Showing 9001 words to 12000 words out of 79746 words

Chapter 4 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

sai gaisawa suke da ita. Yayin da 'yan bakin-ciki, wato wadanda ke da 'ya'ya a
makarantar ba a kuma kirawo 'ya'yansu ba sai zumbure-zumbure suke yi mata, ko a jikinta wai
an tsikari kakkausa. Haka nan Mairo ce dalibar da aka fara kira ta amshi allonta daga hannun Mai girma shugaban
karamar hukumar Kumbotso. Malaminsu ya karanto mata farkon suratul Bakara tana bi
tiryan-tiryan cikin kira'ar da ta fi ta malamin.
Bayan nan Mairo ta karbi kyautar dalibar da ta fi kowa iya Tajwidi, sannan daliba mafi da'a a
gaba dayan daliban shekararsu. A sa'ilin da maigirma Chairman ya amshi lasifika domin
gabatar da jawabinsa na babban bako mai jawabi. Budar bakinsa sai cewa ya yi
"Na dauki nauyin karatun wannan yarinya MARYAM BEDI a makarantar sakandiren 'yammata
ta gwamnatin tarayyah da ke Minjibir".
Gabadaya aka sa kabbara. Abokan Malam Bedi suka shiga taya shi murna, ya rasa inda zai sa
kansa don farin ciki. Mairo ta riga su komawa gida domin an ce su tsaya za su gana da
Chairman.
Inna Hure na shigowa ta suri Mairo ta goya a baya, ta sa zane ta daure ta, ta sa majanyi ta kara
daurewa. Ta shiga zagaye dakin da ita, ita kuwa sai dariya ta ke. Kamin su zauna gabadayansu.
Malam Bedi ya gabatar musu da bayanin da maigirma chairman ya yi masa na cewa, zai
tallafawa karatun Mairo a babbar makaranta ta gwamnatin tarayya. Zai mika komai ta hannun
shugaban makarantarsu ta boko tunda dama gab ta ke da zana jarrabawar fita firamare. Ya
kare da cewa.
"Amma fa makarantar ta kwana ce".

Nan da nan farin cikin da ke makale a fuskar Inna Hure ya yaye, Mairo ta lura da hakan, ta ce
"Haba Inna, wannan ba wani abu ba ne. Zan dinga zuwa hutu kuma ana zuwa ziyara. Kin san
Lanto ma ta gidan Kado tana makarantar kwana a Kwa. Duk bayan watanni uku dawowa ta ke.
Sannan bayan kowanne wata ana zuwa ziyara". Inna ta ce "To ni wa zai kai ni birni? Har in gano ki a kowanne wata?"
Ta ce "Allah Shi zai kai ki, ga iyalin Baba Abbas za su iya raka ki".
Nan da nan Hure ta yi kicin-kicin da fuska ta ce "Ke, raba ni da wadannan mutanen. Ni dai na yi
hakuri har ki zo hutun".
Mairo ta yi murmushi ta ce "Shi ke nan Inna".
Malam dai jinsu yake a zuciyarshi yana mamakin dalilin Hure na kin son yin zumunci da iyalin
dan uwansa. Bai sani ba ita a ra'ayinta shi ne, idan har zata ke shiga shirginsu wata rana za su
sake yin yunkurin rabata da Maironta don taje tayi masu bauta amma ba don Allah ba.

Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, su Mairo aka kammala zana common entrace, aka zauna
gida zaman jiran sakamako. Ba jimawa ya fito, shugaban makarantarsu ya mikawa Chairman.
Cikin sati uku sai ga takardar daukar Maryam Bedi, cikin sabbin daliban FGGC Minjibir na
shekarar.

