Showing 27001 words to 30000 words out of 79746 words

Chapter 10 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

kwashe tuwon dare".
Ta ja kujera ta soma wanke-wanken, Hajara ta sake cewa "Ki dinga iza min wutar nan, sallah
zan yi".
Ta ce "To".
Hajara na shiga bayi Habiba ta fito, ta ce "Cika min randar can da ruwa, ga kuma
tsummokaraina ba yawa, ki dauraye min su".
Ta zube mata tulin atamfofinta a gefe, ta ce "To bari in karisa wa Aunty Hajara wanke-wanken,
ta ce tuwo zata kwashe".
Habiba ta ce "Inye, wato aikin Hajara ya fi nawa don ni kin raina ni, sabida ina sakar miki
fuska?"
Ta tsame hannunta daga wanke-wanken zata fara yi mata wankin Hajara ta fito daga bayi ta ce
"Au, bar min wanke-wanken za ki yi sabida kina tsoronta? To ba zaki yi wankin ba, sai kin gama
mini".
Suka soma bala'i a tsakaninsu, Mairo dai tsayawa ta yi kawai tana kallonsu.
Baffa ya shigo yana "Kaiconku! Harshenku a matsayinku na matan aure, amma har a makota
ana jiyo ku, asararru wadanda ba su san mutumcin kansu da martabar da Allah Ya yi musu na
matan aure ba".
Ya dubi tulin aikin da suka tilawa Mairo yana salati, ya ce "Habiba waye zai yi miki wannan
wankin?"
Ta yi shiru, ya ce "Da ke nake magana fa".
Ta soma rawar murya amma ba ta fasa tsiwa ba, ta ce "Au... to, kana nufin haka zamu aje
gansamemiyar budurwa kamar Mairo sai dai mu tuka mu bata ta ci ta side hannu ta mike a
katifa?"
Ya ce "Ina almajirin da nake biya yake yi muku wankin?"
Cikin rashin gaskiya ta ce "Bai zo ba".

Ya ce "To kwashe kayanki maza-maza tun kafin mu sa kafar wando daya da ke, idan ya zo ya yi
miki, ko ki tura 'ya'yanki su kirawo shi ya yi miki, amma bazan lamunci wannan rashin arzikin ba.
Mairo ba baiwar uwar kowa ba ce a cikinku, wallahi-wallahi bazan yarda ku maidata baiwa ba.
Bazan hanata ta taimaka muku da ayyukan gida ba, amma banda wankau da dakau. Ke
Ladidi!"
Ya kwala mata kira, ta fito a razane, "Zauna nan don ubanki, ku yi wanke-wanken tare ko in
kwashe miki hakora yanzun nan".
Ta ja kujera ta zauna tana zumbure-zumbure, suka soma wanke-wanken tare.

Wannan tsayawa tsayin daka da Alhaji Abbas ke yi akan Mairo da al'amarinta, ya sayo mata
matsananciyar kiyayya a gurin iyalansa, sun dauki tsanar duniya sun daurawa marainiyar Allah,
daga su har 'ya'yansu, su suyi mata, 'ya'yansu su yi mata, amma ba zasu kwabe su ba. Barin
Ladidi da ji ta ke da da hali, da ta cakawa Mairo wuka ta mutu kowa ya huta da bala'in Baffa a
kanta.
Kwana bakwai kacal da dawowar Mairo daga makaranta, duk ta bi ta kare kamar kudin guzuri,
sai karan hanci da idandunan kadai, sabida rashin dadin rai da rashin kwanciyar hankali. Bata
taba ganin mutane marasa imani da rashin darajja dan Adam irin Habiba da Hajara ba.
Amma a kullum tana yi musu uzuri da yafe musu cikin zuciyarta. Ba kowa ne zai iya rike dan
mutum ba a wannan zamanin, tunda dai sun yarda su zauna da ita, to ba zata kasa yi musu
biyayya ba iyakar iyawarta.

