Showing 24001 words to 27000 words out of 79746 words

Chapter 9 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

ta damu ba, ta ci gaba
da ayyukan gabanta.
Karfe biyu na rana agogonsu na can, ta sake gwadawa ko za ta samu, amma wannan karon ma
an sanar da ita wayar a kashe ta ke. Yinin ranar zungur, haka ta yi ta nemansa amma ba ta
samu Habib ba.
Abu kamar wasa, har kwana uku ba su samu wayar Habibu ba, sannan ita ma idan ta buga ba
ta shiga. Hankalinta ya tashi, amma ba ta bari Mairo ta gane ba.
A rana ta hudu ne dabara ta zo mata. Ta kira layin Baffa, bayan sun gaisa ta ce, ko yana da
labarin Habibu? Sun kasa samunshi a waya.

Baffa ya yi gyaran murya ya ce
"Tun ranar da ya zo, ya samu sakon cewa amininshi Amiru ba lafiya, don haka ya tafi Abuja
wajenshi ban san halin da suke ciki ba".
Dina ta yi zugum! Da waya a hannu, tunani iri-iri babu wanda ba ta yi ba. Ba ta fatan ya
kasance ciwon Amirun yana da alaka da soyayyar Mairo. Ta sanshi bai iya daukan al'amuran
rayuwarshi da wasa ba. Idan ya ce, yes to da gaske yana nufin yes din, babu gudu babu ja da
baya, raba shi da abin nan da yake so sai wani babban ikon Allah. Sannan Amiru mai-nasara ne, bai taba sanya abu a gabanshi ya kasa samu ba.

Jin motsin fitowar Mairo daga kicin ta yi azamar sauke taguminta ta kakaro murmushi, wanda
iyakacinsa fatar bakinta, ta ce
"Baffa yana gaishe ki, yanzun nan muka yi waya da shi".
Ta aje farantin da ke hannunta akan centre-table, ta ce "Ina amsawa. Ni Yaya Habibu lafiya dai
ko? Tun ranar da ya tafi har yau ban kara jin wayar shi ba".
Dina ta shirga karya
"Am, eh, ya kira kina barci ne shi yasa ban tashe ki ba".
Ta ja farfesun kifin da Mairo ta aje mata, ta soma shan romon da cokali. Tana satar kallon Mairo
ta wutsiyar idonta. Wadda ta maida hankali ga labaran CNN da Mu'azzam Kanti, ke kwararowa.
(Alkawari bayan rai). Amma a zahiri ba sauraronsa ta ke ba, kewar dan uwanta ne ya dame ta,
da rashin jin dadin rayuwar ko ta yaya, da ta samu kanta a ciki. Ba ta rasa ci ba, ba ta rasa sha
ba, mai kyau kuma mai dadi, amma zuciyarta a kuntace ta ke babu dadi. Tana ji a jikinta wani
bakon al'amari mai GIRMA na shirin faruwa da ita, wanda ba zata ce mene ne ko na mene ne
ba.

Washegari da asuba bayan ta idar da sallah, ta yi azkar din safiya kamar yadda ta saba. Ta
yaye labulen dakinta tana kallon yadda snow ta yi musu lullubi. Amma hakan bai hana Bature
yin harkokin gabansa ba.
Yau ranar ta kasance lahadi, don haka ba zata je makaranta ba, kai kofofi da tagogin gidan ma
duk lullube suke da dusar kankara. Room heater da ke aiki a dakin bata taimaka ba ko kankani
wajen rage azabtaccen sanyin da ta ke ji ba, wanda idan da sabo, to sun saba.
Ta hau kwamfuta don duba emails dinta. Bayan ta yi wa sanyi mugun shiri cikin bakaken coat
da bakin wandon jeans mai kauri, hand-socks (safar hannu) da leg-sock (safar kafa) duk
bakake wul. Sakonnin suka soma bayyana, inda welcome-screen ke tabbatar mata tana da
sabbin sakonni guda goma sha biyar. Ta soma budawa, yawanci duk daga Nabilah suke, tana tambayarta abin da ya samu wayarta ta
kasa samunta. Ta mayar mata da amsa cewa, ta yiwa Yaya Habibu laifi ya kwace, sai na Ir’eesh
inda ita kuma ta ke sanar da ita cewa akwai test' karfe sha biyu na ranar washegari, wato litinin.
Sai na wani dan ajinsu Henry baturen Brussels inda yake sanar da ita ya wuce kasarsu don
mamarshi ta rasu. Ta taimaka tayi masa wani assignment, ya neme ta a wayarta bai same ta
ba.
Ta yi mishi ta'aziyya ta tura, sai wani guda daya da ya yi matukar daukar hankalinta,
kasancewar an yi shi ne cikin harshen Hausa, da rubutu in italic, sannan babu sunan wanda ya
aiko, sai logo na hular ilmi. Ta soma bin rubutun a gurguje.

