Showing 54001 words to 57000 words out of 79746 words

Chapter 19 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

ta tashi da kewar Dina kwarai a ranta, ba abin da ta ke so irin ta ji muryarta. Ya
dawo daga sallar juma'a shi da Daddy daga babban masallacin Abuja kamar yadda suka saba
kowanne sati idan suna nan. Ta rasa yadda zata yi ta roke shi ya ba ta aron waya. Dabara ta
fado mata don haka ta nemo biro da 'yar takarda ta rubuta mishi, ta soke a jikin kofar dakin da
ta tabbata shi ne nasa.
Ya zo shiga dakin don sauya manyan kayan da ke jikinsa ya cimma sakonta. Ya yi murmushi ya
sumbaci takardar ya share ta bai ce mata komai ba.
Sai da daddare sun yi shirin kwanciya, bayan ya jefa filonshi ya mike. Ta zuba tagumi a gefen
gado abin duniya ya dame ta, idan jurinta miskilanci ta gamu da wanda ya fi ta miskilanci. Ta
juyo kadan, ga dukkan alamu barci mai nauyi ya tafi da shi. Cikin sanda kamar barauniya ta iso
gabanshi don ta dauki daya daga cikin wayoyinshi sai caraf! Ya damke hannunta tareda wayar
ya kuma bude lumsassun idanunshi sannu a hankali a kanta.

Kunya ta duniya Mairo ta gama jinta. Ashe ba a yi komai ba sai sanda ya fizgota ta fada gaba
daya a jikinshi. Ta rasa inda za ta sa kanta don kunya, fargaba da wani bakon tsoro da ya
ziyarce ta duk a lokaci guda.
Jikinta ya soma rawa kamar mazari, amma hakan bai sa ya cikata daga sassaukan rikon da ya
yi mata ba. Duk yadda ya so da su hada ido cikin dan sauran hasken fitilar baccin dake dakin
amma Mairo ta ki. Runtse idon ta shiga yi da karfi. Wani sabon Son mijinta AMIRU da kaunarsa
ne farat daya suke tsirgawa a zuciyarta. Wadanda bazata iya tantance tun tsahon wane lokaci
hakan ya soma ginuwa a zuciyarta ba. Yana danne wancan feeling din mai karfi da dukkan
tasirin sa, wanda zuciyarta ta dade tana kallon Amiru dasu. Tareda gina mafarkanta da shi a
kansa.
Ya dago fuskarta daga kirjinsa, a wannan lokacin ya yi nasarar hango cikin kwayar idanunta,
cikin murya irin ta wanda ya tashi daga bacci ya ce
"Sata ko Mairo?"
Ta ce
"A'a, ina so in kira Anti Dina ne, kuma na fada maka ai ba ka ba ni ba".
Ya ce
"Ni ban kai kararki wajen Anti Dinan ba, sai ke za ki kai karata?"
Kamshin 'mouth fresh' dinshi na fizgarta, yana sanya mata rashin kuzari ta ce,
"Me ka yi min da zan kai kararka, kuma nima me na yi maka da zaka kai karata?"
Ya ce,
"Kin yi min laifuffuka da yawa Mairo, wadanda idan na fadawa Anti Dina sai ta zane ki wallahi".
"Dame-dame ne laifuffukan nawa?"
"Ai ba ki ma sansu ba?"
"Da na sani bazan tambaye ka ba".
"To sunkuyo nan na fada miki".