Wata mota kirar Kia-Rio ta yi fakin a kofar gidan Alhaji Abbas, misalin karfe goma dai-dai na
safe. Lokacin Alhajin bai kai ga fita kasuwa ba. Nabilah Bebeji, ta fito daga mazaunin direba
tana duba agogon hannunta, ta doshi kofar gidan Alhaji Abbas, tana mai addu'ar Allah dai Ya sa
Baffan Mairo bai fita ba. Ta yi sallama a tsakar gidan, Habiba ta amsa yayin da ta bi ta da kallon mamaki. Sanye ta ke da
atamfa mai karshen tsada shudiya ta karkata dauri mai ban sha'awa kamar nadin inji, a
hannunta 'yar matsakaiciyar jaka ce, samfarin Louis Buittion da takalminta marar tudun
dunduniya. In ban da kamshin turaren Rasasi (blue-royale) ba abin da ke tashi a jikinta, ta yane
jikinta da gyale kalar atamfarta, daure a hannunta agogo ne shudi samfurin polo.
Jiki na rawa Habiba ta dauko sabuwar tabarma ta shimfida mata, ta tsugunna har kasa ta
gaishe ta, ta gaya mata ta zo wajen Mairo ne. A lokacin Mairon tana bayi tana wanka, cikin
bakin-ciki karara Habiba ta yi mata nuni da dakin su Mairo kamar ba ita ce mai yi mata fara'ar
da ta ke yi mata ba. Dakin tsaf ya ke, da yake Mairo ba ta wasa da tsaftarsa, sau dubu Ladidi zata bata, sau dubu
zata gyara.
Ta samu gefen katifar Mairo ta zauna, ta dauki wani littafi na Mairon da Mairon ta aje, da alama
shi ta ke karantawa kamin ta shiga wankan na Dynasties the Ashtons (Condition of marriage),
ta ce "Maryama na nan da karance-karancenta".
Dai-dai lokacin da Mairon ta shigo, kanta na yararin ruwa domin wankan sallah ta yi, zata soma
sallah. Ta harari Nabilah ta ce, "karfe taran ke nan?"
Ta yi murmushi ta ce "Go-slow ya tare ni, amma ai na yi kokari, ke fa da sai yanzu kika yi
wanka, ni tun asuba Momi ta tashe ni wai inyi maza in shirya in dauko mata Mairo ta ganta".

Ta yi murmushi, ta ce "Yau dai da yardar Allah zan ga Momi".
Ta ce "kwarai kuwa".
Mairo na shiryawa Nabilah na kallonta cikin yin tazbihi ga Sarkin halitta da Ya kaga halittar
Mairo.
"MAIRO MATAR MANYA CE". Nabilah ta ayyana a zuciyarta. Wani irin jiki lukui-lukui kamar mai
shiga wankan inji, ga kwantaccen gashi na fulanin usuli, wanda ke kwance lambam akan dogon
wuyanta yala-yala da shi kamar ba zai kitsu ba, alhalin ba ta taba shafa masa relader ba koda
wasa. Idanuwanta dara-dara, farare kal masu wani irin maiko da sheki (oily-eyes). Kai ita ba ta
taba ganin mace mai lafiyayyen kugu da shafaffar mara irin Mairo ba. Kai ka ce idan ta sunkuya
karyewa zata yi. Tana sharce kanta ta lura Nabilah kallonta ta ke, ta ce "Ke don Allah wannan
kallon fa?"
Ta ce "ke din ce, abun kallon ce Mairo, duk mijin da ya aure ki ya caba, ai ban san haka kike da
kyau ba sai yau".
Ta yi murmushi ta ce "Ni kuma ban taba ganin mai kyau irin naki ba Nabilah".
Ta ce "Kayya! Gyara ne kawai Mairo, ina maganar natural beauty ne".
Sai Mairo ta ja bakinta ta tsuke, ba ta kara cewa komai ba.
Ta kammala shiryawa tsaf cikin atamfarta ta ganin sarki (Ghana wad), wani tausayi ya kama
Nabilah, mace har mace, sai dai ba kayan ado, da da suttura ya ya za a ga Mairo? A hakan ma
Mairo abin a juyo a kalla ce, ina ga ta samu sutturu da kayan gyara? Sai dai duk yadda ta so ta
dinga taimakawa Mairon tun a makaranta Mairon ba ta yarda, cike ta ke da wadatar zuci, kuma
cikin godiyar Allah.
Mairo ta yi wa Nabilah jagora zuwa dakin Baffa. Ta zube a kasa ta gaishe shi, ya amsa cikin
far'a da cewa, "Lafiya kalau Nabilah, an gama karatu sai aure ko, ko kuwa babbar makaranta za
ki wuce kamar kawarki?"
Ta ce "Eh, makaranta zan wuce".
Ya ce "To Allah Ya ba da sa'a".
Sannan ta gaya mishi ta zo ta dauki Mairo su je gidansu, iyayenta su ganta. Ya ce "Babu
damuwa, don Allah kada Mairo ta kai dare".
Suka ce "Insha Allah".
Cikin nutsuwa Nabilah ke tuki har suka hau kan titin sakateriyar Audu-Bako, Mairo ta dauka
Tarauni suka nufa, sai ta ga Nabilah ta karya akalar motar ta sha round ta hau kan titin state
library, ba ta kai karshen titin ba ta yi kwana ta shiga unguwar Ahmadu Bello Way, ta tsaya a
harabar gidansu mai lamba dari da biyu (No. 102), suka rufe motar suka karasa cikin gidan. Tun Mairo na mamakin tangama-tangaman falullukan da suke wucewa har ta daina mamaki, sai
tazbihi ga Allah Mai azurta wanda ya so. Ba ta taba shiga gida irin wannan ba ko a mafarkinta.
Ba su tsaya a ko'ina ba sai a babban falon Momin Nabilah, wadda ta fito tana tafa hannu tana
'Lale da Mairon Nabilah". Ta yi murmushi ta zamo daga cikin kujera tana gayas da Momin, kamin ai haka tuni Nabilah da
wata dattijuwa wadda da alama mai aiki ce sun cika gaban Mairo da kayan tande-tande da
lashe-lashe irin wadanda ba ta taba ci ba a rayuwarta.
Shi ma Daddyn Nabilah ya sauko yana marhaban da Maryam. Ya zauna a cikin su, Mairo duk ta
kasa sakewa sabida bakunta da rashin sabo. Saukin kan iyayen Nabilah ya burge ta. Ta
tabbatar Nabilah 'yar gata ce ta karshe, ita kadai ce kwallin kwal, a wurin iyayenta. Daddy ya ce

