Showing 21001 words to 24000 words out of 79746 words

Chapter 8 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

abin da kake ji, shi da Malam Tanimu suna gaba. Ta kama jikinta tsan-tsan sabida
gwaruwar da kanta ke yi da jikin motar sabida rashin kyawun birjin Gurin Gawa. Shi da Malam
Tanimu suna ta hirarsu ba abin da ya dame su, ita kuwa sake-saken da ta ke yi cikin ranta na
abin da zata je ta tarar a gidan Baffanta da 'ya'yansa marasa adadi da rashin tarbiyya ta ke yi.
Sai da suka hau titin gidan zoo sosai sannan motar ta daidaita, tafi-tafi har suka iso gidan Sarki
suka billa Yakasai ta nan.
Kugin karshe da kwarababbiyar motar ta yi a kofar gidan Alhaji Abbas Maigoro ne. Gida ne
ginin siminti mai dakali hagu da dama da manyan zaure irin ginin masu kudin da. Yara kanana
da samari suna ta shige da ficen su. Gabanta ne ya soma dukan uku-uku sabida haka ta yi
hamzarin jan Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un har ta samu bugun zuciyarta ya yi dai-dai. Suka ce ta shiga cikin gidan ta turo musu Alhajin suka fito kan dakalin gidan suka zauna. Cikin
sanyin jiki Mairo ta fito tana tafe tamkar macijiya sulu-sulu abin tausayi. Ta yi sallama a tsakar
gidan, Uwargidan Hajiya Habiba ta amsa, wadda ke tukin tuwon dare a bakin murhu.
Ta karasa inda ta ke ta tsugunna tana gaishe ta cikin nutsuwa. Ta amsa da alama ba ta gane ta
ba, ta ce "Yammata daga ina? Ban gane fuskar ba".
Ta dukar da kai ta ce, "Gurin-Gawa".
Habiba ta kalle ta sosai na 'yan dakikai, nan da nan fara'ar da ke fuskarta ta bace. Ta juya ta ci
gaba da tukin tuwonta. Cikin halin ko'in'kula ta ce
"Auyo! Ce min zaki yi MAIRON HURE shalelen HURE, sai yau tasan mu mutane ne da ta turo ki
ki gaishe mu? Ce nake har jinya kuka yi anan ta tsayin watanni ba ku san hanyar gidanmu ba,
sai dai kullum mu tuka mu ba ku? Ince ko yanzun ma ba tasan kin zo ba kada mu moran mata
ke?" Mairo ta share hawayen idanunta, ta ce "Tare muke da baki suna zaure, sun ce suna son ganin
Alhajin ne".
Sai da ta mula ta ce "Ba ya nan, yana kasuwa, amma yana gab da dawowa".
Ta taso sumui-sumui ta fito dakalin gidan ta fadawa su Malam Tanimu sakon Hajiyar.
Ta ci gaba da tsayuwa a zauren ba ta koma cikin gidan ba. Malam Tanimu ya ce "Bude motar ki
kwaso kayanki mana ki shiga da su?"
Jikinta ya yi sanyi lakwas ko numfashi da kyar ta ke shaka, ta ce "A'a, mu dai jira Baffan".
Dagaci ya yi nazarinta yana taunar goronsa, ya ce "Mairo ki saki jikinki, nan fa gidanku ne,
gidan ubanki ne".
A ranta ta ce "Kayya Uba guda daya ne, na tabbata na rasa nawa".
Suna nan zaune ita kuma tana tsaye daga cikin zauren kusan rabin awa, Ladidi diyar Alhaji
Abbas wadda ta ke kusan tsararta ta dawo daga unguwa rike da hannun kanwarta Rahma ta ci
kwalliya kamar me? Tana yafe da wani dan gyale mai kama da abin tatar koko, ta daga ido tana
kallon Mairo kana ta kyabe baki ta ce "Ah! Yau wace rana?" Ta yi murmushi, ta ce "Ladidi ke nan, kuna lafiya?"
Ta sake kyabe bakin (ga alama al'adarta ne yin hakan a duk sanda zata yi magana), wanda

