Showing 60001 words to 63000 words out of 79746 words

Chapter 21 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

tambayarshi shi ne, har yau babu ajiyarshi ne?
Da ya fadi hakan zata yi sauri ta kashe wayar, sabida kunya.
To haka rayuwarsu ke tafiya, cikin so da kauna, ba sa taba gundurar juna. A Najeriya ne ko a
Michigan, har Mairo ta kare karatunta, ta fiddo kwalin first class degree a B.Sc Sociology.

Har zuwa wannan lokacin shiru, babu haihuwa babu alamarta, don ko batan wata Mairo ba ta
taba yi ba. Tun abun na damunsu har suka hakura suka fauwalawa Allah.

Sai dai kuma kamar yadda kowanne dan Adam ba ya rasa makiya, to hakan ce ta faru da Mairo
daga dangin Amiru, musamman a Gaya da suka fara kishin-kishin Amiru ya auro musu juya,
don ma Hajiya tana tsawatarwa ne amma har su Sabah sun soma sauya mata fuska.
Aka soma yi wa Amirun tushen 'yammata, 'ya'yan gata, kyawawa wadanda suke ganin zasu iya
gogawa da Mairon da duk abin da ta ke takama.
Zuwa lokacin shi ma Habibu ya yi 'retire' daga 'barclays', haka Dina ta bar kotun da ta ke aiki.
Sun tattaro da 'ya'yansu duka sun dawo gida Najeriya garin Abuja, cikin unguwar colorado
close.
Don haka Mairo cikin farin ciki ta ke, ga ta ga iyayenta, wadanda su ne kadai ta ke gani ta ji
dadi, kasancewar Hajiyar ma ta soma daukar hudubar 'ya'yanta da 'yan uwan mijinta na Amiru
ya kara aure.
Daddy bai san abin da ke faruwa ba na matsalolin da Mairo ta soma fuskanta cikin gidan ba. A
lokacin tana hidimar kasa a nan jami'ar Abuja, ta kai ga ko ta gaida Hajiya a ciki ta ke amsawa
don gani ta ke Mairon ta mallake mata da, yadda har ba ya damuwa da samun dan kansa.
(Matsalarmu ke nan al'ummar Hausa, babu ta yadda za a yi a ga mace na zaune lafiya da
mijinta yana sonta, yana gudun bacin ranta, sai a ce ta mallake shi.
An fi so a ji kullum yana kawo kararta ana yi musu sasancin sulhu, ko ya dinga aura yana saki,
ko ya dinga aibatata cikin yan uwansa, Allah Ya sa mu gane mu gyara zuciyoyinmu, amin).

A yau ne Amiru ya shirya musu 'wedding anniversary' na cikarsu shekaru biyar da aure. Taro ne
da ya tara manya-manyan ma'aikatan bankunan Najeriya, bankunan kasar America, irin su
World Bank, Barclays, Bank of America, Comerica, Citigroup, HSBC, Chase... da sauransu.
Abokansu na karatu ne da yawa da suka watsu a wadannan bankuna suka gaggayyato. Taron
wanda aka gabatar da shi a wani conference hall na 'hotel' din 'Nicon Noga' ya yi matukar yin

armashi, kowane bako da maidakinsa, wato by couple'.
Mairo da Amiru sun samu kyaututtuka na ban mamaki daga 'yan uwa da abokan arzikinsu. Kudi
wannan tsurarsu da Mairo ta samu sun tasarwa lissafi mai girma, ba’a maganar sauran kadarori
irinsu gidaje, hannun jari da sauransu.
Daddy kadai abin da ya bayar ya girgiza kowa, wai! Ina wuta a jefa marainiyar Allah Mairo a
wajen kannen Amiru, dangin Hajiya da dangin Daddy da suka zo daga Gaya.

Sun sha alwashin idan Habibu a tafe yake yana tsaface musu Da ta yadda har ba ya jin
shawarar kowa sai tashi, baya ganin owa nasa da gashi sai shi, to su a can suka kwan, kuma
acan suka wuni.
Gadararsu shi ne Amiru shi ne silar arzikinshi, wannan bai ishe shi ba, sai da ya kakaba mishi
kanwarshi da a yanzu ta zame musu alakakai, karfen kafa.
Don haka sun sha alwashin sai Amiru ya yi auran dangi, kuma sai sun raba shi da Habibun
koda za su yi yawo tsirara ne.