"Kinga na farko ba kya gaishe ni da safe, sannan ba kya zuwa dakina taya ni kwana, sai dai ni
na biyo ki dakinki. Sannan idan na biyo ki ba kya hada makwanci da ni, sai ki bar ni a kasa ki
dare gadonki. Haka Dinan ta fada miki tana yi wa Habibu? Ko ba ki ga har kaya ita ta ke saka
mishi ba? Amma ke bana jin ko inda nake wanka kin sani a gidan nan ko don har yanzu ba kya
sona?"
Taji zafi a ranta da kalamansa. Da zai taimake ta da ya daina zancen rashin so a tsakaninsu. Ta
ce
"Maganar ina sonka ko bana sonka, tunda mun riga mun kasance cikin inuwar AURE, to bata
taso ba, bare kuma ni wallahi ban taba jin kiyayyarka a raina ba. Ko wancan lokacin da na fada,
na fada ne kawai don ban amince da irin son da zuciyata ta ke yi maka ba".
Ya lumshe ido a hankali, tare da sake yi mata muhalli cikin ni'imtaccen kirjinshi mai cike da
gargasa.
Yace “wane iri ne shi wancan son?” Ta dan rufe ido kafin tace “irin na shirme!”.
“Wane irin so ne irin na shirme?”
Amiru ya tambaya cikin mamaki.
Mutsu-mutsun kwacewa ta hau yi, ko zai kashe ta bazata iya yi masa wannan bayanin ba.
Sako riko ta yayi da karfin da yafi na dazu, ya juyo ta sannan ya sa hannu ya dago habarta.

Yana iya ganin kyallin dake cikin idanunta wadanda ke cike taf! Da soyayyar data mamaye su.
Soyayya mai cike da kauna mara algus or material attachement. Zaiyi rantsuwa bai taba ganin
wannan yanayin cikin kwayar idanunta ba, wani yanayi da yake matukar jira, yake kuma da
yakinin zai iya cigaba da jiran zuwansa cikin idanun Mairo har nan gaba da shekaru goma kafin
ya yarda ya hada shimfida da ita.
"To yanzu fa? Mairo! Mairo yanzun kina sona?"
Amiru ya tambaya, da wata murya tamkar ba tashi ba.
Sai ta yi murmushi, irin wanda bai taba gani bisa siraran labbanta ba.

Wannan kadai ya tabbatar mishi da cewa, ya gama mallakar soyayyar Mairon, saura da me? A
take shi ma ya soma mallaka mata ta shi. Cikin wani irin salo mai ban mamaki da Mairo ba ta
taba tunanin akwai irin wannan soyayyar a duniya ba. Koda a duniyar karance-karancen novels
dinta kuwa. Su Hajiya Mairo, tun ana dauriya, ana cijewa, cikin bin shawarwarin uwardakin ta Dina, har
lissafin ya soma kwace mata......aka kai ga gejin kiran Anti Dinah, Baffa, da Yaya Habibu su zo
su kawo taimako. Yau har Ladidi da Nabilah sun sha kira don tana ganin karshen rayuwarta
yazo! Shi kanshi Amirun ya rasa control din kansa, ta yadda har zai yi tunanin cewa Mairon
virgin ce, ba kamar matarshi ba. Tunda yake a rayuwarsa bai san akwai Hurul-eeni tun a duniya
ba. Bai san aure iri-iri ne kuma suna ya tara ba. Don haka bai farga da aika-aikar da ya yi ba,
sai da ya duba ya ga Mairon ta sume mishi.
Ba ita ta dawo hayyacinta ba sai da sanyin ruwan 'ragolis' ya ratsa kwanyarta, da sauran
sassan jikinta. Ya rungume ta sosai, tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanyata, cikin shauki ya ce
"Mairo kar ki gudu ki barni! Mairo ki ci gaba da zama da ni ko ba kya sona, ni ina sonki da
dukkan ruhi na! Ki rike naki son ko bazaki bani ba! Zan zamo ‘impotent' a duk ranar da kika guje
ni, ko kika juya min baya...!"

***





MAIRO A GIDAN AURENTA!


Zuwa yanzu, wato watanni biyu a gaba, Mairo an zama manyan mata, an iya komai na kula da
miji. Ta iya daukewa mijinta lalurar da mata hudu ba zasu iya dauke masa ba. Soyayya, kauna
da shakuwa ke kara kamari tsakaninta da mijinta. Ga kauna da kulawa da ta ke samu daga
surukanta kamar su suka tsugunna suka haife ta. Cikin wannan dan tsukin Amirun ba ya samun zama sosai, sabida shirye-shiryen bude bankinsu
da suke yi shi da Habibu. Shi Habibun ke tafiyar musu da komi ta can, shi kuma yake tafiyar da
komi ta nan.
Gaba daya ya mance da wata Harrit da ya sanya lambarta a (divert call), sannan a ka'idarshi

bai daukar wayar da bai san lambar ba. Al'amuran gabanshi kadai sun ishe shi, sannan Mairon
shi kadai ya sanya a gaba, a yadda yake ji cikin ransa, ta ishe shi rayuwar duniya da lahira.