kwata-kwata ba ya mata kyau, don ko daya ba ta da kyawun fuska. Ta ce "Gidan namu ne bai
ishe ki shiga ba da zaki tsaya a zaure, ko kuwa wani sabon salon gulmar ne Hure ta koya miki,
ta ce idan kin zo ki yi mana, don Baba ya ce mun wulakanta ki?"
Ta bude baki tana kallonta kawai cikin mamaki, ba ta ce komai ba, ta yi ciki sai ta danne
zuciyarta ta bi ta a baya.
Suna shiga Habiba ta ce "Ai na dauka tafiya ta yi babu sallama, saboda uban nata ba ya nan".
Ta sake kyabe baki, ta ce "Can soro na ganta a tsaye, salon ta ja mana magana wajen Baba".
Amarya Aunty Hajara ta yane labulenta jin cece kucensu, ta ce "Wa nake gani kamar 'yar gidan
Hure?"
Habiba ta ce "Ke ma dai kya fada, ai ni na dauka batan kai ta yo".
Hajara ta saki labulenta tana cewa, "Allah Sarki! Alhajin yana kan hanya don nasan dai ba
wajenmu kika zo ba".
Mairo dai na tsaye tamkar mutum-mutumi. Tana mamakin rashin mutumci irin na matan Alhaji
Abbas. Babban mamakinta daga Habiba har Hajara babu wadda ta ce ta shigo daki.
Haka Ladidi ta shige dakinsu na 'yammata ba ta kara bi ta kan Mairo ba. Ta ci gaba da tsayuwa
sororo! Wannan yaro ya shiga, wannan ya fita duk ba su santa ba. Wannan ita ce rayuwar da
Innarta ta ke guje mata ke nan ta matan birni marasa karah da rayuwar kowa yai ta kansa, ko
kuwa abin nan da Bahaushe ke cewa, kowa tasa ta fishshe shi. 7/29/21, 10:05 PM - Kawata: 0989
Ta dago idanunta jage-jage da hawaye, don ganin ko wane ne wannan? Da haka kawai zai zo
ya dafata? Ko ta ce da wani tana neman taimako ne? Wa za ta gani? Yaya Habibu ne!
Cikin matsanancin mamaki ya ce, "Mairo?"
Ba ta amsa ba, illa ta bi shi da kallo, da jajayen, idanunta. Ya sake cewa
"Me ya kawo ki nan? Ina za ki je?"
Nan ma shiru ta yi masa, sai kallonsa ta ke kamar ta rufe shi da duka don haushi. Ya ishe ta da
tambaya, ya barta ta ji da kukan zuci, da takaicin da ya dame ta. Don ji take kamar Amiru ya
bula mata kura, ya ja motar rayuwarshi, ya barta.
A nashi bangaren, shima Habibun, haushi ne ya kama shi, ya ce
"Kina ji ina magana kin yi kunnen uwar shegu da ni? Na ce me ya kawo ki nan, kuma gurin wa
kika zo? Ina zaki je?"
Nan ma shiru ta yi masa, kamar da dutse yake magana, kuma ba ta dauke idanunta daga
kanshi ba. Ta kafe shi dasu kurrrrr! Kamar shi ne ya kori Amirun. Iyakar fusata Habibu ya fusata,
ya fizgi hannunta suka fito harabar adana motoci na airport din, yana baza ido don gano inda ta
yi fakin. Daga can ya hango motar ta yi mata wani banzan fakin a inda aka rubuta no parking, Security
ne cikin fararen kayan ma'ikatan gurin tsaye jikin motar, wato sun kamata.
Ya yi tsaki, tsut…, suka doshi wajen, har yanzu yana rike da hannunta, sai janta yake kamar
kayan wanki. Ya mika hannu ya zare makullin ya soma ba su hakuri ya nuna musu Mairo ya ce
ga dukkan alamu ba cikin nutsuwarta ta ke ba, su yi mishi uzuri su ba shi motar.
Abinka da malam bature da bai san cin hanci da rashawa ba, gami da bin ka'ida da dokar duk
da aka shimfida masa, kememe sun ki yarda, sun dage dole su dangana da ofishinsu in har
suna son motar su, don a ka'ida mai matsala a kwakwalwa, ba a yarda ya tuka abin hawa ba,
ya ce lafiyarta kalau, tension ne kawai, suka ce idan haka ne ke nan tana sane ta karya musu

