Showing 15001 words to 18000 words out of 79746 words
Chapter 6 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf
karfinta ta wulwula ta fada kwatami da baka, abin tsautsayi, sai kulbar (macijiyar) nan ta huce
fushinta a kafar Mairo, wato ta sare ta.
Kausar ta mike cike da bala'i a lokacin idanunta suka gane mata abin da ke faruwa, dai-dai
lokacin kulbar ta sulale tana komawa inda ta fito, ga kuma Mairon da ta angije ta kwance a kasa
ba yadda ta ke. Ta daura hannuwa aka ta rafsa ihu, wanda ya ratsa gaba dayan hostel din,
student da metron suka fito. Kausar ta ce “macijiya ce ta sare ta.” Ai jin haka captain ta suri Mairo, sauran yara suka bi ta yuuu! Har da su Kausar sai gidan
principal ana buga mata kofa.
Ta fito a gigice ita ma nan take ta bugawa school doctor waya, nan da nan sai ga ta, aka wuce
da Mairo asibitin makaranta, Doctor ta dukufa ga son ceto ranta.
Kausar da Nabilah suka kasa komawa hostel ko babu komai akwai tausayin rai a zukatansu,
balle ita Kausar da tasan hakikanin yadda abinda ya faru. Nadamar abubuwan da ta ringa yi wa
Maryam Bedi, suka shige ta. Ta ji tausayin Maryam matuka, ta kuma tambayi kanta, shin ko
wace irin zuciya ce da ita? Irin su Maryam ne masu rama sharran da hairan, babu shakkah ta yi
nadama.
Nabilah ta yi mamakin damuwar Kausar akan Maryam ta yi yawa, ta kasa ko magana. Ta ce
"Kausar kowa ya koma hostel sai mu, ni fa tsoro nake ji".
A salube Kausar ta sa kafa cikin dan karamin asibitin ta samu benci ta zauna, ba ta da niyyar
tashi. Nabilah ta biyota cikin mamaki, ta ce "Wai me ya faru ne? Ba zaki zo mu tafi ba?"
Ta ce "Je ki abinki Nabilah. Amma ni a nan zan kwana".
Nabilah ta kama baki, dai-dai lokacin da Mummy Dukku wato principal ta fito zata koma gidanta.
Ta hango su Nabilah ta ce, "Ku kuma me kuke a nan ba ku koma hostel ba?"
Kausar sai ta sa kuka. Ta matso ta dafa kanta domin ta santa farin sani sabida mahaifinta, ta ce
"kawarku ce ince ko?"
Nabilah ta yi saurin cewa "A'ah, dakinmu ne kawai daya".
Mummy ta lura da kukan da Kausar ta ke sosai ta ce, "Ke kuwa tausayinki ya yi yawa Kausar,
alhamdu lillahi dafin bai shiga cikinta ba, kuma Doctor ta zuke shi. Insha Allah zuwa safiya za ta
warware, tashi ku tafi dare ya yi sosai".
Sai da suka je daki ne Kausar ta ke gayawa Nabilah hakikanin yadda akai maciji ya sari
Maryam. Ta ce "Yanzu ni tashin hankalina shi ne, idan ta mutu ban nemi gafararta ba ina zan sa
kaina?"
Jikin Nabilah ma ya yi sanyi, ta ce, "Allah Sarki, irin su ne ake cewa masu halin 'yan aljannah".
Suka yi jugum-jugum har wayewar gari ba su runtsa ba, nadama ta ishe su, sai kuma kaunar
Maryam farat daya ta bi zuciyoyinsu.
Washegari Uncle ya zo kiran suna kamar yadda ya saba, cike da mamakin rashin ganin
Maryama a class don kullum ya shigo idanuwanshi akan wurin zamanta yake. Duk da haka bai
fasa kiran sunan ba, har ya zo No. 40, shiru ba ta amsa ba.
Ya dago manyan idanunsa ya zubawa Kausar cike da zargi kamar ita ce ta boye Maryaman.
Ya ce "dakin ku daya, tana ina ban ganta ba?"