A wannan daren na ranar talata shiri yake don tashi zuwa Washington a washegari, domin mika
takardar yin retire daga aiki a World Bank, a gefe guda kuma ga Mairo ta dira shagwaba ita dai
sai ya tafi da ita ta ga Yaya Habibu da Dina.
Ya kamo hannunta ya ce
"rigimarki yawa gare ta Mairo, na fada miki Washington za ni ba Michigan ba. Kuma ba dadewa
zan yi ba, karkari na yi sati biyu. Ina duba yiwuwar komawarki makaranta, idan komi ya dai-daita
gidan Habibun zan barki ki zauna gaba daya".
Ai da jin haka ta yi tsalle ta dane shi cikin nuna farin cikinta a fili. Inda shi kuma ya juyo ta
gareshi ya bi ta da deep-kisses tsakiyar bakinta, wuyanta, da idanunta; mai nuni da cewa, lallai
zai yi kewarta.
Ita da Sabah suka yi mishi rakiya filin jirgi a asubahin washegari. A gaban Sabah ya rungume ta
yana fada mata wasu irin kalamai masu rikirkita kwakwalwa cikin kunnuwanta. Sabah sai ta sa
mayafinta ta kare fuskarta tana murmushi. A zuciyarta kuwa addu'a ta ke, Allah Ya ba ta miji irin
Yayanta. Yana sauka a Washington ya tarar tuni Raymond da Franklyn suna jiran isowarshi, don haka
suka zubo jakarshi a bayan mota suka nufo cikin gari.
Kai tsaye gidanshi suka nufa suna tafe suna yi mishi bayanin muhimman abubuwan da suka
gabatar (in his absence), ci gaban da aka samu da shortcomings din duk da ya biyo baya. Suna
sanyo hancin motarsu a farfajiyar gidan ya ga bakuwar mota kirar (Ferrari 458) kusa da ta
Harrit. Bai kawo komi a ranshi ba, don ya yi zaton baki ne Harrit din ta yi kasancewarta ma'abociyar
hulda da jama'a, don haka ya yi amfani da mukullinshi ya bude kofar. Su Raymond suna daga
waje suna magana. Ya ratsa falon babu kowa, ita ba musulma ba, balle ya yi mata sallama don
haka kai tsaye ya sanya kai 'bed-room' dinsu. Idanunshi kuwa suka yi kyakkyawan gani. Harrit ce kwance tare da wani bature dan uwanta haihuwar uwarsu-ubansu cikin halin turmi da
tabarya.
Ya tsaya kawai yana kallon tashin hankalin da bai taba gani a rayuwarshi ba, wanda a take ya
tabbatar ba komi ba ne, hakkin iyaye ne da son zuciya suka jawo mishi (al'ummar musulmi irin
Amiru sai a yi hattara, kafiri har gobe kafiri ne, duk soyayyarsa gareka kuwa, kuma babu
soyayya ta hakika tsakaninshi da musulmi sai yaudara da soyayyar manufa). Jikinsu ne watakila ya ba su ana kallonsu, su duka suka juyo a razane, amma abinka da nasara
da babu digon kunya ko tsoron Allah a tare da shi, sai suma suka zuba mishi idanun.
Ya yi saurin dauke idonsa ya fito falon ya barsu a nan. Ya zauna cikin kujera yana fidda wani irin
wahalallen numfashi yana fesarwa da kyar, yana shaka da kyar.
Idan wani ya fada mishi Harrit zata yi mishi haka ba zai taba yarda ba, ya godewa Allah da bai
taba kusantar Harrit ba tare da ya yi amfani da kwaroron-roba ba. A take ya fiddo takarda ya
dora biro ya rubuta mata sakin aure kamar yadda addininshi ya tanada.
Ya leka waje ya kira Raymond da Franklyn ya ce, ya ba su minti goma su fitar da duk wani abu
da ke cikin gidan su loda mata shi a waje.
Ya leka dakin ya cilla mata takardar sannan ya kara fadi mata da bakinsa cewa ya sake ta saki