doka? Don haka dole su dangana da ofishinsu, amma ba zasu bada motar ba.
Cikin matsanancin fushi, Habibu ya dubi Mairo
"Kin kyauta, kin ga abin da kika jawo min ko?
Yau shekaruna goma cur cikin kasar America, ban taba zuwa ofishin 'yan sanda ba, don haka
sai ki bi su ku je, ki yi musu bayanin dalilinki na karya dokarsu, tunda ni kin yi min banza, sai ki
je ku karata.......”
Ya cika hannunta zai tafi, ta riko bayan rigarsa tana kuka. Ya ce
"Wallahi bazan je ofishin 'yan sanda ba, sai dai ki hakura da motar, ki bar musu mu tafi, kuma
wallahi-wallahi ba zan sake siyan wata ba".
Ta ce ta yarda, don haka suka bar motar a nan, suka nufi motar Habibun.

Allah Sarki, dan uwa rabin jiki! Sun yi nisa sosai danja ta tsaida su, ya saci kallon Mairo da ke
kujerar gefensa, ya ga har yanzu kuka ta ke mara sauti, ta rufe fuska da mayafinta. Sai ya
hadiye fushinsa, ya soma lallashinta cikin dabara.
"Ni dai idan don na tambaye ki inda za ki ne kike min wannan kukan, to ki yi hakuri. Mantawa na
yi, ashe fa Amiru ya fada min ba kya son tambaya.
Ban da abinki Mairo, idan wajen Junaid kike son zuwa, jirgi ya tashi ya barki, ai sai ki fada mini,
na yi miki booking din wani, amma ba ki sunkuya cikin dubban mutane kina rafka kuka ba,
kamar wata mai tabin hankali. Yana ina Junaid din? Nigeria ko Russia?"
Cikin kuka ta ce
"Ni fa tunda na yi maka wancan alkawarin, ban sake tuna zancen Uncle Junaid ba".
Ya ce "To ina za ki? Ko AMIRU kika biyo?"

Hantar cikinta ta karta, ta rasa me zata ce masa, don haka ta ja bakinta ta yi shiru. Habibu ya
kuta ya ce
"Hakan da kike yi, kina ganin mutumci za ki sayawa kanki?
Shi wancan bai ce yana sonki ba, sabida neman gindin zama kika kwashi jiki kika je gidansu
don rashin hankali da rashin mafadi. Shi wannan da ya ce yana sonki, kin ce ba kya sonshi,
sabida kar ki ci amanar wanda bai ce yana sonki ba. Ya hakura ya bar miki kasar ma baki daya
ba garin ba. To uban me kika biyo shi ki mishi? Da kin same shin me za ki ce masa? Yi hakuri na tuba, ka zo
ka aure ni ko me? To ni bana son rashin hankali da rashin mutunta kai, aikin zubar da kima, da
wulakanta kai. Kin riga kin ce ba kya sonshi, to a barshi a hakan. Allah Ya kawo miki wanda kike
so. Don wanda ya ce ba ya sonka tun farko, daga baya ya dawo ya ce yana sonka, to akwai
dalilinshi na yin hakan. Wato za ki yi A RASHIN UWA... akan yi UWAR DAKI...? To ba da
abokina ba!
Idan auren kike so ki yi, ki je ki nemo Junaidun, tunda ba kya son karatun da nake sonki da shi.
Abu na dan lokaci kalilan, ba zaki maida hankali akai ba, mazan nan da kike gani, dukkansu
matsala ne, shi kansa auren idan ba a tsaya anyi shi cikin nutsuwa ba, babu inda ya ke zuwa.
Don haka yarinya, kama kanki. Wayar ma daga yau ba zaki sake rikewa ba, kamar yadda babu
ke babu tukin mota. To kin ji".

Dai-dai lokacin da ya yi fakin a harabar gidansu, ya juya bayan motar ya dauko falmaran din
suit' dinshi da wayoyinshi ya fito, ita ma ta fita, ba tare da ta yarda sun kara hada ido ba.