Kirjinsa har wani harbawa yake da sauri-da-sauri. Fargabarsa kada ace da shi iyayenta sun cire
ta daga makarantar sabida su Kausar. Bakin-cikinsa shi ne yau ace Maryama ta bar makarantar
nan. Tashin hankalinsa shine ko sunan kauyensu bai sani ba, alhalin yanzu yadda yake kaunar
Ilham haka yake kaunar Maryama. Idan zai iya rabuwa da ita, to hakika zai iya rabuwa da
Ilham.
Cikin in-ina Kausar ta ce "Maciji ne ya sare ta, tana kwance a maternity..."
Tun kamin ta kai karshe Uncle ya fita. Ya doshi maternity cikin matsanancin tashin hankali, ko
gani ba ya yi sosai. Ya banka kofar da kafarsa babu neman izini.
A kwance ta ke, idanunta a rufe, rana daya kacal ta zabge, ta yi wani irin fari fat kamar babu jini
a jikinta, sannan ta kumbura kamar an hura balam-balam.
Nurse din da ke kokarin daura mata 'drip' ta juyo a razane ta dube shi, bai kula ta ba ya karisa
gaban gadon da Maryam ke kwance ya tsaya kurum yana kallonta. Kamar an ce da ita bude
idonki, ko kuma alamar tsayuwar mutum ta ji a kanta oho, ta bude fararen idanunta a hankali
wadanda suka kumbura suka yi mata nauyin budewa, a hankali ta ce "Uncle…….." Sai hawaye
suka zubo ta gefen idonta.
Ya yi saurin kama hannun damanta, ya ce "Sannu Maryama, sannu kin ji. Allah Ya ba ki sauki".
Ya juya ga nurse din ya ce "Edcuse me madam Serah, na yi miki shisshigi cikin aikin ki. Maryam
na daga cikin dalibai na masu muhimmanci a gare ni. Ki yi hakuri".
Ta yi murmushi ta ce "Ai na ga alama, wannan patient din taka akwai raki da saurin kuka. Na
dauka dadi zaki ji da kika ga Uncle sai kuma ki kama kuka?"
Mairo ta maida idanunta ta rufe tana murmushi. Ta nemi ciwon da jikinta ke yi ta rasa, sabida
kasancewar Uncle Junaidu tare da ita.
Suna magana a kanta shi da Madam Serah ta gaya mishi wannan macijiya ta dade tana sarar
dalibai, anyi duk iya kokarin da za a yi don ganin an fitar da ita daga makarantar an rasa. Wani
zubin sai a yi tsammanin ma ta mutu don sai a yi shekaru biyu ba a ji duriyarta ba. Amma yanzu
kam za a daukaka zancen zuwa federal da yardar Allah za a fitar da ita. Ya ce "Maryama ta kumbura, ta yi biyun yadda ta ke".
Ta yi murmushi ta ce "Jini ne babu isashshe a jikinta, wanda aka zuke tare da dafin amma
already an tafi a sayo wanda za a sanya mata a asibitin Aminu Kano".
Hankalin Uncle ya tashi, ya ce yana son ganin Doctor Nanah, ta ce tana ofis ka karisa.
Ya samu Dr. Nanah a ofis cikin tashin hankali. Ta ce "Yaya dai Uncle Junaidu?"
Ya ce "So nike ki debi jinina idan ya yi dai-dai ki sanyawa student dina".
Ta ce "To bari in diba kadan a auna a gani".
Ta zuka kadan a sirinji ta mikawa lab asisstant ta auna, ya nuna (negatibe), ga duk wasu
gwaje-gwaje da akayi, sannan dukkansu a 0+. Ya kwanta ta debi leda biyu ta ce ya ci gaba da
kwanciya ya huta. Ta ba nurse ta sanyawa Mairo ta dawo tana fada mishi irin abincin da zai
ringa ci har zuwa kwana bakwai.
Nan da nan labari ya watsu cikin FGGC cewa Uncle Junaid ya yi donating jini wa Maryam. A'ah,
cece-kuce ya soma (round) zagaye makarantar musamman daga 'yan ajinsa da daman suna
hankalce da su. Yara kanana da su amma sun iya gulma. 'Yan manyan aji kuwa masu yi masa
asirtacciyar soyayyah, wadanda a da ba su san da Maryam din ba suka zo suna kallonta, duk ta
takura ta rasa inda zata sa kanta, balle da ta lura har da masu yi mata mugun kallo.