uku. Ko babu sakin dama auren ya riga ya gurbata a nashi addinin. Ya kuma sanar da su minti
goma suka kara yi mishi cikin gida 'yan sanda ne za su raba shi da su.
Harrit sai kuka ta ke tana ba shi hakuri, ta kama kafafunshi ta rike tamau! Jan gashinta (blonde)
ya baje a bayanta da fuskarta kamar na mahaukaciya. Tuni kwarton nata ya gudu, ta gaban
Amiru ya rarrafa ya wuce da rigarsa a hannu, da ya ga ya iso kofa lafiya sai ya taka da gudu iya
karfinsa ko motarshi bai dauka ba. Su Raymond ne ke cika umarnin ubangidansu. Masu fushi
da fushin wani. Fatali kawai suke da komai dake cikin gidan. Ya fizge kafarshi cike da kyama
yana ja da baya tamkar ta dana masa garwashin wuta, a baya in Habibu ya ce kyamar Harrit
yake mugun haushinsa yake ji, amma a yau ji yake har zuciyarshi na tashi da kallonta, ya fice
babu waiwaye yana mai kara jaddada mata cewa, kada ta sake ya dawo ya ganta ko wani
tsinkenta a cikin gidanshi.

Bai kara bi ta kan Harrit ba, don ya lura idan ya ce bakin cikinta zai sa a ranshi shi ne zai cutu a
banza. Amma alal hakika Harrit ta sanya kasar America ta fice mishi a rai. Dan burbushin kewar
kasar da ya rage a baya ya kara zagwanyewa
Ya samu kanshi da rashin yarda da kowa, hadi da shi kansa kuwa. Mairo ce kadai yake tunawa
ya ji sanyi a zuciyarshi. Itan kam ya yarda da ita da wata irin yarda da bai taba yiwa kowa ba
bayan Habibu in ka cire iyayensa, bayan budurcinta data kawo masa cikin girma da daraja,
yana da wata irin yarda akanta, yana samun wata irin nutsuwa a duk lokacin da yake tareda ita.
Amma ita kanta Mairon a yau sai yaji bazai iya magana da ita ba. Don haka ya kashe dukkan
wayoyinshi.

Cikin sati daya rak! Duk abin da ya kai shi ya gama shi, hankalinshi ya yo gida kwarai, amma
dole ya biya wajen Habibu maganar karatun Mairo.
Don haka daga Washington kai tsaye Michigan gidan Habibu ya nufo a Detroit. Habibun ya je
da kanshi filin jirgi ya taho da shi.
Hakika idan ka dube shi zaka lura cewa, a razane yake, a firgice da al'amarin mata. Ita ma
Mairon sai yake ganin kamar kafin ya koma zata yi mishi haka! Don haka ya kulle kanshi a hotel
din (RAMADA INN) tare da kulle wayoyinshi don ya samu daidaituwar kwakwalwarshi da
tunaninshi. Ba abin da ke tashinshi daga shimfidarshi sai sallah da cin abinci, shi kansa Habibu
bai san inda ya shiga ba.
Tsayin sati guda sannan ya samu ya yi 'regaining consciousness'. Sannan ya nufo gidan
Habibu. Habibun ya ganshi kamar daga sama, koda wasa bai yi gigin fada mishi abin da ya faru
ba, don yasan dariya zai yi mishi, dariya har da ta keta, tunda babu yadda bai yi ba ya nuna
mishi illar da ke tattare da auren mushrikiya, amma Amirun bai gane hakan ba, sabida giyar
soyayya na dibanshi a wancan lokacin, don haka idan yana da kunya ai ba zai neme shi ba. Da
ya tambaye shi Harrit sai ya ce da shi, sun rabu ta koma Philppines, bayan idan za a kashe shi
bai san inda ta nufa ba.

