Showing 6001 words to 9000 words out of 79746 words

Chapter 3 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

"Don Allah ko kinga Mairon Hure?"
Ta ce, "Na ganta ta mika kwanar gidan su".
Ya ce, "To madallah. Ta yi gaba abunta dai-dai sanda Malam Bedi ya cimmasa da cazbaha a
hannunsa ya ce, "Mai kake tambaya ne?"
Ya ce "Mairo mana, sama ko kasa na nemeta na rasa?"
Dariya ya ba wa Malam Bedi, ya ce "Mairon ce zata zauna maka waje daya? Ai yadda kasan

tsuntsuwa haka ta ke. Idan dai ba gaban Innarta ba ne babu inda zata zauna. Ai jin ku kawai
nakeyi da ka ce wai ta zauna nan mu fito".
Ya girgiza kai suka ci gaba da tafiya yana ba shi labarin Mairo. Wanda duk mai bakanta zuciya
ne ga Habibu.
Ya ce "A rana in ba a kawo min kararta sau hudu ba, a kawo sau shida. Malaminsu ya gaji da
sulalewar da ta ke yi, ya ce ta yi zamanta gida. Ni al'amarin Mairo ai sai addu'a. Kuma duk Hure
ce ta jawo".
Habibu ya yi kankan da murya ya ce "A gaskiya Baba kai ma da naka laifin. Mai yasa idan Innar
ta yi hukunci akan Mairon ba ka ketarewa? Yanzu sabida Allah kamar Mairo ace har yanzu ba
ta shiga makarantar boko ba, sai yaushe? Sai karatun ya wuce lokacinta? Fisabilillahi ina
matukar takaicin rayuwar Mairo. Ina tausaya mata, domin dai ita 'ya mace ce, gidan wasu zata
je ba da jimawa ba.
Babu mijin da zai iya zama da ita da wannan rashin tarbiyyar wadda ni ba haka aka yi mun ba".
Ya yi shiru kamar zai yi kuka, zuciyarshi na matukar kuna.

Malam Bedi da alama zancen Habibu na shigarsa. Ya ce "Yanzu ni me zan iya akai Habibu? Ba
karamin abu ba ne Hure ta amince akai Mairo makarantar book ba. Ni kuma bana son tashin
hankali balle abin da zaya bata mini rai, ina zamana lafiya".
Habibu ya dubi mahaifinsa cikin ido, ya ce "Shin Baba kai ko Inna wa ke auren wani?"
Malam Bedi ya ce
"Ni ne".
Ya ce "To matukar kai ke da iko da ita dole ka ba ta umarni. Kuma dole ta bi idan dai ita matar
kwarai ce. Ka daina tsoron sababinta, kai ma ka bude mata murya. Ita ma ta iya ta bude maka
makogwaro balle kai?"
Ya yi murmushi ya ce "To yanzu me za a yi?"
Ya ce, "Ni zan je na samu hukumar makarantar in musu bayani har halayenta duka zan fada
musu, don su yi hakuri da ita, su kuma san matakin da za su dauka a kanta idan ta gudo ba tare
da sun yi la'akari da fadan Inna ba. Ga kuma makarantar islamiyya da na ga yara suna zuwa da
hijabinsu da uniform, nan ma zan je in ba da sunanta su sanyata ajin da ya dace da ita. Kai kuma aikinka shi ne ka tabbatar tana zuwa akan lokacin, da son ranta da na Innar ko
babu?"
"Malam Bedi ya ce "Sha Allahu za a yi kokari. Allah dai Ya yi maka albarka Habibu, idan ban da
kai dan uwanta wa ya damu da ita balle har ya ce a sanyata makarantar?"
Habibu ya ce "Sai abin da ya kawo ni, amma ina ganin mu samu gindin bishiyar can mu zauna,
maganar ta zaune ce".
Malam Bedi ya ce "Inji dai ALHERI ne?"
Ya ce "Alheri ne, idan Allah Ya so Ya yarda, kai ma ka yarda".

