dina kamar na jariri
ya kama nata, ta ja ta cikin gida. Bayan ta bi 'ya'yanta daya bayan daya da kisses da runguma. Wata dattijuwa ce tsohuwa tukuf, sanye da atamfa super holland zaune a can kuryar
kayataccen falon bisa darduma tana lazimi. Da gani babu tambaya, ita ce uwar Baban Dina.
Habibu da yaran suka zauna a kujera yayin da Dina da wata yarinya budurwa da alama mai aiki
ce suka shiga hidimar fito da warmers, plates, da cokulla. Ba ta katse laziminta ba, shi ma
Habibun fita ya yi don samun jam'in sallar la'asar. Mairo tana fashin sallah, don haka suka
zauna ita da yaran da Dina suna cin abinci.
Dina ta rasa ina taka-saka-ina-taka-aje da Mairo? Soyayyar Habibu ta shafe ta. Ganinta ta ke
tamkar kanwarta ta jini.
Sai wajejen karfe biyar Habibun ya shigo, lokacin Hajiya ta idar da laziminta, suka soma
gaisawa da Habibu. Itama Mairo ta duka tana gaishe ta. Dina ta ja ta dakin da ta sauka, ta hada
mata ruwan zafi a baf da turarukan wanka, ta ce ta shiga ta yi wanka. Mairo ta ce, "Ai na yi
wanka da safe". Ta yi murmushi, ta ce "Sakewa za ki yi, ita mace so ake ta yi wanka sau uku a rana. Idan hakan
bai samu ba, ta yi sau biyu. Sannan na ji smelling din jikinki bai min yadda nake so ba".
Don haka Mairo ta hau wanka, cikin kwami da ruwa mai dumi, da kamshin bathrobb din
desire-dunhill mai sanyaya zuciya da ni'imtata. Da sabulun da ko a mafarkinta ba ta taba gani
ba, wanda in ka yi wanka da shi, ba sai ka shafa mai ba. Ta ji fatarta har wani santsi ta ke da
sheki. Jikinta ya yi laushi tubus. Ta dauro alwala ta fito, ta samu Dina na jiranta zaune a bakin
gado.
Ta zube mata kayan shafa da turarukanta, ta ce ta shafa, sannan ta dauko riga da siket masu
kauri na Bersace ta ce ta sanya.
Ta zaunar da ita a gabanta ta sa dryer tana busar mata da gashi, sannan ta bi layi bayan layi na
gashin ta shafe shi da Indian hemp ta taje ta matse da bound, ta bi jelar ta jere da ribbons kala
uku masu taushi. Nan da nan sai ga Mairo ta fito kamar Sushmita Sen. Dina ta yi murmushi ta
ce "Maryama, haka kike da kyau kamar Habibu?" Mairo ta ji kunya, ta sunne kanta tana dariya, ta ce "Anti Dina ai ke kin fi Yaya Habibu kyau, fari
kawai ya fi ki".
Ta ce "Allah Ya nuna min ranar da tawa Mairon, zata girma ta tashi kamar wannan Mairon.
Kinga yadda na ganki yanzun nan, haka nake so kullum na ganki. Ita mace ba abin da ya fiye
mata jikinta daraja. Idan ta gyara shi, to ta gyara martaba da mutumcinta, mijinta zai like mata
tamkar kaska, ya ji ba abin da ya ke so ya kusanta a duniya sai ita. Shi kamshi wata rahma ne da Allah Ya saukar mana mu mata, kuma shi ne babban sirrin rike
da namiji. Kin ji ko Mairo?"
Mairo na dariya ta ce "To ai ni ba ni da mijin".
Ita ma ta tayata dariyar ta ce "Zai zo ne, gallele kuwa, ni na gaya miki".
Can dakin baki suka iske Habibu, shi ma ya sake fesa wanka, ya yi shiri cikin T. shirt din DKNY
fara sol da ratsin jaja-jaja da wandon jeans kai ka ce saurayi ne dan shekaru ashirin da biyu,
babu mai yarda ya aje 'ya'ya uku a duniya, ya bi Mairo da kallo don da fari bai ganeta ba, ya ce
"Kai! Halitta!!" Suka kyalkyale da dariya ita da Dina. Ya soma hararar Dinan cikin wata irin soyayyarta da ta
kara ratsa zuciyarshi, ya ce "Shikenan kuma don kin yi kanwa ni kin yaye ni?"