da Mairo da zarar takardunsu sun fito ta kawo mishi zai taimaka su samu gurbi a jami'a ita da
Nabilah, ta yi godiya sosai.
Karfe biyar na yamma Mairo ta yi haramar tafiya. Akwati guda Momi ta shake mata da kayan
shafa da dogayen riguna kala-kala, Nabilah ta maidota gida.
Tana shigowa idanun Hajara da Habiba akan jakar hannunta. Jikin Habiba har rawa yake, ta bi
bayan Mairo tana son ta ji ina Mairo ta samo wannan diyar arzikin, har ga shi ta dawo da
galleliyar jaka cike taf da kaya.
Har karo suke ita da Hajara wajen shigowa dakin. Habiba ta ce "Bude jakar mu gani, me muka
samu?"
Hajara kuma ta ce "Wannan bakauyar ta iya bude irin wannan jakar ne? Gafara nan ki gani".
Ta jawo jakar ta soma kici-kicin budewa. Ta zazzago duk kayan da ke ciki tana al'ajabi. Habiba
ta ce "Ina kika samo wannan diyar arzikin kuma?"
Mairo ba ta yi magana ba suka soma kasawa, Habiba ta daga rigar da ta fi kowacce kyau a ciki,
ta ce "Wannan zata yi wa Ladidi". Ta sake daga skirt da rigarshi ta ce, "Wannan sai a bar wa
Batulu idan ta kara girma zata yi mata dai-dai, ke ki rike wannan din".
Ta tura mata wata 'yar yaloluwar rigar barci suka tattara kashi uku bisa hudu na kayan suka yi
waje da sauri har suna tuntube tareda karo da juna kada Baffa ya jiyo su suka gudu dakinsu.
Mairo ta ce, "Allah na tuba, suttura tsumma, mene da zan damu kaina?"
Duk da Baffa ya hana a bata aikin wahala wanda ya fi karfinta ba su fasa ba a bayan idonsa.
Mairo na hakuri da su da kokarin kyautata musu su da 'ya'yansu a kullum, amma ta rasa dalilin
da yasa mutanen nan suka ki jininta, ko zata wuni tana aikin bauta, shara, wanke-wanke, wanki
da wankin bandaki ba zata taba yi musu gwaninta ba, balle kalmar “madallah” ko “an gode” ta
gitta a tsakani.
Watanni uku cif da gama makarantar su ta samu labarin fitowar jarrabawarsu, don haka ta soma
shirin zuwa gidan su Nabilah don su je makaranta su karbo sakamakonsu.
Baffa da kanshi ya kaita gidan su Nabilah tana yi masa kwatance tana nuna masa hanya har
suka iso gidan. Ya sauke ta ya juya da cewa, idan sun dawo Nabilar ta maidota gida.
Amma Allah sarki, sai ta tarar da Nabilah kwance ba ta jin dadi. Ta zauna a gefen gadon da ta
ke kwance ta dora hannu akan goshinta, zafi rau! Momi ta shigo da filet a hannunta mai dauke
da soyayyar plaintain da dankali da kwai, ta ce "Ungo ba ta Maryam da kanki, watakila zata ci,
tunda ni nayi-nayi ta ki karba". Mairo ta ce "Haba Nabilah, ciwo da rashin cin abinci ai abin ba kyau, ki daure ki ci ko kadan ne
don Allah".
Ta karba tana kokarin mikewa, Mairo ta tusa mata filo a bayanta don ta ji dadin jingina. Momi ta
fita ta bar su. Tana fita Nabilah ta fashe da kuka mai tsanani. Hankalin Mairo ya tashi, ta ce
"Lafiya Nabilah? Wani abu ya faru ne?"
Cikin kuka ta ce, "Me ye bai faru ba? Hajiyar Daddy ce ta zo ta ce ba ta yarda na ci gaba da
karatu ba, aure za a yi min da wani cousin dina. Bayan kuma bana sonsa, kuma sati mai zuwa
za a daura auren, shi ma bai ce yana sona ba, wai wata Igbo ya zo musu da ita daga can inda
yake karatu a Kudu, shi ne ba su amince masa ba, suka ba shi ni. Allah na tuba auren soyayya
ma bai tsira ba a wannan zamanin balle auren tushe? Sabida Allah na yi kama da matar tushen
iyaye?"
Mairo ta rasa abin da zata ce "Ki ce ba ciwo kike ba, tunanin aure ne. Ni ban ga aibu a nan ba,