Dina na kicin tana hada musu abincin dare, a yayin da su kuma suke baje a falon suna aikin
takardunsu cikin systems.
Kallo daya Habibu ya yi mishi ya tabbatar yana cikin wani bacin rai mai zurfi, ya yi tambayar
duniyar nan amma zurfin ciki irin na Amiru ya hana shi fadar abin da ke damunsa.

Shi kuma Habibun ya takura sai ya ji, daga karshe ya yanke shawarar fada mishi ko da kuwa
zai yi mishi dariyar ne, akalla ya samu rangwamen radadin da zuciyarshi ke yi da nauyin da ya
danne ta.
Habibu ya yi shiru, can kuma ya ce
"Ban yi mamaki ba. Shi arne wannan (adultery) a wajenshi ai ba wani abu ba ne extraordinary.
Sai a yi hattara, Allah Ya kara tserar da mu daga kutungwila da kaidin ZUCIYA.
Amma ni a ganina wannan ba wani abu ba ne da zaka sanya shi a ranka har ya haifar maka da
hawan jini, tunda ka san abin da ka aura ai ka aura din. Sannan sabawa mahaifa ai ba abin da
ba zai janyo mana ba mu 'yan Adam, don haka sai mu yi fatan Allah Ya kiyaye gaba, Ya sa mu
gama da duniya lafiya". Ya ce.
"Ina son farantawa Mairo Habibu, kamar yadda ta ke haifar min da nau'o'in farin ciki a kullum.
Don haka nake ganin zata dawo nan ta karasa karatunta kamar yadda ta faro shi cikin nasara.
Ba zan bari ya kasance ni din na yi silar rabata da burin rayuwarta ba, da tubalin da ka jima
kafin ka assasa. Don ko a yanzu na fita na dawo kullum sai na ganta tana bitar littafanta, duk da
cewa bata taba yi min korafi akan hakan ba. Ni da na yi mata na ga farin cikinta fiye da kullum,
tayi min abinda bata taba yi ba, idan na samu sarari zan dinga lekowa akai-akai insha Allahu". Habibu ya ji dadin wannan karamci da Amiru ya yi mishi, don shi ma abin yana damunshi, don
bai san tsarin sa bane shi yasa tun farko bai neme shi da zancen ba. Don haka a washegari
suka nufi Michigan State University tare don gyara mata registration dinta.
Ya rage saura kwana uku Amiru ya dawo, Hajiya ta yi kiran Mairo, ta hadata da wasu jarkokin
magani da zuma roba guda da Mairo ba ta san ko na mene ne ba. Ta ce, ta je ta yi ta
kwankwada, ta kawo mata jarkokin kafin kwana uku.
Ta bi umarnin Hajiyar don tasan ba zata ba ta abin da zai cuce ta ba, bare wannan magani mai
shegen dadi da zaki.
A'ah! Ai tun a washegari ta ji yanayin jikinta na sauyawa, ba abin da ta ke bukata sai dawowar
Ameeeru, da yake saukar karfe shidda na yamma za su yi, don haka tun safe tana kicin dinta
tana hada abincin tarbar angon nata.
Da taimakon daya daga cikin masu aikin Hajiya da Hajiyar ta bata don su Sabah duk sun koma
makaranta, komai ya hadu.
Babu yadda Hajiya ba ta yi ba ta je airport ta tarbo shi ba, amma kunya ta hanata. Wannan na
daga cikin halayen yarinyar da suke kara mata kaunarta.
Ta lura bayan kunya, tasan mutumcin kanta, kuma ta iya zama da kowa da wata mu'amala ko
ya ya ta hadata da shi.
Tana sassan Hajiya suna sauraron labaran MBC a lokacin da ya iso, daga bakin kofa ya tsaya,
ya tokare kofar da hannunshi na dama yayin da na hagun ke dauke da falmarar din ‘Italian suit’
ruwan toka, wato 'grey' da ke jikinshi.
Ya rausayar da kai yana kallonta, da kyawawan idanunshi, ba tare da ita din ta sani ba.
Sassanyan kamshin 'miyaki' da ya bakunci hancinta shi ya ankarar da ita tsayuwarshi a bakin
kofar n wasu mintuna.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login