A wannan dan tsukin Mairo ba ta samun zama, sabida shirye-shiryen fara karatunta a 'Wayne
State University' da ke Michigan. Komawa karatun da ya janyo mata kace-nace da dama har ta
gwammace dama ba ta tarki zancen ba.
Domin Hajiya ta kira Amiru kai tsaye ta fada mishi cewa ba ta yarda ba. Idan ba zata yi karatun
a nan ba, to ta bar shi, amma sun daina daukar wannan rainin hankalin na Habibu da mace
tana gidan aure zata tsallake ta tafi wata uwa duniya wai karatu.
Amiru ya sha mamaki kwarai, don bai taba ganin ranar da wani sabani ya gitta tsakanin Hajiya
da Mairo ba. Biyayya ta ke mata tamkar ta yi mata sujjada. Hajiyar da ke fada da shi idan ya
batawa Mairo rai, amma yau ita ce ta ke mishi magana kamar ba ta taba sanin Mairon ba. Bai
san ba abin da 'zuga' da 'karfar baka' ba sa jawowa ba. Cikin nutsuwa ya soma yi mata bayani
cewa.
"Hajiya babu hannun Habibu a cikin wannan lamari. Idan ma da wanda yake da ruwa a ciki to ni
ne. Don ni na amince mata, Mairo tana karatunta na aure ta, wanda hakan har ya janyo mata
asarar shekara guda, kuma Hajiya wanda ya saba karatu a waje ba zai iya karatu cikin
gurbatattun jami'o'inmu ba. Da wannan dalilin da kuma wasu da yawa ya sa….." "Kai! Rufe min baki!! Shirmen banza shirmen wofi, sallamamme , bawan mace. Da dai ba a san
asalin balbelar ba ne zata zo ta ce da mu daga Makkah ta zo, kuma kowa ya samu rana ai sai
ya yi shanya inda yake so.
Don haka ka tashi ka ba ni waje, maganar karatu na soketa. 'Ya'yan Abdurrahman Gaya ma a
nan suke karatun, bare wata 'yar karkarar da ko kwalta babu.
Allah dai Ya isa tsakanina da Habibu, tunda ya mayar min da da sammatacce. Ya kanainaye
dukiyarka, kanwarshi ta kanainaye zuciyarka ta tsiyata ka, don ba na jin abin da ta samu din
nan kai ka samu rabin-rabinsa. Sabida haka wannan hadin gwiwar da aka yi aka bude Habib
Bank raba shi za a yi, wallahi ba zan yarda ba. Ku biyu ke da banki, amma sunasa ne shikadai
keda bankin. Sabida kai wawa ne. Don haka na ba ka kwanaki bakwai ka kawo min takardun
komi mai nuna ka raba dukiyarka da ta Habibu, idan ba haka ba, wallahi TSINE MAKA ZAN
YI!!!"
Haka ya taso ya fito ko gabanshi ba ya gani. ya yi taga-taga zai fadi, ya yi saurin dafa bango.