Ta soma yi masa alama da ido, Mairo na jinsa. Itama Mairon juyawa ta yi ta fice a ranta tana ce,
'Ku cinye kanku da soyayyar".
Ai kuwa tana fita ya yi super ya suri Dinan yana cewa "Gaya min wanda ya ce da ke kanwa ta fi
miji????"
Mairo wajen Hajiyar su Dina ta koma tana goga goro a magoginsu na tsoffi, da gani ka ga 'yar
gatan tsohuwa da da ya hucewa takaicin duniya. Ga wasu mulmulallun awarwarayen zinari a
hannunta guda uku, sai walwali suke, tufafin jikinta kadai, sun ishi karamin talaka jari. Ta zauna
gefenta ta ce "Hajiya kawo goron in goga miki". Ta mika mata dankwalelen goron fari sol da magogin ta soma gogawa, in ya taru ta mika mata
ta hambuda a baki. Tana bai wa Mairo labarin Dina.
Ta ce "Kin ganta nan, duk cikin jikoki na ashirin da biyar na fi sonta. Sabida halayenta na kwarai
da rashin daukar rayuwa da fadi. Babanta shine da na biyar cikin 'ya'ya biyar da na haifa suna
mutuwa, shi kadai ya tsaya. Kuma daga shi Allah bai kara ba ni da namiji ba, sai kannensa
mata guda biyar. Ita ce 'yarsa ta fari, sai tarin kanne guda bakwai. Ta kawo Yayanki dalibi da ba shi da komai ta
ce ita shi ta ke so ta aura. Da fari ba mu yarda ba, tunda ba mu ga iyayenshi ba, shi kuma ya
ce, ba zai koma gida a wancan lokacin ba.
Ya fito neman ilmi da arziki ne sai Allah Ya yi mishi zai koma, don haka muka saduda muka yi
musu aure. Da ya ke abokiyar arzikinshi ce ga shi Allah Ya azurta su, da 'ya'ya da dukiya. Allah
Sarki, ashe iyayen da ya nema don su huta, kamar yadda nake hutawa a tsufana, Allah bai yi
za su mori arzikinsa ba. Ki saki jikinki, ki kwantar da hankalinki da Dina, zata zame miki uwa, abokiya, kuma Yayar
kwarai, kin ji Maryamu?"
Ta girgiza kai, ta ce "Na ji Hajiya, Yaya Habibu ma ya gaya mini".
Dina da Habibu suka shigo, sun jero, tsawonsu daya, takunsu iri daya, sai annuri ke fita daga
fuskokinsu, ga dukkan alamu an ci soyayya an koshi. Ta dubi Hajiya da Mairo da ta takarkare
sai nika goro ta ke yi, ta yi dariya ta ce "kawa da kawa, hirar me ake yi?"
Hajiya ta ce "Ina ruwanki da hirarmu? Ko mu mun tambaye ki hirar me kika je taya mijinki?"
Habibu ya nitse cikin leather yana amsa waya da thuraya dinsa, cikin wani dan bantan uban
Turanci kamar Karl Mad sabida yadda Turancinshi ke fita tar-tar irin wanda Mairo ba ta taba ji
ba. A da, tana tsammanin a duniya babu wanda ya iya Turanci irin Uncle Junaidu, ashe Junaid
rarrafe yake yi, ga wadanda suka mike suke dabo, suka tsaya da kafafunsu.
Kwanansu uku a Dutsinma suka tattaro suka yo Kano, Mairo dai kamar ba zata tafi ba sabida jin
dadin zama da Hajiya, har hawaye ta ke da suka fito za su tafi, Habibu da Dina na mata dariya.
Hajiya ta cika mata Bacco fal da atamfofin edclusibes irin wadanda 'ya'yanta ke kawo mata, don
ta dinka, amma ta tattara ta bai wa Mairo. Wannan a jinin Mairon yake, FARIN JINI da shiga
zucci. Idan ka zauna da ita yini guda, zaka so ka kwana da ita. Idan ka kwana da ita, zaka so
kayi wata tare da ita, idan ka yi wata tare da ita zaka so ka yi zaman shekara da ita, haka idan
ka yi shekara da ita, zaka so ka zauna da ita har zuwa karshen rayuwarka.