A na so kuma ta isa makaranta cikin sati biyu, hedimasta ya kira Malam Bedi ya damka masa
ya kuma gaya masa ya hadawa Mairo kayan abinci da ake hadawa dan makarantar kwana, ya
kuma ba shi katifar Mairo da filo, domin makarantar ba sa bukatar akwatun karfe.
Malam Bedi ya dawo gida shi da Hure aka hau shawarar abin da za a hadawa Mairo, Hure ta
daka mata kuli-kuli ta kuma shanya mata Rama mai yawan gaske, da zata dinga jikawa idan ta
yi sha'awa ta kwada ta ci, kwaki kwano biyar, kanzo kwano uku, yaji rabin kwano, omon wanki
da sabulun wanka. Man shafawa da man kitso, man kuli da manja. Mairo ta ce, su sayo mata
brush da maclean, aka siyo a Fanshekara. Shi ke nan kaya sun hadu sai tafiya.
A daren Inna Hure ta kwaba lalle ta yaba mata a kafafunta aka daure aka kuma zura hannun
dama cikin dumar lalle, shi ma kan safe ya yi jawur kamar jini, duk adon tafiya makaranta ne.
Aka tsefe kai aka yi mata kitson doka guda takwas. Babanta da Hedimasta su za su kai ta
Minjibir, don haka tun karfe bakwai hedimasta ya ke buga musu zaure da yake shi ma Chairman
ya cika shi da abin arziki duk don ya kula da karatun Mairo.
Mairo na kuka Innarta na yi, a haka suka rabu. Hedimasta dauke da katifar kwanan Mairo,
malam Bedi rike da dindimemiyar (Ghana Must Go), a haka suka doshi tasha. Hedimasta na ce
da Bedi daga wannan zuwan da zamu yi da kai, duk hutu kai kadai zaka dinga kawota, don
haka ka dinga kula da duk abin da na yi". Malam Bedi ya ce "To, angode dai".
Suka samu bayan motar rake suka dane, ta fito da su Fanshekara, daga nan suka hawo motar
Bata/Kuroda. A nan suka hau motar Minjibir, Mairo a maleji su kuma a kujerun gaban motar.
Tafiyar awanni biyu ta kawo su Minjibir, aka sauke su a tasha. Daga nan suka hau tasi aka kai
su har kofar FGGC. Suka gaisa da maigadi, suka ba shi ajiyar kayan su suka karasa cikin
makarantar. Jikin Mairo ya yi sanyi matuka ganin irin tsaleliyar makarantar da aka kawo ta.
Ta daga ido tana hangen dalibai cikin kayan makaranta iri daya, cikin tsari da nutsuwa.
Kowacce a nutsenta ta ke tsaf, tana tafe cikin kamala. Ba ka jin hayaniyar komi sai sautin
malamai suna koyarwa cikin azuzuwa, shi ma din a tausashe.

Mairo ta kalli kanta sama zuwa kasa, ta hango bambanci a farrake tsakaninta da irin jefi-jefin
daliban da ta ke ganin suna wulgawa.
Gabadaya sai ta ga kanta kamar wata almajira, duk da kuwa ta kure adaka, ta sha lalle. Ga
jambaki jawur ta rambada ta yi kuma jagira da digo a tsakiyar goshinta. Duk da hakan ba ta ji ko
dar na zama a wannan makarantar ta yi karatu ba. Ta yi tunanin cewa, ba wannan ne abinda ya
kawota ba, darasin da za a koya mata ne, Yaya Habibu ya dawo ya yi alfahari da ita. Suka tambayi ofishin shugaba aka nuna musu. Kai tsaye can suka dosa, Mairo na kallon yadda
daliban wani aji da babu malami a ciki suka yi cincirodo a taga suna kallonta. Sai hankalinta ya
tashi matuka, don haka har ta riga Hedimasta tura kai ofishin shugaba, don dai ta tsira daga
kallon wadannan yara. Shugaban makarantar Halima Dukku, ta yi tsai da ranta ta cikin gilashinta tana kallon
harbatsatstsiyar dalibar da aka kawo mata. Ta jinjina kai ba tare da ta tofa ba, ta karbi takardun
hannun Hedimasta ta sa hannu bayan ta duba ta kuma shigar da sunan Maryam Bedi cikin jerin
daliban da makarantar ta karba a wannan shekarar. Ta sa aka ba ta uniform, house-wear da
sauransu. Ta kalli takalmin da ke kafar Mairo ta ga silifa ne, wani bakikkirin da shi, ya kuma
hadu da wata kafa jawur kamar gauta. Ta ce ba sa ba da takalmi don haka aje a sayo mata