Dina ta tari mijinta kamar yadda ta saba a kullum, amma ya sakar mata harara. Ya fincike jikinsa
daga jikinta ya juya ya kara hararar Mairon da ke shigowa sumui-sumui kai a kasa, kamar wata
munafuka, ya dawo da dubansa ga Dina.
"Da saninki Mairo ta dauki mota ta tafi airport?"
Dina ta yi shiru, ya ce "Magana nake, ko ke ma sullutun za ki mayar da ni ku barni na yi ta
magana ni kadai?"
Ta ce "To me ya faru?"
"Ya zan tambaye ki kema ki tambaye ni? Amsa nake son ji kawai, kina sane ta tafi ko a'ah?
Yanzu na je kai Amiru zai tashi zuwa Najeriya na ganta tana kuka akan titi uban me ta je yi?"
Dina ta hau kame-kame ganin yadda ya hasala sosai, ta ce
"Am... Eh, ai sako zata kai wa Amirun".
A fusace ya ce
"Sakon me?"
Ta ce "Ka ga Allah ban sani ba, can tsakaninsu".
Ya yi dogon tsaki, ji kake 'tsiiittt!' Ya maida kallonshi ga Mairo
"Ba ni wayarki".
Ta soma dube-dube a falon inda ta cillar da ita, can ta ganota bayan room heater, ta dauko ta
mika mishi. Ya kashe ta gaba daya ya jefa a aljihun wandonsa da sassarfa ya nufi bangarenshi
ya barsu nan tsaye cirko-cirko kamar an dasa su a wurin.

Dina ba ta yi gigin binsa ba, don tasan halin kayanta sarai, idan ya yi fushi yana bukatar a daga
mishi kafa, har sai ya sauko don kansa, wanda ba ya daukar dogon lokaci yake yin hakan. Ba
ya son aje ana wani lallashin shi ko ace za a ba shi hakuri.
Ta kama hannun Mairo suka nufi dakin Mairon suka zauna a bakin gado. Ta ce "Kin same shi?"
Ta girgiza kai, wasu hawayen suka zubo.
Dina ta sa yatsunta tana share mata, "Kada ki yi kuka Mairo, mika dukkan lamurranki ga Allah.
Amiru yana sonki, na kuma tabbata zai dawo. Shi ma Junaid yana sonki, ina tabbatar miki da
shi ma akwai ranar da zai zo. Allah kadai Ya san mijin ki a cikinsu, don haka ki dukufa ga
neman ZABIN ALLAH ba zabin zuciyarki ba".
Don haka Mairo ta tattara shawarwarin iyayen rikonta, wato masoyan nan nata guda biyu, da ba
ta da ya su a duniya: Yaya Habibu, da Maidakinsa, Dina. Ta karbi shawarwarin su da hannu
bibbiyu, ta fuskanci jarrabawar karshen shekara da ta tunkarota, wadda daga ita zata shiga
shekara ta uku, kuma ta karshe da zata hada digiri dinta.
***
A yau suna da tutorial class, kan wani kwas da zasu fara jarrabawa a kanshi. Mairo ta fi duk
'yan ajin su fahimtar wannan darasin, don haka suka bukaceta da ta yi musu karin bayani.
Maryam Muhammad Bedi, ta fito gaban ajinsu ta tsaya rike da takardu, domin wani abu ne da ta
kware a kai, wanda Uncle Junaid ya koyar da ita, wato dabarun speech in public, ba tare da jin

ko da dar a zuciyarta ba.
Ta soma feso sassanyan Turanci daga makogaro zuwa harshe, sannan siraran labbanta su
furta. Kai ka ce diya ce ga Herbert Spencer. Tana bayani ne akan Segmund Freud's stages of
psycho-sexual development, tana farke theory tana yin kaca-kaca da ita tun daga
phallic-stage... Anal stage... da 'yan uwansu. Sannan ta koma kan SOCIAL CLASSES; the BOURGEOISIE and the PROLETARIAT………. !!!
Habibu da ke cikin 'yan ajin ya sanya mask (fuska) sai ya soma kuka.
Sannan ya taso ya fito, zuciyarshi cike da alhinin ina ma ace... Malam Muhammad Bedi, zai
dawo duniya yau ya ga Mairon shi na koyar da turawa, da sauran jinsin al'umma.