Karfe uku dai-dai na rana suna cikin Kano, Habibu ya karya kan mota suka shigo Yakasai. Tun
daga nesa wani dankareren European Billa (Bungalour) ya dauki hankalinta, ya karkada mata
'ya'yan hanji. Abin mamaki a get din gidan Habibu ya sanya hancin motarsa kirar Porsche.
Zuciyarta na gaya mata, wai wannan gidan Baffa ne? Amma wani sashen na karyatawa. To idan
ba shi ba ne, wanne ne? A nan dai gidan Baffa ya ke, ga makotansu nan ba su motsa daga inda
suke ba, su ma sun samu arzikin sabon fenti irin na gidan. Dama dai gidan Baffan babba ne, ga
kuma bene an daura, ko ina gilashi da tile ke zagin idonka.
An fidda sashen baki daga gaban gidan, a cikin gidan kuma sashe biyu ne na matan gidan,
sashe guda na yara, Baffan yana sama, sai dakin 'yammata. Kowanne daki an kafe plasma a
sama tana ta aiki cikin tasoshin tauraron dan Adam, ga dindima-dindiman kujeru masu nishi
'yan Italy da labulaye masu garai-garai da gani tafiyayyu ne tun daga China. Abin dai ba a cewa
komai sai a gaida Habibu, a gaida ma'aikatan Julius Berger. A gaida Habibu da aikin ZUMUNCI,
da rama hairan da hairan.
Suna tsayuwa su Rahma suka diba yuuu! Suka yi cikin gida suna ta ihu, “turawan sun dawo da
Mairo, ba su sace ta ba. Baba ga Mairon nan sun dawo da ita".
Baffa dai baki ya ki rufo, ya fito ya taro su, Abbas ya gane shi, ya je ya kama hannunsa, Hajara
da Habiba kowacce ta fito daga bangarenta bakin nan kamar gonar auduga, har rige-rigen
daukar Mairo karama su ke. Mairo fa ta fara jin tsoron al'amarin Habibu. Allah dai Ya sa ba
kungiyoyin nan na matsafa da sassan jikin mutum ya shiga ba. Allah Sarki! Da tasan Barclays
da ba ta ce haka ba.
Hankalinta na kan 'yar uwarta Ladidi da halin da ta tafi ta barta a ciki. Don haka suna shigowa ta
tambayi Habiba "Ina Ladidi?"
Habiba wadda ke jin kamar ta suri Mairo ta goya don ta samu fada wajen Baffa wanda ya daure
musu fuska tam ya ki kula su don yasan duk borin kunya suke yi. Ta nuna mata dakin da Ladidi
ta ke, ta ce "Halan Mairo a inji matar Habibu ta sakaki ta wanke?"
Mairo ta yi murmushi ta ce "A'ah, a lagireto ne".
Ta wuce ta barta nan, tana ta sosa keya don kunya.
A dakin ta cimma Ladidi, an yi dai-dai cikin Italian bed, ana shan lemon Safari ana kallon tashar
Zee-Aflam, ba tasan sanda dariya ta kubuce mata ba, don kwata-kwata ba ta yi matching da
gadon ba da dakin gaba daya, ta fi dacewa da mai aikin dakin ba mamallakiyarshi ba.
Tana ganin Mairo ji kake kat, ta kware. Ta dinga tari ba kakkautawa. Mairo ta zauna a bakin
gadon tana yi mata sannu. Ta mutsittsike ido ta ce "Mairo ke ce kuwa?"
Ta ce "A'ah, ba ni ba ce, Ladidi ce".
Ladidi ta soma kuka ta ce "Don Allah Mairo ki yafe mini. Ga shi dai tun a gidan duniya mun ga
ishara, dan uwa duk lalacewarshi ba abun wasa ba ne, sai dai nasan kome zan fada miki a
yanzu ba zaki yarda ba, za ki ce don na ga Habibu ne, ko don abin da ya yi mana, amma
wallahi ba haka ba ne. Yadda kuma kika rufa min asiri a duniya, Allah Ya rufa naki duniya da
lahira". Ta sa habar zaninta ta share ido.
Mairo ta ce "Duk ba wannan ba Ladidi. Ki tuba ga Allah, ki sani cewa, Yana kallonki, idan su
Baffa ba sa kallonki. Yau idan Baffa ya samu labarin kin cire ciki har sau biyu a wane yanayi
kike tunanin zai tsinci kansa? Idan ba kya tsoron Allah, ai kya ji wa kanki tsoron cututtukan
zamanin nan da ba su da magani. Idan aure kike so ki fidda daya