sandal ko cambus.
Hedimasta ya ce su yi masa alfarma ya bada kudin a siya mata, su baki ne a garin ba su san ko
ina ba. Ta kira leburanta, ta hadasu dashi, ya gaya masa sandal dari takwas ne, kambas dubu
daya da dari biyar mai saukin kudin kenan. Gabadayan su shi da Malam Bedi suka hada baki
suka ce, "Mai ka ce?" Ya sake maimaitawa. Malam Bedi ya hau salati amma shi Hedimasta da yake da dan karatunsa
na yaki da jahilci sai ya ce"Au to, ba mu sani ba ne, domin yanzu a aljihuna kwata-kwata naira
dari hudu ne, ga shi a ciki zamu hau mota. Amma ga wannan". Ya mika masa dari biyu, ya ce,
"Ko irin na dankon nan ne mai igiya a saya mata idan zata dawo sai a nemo". Haushi ya ishi leburan ya juya zai fita abinsa, shugaba ta yi gyaran murya ta dauko gudar naira
dari biyar guda hudu ta mika masa, ba tare da ta ce komi ba.
Malam Bedi ya dinga zuba mata godiya, ta ce, "Babu komi, ai da na kowa ne". Ta sa aka kira
mata wata prefect ta hadata da Mairo da kayanta gami da littattafai wadanda suke cikin kudin
makarantarta, amma babu jaka, ta ce su sayo mata daga baya, ta ce ta kai ta hostel.
Sai a lokacin ne kuka ya zo wa Mairo, shi ma Malam Bedi duk da dauriyarsa sai da ya sa habar
babbar rigarsa yana share hawaye. Suna dagawa juna hannu har su Mairo suka kule cikin
hostel.
Bayan prefect din nan ta damka Mairo a hannun house-captain dinsu sai ta koma aji.
House-captain ta nunawa Mairo dakinsu ta ba ta gado ta shimfida katifarta ta ce, to ta sanya
uniform ta tafi aji don kowa yana aji. Sai dai fa a ranta tana mamakin yadda aka yi wannan
bakauya ta zo makarantarsu. Mairo ta tube kayanta ta sanya na makaranta ta bi bayan captain har ajin da aka ba ta, wato
JSS 1A. Ta je staff room ta nemo class master dinsu ta hada shi da Mairo, ta koma nasu ajin.

Mairo ta yi tsuru a gaban allo, a lokacin da Uncle ke gabatar da ita a matsayin sabuwar daliba a
ajin. Abin da Mairo ta lura da shi shine, gabadaya 'yan ajin wani irin kallo suke mata na raini da
kyama, suna kyabe baki duk sai ta ji ta muzanta.
Uncle ya nuna mata kujerar zama gefen wasu fararen yara 'yan gayu guda biyu, da ba su fice
tsaranta ba. Ai kuwa suka soma matsawa jikin junansu suka takure suka ba ta katon fili.
Malamin ya lura da irin karbar da Mairo ta samu a ajinsa, duk sai ya ji tausayinta ya kama shi.
Ya dube ta ya ce, "Sake gaya min sunanki, ban gane abin da principal ta rubuta sosai ba".
A hankali ta bude dan kankanin bakinta ta ce
"Maryam Bedi".
Ya ce "What a nice name, maryama, saki jikinki ki zauna a inda na umarce ki. Ba ruwanki da
kowa sai abin da ya kawo ki, kina ji na?"
Ta gyada kai, amma ba ta amsa ba.
Ta karasa inda ya nuna mata ta zauna a darare. Yarinyar kusa da ita ta ja tsaki, tsuuu! Ta
murguda baki ta juya mata keya. Ta dauki tulin littattafanta ta zura su cikin lokar kujerarta tunda
ba ta da jaka.
Uncle ya fita cike da tunanin wannan yarinya. Yana daga cikin malaman da ba sa son ganin
rashin walwala ko yaya daga dalibansu. Abin da ya lura shi ne, Maryama ta shigo makarantar
da ta fi karfinta. Ya fi kowa sanin girman kai da ji da kai na daliban FGGC don haka ya samu
kansa da tausayin 'yar yarinya, Maryama.