"Nasarar dan Adam a rayuwa, ana gane ta ne tun daga kuruciyarshi. Mutanen da suka samu
kansu cikin gwagwarmayar rayuwa daga yarintarsu zuwa giramansu ba sa karewa haka a
banza.
Ina da yakinin cewa, kina daya daga cikinsu, ci gaba da kokari har sai kin cimma burinki na
zama ‘malamar makaranta’, kada ki bari soyayyar da ke zuciyarki ta zamo barazana ga ci
gaban rayuwarki. Dora soyayyarki akan turba ta hankali da tunani, ba don fita daga wani kunci
ko matsatsi na rayuwa ba". -mai son ki.

Ta karanta ya fi cikin 'ya'yan carbi, amma ba ta fahimci me mai sakon ke son isarwa gare ta ba.
Wa ya ce da shi tana cikin soyayya ko cikin matsin rayuwa? Ta yi tsaki mai karfi ta goge sakon
daga cikin akwatun adana sakonta, amma ba ta iya ta goge shi daga kwakwalwarta da
zuciyarta ba.
To haka washegari, mai 'logo' na hular ilmi ya sake turo mata da gajeren sako.

"........ Some one misses you!".

Abin sai ya koma ba ta haushi, wannan karon ma ta goge ba tare da ta ba da amsa ba. A
ganinta ko waye, yana son yi mata yawo da hankali ne. Ta so ta fadawa Dina, amma ganin
Dinar kwana biyun nan ba ta cikin walwala sai ta kyale ta.
Karfe tara na daren ranar, suna bisa tebir dukkaninsu, har yaran, suna cin abincin dare, daga

can kicin Lynder ke ta goge-gogenta. Wayar Habibu ta shigo wayar Dina, kar ku so ku ga
mazari a wurin Dina garin rawar jiki ta datse kiran da hannunta. Ya sake kira a karo na biyu,
wannan karon Allah Ya ba ta ikon amsawa.

Muryarshi ba ta fita sosai, kamar mai fama da mura ya ce "Yaya kuke? Ya Mairo da yaran?"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Duk lafiya muke. Haba Habib? Ka barmu cikin fargaba. Akalla ko mene
ne ya faru da kai ka daure ka sanar da ni, sannan ka kulle wayar. Duk kwanakin nan hankalina
a tashe ya ke".
Ya ce "Ki yi hakuri, bana cikin hayyacina ne, I don't want to lose AMEERU. (bana so in rasa
Ameeru). Ki debo passport dinku a dakina, daga gobe zuwa jibi ku nemi jirgi ku taho, ki kai
yaran gidan Sultana sabida makaranta, ku taho ke da Mairo".
Dina ta kidime "Lafiya? Me ya faru da Amirun?"
Bai ba ta amsar ko daya ba, ga dukkan alamu kuka Habibun ke yi kasa-kasa, wanda ba ya so
ta jiyo. Hankalinta idan ya yi dubu ya tashi. Ba kankanin abu ke sa Habibu kuka ba. Kada Allah
Ya sa abin da ya darsu a zuciyarta yanzun ya zam tabbatacce.
7/29/21, 11:15 PM - Kawata: 666667778888




