Showing 12001 words to 15000 words out of 79746 words
Chapter 5 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf
sai ya dwo.
Malamin maths ya shigo ya fara ba su darasi, Mairo ta tattara hankalinta akan malamin
gabadaya, ba ta damu da hararar da Nabilah ke mata ba. Ya gama ya fita, sai ga Uncle ya
dawo wanda kuma shi ne yake daukarsu darasin Turanci.
Yana koyarwa, amma rabin hankalin sa na kan Mairo. Ya lura sabanin ragowar ‘yan ajin,
Maryama ta ba shi dukkan 'attention' dinta, da wani muradi cikin kwayan idanunta. A zahiri
wannan yarinya bakauyiya ce lakadan, amma ga dukkan alamu, ba haka Allah Ya yi nufin
barinta ba. Ya kammala darasinsa ya ba da aiki 'Essay Writting' mai take guda uku, ya ce kowacce ta zabi
wanda za ta iya yin sharhi a kansa. A rubuta a kawo masa washegari. Hankalin Mairo ya tashi,
domin dan ilimin nata bai kai nan ba. Magana ce ake so su rubuto da harshen Turanci akalla
shafi daya da rabi na littafi. Aka kada kararrawar fita break, amma Mairo ba ta yi niyyar fita ba. Ta kurawa aikin 'assignment'
dinta ido tana tunanin ta inda za ta bullo. Ba ta ankara ba ta ji wani sassanyan kamshi na dukan
hancinta da kuma alamun zaman mutum a bencin gabanta. Ta dago a hankali tana kallonsa,
Uncle ne. Ya ce "Yaya dai Maryama, kowa ya fita cin abinci, amma ke ban ga alamar kina da niyyar fita
ba?"
Ta sadda kai cikin kankanuwar murya ta ce
"Ina tunanin yadda zan yi aikin da ka bayar ne".
Ya yi murmushi ya ce "Aiki ne kuwa mai sauki, amma ga wanda ya gane tambayar. Wacce
tambaya kika dauka a ciki?"
Ta sunkuya tana kara nazarinsu, ta ce "Ina ganin ta daya za ta fi mun saukin amsawa, tunda
daga karkara na ke, 'Yadda ake bikin sallah a karkararmu".
Ya yi murmushi, ya ce
"Ni kuwa sai na ga tambaya ta biyu zata fi dacewa da ke 'Ranata ta farko a sakandire', za ki
kawo 'points' sosai wanda zai taimaka ki yi 'scoring' maki mai yawa. Kinga sauyin abubuwa da
dama, a zuwanki babbar makaranta. Haka ne ko ba haka ne ba?"
Ta yi murmushi, wanda ya lotsa kumatunta hagu da dama. Akwai wani asirtaccen kyau a tare
da Mariama, wanda rashin gyara da rashin gogewa ya boye shi. Yarinya ce kamar diyar
Larabawa, sai dai fatarta a dafe ta ke, kamar an shafa mata shuni, wanda kai tsaye ya
banbantata da sauran yaran makarantar. Ta ce "Haka ne Uncle. Na gane cewa, ashe mu ba mutane ba ne, ababen kyama ne ga wasu
jinsin al'ummah. Abin dariya ga wadanda Allah Ya yiwa falalar rayuwa. Ban san cewa ni 'yar
talaka ba ce sai yanzu, tunda kuwa ban taba neman abin da zan ci na rasa ba, sai na dauka
iyakarta ke nan. Ashe akwai masu shi fiye da ni, amma idan da ace ni ce a matsayin mai shi
din, ba haka zan yi wa mara shi ba!".
Mamakin kalaman karamar yarinya kamar wannan ya kama shi. Sai dai ya kula magana ta ke
tun daga karkashin zuciyarta, ba wai tunaninta ba ne.
Ya ce "Mariama!"
Ta dago ta dube shi, amma ba ta amsa ba.