Ya alkawarta wa ransa taimaka mata iyakar iyawarsa, har sai ya ga ta saki jikinta tamkar sauran
dalibai ‘yan uwanta.
Da aka tashi daga aji Mairo ba ta san dawar garin ba. Ta dai ga kowa na fita da littattafansa
babu wanda ya kulata, kai ba ta ma ishi kowa a ajin kallo ba. Sai ta kwaikwayi yadda suka yi,
wato ta kwaso littattafanta masu yawa da matukar nauyi ta nufi hostel kamar yadda ta ga sun yi.
Tana shiga dakin sai ta ga wadannan fararen yaran sun rigata isa har sun tube uniform sun sa
na hostel, ashe su ma a dakin suke. Suna ganinta ta shigo suka kara yin kicin-kicin da fuska
kamar an aiko musu da sakon mutuwa, musamman da suka fahimci a kusa da gadonsu ta ke.
Dayar ta yi tsaki ta canza harshe tana cewa da kawarta, "See this girl, i donno what she is
looking for here..."(kalli wannan yarinyar bansan me take nema a nan ba).
Kawar ta ce, "Kaddararmu ke nan, daki daya, aji daya, mts!"

Jikin Mairo ya kara yin la'asar, amma sai ta dasa wa ranta ta rabu da wadannan yaran ta yi abin
da ya kawo ta. Ta ajiye litattafanta ita ma ta tube uniform tasa na hostel irin wanda taga sun
sanya, ta nufi famfunan da ta ga ana alwala, ita ma ta yi ta nufi masallacin da ta ga ana shiga
da sauri ta samu jam'in sallar azahar. Da aka fito yunwa ta addabe ta, ta soma tunanin ta je ta kwada kwadon kwaki sai ta ji wata
senior na fadin a fita ‘dining’ za’a rufe hostel. Ta dinga maimaita kalmar 'dining' a ranta, ko mene
ne? Ta ga dai kowa fita yake yi sai ta bi bayan wasu yara ba tare da sun san binsu ta ke ba, har
zuwa wani katon dakin cin abinci inda ta ga dalibai a zazzaune kowa da filet dinshi ana ta cin
abinci.
Yawun bakinta ya tsinke, ta bi layin da ake bi a karba ita ma ta karba, jallof din shinkafa ce da
yankan nama biyu da soyayyar ayaba (plaintain) sala uku. Ta zauna ta ci ta koshi, ta sha ruwa
ta yi hamdala ta mike ita ma ta nufi hostel ta kwanta a gadonta don ta huta zuwa la'asar.
Da aka yi sallar la'asar kuma suka koma aji zuwa karfe shida. Haka dai ta yi ta bin abin da ta ga
ana yi, har lokacin barci.

A sannan ne ta samu damar kwashe kayanta da ke cikin (Ghana Must Go) ta jera a loka, kamar
yadda ta ga kowa ya yi. Yaran nan makotanta suka fito da wani irin abu cikin kwali da ba ta taba
gani ba suna ci, suna korawa da lemon gwangwani suna hira da Turanci, suna kallonta, ita da
kullin kayan kuli-kulinta suna ta dariya. Duk ta bi ta sha jinin jikinta, amma ba ta daga kai ta kalle
su ba, ta jika ramarta cikin 'yar robarta ta ajiye akan lokarta tana jira ta jiku ta kwada da kuli.
Tana ganinsu har lekowa suke da kai suna leka robar ta, amma ragowar jama'ar da ke dakin ba
ruwansu da ita, kowa gararin gabansa yake yi. Ta rasa dalilin wadannan yara na sa mata ido da
wulakanci a gare ta, daga baya ta fuskanci daya sunanta Nabilah, daya kuma Kausar.
Ta kwada ramarta ta ci ta koshi, ta sha ruwa ta kwanta a katifarta da ko zanin gado babu. Ta
rufa da zanin atamfar Innarta, wadancan yaran kuwa irin bargonta da hedimasta ya cinye suka
rufa da shi. Hatta filon ya dauke ya cinye saboda rashin tsoron Allah irin nasa. Aka yi (light-off)
na gabadayan hostel din, ta shafe jikinta da addu'o'i ta kwanta. Washegari da aka yi sallar asubah ta ga kowa yana bin layin wanka, don haka ita ma ta bi ta yi
wankanta ta yi sallah a masallaci tare da Imam. Daga nan aka tafi aji.
Suna shiga aji ta ga mutanenta sun dauke bencin gabadaya sun maida shi wurin da ba kowa
sun zauna, sun kuma kira wata yarinya sun zaunar da ita a wajenta. Ta rasa inda za ta zauna,

