Showing 78001 words to 79746 words out of 79746 words
Chapter 27 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf
juna tsakanina dasu. Don haka bana bayan kowa,
zabi yana gare ki, kamar yadda shari’a ta baki dama. Ina so ki gaya min wanda kika fitar ni
kuma ranar da na sanya ba zan daga ba zan daura aure”.
Kanta a sunkuye ba ta yi magana ba, har sai da Baffa ya gama yana sauraron ta. Ganin ta ki yin
magana ya ce,
“Kefa nake saurare Mairo”.
Daga can kasan makoshinta ta ce,
“Baffa ni bani da zabi a cikinsu, kamar yadda ka ce sharia ta bani damar in zaba, ni kuma na
baka wannan damar, ka daura da duk wanda ka ga ya dace. Duka ina son su ina kaunar su,
don haka ba zan iya zaben daya a cikin su ba”.
Baffa ya girgiza kai yana murmushi. Autar Inna Hure, bai san sanda zata daina yarinta ba!.
Ya ce,
“To shi kenan, tunda haka kika ce, na kuma gode da wannan GIRMA da kika bani, ya nuna min
cewa kin amince ba zan yi miki zaben tumun dare ba.
Da fatan duk wanda na zaba miki a cikinsu za ki yi min biyayya shima ki yi masa, ba tare da an
tsaya yin wasu tone-tone da kwakulo laifin da ya riga ya shige ba, za ki zauna lafiya dashi har
karshen rayuwarmu”.
Kanta a kasa ta ce,
“Na yi wannan alkawarin Baffa”. Ya ce, “To tashi ki koma kan aikin ki, Allah ya yi miki albarka”.
Cikin zuciyarta ta ce, “Amin”. Ta taso ta fito kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Daga Amiru har Junaid ba ta kara jin duriyar kowa ba. Ta bi shawarar Nabilah, da ta ce
dukkansu kar ta neme su ta rabu dasu.
Sai ana i gobe daurin auren da ba ta san da wa Baffa zai daura ba a cikinsu. Text din
Uncle Junaid ya shigo cikin wayarta da misalin karfe uku na sulusin dare. Ta zaro wayar daga
karkashin filonta, hannunta na rawa ta duba, ga abin da ke rubuce.
SAKON UNCLE JUNAID GA MAIRO!
“Marriage is much more important than mere relationship. It’s the root of all family tree. Any
mistake in sowing the seed will be disastrous.... a mature seed has better chances for
germinating than an immature one.... A garden close to one’s home has to be watered and
tendered than that which is very far away................... -Mai son ki.
(wato aure yafi muhimmanci fiye da dangantaka kawai. Domin shine jijiyar bishiyar iyali gaba
daya, don haka hadari ne babba asamu kuskure wajen dasa wannan bishiya.... kosashshen iri
zai fi saurin yado fiye da talalabuwa.... lambun da yake kusa da gidan ka zaka fi bashi ruwa da
kulawa, fiye da wanda yake nesa.............).
Ta karanta ya fi cikin carbi, kafin ta fahimci me sakon Uncle yake nufi. Yanzu ne ta fahimci ashe
duk sakonnin nan da ake turo mata tana Michigan da ‘logo’ na hular ilmi, ashe Uncle Junaidu
ne. Ta kifa kai cikin filon ta, tana kuka mara sauti. Kukan tausayin Uncle Junaidu! A lokacinda ta
fahimci Uncle Junaid ya sadaukar da soyayyarshi ga aurenta da ‘ya’yanta..... Ta yadda har ya
kira alakarsu da ‘mere relationship’. Ita ma ta yarda ta amince AMIRU SHI NE ZABIN ALLAH,
ba zabin zuciyarta ba......!!!
[8/20/2019, 06:30] Meema: Daga kowanne bangare ba su samu matsala ba, sun samu kwarin
gwiwa daga Baffa, Yaya Habibu da Alh. Abdurrahman Gaya. Wadanda burinsu kenan. Hatta
Hanan wadda ke da 'ya'ya biyu a lokacin da mijinta Ramadan ta samu halartar walimar maida
auren Dr. Mairo da Amirunta, Amina da Uncle Junaidu, wadda aka gabatar a ranar asabar,
juma'a, ashirin ga watan maris, daruruwan jama'a suka shaida daurin auren Mairo da Amiru a
karo na biyu, a kofar gidan Alh. Abbas mai goro.