Ya ce "Ina son ki sa wa ranki cewa, ba duka mutanen da kika tarar halinsu daya ne ba. Kowa da
kika gani a duniya da irin halayyarsa. Wani yasan darajar kansa, yasan ta mutane, wani bai san
darajar kansa ba, bai san ta mutane ba. Wani yasan darajar kansa bai san ta mutane ba.To
wannan ba cikakken mutum ba ne, kuma shi ne wanda Allah Ubangiji Ya yi alkawarin dankafar
da shi a duniya da lahira sabida girman kansa. Da zarar ka yi tunani ko ya ya cewa, kai wani ne,
to kai ba kowa ba ne a wurin Ubangiji.
Sabida haka a yadda kika dau kan naki a ba kowa ba, ci gaba da hakan. Amma kada ki yarda
da cewa, sai wun fi ki ne. Ido biyu gare su, kunne biyu, kafafu biyu, hannaye biyu, ke ma su
gare ki. To akan me za ki yi tunanin sun fi ki? Wanda ya fi ki kawai shi ne wanda ya fi ki tsoron
Allah!”. Jikinta ya yi sanyi, ranta ya yi fari. Tana dubanshi da kyawawan idanunta, ta ce "Uncle kana
nufin ni ba abun kyama ba ce?"
Ya girgiza kai "Ko daya Maryama. Da za ki daure ki fidda su a gabanki ki yi karatu sosai ki dinga
gyara kanki, sai kin fi su kyan gani. Ko a yanzu haka kin fi su, gyara suka fi ki. Ba kawa kika zo
nema ba, ilimi kika zo nema, irin wanda suka zo nema. To akan me za ki damu da su? Ai abu
daya za ki damu da shi, shi ne ki dage ki ga cewa ba su fi ki kokari ba". Ta yi murmushi ta ce "Uncle kana da kirki, sai na ke jinka kamar Yaya Habibu. Shi ma haka
yake yi min irin maganganunka. Da zai zo ya ganni a makarantar nan, ban san irin farin cikin da
zai yi ba".
Ya ce "Yaya Habibu yana ina yanzun? Ni kuwa inje in gaya masa, ga ki a babbar makaranta".
Ta washe baki ta ce "Ayyah, yana da nisa, yana karatu ne a kasar waje, amma komi nake yi sai
in yi ta ganin kamar yana kallona, sabida shi ne ya dage, ya sani a makaranta".
Ya ce "Ni kuwa gani na dage da yardar Allah sai kin yi karatun da Yaya Habibu zai dawo ya yi
alfahari da ke, amma hakan ba zai yiwu ba sai da goyon bayanki Maryama, wanda ba komi ba
ne da ya wuce perserbearance (jajircewa) da ba da himma".
Ta sake yin murmushi har kumatunta suka lotsa, ta ce "Na gode Uncle, kuma na yi maka
alkawarin I'll persebere".
Ya yi mata tafi guda daya ya ce "Good Maryama, ina neman alfarmar ki rike ni a matsayin Yaya
Habibu",.
Wani farin ciki ya bayyana a fuskarta, ta ce "Kenan ka yarda na rinka kiranka da Uncle Habibu?"
Murmushi ya yi, "A'ah, UNCLE JUNAIDU. Sunana Junaidu Galadanchi".
Ta ce "Galadanchi?"
Ya ce "Eh, kin santa ne?"
Ta ce "A'a, ban taba ji ba ne. Garinku ne Galadanchi ko sunan Babanka ne?"
Da alama Maryama matambayiya ce, kuma matambayi ba ya bata. Hazakar yaro na da alaka
da yawan tambayarsa (curiosity).
Ya ce "Galadanchi karamar unguwa ce a cikin birnin Kano. Sai dai tarihinta mai girma ne ga
Kanawa. Duk wani Ba-Kano ya san Galadanchi, sannan mu 'ya'yan cikinta muna alfahari da ita
da kasancewarmu 'ya'yanta.
A Galadanchi ne aka fara samun Dr. a ilimi a jihar Kano. Haka idan kika bi tarihin manyan 'yan
bokon Kano, da mayan malaman Jami’ar Bayero, wadanda suka fito da jihar Kano a tsakanin
jihohi 'yan uwanta, to duk 'yan Galadanchi ne. sannan gasu da kyau, ga Alkur’ani da Tajwidi a
cikin kansu". Ta ce "Ina fatan wata rana, in ziyarci Galadanchi".