Ranar Litinin. Tun asuba da Mairo ta tashi ta yi sallah ba ta koma bacci ba, ruwa ta taro a famfo
ta yi wanka ta shafa mai, ta sanya uniform dinta ta shirya tsaf ta zauna jiran fitowar Baffa.
Ba shi ya fito ba sai karfe takwas dai-dai na safe. Ya yane labulen dakin su Mairo cikin sallama
ya ce "Ya ya kin gama kimtsawa mu tafi?"
Ta ce "Na gama Baffa tun dazu".
Ya sa hannu ya daukar mata katuwar jakar, ita kuma ta dauki karamar suka fito. Ta leka dakin
Habiba da Hajara ta yi musu sallama suka amsa duk cikin yanayi daya, wato a yatsine, don ita
Habiba ba ta so wannan komawa makarantan na Mairo ba, so ta ke abar musu ita tai ta yi musu
bauta, don Ladidi ko za a kashe ta ba zata yi musu bautar da Mairo ta yi musu ba cikin kwanaki
ukun da ta yi tare da su ba.
Shi kuwa Baffa Allah-Allah yake ya maida Mairo makaranta don ta huta da kwarzabar su. Idan
ya tuno daga wannan zangon Mairo ta gama makaranta hankalinsa tashi ya ke. Ya soma
tunanin da ta gama makaranta idan ta samu masoyi zai ganganda ya yi mata aure, idan ma ba
ta samu ba ko cikin mutanensa ya nemi wani wanda ya yaba da hankalinsa ya ba shi ita, shi dai
ta bar gaban su Habiba, sai hankalinshi ya kwanta.
Ya bude boot ya zuba kayan, ita ma ta sanya jakar hannunta. Ya bude kofar wajen mai zaman
banza ta shiga ta zauna, sannan ya zagaya shi ma ya shiga ya tayar da motar suka mika kan
titi.
Karfe goma dai-dai suna cikin Minjibir, duk wasu shige da fice na dawowar dalibi Mairo da
Baffanta sun kammala cikin dan lokaci. Suka yi sallama da Baffan ya kada kan motarshi ya tafi,
ita kuma ta nufi ajinsu.

Tun daga nesa ta hango Uncle yana rubutu akan allo, wani irin dadi da farin ciki suka ziyarci