Suka samu kututturen bishiyar wata goriba mai duhu da inuwa mai sanyi suka zauna. Malam
Bedi ya tattara dukkan hankalinsa akan Habibu, yana zake da son jin mai zai fito daga bakinsa.
Shi kuwa Habibun in banda addu'ar neman rinjaye babu abin da yake dannawa Malam din daga
zuciyarsa. Malam Bedi ya ce

"Kai na ke saurare, kuma ka yi shiru".
Habibu ya ce "Eh to, dama Alhaji ne ya ce in zo in shawarce ka, ko kuwa in nemi izninka, idan
ka yarda shi ke nan. Idan ma ba ka yarda ba babu damuwa sai na hakura".
Ya ce (a dan kufule) "Wai mene ne ka ke ta kwana-kwana? Daga ji ba abin arziki ba ne, don
abu idan na arziki ne ba a kumbiya-kumbiyar fadarsa".
Ya yi murmushi ya ce "Yi hakuri Baba. Wani abu ne na zamani ya shigo mana cikin na'ura mai
kwakwalwa wai shi yanar-gizo (internet). Ta cikinshi babu inda ba zaka sadu da shi ba a duniya.
To rannan ina lalube na, sai na ci karo da tallan wata makaranta a Malaysia suna neman
dalibai. Kamar da wasa na cike form dinsu na tura musu. To kwatsam har na manta, shekaran jiya sai ga sako sun turo cewar sun dauke ni, na zo na biya
kudin makaranta na fara karatu. Na samu Alhaji na fada masa, ya tayani murna kwarai, to
amma shi kansa ba ya da kudin da zai iya daukar nauyin karatun, amma yace zai yi min hanyar
da zan mika neman taimako daga gwamnati ta hanyar wani abokinshi mai baiwa gwamna
shawara akan harkokin matasa wai shi ALHAJI GAMBO ADO, kuma ya tabbatar min za a samu
insha Allahu, ragowar shi Alhajin ya yi alkawarin cikasawa daga aljihunshi.
Shi ne ya ce na zo na fada maka tun kamin komi ya yi nisa, kada sai an gama wahala ka zo ka
ce ba ka yarda ba. Yanzu kuwa ba abin da aka yi, sai da amincewarka".

Shiru Malam Bedi ya yi kamar ruwa ya cinye shi, yayinda Habibu ya ci gaba da jifansa da,
"Innahu ala raja'ihi la-kadir". Bai gushe ba yana maimaita addu'arsa sai jin muryar malam Bedi
ya yi tana tambayarsa har tsayin shekaru ko watanni nawa za a yi ana karatun?
Ya yi godiya ga Allah a zuciyarsa, domin da alama akwai nasara, ya ce "Abin ya fi karfin
watanni. Shekaru shidda ne zan yi ina karatu akan na'ura mai kwakwalwa".
Malam bedi ya ce "To daga nan kuma fa?"
Habibu ya murmusa ya ce "Sai na dawo gida na nemi aiki".
Malam Bedi ya ce "A'ah, ba haka nake son ji ba, sai ka dawo ka yi aure ka tara min 'ya'yan da ni
Allah bai bani da yawa ba".
Habibu ya sunkuyar da kai yana murmushi, ya ce "Insha Allahu Baba".
Malam Bedi ya ce "To ka je, Allah Ya tabbatar da ALHERI……....."

Dai-dai nan Habibu ya ji “tim!” A tsakiyar kansa an nannako masa katuwar goriba a tsakar ka.
Kwakwalwarsa ta daure, kansa ya yi dumm!! Kamar an kwala masa dutse. Wata azaba ta
ziyarce shi tun daga tsakiyar kansa har yatsar kafarsa. Kamin ya gama farfadowa daga
takaitaccen suman da ya yi, sai jiyo zazzakar muryarta yayi kamar zata tsige masa dodon
kunnuwa tana fadin "Yaya Habibu sanya min a aljihunka, nawa aljihun bujen ya cika……..".
Suka daga kai su duka biyun suna kallonta, Mairo ce kwance abinta akan reshen bishiya, a
kalla ta fi karfin awanni biyu akan bishiyar. Tunda liman ya tada kabbarar sallah ta yi raka'a daya
ta dago, ta hango goshin kowa a kasa, babu mai kallonta, ta yayibo tabarmarta da zummar
tahowa gida. Sai kuma ta hango nunannun goriba ai kuwa ta daka tsalle ta dare. Duk abin da suke cewa akan kunnenta, sai dai ba wani fahimta ta ke yi ba sabida hankalinta ba
ya jikinta. Ita dai tana tsinkar goribar ta gutsira ta ji idan da zaki ta sa a buje, idan ba zaki ta
cillar. Sai da bujen ya cika ne ga shi kuma ba ta iya barin wannan zazzakar, ta cillowa Habibu
ajiya.