Kanshi ya kulle tamau, kwakwalwarshi ta daina aiki. Bai san yaushe Hajiya ta koma haka ba,
bai san laifin da Habibu da Mairo suka yi mata haka da zafi ba. Bai san me zai cewa Habibu ba.
Ya yi tunanin ko ya samu Daddy ya fada mishi ya ba ta hakuri, kuma ya yi tunanin kada haka ya
janyo ya kara laifi a wajenta.
Don haka a kwanakin da suka biyo baya duka Mairo ta kasa gane kan Amirun nata. Kullum
yana kwance a daki yana tunanin ta inda zai bullowa al'amarin ba tare da ya batawa
kowannensu ba.
Don ta Mairo mai sauki ce, yasan ba ta musu da shi, idan ya ce bai yarda ta koma Michigan ba
yasan ba zata nuna bacin rai ba, zata bi umarninshi.
Amma Habibu fa, me zai ce mishi? Mutumin da ke dawainiya da dukiyarshi dare da rana tana
kara bunkasa tana kara habaka shi yana kwance a gida, sai ya ga dama ne zai dan tabuka wani
abu. Ba ya son sunan Hajiya ya fito ko kadan cikin lamarin kada mutuncinta ya zube a idanun
Habibun. To wannan tunanin su ne suka hadu suka haifar mishi da ciwon kai mai tsanani, wanda ya kai
shi har tsayin kwanaki biyar da yin maganarsu da Hajiya amma ya kasa yin wani yunkuri. Ga shi
yau saura kwana biyu kwanakin da ta deba mishi su kare.
Mairo ta shigo cikin shirin barci dauke da dan karamin faranti a hannunta. Ta zauna a gefen
gadon ta dauko kanshi ta dora a cinyoyinta, bayan ta ajiye farantin da ke hannunta bisa durowar
jikin gadonsu. Ta daura kanta akan nashi tana jin yadda ya yi zafi rau. Cike da tausayawa ta ce.
"Don Allah A.A (kamar yadda ta ke kiransa idan ta so nishadi, wato Amiru Abdurrahman) ka
daure mu je asibiti tunda ka ki yarda na kira Dr. Fred, ya kake so na yi? Jin ciwon kan nan nake
kamar a cikin jikina, sannan ka ce ba zaka hadiyi magani ba? So kake nima ciwon ya kamani
sabida damuwa?" Sai ta sa kuka sosai, ta tura kai cikin kirjinshi. Ya mika hannu yana shafar gadon bayanta a
hankali. Amma bai ce komi ba. Shi kadai yasan halin da zuciyarshi ke ciki. Kukanta na tsuma
mishi zuciya, yana kara gigita shi.
"Ya isa Mairo, ya isa don Allah, ba ni maganin na ji zan sha".
Ta dago da idanunta jage-jage da hawaye tana kallonshi, kwanaki biyar kacal, duk ya rafke, ya
rame, ga wata kasumba mara tsari ta fara bayyana, kamar ba Amiru mugun dan kwsalisar nan
ba.
Ta mike zuwa lokar jikin mudubi, ta dauko kwayoyin paracetamol ta ciri biyu ta hada da gorar
ruwan 'swan' mara sanyi ta ba shi. Da kyar ya ke hadiya yana bata fuska don shi sau dubu gara
a yi mishi allura goma da dai ya hadiyi kwayar magani.
Ya tura yatsunshi cikin sumar kanshi yana cudawa a hankali. Mairo ta gane kwarai, akwai
muhimmin abin da ke damun Amirun nata. Wanda zurfin cikinshi ba zai bari ya bayyana ba. Sai
ita ma ba ta takura da lallai sai ta ji ba. Yinin yau ma ya kare baki daya ba tare da ya hassala
komi ba. Ya rage gobe ne wa'adin da Hajiya ta dibar mishi zai cika, suna kwance kankame da juna
kamar masu jin tsoron kada wani abu ya gitta a tsakaninsu. Ya yi gyaran murya ya ce,
"Maryam".
(Sunan da bai taba kiranta da shi ba).
Ba ta amsa mishi ba, illa ta kalli kwayar idanunshi ta cikin dan hasken fitilar barci (dim light). Ya
sake kiranta a karo na biyu, ya ce.

"Alfarmarki nake nema Mairo, za ki yi mini?"
Ta ce
"Babu alfarma tsakanina da kai, sai biyayya da bin umarni. Don haka fadi abin da kake so, ni
kuma ji da bi shi ne nawa".
Ya kara lullube ta da katafaren kirjinshi, ya sarke 'yan yatsunsu cikin na juna, ya ce.
"Maganar komawarki karatu Michigan, na ke so ki bari, ki yi hakuri, ki yi a nan Gwagwalada ya
fiye min kwanciyar hankali".
Ta ce
"Idan don wannan ne ai babu komai. Sai dai na fi son na yi karatu a jami'a mai nagarta da
tsohon tarihi, kamar Ahmadu Bello ko jami'ar Bayero".
"Duka ki hakura, ki barsu, tunda kika ji na ce 'alfarma' to alfarmar nake nema da gaske. Kin san
haka kawai bazan sa ki yin abin da ranki bai so ba, don haka ki yi min uzuri".
"Na yi maka A.A, Allah Ya ba ka lafiya".
***