Ranar da ta dawo hostel Kausar kunyarta ta ke ji, ko ido ta kasa hadawa da ita. Daga baya da
ta ga Maryam din ma ba ta damu ba harkar gabanta kawai ta keyi, sai ta zo bakin gadonta ta
zauna ba ta ce komai ba.
Nabilah ta shigo itama ta zauna a katifarta abin da ko da wasa ba su taba yi ba. Suka ce "Don
Allah don Annabi Maryam ki yafe mana. Wallahi sharrin shaidan ne, kuma mun gode da
sacrifice (sadaukar da kan) da kika yi mana. Muna rokonki daga yau mu zama daya a
makarantar nan, wato mu zama mu uku cikin amana".
Mairo ta yi murmushi ta ce "Babu komi, ni dama ban taba kullatarku ba, mamaki dai kuke ba ni.
Amma shi ke nan, komi ya wuce".
Daga ranar Maryam, Nabilah da Kausar ba a kara jin kansu ba.
To sai kuma ciwon ciki ya kama Kausar, kullum ba ta iya barci, sai murkususu da kuka cikin
dare, haka suke kwana tsaye a kanta har asubah sannan zata samu barci.
Da suka ga abin ya fi karfinsu sai suka yi reporting ga hukumar makaranta. Aka dauki Kausar
zuwa maternity inda aka gano kabar ciki ke damunta. Nan da nan aka yi hamzarin mikata gida,
domin abin ya fi karfin asibitin makaranta.
Suka koma kewar Kausar tare da yi mata addu'a, kullum, har lokacin jarabawa ya matso.
Kokarin Uncle shi ne Maryam ta saki ranta ta yi abin kirki a jarrabawarta, amma ina! Tunanin
Kausar da halin da ta ke ciki ya hanata zama lafiya.
Ranar da suka soma jarrabawa suka dawo hostel sai suka ga babu ko allurar Kausar a dakin.
Captain da Metron sun kwashe sun bai wa iyayenta.
A gigice Mairo ta fita kafarta ko takalmi babu, kanta babu kallabi. Nabilah ma ta bi ta dakin
Metron suna tambayarta yaushe aka kwashe kayan Kausar?
Ta ce "Allah sarki, wannan yarinyar diyar Gwamnan Jos, ta rasu. Tun satin da ya wuce".
Suka rushe da kuka, suka zube anan suna ta yi. Tsoron Allah Ya kara shigar Maryam da
Nabilah. Tun daga ranar suka koma wasu irin sukuku, ba fuss ba ass. Shi kansa Uncle ya
girgiza da mutuwar Kausar, ya yi ta lallashinsu yana ba su baki. Ya ce da Nabilah abin da yake
ankarar da ita ke nan kan daukan duniya da zafi. Shi Ubangiji ba ruwansa da ko kai wane ne,
dan wane ne, wane ne ubanka face ayyukanka kyawawa.
Nabilah ta fi Maryam ramewa, ta fi ta gigicewa, domion dai ta fi ta shakuwa da Kausar. Sannan
ta kara rungumar Maryam a matsayin 'yar uwarta don sai ta ke ganinta kamar Kausar.
Aka yi jarrabawa aka kare, sai hutu sati mai zuwa. Sai dai fa daga Maryam har Nabilah
kowacce cike ta ke da zullumin sakamakonta. Uncle ya yi fushi da Maryam sosai, domin ta
dauko na talatin da takwas yayin da Nabilah ta dauko na arba'in.
Ta kaskantar da kai ta dinga ba Uncle hakuri, ta tabbatar masa zango mai zuwa za ta dage ta yi
abin da zai ji dadi. Mutuwar Kausar ke nukurkusarta har zuwa lokacin.
Ranar hutu malam Bedi sammako ya yi domin hedimasta ya gaya masa tun ana saura kwana
uku, don haka a kwanakin nan barcin da suka yi kalilan ne sabida dokin dawowar Mairo. Barin
ma Inna Hure da shiga goma, fita goma sai ta siyo abin da zata ajiyewa Maironta. Tun daga kan
goriba, kurna, goba, magarya, dinya da ire-irensu wadanda tasan Mairon na so babu wanda ba
ta nemo ta ajiye mata ba.