Don haka Mairo yau da ta dawo gida ta ga sauyi sosai daga Yayan nata. Domin dai ya tabbatar
ta tsaida hankalinta tana karatun, kamar yadda yake so. Yaje makarantar ne ya shiga cikin ‘yan
ajinsu don yayi supervising hakan.
Shi da Dina ne cikin three seater suna aiki cikin takardu da kwamfuta. Ya daga kai ya dube ta
yana murmushi, a lokacin da tayi sallama ta shigo.
"Mairo 'yan makaranta......Mairon Dina….. Mairon Yaya Habibu".
Ta yi murmushi, har kumatun ya lotsa. Za ta wuce cikin daki ya ce.
"Zo zauna, mota zan sake miki".

Da hanzari ta dago ta dube shi. Ya daga mata gira (in affirmation) watau cikin tabbatarwa "Gaya
min duk irin motar da kike so ni kuma na yi alkawarin zan yi kaffara in saya miki. Sannan ki mai
da walwalarki kamar da, bana son ganin wannan shiru-shirun da kika koma. Sannan Dina ta
fada min ko hira kin daina yi da ita, kullum sai karatu. A dinga rage karatun, a dinga baiwa
zuciya da kwakwalwa dama su huta, sai karatun ya fi zaunawa sosai.

Zan tafi Nigeria gobe, akwai muhimman al'amura da zamu gabatar ni da Amiru a Abuja, zan yi
sati daya, me kike so in kawo miki?
Dina ta rubuta min kayan abincinmu na gargajiya su kuka, daddawa, rogo, kubewa da
sauransu. Ke kuma fa?"
Ta yi murmushi kanta a kasa ta ce, "Ladidi nake son gani".
Ya ce
"Ai an yi mata aure. Kina ganin zan rabo mace da gidan aurenta ne na kawo ta? Ai mijinta ba
zai so ba, ki yi hakuri ki kare karatun gida za mu koma gaba daya. Gobe sai ku je da Dina ki
zabo motar da kike so, zan bar komai a hannunta".
Ta yi godiya, ta kama hannun Little Mairo suka nufi dakinta.
Dina da Habibu suka bita da kallo, dukkansu ba haka suke son ganinta ba. Gaba daya ta
sauya, tun ranar da Amiru ya tafi, daga daki sai daki, daga littafi sai littafi na gaggan malaman
sociology. Habibu na addu'ar Allah Ya sa ba sociology'n ne ya soma taba mata kwakwalwa ba.
Shi yasa tun farko bai so ta zabi wannan kwas din ba, amma ta dage ita nan duniya shi ta ke
so, ba don komai ba sai don ta zama Uncle Junaidu. Ita Dina da yake tasan dawan garin, wato
Mairo ta soma kamuwa da matsananciyar soyayyar Amiru sai ba ta damu sosai ba.

Habibu ya daga Nigeria a washegari, da tsarabar Baffa da iyalinshi rankatakaf! Da aiken Mairo

ga Ladidi. Ita da Dina suka shiga gari suka yo cefanen kayan abinci da kayan amfanin gida da
ya kare, sannan suka nufi wani kamfanin motocin (General Motors) dake nan cikin Michigan ta
zabi mota irin tata ta da, watau GMC Terrain ruwan makuba, suka shirya payment Dina ta biya,
ta karbo rasidi da takardun mota aka biyo su da ita gida.
Duk a kokarinsa na son farantawa 'yar uwarshi, yana sauka a gidan Baffa ya kira wayar Dina,
ko gaisawa ba su yi ba, ya ce ta hada shi da Mairo, ga Ladidi ga Baffa. Farin cikin da Mairo ta
samu kanta da jin muryar Baffa da Ladidi ba zai fadu ba.
Sun dade suna hira, inda Ladidi ke sanar da ita tsohon ciki ne da ita, ta yi mata fatan sauka
lafiya, sannan ta baiwa Dina suka ci gaba da hira ita da Habibu.
Washegari Dina ta kira shi don su gaisa, amma wayarshi a kashe, sai ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login