Murmushi ya yi "Insha Allahu za ki je Galadanci Maryama. Yanzu dai jeki ci abinci kamar sauran
dalibai, idan kun fito 'pref' da yamma sai ki rubuta aikin gobe ki kawo mani".
Ba musu ta mike ta nufi kofar fita. Bai daina kallonta ba har sai da ta kule ya daina ganinta.
Shi kam bai san dalilin da ya sa ya damu da yarinyar ba. Haka dan zaman da suka yi a yanzu
ya kara sanya mishi jin son taimakonta.
Mairo da ta fito 'pref' ta yagi takarda kamar da wasa, ta soma rubuta 'essay' dinta mai taken 'My
first day in secondary school'. Da jagwalgwalallen turancinta mara 'tenses' har haduwarta da
Uncle a aji ta rubuta, inda ta ce, ba ta taba haduwa da mutum mai kirkinsa ba. A karshe ta ce
“shin ko mutum nawa ne masu jin kai irin UNCLE JUNAIDU? Ta ce, Uncle Junaidu ya sa mata
burin son zama malamar makaranta, wanda a da ba ra'ayinta ke nan ba.
Ta sake bin jagwalgwalonta ta yi dan gyaran da zata iya, ta sanya a tsakiyar littattafanta.
Washegari da karfin gwiwarta ta shiga aji, to amma Uncle bai tambayi 'assignment' din shi ba
sai da period dinsa ta shiga. Yana bi daya bayan daya yana marking har ya zo kan na Maryama
Bedi. A zahiri duka 'yan ajin sun fi ta iya Turanci, da kula da 'tenses' sabida su sun sami
kyakkyawan tushe daga makarantu masu tsada. To amma idea da ke cikin rubutun Maryam
fasaha ce tsagwaronta.
Ta yi rubutunta kamar da gasket, tana magana kamar akan idonsa abin ya faru. Ya kirata yana
nuna mata kura-kuranta, tare da cewa "Matsalarki daya ce a Ingilishi (tenses), don haka
darasinmu na yau tenses ne".
Nan da nan ya fara darasi inda Mairo ta dauki dukkan hankalinta ta likawa Uncle. A yau da aka
fita break ma ba ta yi saurin fita ba, ta zauna ne tana aikin lissafi (maths). Uncle Junaid ya
kwankwasa desk dinta, ta yi hamzarin dagowa kamin ta yi murmushi ta ce "Uncle dama ba ka
fita ba ne?" Ya ce "A'ah na fita, dawowa na yi. Tun daga staff room na hango ki kina rubutu, zuwa na yi na
gaya miki ki daina zama cikin aji yayin da kowa ya fita. Komi na makarantar nan cikin tsari yake,
yanzu lokaci ne na cin abinci ba na yin aiki ba. Idan wani bai ga abinsa ba yana iya cewa ke
ce". Ta rufe littafin ta mike ba tare da ta ce dashi komi ba. Ta nufi hanyar fita, har ta kai bakin kofa ya
ce, "Maryama".
Ta juyo cikin damuwa, ya ce, "Ina fatan ba ranki ne ya baci ba?"
Sai ta koma dariya, ta ce "A'ah Uncle".
Ya ce "To mai yasa kika yi shiru?"
Ta ce "Ka yi hakuri Uncle Junaidu".
Ya yi murmushi ya bi hanyar kofa shi ma ya na kissimawa a ranshi Maryam na daga cikin
miskilan yara.
Cikin sati biyu kacal Mairo ta fahimci tsarin komi na makarantarsu, sai dai ma ta nuna wa wani.
Babu ruwanta da su Kausar, duk kuwa da basu fasa yi mata izgilanci ba, a daki ne ko a aji. Sai
dai su kansu sun san akwai wani aminci, ko kuwa shakuwa ta musamman tsakanin Maryam da
Uncle, don haka basa yi mata a gabansa. Saboda Maryam Uncle Junaid ya kirkiro tutorial class
da yamma da yake yi akan darasinsa English da darasin Uncle Wahhab (mathematics), wanda
ba karamin taimakawa Mairon ya yi ba.
Duk wasu matsalolinta akan karatu Mairo ba ta shayin gayawa Uncle Junaidu shi kuma ya
tsaya mata kamar Yayanta. Shi kansa bai san mai yasa ya tsani Kausar da Nabilah ba, tun
daga ranar da ya lura sune kawai matsalar Maryama cikin makarantar.