Wannan aure ya ga kusoshin ilmi, daga Kano da wajenta, da daukacin jami'o'in Najeriya.
Furofesoshi, kwamishinoni da daktocin ilmi, abin ba a cewa komi.
Daga Mairo har Ameeru babu mai ra'ayin bidi'o'i, dokance suke da a sake mallaka musu juna.
Tsohuwar soyayya ce ke aiki tare da taimakon sabuwar soyayya. Ta dankawa Alh.
Abdurrahman da Hajiya Aisha jikokinsu kamar yadda suka nemi alfarmarta, sai fatan Allah Ya
ba ta wasu masu albarka.
Tana nan zaune a bakin gadonta, tana jiran angon wanda ke can yana ganawa da bakinshi, tare
da duba agogon hannunta.
Rabin awa kenan da fitar Dina, ta fada bayi ta sake sheko wanka mai suna wanka, tunda kuwa
ba ta taba yin irinshi a rayuwarta ba. Ta feshe jikinta da 'fehrenheit' da 'cerruti' dinta kamar
yadda ya ke a al'adarta.
Tana kokarin sanya kayan barci ya turo kofar ya shigo cikin bulalen 'pyjamas' yana rike da wani
dan fulas mai tsananin kyau. Kunya ta kama Mairo, kamar bata taba sanin Amirun nata ba,
wanda hakan ya janyo ta sanya rigar a bai-bai.
Amir ya yi murmushi, ya rausayar da kai ya iso gare ta, ya ajiye filas din hannunshi a gefe, ya
dora kanshi a dogon wuyanta. At last! Sa’ar tashi ce a karo na biyu. Gashi ga Maironsa, bayan
gushewar shekaru uku kwarara, cikin duniyar kuntatacciyar soyayya. Shikuwa me zai yiwa
Uncle Junaidu, ya biya shi a wannan duniyar? Babu, sai adduar Alheri. Kyawawan fuskokinsu suka zahhara cikin mudubin. Dukkansu suka saki sassanyar ajiyar
zuciya mai nauyi. Wadda ke cike da godiya ga Allah!
Cancarakas! Ya dagata ita da filas din da ya shigo da shi sai 'bed-room' dinsu. Ya zaunar da ita
a bakin gado, ya mika mata filas din, ya ce.
"Sako ne daga Nabilah, ta ce hannu-da-hannu na baki. Ya zama shi ne cimarmu a wannan
daren, sai dai ban san ko mene ne a ciki ba".
Ta soma kicin-kicin bude filas din, da kyar ta samu ta bude. Suka bi cikin filas din da kallo
dukkanninsu.
“Kwadon Rama” ne wanda ya ji kuli-kuli, tumatur da albasa sai kamshi ya ke. Dariya ta kama
Mairo, don ta lura Nabilah dai na son a TUNA BAYA…..... ne.
Mairo ta soma cin kwadon ramarta sosai, kunnenta kamar ya tsinke don dadi. Ta kusa cinyewa
ya rike fulas din, ya rausayar da ido yana yi mata kallon nan nasa da shanyayyun idanun nan
nasa, wanda ya kassara kuzarin jikinta. Ya tada wani tsohon al'amari, wanda ya riga ya shude a
tsammaninta. Amir da Mairo, suka ce “Takori kauce a nan, yau bama bukatarki”. ***
Washegari Daddy yayi kiransu, ya danka musu ‘passport’ dinsu, mai dauke da visar kasashen
duniya guda uku; Athens, Amsterdam da Pretoria. Yace da Amir yayi amfani da hutun sa na
karshen shekara suje su huta tsayin watanni uku.
Mairo bata tashi dawowa ba, sai da guzurin ciki watanni biyu dan Pretoria. Bayan sun dawo ta
nemi chanjin wajen aiki zuwa jami’ar Abuja, ba da son ranta ba, sai don ta samu kasancewa
full-time da mijin ta. Abin son ta. Uban ‘ya’yanta kuma abin kaunarta; Dan Abdurrahman Gaya.