A yau ne Hajiya ta yi kiranshi don jin inda suka kwana. Ta tsare shi da dara-daran idanunta,
kafarta daya akan daya cikin luntsumemiyar kujerar falonta. Ta ce.
"To yaya, kai nake saurare?"
Ya ce, "Maganar tafiya karatu ai an barta Hajiya, tunda ba kya so".
Ta mika mishi hannu, ta ce.
"To ba ni takardun".
Ya yi wuki-wuki da ido, can ya ce.
"Habibun ne ba ya nan, idan ya dawo za mu zauna a ware a kawo miki……..".
Sai hawaye sharr-sharr wasu na korar wasu, domin gani yake Hajiya ta gama tozarta shi, a duk
ranar da ya doshi Habibun da wannan zancen. Domin Habibun zai yi zargin abubuwa da dama,
ciki kuwa har da tunanin ko Amirun na zarginshi da cin amana ne, ba zai taba kawowa ranshi
Hajiya ce ta sa shi ba sabida yadda ta dauke shi kamar dan cikinta, shi ma yake daraajjata
kamar mahaifiyarsa.
Hajiya ta kama baki, tana cewa.
"Yanzu sabida ina so na rabaka da abin da zai cuce ka, shi ne za ka sanya ni a gaba kana yi
min kuka?"
Ya dago sosai yana dubanta da idanunshi da suka kada suka yi jawur. Muryarshi abin tausayi
ya ce.
"Hajiya, Habibun ne zai cuce ni?"
Ta girgiza kai.
"A'ah, ba zai cuce ka ba. Ni uwarka ni ce zan cuce ka. Habibu sai ya je kauye ya biya
malamansa. Tashi ka je, na yafewa Habibu da kanwarshi Mairo kai, idan har ba zaka kawo min
takardun komi na dukiyarka ba. Kuma zan maka Habibu a kotu sai ya ba ni dukiyar da na!"

Zuciyarshi ta bushe da etsoro da al'ajabi. Ya ce, "Hajiya me ya yi zafi da za ki kai Habibu kotu?
Ki kara min alfarmar kwana biyu. Na yi alkawarin zan cika umarninki ko da hakan shi ne aiki na
karshe da zan gabatar a rayuwata".
Fitowa ya yi zuciyarshi na suya, ya zaburi mota bai tsaya a ko'ina ba sai a kofar gidan Habibu.

A lokacin Habibu na shirin shiga mota zai fita, shi kuma yana danno hancin motarsa (Camero, 2
door) cikin 'gate' din Habibun. Don haka ya fasa shiga motar ya jirashi har ya karaso ya fito
daga motar.ŕ
Ba karamin faduwar gaba ce ta samu Habibun ba ganin irin halin da aminin nashi ke ciki. Suka
rankaya suka koma cikin gidan. Dina ba ta nan, ta je Malaysia ita da yara, duba jikin mahaifinta
da ba shi da lafiya.
Habibu ya isa ga firij, ya dauko mishi gwangwanin 'coke' ya bincire hancin ya mika mishi ba tare
da sun gaisa ba. Ya karba ya yi kurba daya, amma ya kasa wucewa a makoshinsa. Dole ya
furzar da na bakinshi idanunshi sun kara kadawa sun hargitse.
Habibu ya zauna a gefenshi, ya ce
"Be a man, plz! idan kana raye ba abin da ba zaka gani ba".
Ya rausayar da kai cikin amincewa da kalaman Habibun. Ya ce
"Alfarmarka nake nema, sai dai bana son ka tambaye ni dalilina, na yin hakan".
"Ba zan tambaye ka ba Amiru. Fada min komi tsaurinta".
"So nake na janye komi nawa daga cikin 'Habib Bank!!".