Duk sammakon Baban Mairo bai isa makarantar ba sai da aka soma dadewa.
Mairo da Nabilah na zaune karkashin dalbejiya dukkaninsu cikin damuwa suke na rashin ganin
kowa nasu. Nabilah ta ce "Da na san gidanku Maryam da na zo kamin na wuce Lagos hutu
wurin Auntyna".
Maryam ta jinjina kai ta ce "Ba zaki iya zuwa gidanmu ba, can ne cikin surkukin kauye, cikin
Fanshekara".
Nabilah ta ce "Don ba kisan yadda nake son zuwa kauye ba ne, idan kuma kin musanta hakan
ki gaya min ki gani".
Ta dauko biro da jotter tana jiran ta bakin Mairon.
Mairo ta ce "Fanshekara, motar Gurin Gawa, idan an shiga Gurin Gawa, sai a tambayi gidan
Malam Bedi kowa ya sani. Idan kuwa yara ne kika ce musu 'MAIRON HURE' da gudu za su
rako ki".
Duka Nabilah ta dauke cikin jotterta, wanda ke bayansu ma ba su san da tsayuwarshi ba shi ma
ya dauke cikin kakkaifar kwakwalwarsa.
"Lah, ga Babana nan!". Mairo ta fada cikin matsananciyar murna, kamin ta kwasa da gudu ta
rungume Malam Bedi. Nabilah ta dago daga rubutun da ta ke ta bi bayan Mairo da kallo, sai ta
hango ta rungume da wani yagulallen tsoho, sanye cikin yadin algarara, kanshi duk furfura. Ta
ce a ranta, "Ya za a yi ace wannan ne ya haifi Mairo? Ya fi kama da kakanta fiye da babanta". Ba tasan cewa ba wai shekarun da ya yi a duniya ba ne suka janyo masa wannan tsufan ba,
a'a, wahalar rayuwa ce kawai ta noma, girbi, da sussuka irin ta kowanne manomin kauye.
Tausayin Mairo ya kamata, ta tabbata ita 'yar talaka ce futuk, amma she is contented with what
she habe (a gamshe ta ke da abin da ta ke da shi, ba ta taba kwadayin abin hannun wani ba).
Mairo ba ta taba tambayar Nabilah ita 'yar waye ko daga ina ta fito ba. Wannan ya sa Nabilah
tambayar kanta, shin Maryam wace iri ce? A zahiri miskila ce, abin da tasa a gabanta shi ne
kawai ya dame ta.
Ta mike ta tadda su tana gayas da Malam Bedi cikin tsananin girmamawa.
Mairo ta ce "Baba Nabilah sunanta, ajinmu daya, dakinmu daya. Da har da Kausar amma ita ta
rasu".
Fuskarshi ta nuna bai ji dadi ba, ya ce, "Sannunki Nabilah, Allah Ya jikan Kausar".
Idanunta ya ciko da hawaye, ta juya tana sharewa ta ce, "Amin".
Babu irin neman da ba ta yi wa Uncle ba, don su gaisa da Babanta, amma ba ta ganshi ba. A
haka cikin rashin jin dadi ta yi sallama da Nabila rike da 'yar jakar kayanta ta buhu (Ghana Must
Go) suka fita. Sun sha wuya matuka irin ta motocin haya kamin Allah Ya kawo su gida.
Ganin irin wuyar da Babanta ya sha ya sa ta alkawarta wa ranta daga wannan hutun zata hutar
da shi kai ta makaranta da dawo da ita, tunda ta gane hanya zata dinga tafiya da kanta.
Tunda yaro ya shigo da jakar Mairo Hure ta biyo bayansa da saurinta. A soro suka yi kacibus,
da Mairon nata. Suka rungume juna kamin Hure ta soma hawaye ta ce "Ashe wannan ranar
zata zo Mairo, ranar da zan kara ganinki?"
Mairo kuwa baki ya ki rufuwa a haka suka karasa cikin gidan kamar wadanda suka shekara ba
su ga juna ba.
Inda duk Inna ta mika hannu sai ta zarowa Mairo abin sawa a baka, ta ci ta yi nak! Ta ci girkin
Innarta da ta yi kewa, ba kadan ba. Duk da cewa abin da ta ke ci a makaranta ya fi na gidansu
amfani a jikin dan Adam.