Ya bude baki da kyar ya ce "To sauko mu tafi".
Ta ce "Bari na tsinkowa Baba".
Ya ce "A'ah, shi baya da karkon hakori".
Ta kamo reshe bayan reshe tana bin jikin bishiyar cikin kwarewa har ta sauko suka taho gida.
A ranar da ciwon kai ya kwana, amma bai daina yi wa malam Bedi magiya da naci akan
makarantar Mairo ba, ko baya nan. Malam din ya yi masa alkawarin kada ya damu, da yardar
Allah kamin ya dawo Mairo ta kimtsu.
Washegari ya je ya ba da sunanta a makaranta aka sata aji uku. Ya yi musu bayaninta
dalla-dalla wani malami da yake makocinsu ne ya ce ya san Mairo farin sani, ko shi yana
takaicin rashin sa ta makaranta, to amma kowa ya san sababin Inna Hure, idan dai akan Mairo
ne, shi yasa kowa ya sa mata ido. Amma insha Allah zai tsaya a kanta kamar yadda zai
tsayawa 'yar cikinsa.
Habibu ya yi godiya mai tarin yawa, ya nemi taimakonshi a kan ya taimaka ya bayar a dinka
mata uniform, ya kirgo kudi ya ba shi har na littattafai da jakar makaranta. Sannan ya nufi
islamiyyar yaran Gurin-Gawa, nan ma ya ba da sunanta. Sun tabbatar mishi ba komai ai irin su
Mairon ake son a gyara.
Hankalinsa bai kwanta ba, sai da ya ga Mairo ranar litinin cikin kayan makaranta da jakarta a
rataye ta tafi makaranta. Duk da Inna Hure na kumbure da shi, bai damu ba, tunda ya cika
kudurin da ya dade yana damun zuciyarsa. Don haka koda ya je yi mata sallama zai komo
Kano ta yi masa kunnen uwar shegu. Hure ta ga tijarar Malam Bedi irin wadda ba ta taba gani ba, ba ta kuma taba tsammanin ya iya
ba, domin cewa ya yi idan Mairo ba zata je makaranta safe da yamma ba, to dukkaninsu su zo
su fice masa a gida, su tafi duk duniyar da za su.
Ba ta yi magana ba, amma a cikin ranta tasan wannan aikin Habibu ne, don yadda Malam din
ke jin maganar Habibu ko ubansa sai haka. Abin da ta ce da shi kawai shi ne, "Saboda ka
tabbata tsohon bakauye ka zauna dan ka ya fi karfin ka".
Ya ce "Eh, koma mai zaki ce ki ce, amma Mairo da uwarta ba su zama min cikin gida muddin
Mairo ba zata nemo ilimi ba. Me ye marabarta da dabba? Babu! Dabba ce aka sani da hawa
bishiya da cin abincinta daga 'ya'yan itace, amma ba dan mutum ba".

Habibu ya karkace kai ya yi ta ba Innarshi hakuri, ya ce "Inna ku yarda da ni, ba ni da nufin
cutarku, sai dai ma na yi kokarin ganin duk abin da zai zamto cuta a gare ku na yake shi iya
karfina. Ina nufin Maironki da alheri ne, bayan wannan ba wani abu. Ke da kanki wata rana za ki
gane gata na yiwa rayuwar Maryam. Don Allah Inna ki sauko ki yafe min, kisa min albarka!". Zuciyarta ta yi sanyi lakwas, ta ce "Ai shi ke nan, nasan iyakar gaskiyar ke nan, laifina shi ne,
ina son Mairo da yawa".
Ya yi murmushi ya ce "Hakan ma ba laifi ba ne. Sai dai ki yi kokari kada son da kike mata ya sa
ki kasa lankwasata. Ni ma ina son Mairon ki, son da bana yi wa kowa a duniya, amma idan har
da gaske ina sonta, dole in inganta mata rayuwa da gishirin zamani, wanda idan babu shi miya
duk dadinta lami ce. Wannan gishirin kuwa ba komi ba ne, face wannan ilimin dana ke so Mairo
tayi. Shi ne zai haskaka mata ragowar bangarorin rayuwarta, tasan kanta, tasan inda ta sa

gaba.
Amma a yanzu wallahi Mairo ba ta da maraba da 'ya'yan birrai".
7/28/21, 10:59 AM - Buhainat: 80