zuciyarta. Ji ta yi tamkar Baba da Innanta ne suka dawo.
Daga can mazauninsu Nabilah ta hango ta, ta kuwa sheko da gudu ta rungume ta, ba tare da
la'akari da cewa akwai malami a cikin ajinsu ba. Ya dakatar da rubutun ya juyo, juyowar da ta ke
nufin al'amura da dama a gare su a wannan ranar.
Mairo ba ta iya ta hada ido da Uncle ba saboda matsanancin kwarjinin da ya yi mata a yau, shi
kuma kokari yake ya kalli cikin kwayar idanunta cike da tuhuma da tarin laifuffukanta gareshi. Ya
mannawa Nabilah harara ba shiri ta koma cikin nutsuwarta, kai tsaye Mairo ta wuce wurin
zamansu shi kuma ya cigaba da bada darasi cikin wani sabon kuzari da nishadi gami da wani
karfin gwiwa da ya same shi duk a lokaci daya.
Aka fita break amma ita da Nabilah ba su fita ba, sun nutsa hirar bayan rabo. Nabilah ta ce
"Yaya Inna? Kusan kullum sai na yi mafarkinku Mairo, tun bayan rasuwar Baba nake jin
tausayin Inna, ina gayawa Mamana da Daddy. Dama idan kika yi sati baki dawo makaranta ba
zan bi sawunki ko makaranta ta yi min izini ko ba ta yi ba". Idanun Mairo suka kawo kwallah, ta ce "Innar ma na rasata Nabilah ... Ba ni da kowa a yanzu
sai Baffana sai Allah da Ya halicce ni. Na zama marainiya Nabilah, ba uwa ba uba…...."Hawaye
suka kece mata, ta dukar da kanta cikin cinyoyinta ta ci gaba da kuka.
Nabilah ma sai ta sa kuka, tana tuna Inna da kirkin da ta yi mata. Sun dauki mintuna suna kuka,
kamar wasu kananan yara. Ba su san yaushe Uncle ya shigo ba, har ya tsaya a kansu. Ya
sanya hannu ya kwankwasa desk din da suke sunkuye. Duk hirarrakin da suke yi ya ji su, ya
rasa inda zai sa kansa da tausayin Mairo. Ba kankanin abu ne ke sanya Junaidu kuka ba,
amma a yau ya ce Maryama I cannot control my tears……….."Suka dago ido suka dube shi
cikin ido, Mairo da Junaid ke kallon juna, irin kallon da ba su taba yi a rayuwarsu ba. Wani
muhimmin al'amari na samun muhalli cikin kwayar idanunsu. Nabilah sai ta bude baki, galala!
Tana kallonsu, tana cewa cikin ranta "A yau dai, dole Mairo ta yarda Uncle Junaid yana
sonta……..".
Mairo kwana ta yi ba ta yi barci ba, baya ga dacin mutuwar iyayenta da ya dawo mata sabo fil,
sai kuma SOYAYYAR Junaid da ke dawainiyya da zuciyarta, amma ta kasa ganewa, sabida
kuruciya da wauta. Ga dai zahiri al'amarin ya sauya, amma ta sanya kafa tana takewa da
gan-gan. A ganinta mai Junaid zai ci da 'yar kauye kamarta? Sai dai ta ce zuciyarta na yaudararta, tunda
shi din bai furta ba. To ita ma ba zata taba yarda da tunaninta ba.
Shirye-shiryen jarrabawar fita ya kankama. A wannan dan tsukin Uncle ya takura musu matuka
da karatu, musamman akan lissafi (mathematics) da Ingilishi (English). Burinsa kawai Mairo ta
lashe dukkan takardunta. Ta gama makaranta with flying colours', ta samu gurbi a babbar
makaranta, ta yi karatun da zata dogara da kanta cikin kowanne hali. Idan hakan ta faru to shi
kam Alhamdu lillahi... Ya sauke nauyin alkawarin da ya daukar wa Malam Bedi, sannan ne yake
jin zai fallasa mata soyayyar shi, don haka wannan ba lokaci ne da ya dace ya fallasa
asirtacciyar soyayyarsa ga Mairo ba. Ya manta masu iya magana sun ce "A BARI YA HUCE...
Shi ke kawo da rabon wani.
Ba ta da abin da zata ce da Uncle Junaidu sai godiya, domin da taimakonshi da kwarin gwiwar
da ta ke samu daga gare shi ne ta zana jarrabawar Jamb, Waec da Neco cikin kwanciyar
hankali, tamkar ba jarrabawa ta zana ba, sabida yadda komi ya zo mata da sauki. Sai dai kuma
wannan gama jarrabawar na nufin al'amura da dama cikin rayuwarta. Rabuwa da UNCLE

JUNAIDU? Wani muhimmin al'amari ne da ke cinta a zuci, da zuciyar ba zata iya jurewa ba, da
harshe ba zai iya bayyanawa ba. Ina ma Uncle zai ce yana sonta ya aure ta? Ya rabata da
rayuwar maraicin da zata je ta fada a gidan Baffanta?
Hawaye suka ciko idanunta. A karo na farko da zuciyarta ta kawo shawarar ta nemi Uncle ta
roke shi ya aureta, ya tserar da ita daga rayuwar kunci da zata je ta fada, ko da ba ya sonta.

Ta shiga neman Uncle cikin makaranta, lungu-lungu, sako-sako, abun kamar wasa ko mai kama
da Uncle babu. Tuni dalibai sun soma tafiya, don duk wacce ta fito daga last paper daukar
kayanta ta ke ta tafi, bayan anyi sallama da kawaye da abokan arziki. Tana tsaye nan cikin
tashin hankali Nabilah ta iskota, "Ga can Baffanki ya zo daukarki yana ta aike a nemo mishi ke".
Hankalinta ya kara tashi da ta tabbatar a yau zata tafi ne, tafiya ta har abada daga Minjibir, ba
tare da ta yi sallama da Uncle ba, wani mutum daga cikin mutane biyu da ke ba ta farin ciki da
buri (hope) a cikin rayuwarta.
Tabbas yau ya sauke nauyin alkawarin da ya yiwa mahaifinta. Ta kammala makaranta cike da
kyakkyawan zaton samun nasara. Muhimmin al'amarin da ke dawainiya da zuciyarta akan
Uncle, ta ke so ta sauke, amma babu Uncle a cikin Minjibir, babu alamarsa.