tunda iyaye ne suka hada, ai ALHERI ne, kuma alherin suke nufin ki da shi. Ki yi biyayya ga
iyayenki Nabila za ki ga da kyau a rayuwa.
Soyayya aikin banza ce, don watakila yadda kike son mutum shi ba haka ba ne a zuciyarshi ba.
Na gani akan kaina Nabilah. Har yanzu kuma ban ga inda soyayya ta kaini ba, sai kunci a zuci,
ruhi da gangar jiki. Nabilah yau zan gaya miki abin da ke raina shekara da shekaru. Wato
soyayyar Uncle Junaidu. Na dauka yadda na ke azabtuwa a zuci, da gangar jiki da soyayyarsa,
shi ma haka yake sona, ashe ni ban sani ba, Uncle ba haka ba ne a zuciyarshi ba.
A ranar da na yanke shawarar fallasa mishi asirin zuciyata, a ranar ya zame, ya gudu ya barni,
ba tare da ya sanar da ni komi a kanshi ba. Wanda ke nufin ba ya bukatar anymore mu'amala
da ni. Har yau ni kadai nasan abin da nake ji a zuciyata Nabilah. Hasashenku ke da Innata, bai
zamo gaskiya ba, Uncle Junaidu ba SO NA yake yi ba, tausayina ne da taimako".
Nabilah ta yi shiru cikin mamaki, yau Allah Ya nuna mata ranar da Mairo ta bude bakinta da
kanta ta fada mata cewar tana son Uncle Junaidu.
Ina ma ace shi ma hakan ne a zuciyarshi? Duk duniya ba ta taba ganin mijin da ya dace da
Mairo ba, irin Uncle, wanda yasan zahirinta da badininta, jinin jikinsu ke gauraye guri guda yana
circulating. Amma ba zata taba yarda cewa wai Junaidu ba son Mairo yake ba.
Babu wanda zaka bai wa jinin jikinka sai wanda kake matukar so.
Ta dago a hankali ta dubi Mairo ido cikin ido, ta ce "Wallahi Mairo yadda kike son Uncle, shi ma
haka yake sonki. Zan yi rantsuwa in dafa Alkur'ani akan hakan. Sai dai ban san dalilinshi na
janye kafa a ranar da zaku rabu ba. Zan yi mishi uzuri da wani abu mai muhimmanci a gare shi,
amma haka kawai Uncle ba zai ki yi miki sallama ba, sai ko sakamakon wani muhimmin abu da
ya faru gare shi.
Rashin haduwarku ya zama rahma ke nan ga mutumcinki da martabarki a idanunsa……."
Ta yi saurin duban Nabilah, tana mai daga gira ta ce, "Yes, gara da Allah bai baki ikon ki furta
masa ba, wai ya aure ki koda ba ya sonki. Duk inda yake, Mairo ni na gaya miki ko ba dade ko
bajima WATARANA zai neme ki, ki rike wannan a zuciyarki ki ce, ni na gaya miki".
Ta mike ta fada bandaki tana cewa, "Bara na shirya mu tafi, ni har ma na warke da ganinki
Mairo".
Ta yi dariya, cikin samun nutsuwa a zuciyarta da kalaman Nabilah, ta ce "Dama ba wani ciwo ke
damunki ba, sai shagwaba da gata, da suka taru suka lullube ki".
7/30/21, 1:01 PM - Kawata: B
Sun isa Minjibir ana sallar azahar, zuwan da ya tuna musu da dabdalar kuruciyarsu. Shekaru
shida cur, cikin dalibtaka da al'amura masu dama, da suka faru cikin rayuwarsu, suka tuno
Kausar suka yi mata addu'a. Suka karasa Edam office suka amso sakamakonsu. Ba abin da
suka fadi, sun cinye sun lashe 9 credits ris. Ina ma Uncle na nan, ya zo ya ga girbin abin da ya
shuka?
Nabilah ta kasa daurewa ta tambayi Mr. Kayode malamin lissafinsu, ko ina Uncle Junaidu? Cike
da alhini ya ke sanar da ita cewa, "Yau watanninsa uku kenan da tafiya karo karatu (in-serbice)
zuwa kasar Russia (Ukhrain). Yana daga cikin malaman da federal ta dauki nauyin karo
karatunsu a kasashen duniya talatin da biyar".
Mairo ta samu wani kututturen bishiya ta zauna ta yi kukanta mai isarta, kuka irin wanda ba ta