A shekarar ne kuma akayi bikin kaddamar da Amiru Abdurrahman matsayin gwamnan CBN,
bayan gwamna mai ci a lokacin yayi ritaya. Ba don shekarun shi sun kai ba, sai don kwarewa
da sanin makamar aiki da dimbin tagomashin cigaba da ya kawowa Central Bank of Nigeria a
matsayinsa na tsohon ma’aikacin World Bank. Shima Uncle Junaidu ya samu ‘promotion’ zuwa
‘chancellor’ na jami’ar Bayero bakidaya. Zumunci da aminci bai taba yankewa tsakanin su ba.
Shekara na zagayowa Mairo ta direwa Hajiyar Amiru wani saitin 'twins' din data zabi a bawa
sunan (Ilham da Sagir) kannen Uncle, don bazata taba mantawa da kaunar da Ilham ta nuna
mata ba. Uncle yaji dadi kwarai kuma ya kawo Ilham daga Wales don kawai taga takwararta.
Farin cikin Hajiya Aisha abin ba a cewa komai. Dina ma ta sake samun Hurairah (Hure) bayan
fidda rai. Amina ta samu Atiku, Ikhlas ma matar Uncle ta sake haihuwa. To haka Nabilah duka
hayayyafa suke kamar kaji, sai mu ce Allah Ya raya, kuma Allah Ya kara dankon zumunci.
MASHA ALLAHU LA-KUWWATA ILLA BILLAH...
Maman Safah da Marwah ce....ke cewa.
Sai mun hadu a sabon littafin YAKANAH cikin yardar Maiduka.
Dandano Daga Yakanah
Karfe goma sha dayan dare garin kano yayi tsit, sai iskar hunturu dake kadawa. Malam Ja’afar
ya dauko tabarmar sa ya shigo cikin gida daga soron kofar gida. Zai gitta ta dakin Fati ya jiyo
sheshshekar kukanta. Ya dakata, ya dago labulen yana kallonta.
Tana zaune akan darduma ta kunshe fuskarta cikin hijabi sai kuka take. ya karashe
shigowa cikin dakin yace “Fadimatu kukan me kike yi?
A razane ta cira kai ta dube shi idanunta jawur sun yi luhu-luhu alamar tayi kuka har ta
gode Allah.
Malam Ja’afar ya zauna a wata ‘yar kujera dake dakin yana fuskantar diyarsa. Ta share
idonta da hankici, ta ja shashsheka kafin tace “Baba babu komai” ya jima yana kallonta sannan
yayi murmushi yace “kina tuhumar mu dayi miki auren da baki so, auren mijin ‘yar uwar ki. Ki yi
hakuri, alheri muke nufin ku da shi, ba zaki gane ba sai nan gaba. Idan kun gano gatan da
muka yiwa rayuwarku”
Fati tayi shiru tana sauraron babansu. Taga wannan itace damarta ta karshe. Daga gobe
za’a zarga mata igiyoyin wanda baya sonta. Ta kai kanta kasa tana kuka sosai tace “ku yi min
alfarma Baba. Baba baka taba sa ni in yi wani abu na shallake maganarka ba.
Amma a wannan karon ina so ka dubi hujjoji na. Baba. Dr Sulaiman baya so na, baba Dr.
Sulaiman yafi karfi na. bani da ilimin da zan jera da shi a matsayin matarsa. Baba sulaiman
bazai taba son wata ba bayan son da yake yiwa yaya Hadiza. Baba kune baku sani ba, amma
Dr. sulaiman ya tsaneni ban san laifin da nayi masa ba. Ban taba gaishe shi ya amsa ba, haka
bai taba kallona a matsayini jinin Hadiza ba balle yayi la’akari da wannan ya kaunace ni. In dai
don ‘ya’yanshi ne, ai nima ‘ya’yana ne…zan cigaba da rike su ba sai na zama matarsa ba……”
Ya ce “Amma zaki zama matar wani ko? Kuma babu wanda zai aureki da zugar ‘ya’yan yayar ki.
naji hujjojin ki Fati, amma nima ina so in tambayeki “wane abu ne Hadiza take da shi wanda ya
kaita ga matakin zama matar Babban likita irin Sulaiman???? Tana ‘yar talakawa kamar ki???
Mu biyo Fati da Babanta a littafin YAKANAH yana zuwa bada jimawa ba!!!!
__________-_TAKORI