Sai ta sa fuskarta cikin tafukanta ta soma shesshekar kuka. Nabilah ta rungume ta suka ci gaba
da kukan tare, sai dai ita Nabilah ba ta san hakikanin dalilin kukan Mairo ba.
Ita kuka ta ke na kewa da rabuwa da Maironta, yayin da Mairo ke kuka na tausayawa
rayuwarta. Ta kullaci Uncle mummunar kullata, (irin kullatar data yiwa Habibu) ta tuhume shi da
YAUDARA da wasa da rayuwarta. Ba tasan inda za ta ganshi ba, ta gaya mishi shi kadai zuciya
da ruhinta ke so. Ya taimake ta ya aure ta koda BA YA SONTA. Shi kadai ne namijin da ta ke jin
zata iya aure a rayuwarta. Shi kadai ne ta ke jin zai kula da rayuwarta a bayan idon Baba da
Inna. Shi kadai ne ta ke kalla ta ji shi kamar Yaya Habibu. Yau shekaru dai-dai har shidda
dai-dai da rana daya zuciyarta ba ta taba hutawa da kaunarshi ba.
A da kam ba ta gane ba, amma yanzu ta yarda ta amince da mahaukaciyar soyayyar da ta ke yi
wa Uncle Junaidu. A yau da ta yanke shawarar fada masa don su tallafi rayuwar juna ta neme
shi ta rasa.

*****
K
arfe hudu dai-dai na yammacin ranar ta litinin suka iso gida, inda direban su Nabilah da ke biye
da su don ya ga gidan ya juya da Nabilah, da alkawarin bayan sati zata zo su je da Mairo
gidansu, don ba ta taba zuwa ba.
Tun daga soro Mairo ta soma cin karo da kwanuka, da busasshiyar miyar kuka a jiki. Gabanta
ya ci gaba da faduwa don ta tabbatar ita da rayuwar farin ciki, sun yi hannun riga ke nan. Ta
fado cikin wata sabuwar rayuwa ta MARAICI, wadda Innarta ta ke jiye mata. Ta tabbata Inna
tasan rashin kirki na matan Alhaji Abbas shi yasa a lokacin rayuwarta ta ki yarda ta zauna da
su. Mai za a yi da hali irin na Hajara da Habiba? Sai Allah Ya kyauta.
Karatu dai an kare shi, yanzu zama ne za a yi na din-din-din. Kowacce waina za a toya? To bari
mu bi Mairo da iyayen rikon nata mu gani.

Habiba na daki lokacin da suka shiga, sai Hajara ce a tsakar gida tana tankaden garin tuwo.
Baffa ne a gaba rike da jakar mairo, ita kuma ta biyo bayansa rike da wata jakar.
Hajara ta amsa musu sallama fuskarta ba yabo ba fallasa. Bayan haka ba ta kara tofawa ba.
Baffa cike da takaici ya ce "Hajara baki ga 'yar taki ba ne, ko sannu da zuwa babu? Ai ba a
haka".
Ta cira kai ta jefe shi da harara, "Cewa za ka yi tashi ki yi tsalle 'yar gaban goshina ta dawo, ba
sannu da zuwa ba".
Jin cece-kucensu sai Habiba ta leko. Ita kam tayi fara'a ta ce "Ah! 'Yan makaranta an dawo?
Lale-lale". Ko ba komai ta samu jakar da zata yi ta yi mata bauta.

A dakinsu ta cimma Ladidi ta yi dai-dai sai sharar barci ta ke, dakin kaca-kaca ko'ina kayan
Ladidi ne a watse, nan pant, can brazier dukun-dukun da su. Ba ta ga inda zata dosana
duwawunta ba a dakin, don haka ta aje jaka ta soma tattara mata shirgin waje guda ta gyare
dakin tsaf ta share ta kwashe ta zubar. Ta gabatar da sallar azahar da la'asar da suka wuce ta, ta dauko karamin Alkur'aninta ta soma
tilawa. Ko aya biyar ba ta yi ba cikin suratul Ma'idah, Hajara ta kwalla mata kira. Ta rufe
Alkur'anin ta ajiye mayafi ta fita. Ta nuna mata tulin wanke-wanke ta ce "Kina ganin aiki ya
kacame min amma kika tafi kika kule a daki ko uwar me kike? Oho! Maza wanke su yanzun nan
cikinsu zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login