ta koma karshen ajin ta sanya littafinta daya a kasa ta zauna akai. Zamanta da kamar minti
biyar Uncle din ajin ya shigo. Yana ta jefa ido ya hango Mariaman da ya kwana ya tashi da
tunaninta jiya, amma bai ganta ba.
Gabadaya ajin aka mike, ita ma sai ta mike kamar yadda suka yi, suka hada baki gabadaya
suka ce "Good morning Uncle".
Ya ce, "Morning class, how are you all?"
Suka sake hada baki gaba daya suka ce "We are fine Uncle". Sannan ya yi umarni da a zauna.
A sannan ne ya hangota makure a can layin karshe kamar mujiya, kuma a dandaryar kasa. Bai
ce komi ba ya bude rajista ya yi kiran lambar kowa, ya amsa, sai a karshe ya ce "No. 40". Shiru
ba a amsa ba, a lokacin ya gane lambar Mairo ce, sai ya ce, "Mariama daga yau ke ce no.40".
Ta ce "To".
Ya rufe rajistar ya dinke fuska sosai, ya ce
"Kausar!"
Ta amsa, "Yes Uncle".
Ya ce "mene ne dalilinki na janye benci ki hana Mariama zama?"
Ta yi shiru ba ta amsa ba.
Ya dubi dalibar da suka zaunar a wajen, "Ke Laila ina wajen zamanki? Me ya kawo ki nan?"
Ta yi saurin mikewa ta koma wajenta.
Ya ce "Kausar fito nan".
Ta fito tana gatsina ita a dole ga 'yar masu kudi. Saura kadan ya zabga mata mari, sai dai ya
yaki zuciyarshi ga yin hakan, ya ce ta fita waje ta yi kneel down, har zuwa lokacin break.
Ta cika ta yi fam, kamar balam-balam, dama ga ta buleliya. Ta zobara baki, ta ce "Ai ba ni kadai
na janye bencin ba, har da Nabilah".
Nabilah ta ce "Wallahi Uncle babu ruwana, ita ce ta ce wai ba zata zauna da billager ba".

Bai yi mamaki ba, sai ya bude murya yana tambayar 'yan ajin "Shin dama akwai banbanci
tsakanin musulmin kauye da musulmin birni?"
Suka ce "A'ah Uncle".
Ya ce "To me ye laifin wannan yarinya da kuke kyamarta?"
Wasu daga ciki suka hau matsawa suna cewa "Ta zo ta zauna a kusa da mu".
Amma Uncle sai cewa ya yi, babu inda zata zauna sai bencin su Nabilah, don haka idan
Nabilah da Kausar baza su zauna tare da Maryama ba, sai dai su koma gidan ubansu.

Mairo dai na sauraron ikon Allah. Tana tunanin yadda ta ke abar so a wurin Innarta da Babanta,
amma wai yau ake takaddama akan inda za ta zauna sabida ita an ga alamar ba ta da arziki.
7/28/21, 10:59 AM - Buhainat: 30


A lokacin ta ji wata zuciya na shigarta (determination) akan rayuwa. Ta alkawarta wa ranta idan
ilimi na kawo arziki, to zata neme shi ko don 'ya'yanta. Za ta nemi ilimi har sai ta ga karshensa,
idan har ana gani. Ba zata so a yi wa danta irin wannan wulakancin ba. Uncle ya lura Mairo
kuka ta ke yi, sai zuciyarsa ta karye. Don haka tunda ya gama kiran lambar sai ya fita, bayan ya
tabbatarwa Kausar kada ta sake ta bar kneel down din da yasa ta har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login