taba yi ba a rayuwarta, ko a rashin iyayenta kuwa. Ta tabbatar wani bigiren nata ya kuma
faduwa. Ta dubi takardunta, wahalar shekaru shidda da Uncle ya yi, yau ga shi Allah Ya cika
mishi burinsa, amma ashe ba zai gani ba.
Kuka ta ke kukan sabo, soyayya da kewa. Ta tabbatar ta rabu da Junaidu ke nan har abada! Ya
yi mata nisan da ba zata taba kamo shi ba. ALHERINSA da kyautayinsa masu yawa ne a
gareta da ba zata taba mantawa ba. Soyayyarsa da kaunarsa wani abu ne da ba zai taba
gushewa daga zuciyarta ba. Shi kadai ta fara so, kuma shi kadai zata ci gaba da so har zuwa
karshen rayuwarta, yana sonta ko ba ya sonta. Ta tabbatar ita ke son Uncle, amma shi ba
hakan ba ne a zuciyarsa ba, ai yasan inda zai same ta, da yana sonta da ya neme ta.
Ciwon kana so ba a sonka, matukar ciwo ne da shi. Ya san ba ta da kowa a duniya a halin
yanzu, daga Baffa sai shi, amma ya yi mata haka, ya ki tallafar rayuwarta a dai-dai lokacin da ta
fi bukatar tallafinsa. Ta kullaci Uncle Junaidu kullata mai tsanani, irin kullatar da ta yi wa Habibu
tare da alkawarta wa ranta yin kokari ta yakice shi daga zuciyarta, ta fuskanci rayuwa ta karbeta
a duk yadda ta zo mata.....!!!

***​***


B
ikin Nabilah bai yi armashi ba, sabida amaryar da angon duk sun ki ba da hadin kai, sai iyaye
da 'yan uwa ke ta sha'aninsu cikin farin ciki. Ko yaushe Mairo na tare da Nabilah, don ita kadai
ce zata yi mata magana ta ji. Abinci ma sai Mairo ta lallashe ta sannan za ta ci, don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login