Dariya Inna ta yi, ta ce "To Allah Ya taimake mu ta kimtsu".
Ya ce, "Amin--amin, ko ke fa Innata? Ni ma karatun zan tafi..." Ya warware mata zare da abawa.
Ga mamakinsa sai ya ga damuwa karara ta bayyana a kyakkyawar fuskarta, ita da a kullum, ta
ke nuna ba ta damu da shi ba. Ya shiga kwantar mata da hankali cikin tausasan kalami, yana
nuna mata shekaru shida kamar yau ne, idan da rai da lafiya. Da kyar ya samu ta sa ma abin
albarka. Da wannan Habibu ya koma Kano ya ci gaba da shirye-shiryensa, da taimakon Baffansa. Cikin
watanni uku kacal komi ya kammala, ya zo wa iyayenshi sallama.

Ya ji dadin yadda ya ga Mairo cikin wankanta fes! Ba ta kuma yi masa wannan damuken oyoyon
ba, an fara nutsuwa ke nan.
Ya yi murmushi, ya ce, "Mairon Inna 'yan makaranta, ya ya dai?"
Ta yi murmushi ta kawar da kai ba ta ce komi ba. Ya kamo hannayenta ya ce "Ba ki ga yadda
kika soma sauyawa ba? Ina fatan duk runtsi za ki dage da zuwa makaranta? Zan tafi karatu
Mairo, sai Allah Ya dawo da ni kimanin shekaru shidda a nan gaba. Ki kula da Innarki, ki dinga
tayata aiki, ba wasan 'yar bebi ba kin ji Mairo nah?" Ta shiga damuwa sosai, nan da nan sai ga hawaye rau-rau a idanunta. Ta ce "Yanzu Yaya
Habibu shekaru shidda zan yi ban ganka ba? Ina zaka je? Mai yasa ba zaka ci gaba da zama
gidan Baba Abbas ba kana zuwa makarantar a can?"
Ya ce "Kamar yau ne Mairo za ki ga na je na dawo, idan dai da rai da lafiya. Ki kula da kanki, ki
dinga wanka kullum, ki dinga yanke akaifarki ta kafa da hannu duk sati. Ki kuma dinga wanke
gashin kanki shi ma duk sati, kin ji?"
Ta ce, "Na ji Yaya Habibu, Allah Ya dawo da kai lafiya".

Ya ji dadi sosai, bai zaci Mairo tana da dan hankali ba ko yaya ne, har ta yi wa mutum addu'a.
Ya sa hannu a aljihunsa ya ciro naira ashirin ya bata, ta yi ta murna ta je tana nunawa Innarta.
Haka Habibu ya tafi cike da tunanin Mairo. Yana addu'a, Allah Ya sa ta dore da hakan. Watau
turbar da ya sanyata.
Washegari ya tashi zuwa Malaysia, inda ya samu gurbi a Unibersity of Malaya.

Ya sha wuya matuka kamin ya samu ya mance da tunanin gida. Da taimakon abokinshi Amiru
wanda shi ma dan Kano ne ya samu ya soma fuskantar karatun, amma babu ranar Allah da
zata fito ta fadi bai tuna Mairo ba.
***