Hure ta kasa boye mamakinta, ta ce "Shin mai kike ci a makarantar nan ne Mairo? Kinga kuwa
yadda kika zama buleliya, kika yi fari sai sheki kike?"
Mairo ta sa dariya, ta ce, "Ba abin da bana ci Inna. Tun daga kan kwai, dankali, agada, doya,
madara, nama da kifi ba abin da ba a bamu. Har 'ya'yan itace (fruits) ba dole in zama buleliya
ba?"
A ranar dai Mairo da iyayenta kwanan zaune suka yi, tana ba su labarin rayuwarta a makaranta.
Sai dai fa duk rabin hirarta, "Uncle Junaidu" wanda ya yi ruwa ya yi tsaki wurin sama mata farin
ciki da walwala a cikin dalibai 'yan uwanta.
Malam Bedi ya ce, "To Allah Ya saka mishi da alkhairi".
Sai dai a cikin labarinta ba ta kawo labarin saran sa macijiya ta yi mata ba, don ta tabbata idan
suka ji, kidimewa za su yi su ce ba zata koma ba.
Hutun Mairo gwanin ban sha'awa a gidansu, gabadaya yanayin rayuwarta ya canza, ba ta barin
Innarta da aiki ko ya ya, sai ta karba ta yi. Haka ta ke bin babanta gona tana taya shi shuka da
ban ruwa. Abokinta Rabe da ya ji ta zo hutu daga makarantar kwanan da aka kai ta, sai ya aiko
yaro rannan da yamma wai Mairo ta zo su je su hau tsamiya. Malam na jin sanda ta maida dan
aiken ya tambayo mata Rabe, shin yanzu ta yi masa kama da 'ya'yan birrai ne da zai ce ta zo ta
hau bishiya?
Sai ya yi murmushi yana kara shi wa Habibu albarka a zuciyarsa.
7/28/21, 4:41 PM - Kawata: 4999
******
Uncle Junaidu ya yi mata halarcin da ba zata taba mantawa ba a rayuwarta. Tare da shi aka yi
ta zaman makoki har tsayin kwanaki bakwai, mahaifiyarshi da kannenshi duka ya kawo su sun
yi wa Inna Hure gaisuwa. Ranar da aka yi sadakar bakwai ya tura aka kira masa Mairo azure,
ya kara yi mata ta'aziyya, ya kara da nasihu masu sanyaya rai da karfafa gwiwa. Ya ce ta daure
sati mai zuwa ta dawo makaranta har zangon ya yi nisa ba tareda ita ba.
Ta rantse masa zata dawo amma tana tausayin Innarta, yadda zata barta cikin kewa. Ya ce
"Wata rana aure zaki yi Maryama, ke da Inna sai gani da yawo, ita kanta tasan hakan. Don haka
ki taimake ni in rike nauyin da marigayi ya aza mani akan karatunki".
Bayan tafiyarsa Mairo da Innarta idan ka gansu gwanin ban tausayi. Tunanin Mairo shi ne, wa
zai dinga nomawa Innarta abin da zata ci? Idan wanda ke cikin rumbunsu ya kare? Allah maji
kan bawa, washegari sai ga Alhaji Abbas niki-niki da kayan abinci ya kawo musu. Ya kuma ce,
wannan nauyin ya dauke shi insha Allahu. Sai a nan hankalin Mairo ya dan kwanta duk da Innar
ma ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba.
Shi ma Alhajin ya yi mata zancen makaranta ta ce, insha Allah karshen wannan satin zata
koma.
Hakan kuwa aka yi, ranar litinin ta yi shiri ta koma makaranta. Nabilah ta yi mata ta'aziyyar
babanta wanda ta ji a bakin Uncle Junaidu.
Rayuwar Mairo ta sauya kwarai, ta zama babu walwala, akwai shakuwa da kauna mai tsanani
tsakaninta da mahaifinta, don haka ta ke jin kanta tamkar ita kadai ta rage a duniyar. Sai ta
samu kanta da son yin abin da zai debe mata kewa, don haka ta fara tunanin yin RUBUTU.
Tana yi tana gutsirewa ta ajiye, idan ta ji bai yi mata ba. Kamar da wasa, ta fara rubutun labarai
cikin harshen Turanci a