Habibu ya yi shiru, domin Amiru ke da kaso 60% wanda hakan ke nufin durkushewar bankin da
ya faro da nasara cikin shekaru biyu kacal da kafuwarshi, wanda ke nufin shi kadai (Habibun)
ba zai iya 'running' bankin ba.
Ya tabbatar makiya sun shigo cikin al'amarinsu, amma bai ga laèèifin Amirun ba, wanda da gani
kasan tursasa zuciyarshi yakeyi, wajen furta kalaminshi.
Ya ce "Idan don wannan ne, ai babu damuwa Amiru. Idan har hakan zai samar maka kwanciyar
hankali, ka ba ni kwana goma, insha Allahu komai naka zai dawo hannunka. Sai dai ina so ka
samu lauya, wani daban, ba Dina lauyar bankinmu ba".
Ya ce
"Ni ba ni da wani lauya".
Habibu ya ce
"Dole sai ka nemo".
Ya juyar da kai yana kwararar da hawaye, ya ce
"Daga yau ba zan kara neman kudi ba, tunda su din fitina ne. Ta yadda har wasu suke ganin su
din (kudi) sun fi mutumci da amana, Ya Allah Ka tsiyata ni……….."
A gaggauce Habibu ya toshe masa baki.
"Kana hauka ne?
Kada 'frustration' (bacin rai) ya sanyaka fita daga imaninka. Ka je ka samo lauya, mu yi abin da
zai kwantar maka da hankali".
"Ni na ce da kai hakan kwanciyar hankalina ne?"
"Ba ka ce ba, don haka abar kazar cikin gashinta ba sai an fiffigeta ba".
Cikin satin Habibu, tare da taimakon Barrister Dalha wani abokin aikin Dina daya daga cikin
lauyoyin 'CBN' da Barrister Mujahid lauyan 'starling' sun hattama komi na dukiyar Amiru, ta
koma hannunshi da sunanshi da sanya hannunshi.
Ya kwashi takardu cikin 'briefcase' ya yi sallama a dakin Hajiya. Kallo daya ta yi mishi ta ga
yadda ya zabge, ya yi zuru-zuru sai karan hancin da idandanun kadai, amma hakan bai sa ko
kadan zuciyarta ta russuna ba, da dai ta kyale Habibu da kanwarshi su yi galaba a kanta. Tunda

sanda ta ke nakudar abinta bayan rainonshi cikin mahaifarta, har wata tara da dawainiyarshi
zuwa girmanshi, ai ba su zo sun tayata ba.
Don haka ta kudure sun daina cin arzikin Amiru, kowa ya ci gashin kansa.
Ya zauna a kujerar da ke fuskantarta, kwakwalwarshi na juyawa. Ya mika mata 'briefcase' ba
tare da ya iya hada ido da ita ba.

Ta bude ta zaro takardun ciki ta sanya 'medicated glass' dinta tana dubawa daya bayan daya.
Ita kanta ta razana da ganin abin da Amirun ya mallaka a 'yan kananan shekarunshi.
Bayan ta gamsu da ingancinsu, ta maida su inda suke tana murmushi, ta ce.
"To ko kai fa?
Ba ga shi ba yanzu sai yasan zafin nema ba ya tashi daga cima-zaune? Yanzu wane kasuwanci
zaka soma da wadannan din?"
Ya kalle ta kawai bai yi magana ba. Ta dauka bai ji ba ne, don haka ta sake maimaitawa.
Ya ce ba tareda ya dubeta ba,
"Sadakar da su zan yi".
"Au fushi ka yi, sabida ina yi maka gata Amiru?"
Ya ce
"Ya ya za a yi na yi fushi da ke Hajiya? Ina juya su, kin ce in kawo miki. Na kawo miki kuma ki
ce me zan yi da su?
Ban iya wani kasuwanci ba, bayan wanda nakeyi, ni ma'aikaci ne. Aikin banki shi ne wanda na
iya tsawon shekaru goma.
A yau kin ce na barshi, don kada Habibu ya samu dan wani abu a jikina, wanda bai taka kara ya
karya ba. Bayan kin san duniyar cudarni in cudeka ce, kuma shi ma ba matsiyaci ba ne, yana
da rufin asirinshi wanda da kadan ne bai kai nawa ba.
Haba Hajiya! Shekarata nawa da Habibu bai cuce nin ba sai yanzu da muka zama daya?"
Hajiya ta ce
"Rabi (half) kuka zama ba daya ba, sallamamme, bawan mace. Tunda ba ka so ka yi zuciya
har kana cewa sadakarwa zaka yi, ni ina so, zan yi maka sadakar, amma ba duk ba. Ranar da
tsiya ta isheka ka waiwaye su, nima ina da 'account' din da zan adana maka su su hayayyafa ba
Habibu ne kadai ya iya juya sisi ya koma kwabo ba".
Duk abin nan da ake Daddy bai sani ba, don shi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login