BAYAN TAFIYAR HABIBU
M

alam Bedi tsaye yake akan kafafunshi kan karatun Mairo don cika alkawarin da ya daukarwa
Habibu. Da taimakon Allah Mairo ta saba da zuwa makaranta, kuma lokuttan makarantar sai ya
shafe lokacin da ta ke samu ta hau bishiya ko ta yi wasan 'yar tsana.
Idan ta dawo makaranta karfe daya na rana wanka zata yi ta ci abinci, ta yi sallah. Karfe biyu
cikin ajinsu na islamiyya ya ke mata. Ba kuma za su taso ba sai goshin magriba, don haka
ranakun alhamis da juma'a da yamma kadai ta ke samun hutu. A cikinsu kuma tana tare da
Innarta suna ayyukan gida wadanda ta alkawarta wa Yaya Habibu taimakawa Innar. Rannan Mairo na surfen masara Inna Hure tana bakacewa, Mairo ta aje tabaryar ta ce "Oh
Inna, Yaya Habibu yau watanninsa bakwai ke nan, yana can a cikin Turawa".
Inna ta ce "Wa ya ce miki a Turai yake? Kasar Larabawa ne".
Mairo ta yi murmushi, ta ce "A'ah Inna, rannan na tambayi malaminmu na makarantar book, a
ina Malaysia ta ke? Ya ce min Asia ne, can wajejen India da Pakistan".
Inna ta kama baki ta ce "Ke Mairo, yaushe kika iya Turanci haka?"
Mairo ta ce "Ba Turanci na yi miki ba Inna, sunan kasashe na fada miki".
Wani dadi ya kama Inna Hure, ba tasan sanda ta ce "Kai Allah Ka sakawa Habibu da alheri”

MARYAM BEDI, ta ci gaba da karatunta cike da himma da kwazo. Takan sanya wa ranta cewa,
kawai Habibu na kallonta, yana jin dadin kwazonta. Yana kara mata karfin gwiwa. Ba ta yarda
wai shekaru shidda zai yi bai dawo ba. A ganinta shi ne Habibu na iya dawowa yau, ko gobe,
don kawai ya rutsa ta, ya ga irin kwazonta. Saboda haka cikin shekara guda kacal, Maryam Bedi, ta zama zarrah a ajinsu na boko, kan
gaba a ajin islamiyyah, wadda ke da haddar izfi ashirin na Alkur'ani a cikin kanta.
Sauran littattafan addini kuwa idan ta bude su tana karantawa tana fassarawa Inna tsarki da
alwala, da irin sallar khashi'ai da sallar da ake dunkulewa a jefowa bawa kayarsa, tun kamin ya
tashi akan dardumarsa. Sai Inna ta sa habar zaninta tana share hawaye, ta ce "Ba karamar
cuta na so na yi miki ba Mairo".
Shekaru uku ke nan cif da tafiyar Habibu, kuma a yau ne ranar saukar su Mairo. Ta sha wanka
da sabon dinki na atamfa (hitarget) da suka yi anko gaba dayansu. Ta dora wani sabon farin
hijabi akai, wanda ya tabo har gwiwarta. Ta azalzali Innarta ta yi sauri ta gama shiryawa su tafi
kada wajen zama ya cika ta rasa inda za ta zaunar da ita. Innar kuwa sai sake murza kwalli ta
ke a idanunta yadda zata fito radau!
Ta kuwa fito din, sai kyallin wanka da basilin ta ke. Suka jera abinsu Mairo na ta addu'ar samun
nutsuwa cikin zuciyarta sakamakon ganin cincirodon al'ummar kauyensu wadanda ake nufin ta
yi karatu a gabansu.
Tuni Malam Bedi ya isa wajen tun kamin su zo, yana cikin rumfar iyaye maza, a sahun gaba,
yana ta ware ido don ganin ta inda Mairo zata bullo.
Can ya hangota rike da hannun Innarta, ta samu wajen zaman da ya dace da Innar ta zaunar
da ita, sannan ta karasa cikin 'yan group dinsu suka yi sansani.

Taro ya yi taro, mai gabatarwa ya fara gabatarwa bayan bude taron da addu'a, daga limamin
garin Gurin-Gawa. Maryam Bedi, ita ce wadda aka fara kira ta bude taron da karatun Alkur'ani
cikin daddadar kira'arta kai ka ce diya ce ga Khusairi, inda ta karanto karshen suratul Fathi,

wato ayar nan ta "Muhammadurrasulullah…...."
Gaba dayan jama'ar dake wajen jikinsu ya yi sanyi, sai ga Malam Bedi yana kuka. Da ta dasa
aya aka dauki kabbara kowa na cewa "Ai Mairon Hure ce, diyar Malam Bedi".
Innar kuwa sai washe baki ta ke, bakinta ya ki rufuwa don kuwa duk matan da suka san ita ce
babar Mairo,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login