Ita kuwa kullum kokarinta shi ne, ta boye abin da suke mata, kada ya gane. Don duk ranar da
ya hora su sabida ita, idan sun koma daki akanta suke hucewa. Rannan da ya sa su noma
sabida sun karya bencin ta karfin gaske, duk don kada ta zauna kusa da su, da suka komo
hostel suna ta digar da gumi. Sun yi jawur sabida wahala, Kausar ta yi kuka ta ce "Wai Nabilah
wannan bakauyar kanwar uban Uncle ce ne?"
Nabilah ta ce "A'ah, ina jin tare aka haife su, don shi ma da alama dan talaka ne ya soma
daukar albashi ya je ya sayo gwanjo yana zanzarewa".
Kausar ta ce "Uban wa ya gaya miki? Abokin Yayana ne tare sukai karatu, dan chief justice
Atiku Galadanchi ne. Har gidansu na sani sanda muka zo Kano daga Jos da Yaya Yusuf bikin
wani abokinsu, abin da na kasa ganewa shi ne, mai wannan billager din ta ke gaya masa yake
damuwa da ita? Ni kam da nasan har da irin wadannan a makarantar nan ai da ban yarda
Daddy ya kawo ni ba".
Nabilah ta ce "Ke kika ga zaki iya, amma ni nan idan an yi hutu bazan dawo ba, Edcel collage
zan koma. Minjibir ta rube, ta zama ta yaku-bayi".
Suka kwashe da dariya, Mairo dai na jinsu ba ta dago ta dube su ba, sai rubutunta ta ke kamar
alhudahuda.
Ranar ziyarar 'yan makaranta, wato bisiting day ta zo. Kowanne dalibi ya sha wanka ya yi fes,
ya fito neman nasa. Mairo dama ba ta sa a ka ba, tasan Babanta da Innarta duka ba su san da
wata ranar ziyara ba. Tunda ko radiyo ba su damu da su saurara ba, don haka ta samu can
wani gefe gindin wata bishiyar goba mai inuwa ta zauna akan benci tana nazarin littafin the boy
slabe da ta karbo a library.
Can anjima ta daga kai ta kalli motoci na gani na fada da ke ta fakin yara na rugawa su
rungume iyayensu, sannan a soma kokawar fito da manyan ma'adanan abinci da katon-katon
na kayan masarufi ana ajiyewa.
Waje ya cakude kowa na nemawa 'yan uwansa wurin zama, babu wanda yasan da ita, a lokacin
ne ta ji babu dadi, ta ji kewar Innarta. Idanunta suka cicciko da kwalla. Kamar daga sama ta ji
muryar Uncle a kanta ya ce. "Mariama".
Da sauri ta dago tana kokarin boye kwallar idonta, Uncle ne rike da manyan ledoji guda biyu, a
bayansa wata yarinya ce budurwa da akalla zata girme ta da shekaru biyu da kuma wani yaro
da zai yi tsara da ita, su kuma niki-niki da manyan kulolin abinci da picknick cooler wato irin
kular nan da ake zuba lemuka da kankara mai hade da dan famfo a jiki. Ko ba ta tambaya ba
tsabar kamanninsu da juna ya gaya mata wadannan yaran kannen Uncle Junaid ne.
Ta zame kasa tana gaishe shi, ya ce "Kuka kike ko Maryama, sabida mene?"
Ta share kwallar idonta dai-dai lokacin da shi da budurwar suka zauna akan bencin nata, ta ce
"Lah Uncle ba kuka nake yi ba".
Ya ce "Mai yasa 'yan gidanku ba su zo ba?"
Ta ce "Ba su san ana yi ba".
Ya ce "To ki fada min adires na garinku ni da kaina zan je na taho da su a bisiting na gaba.
Yanzu dai ga kannena Ilham da Sagir sun zo miki bisiting, are you o.k?"
Farin cikinta ya gaza boyuwa, bakinta ya gaza rufo don dadi. Ba tasan mai zata ce da Uncle
Junaid ba, sai ta kama hannun Ilham tana murmushi, ta ce, "Na gode Ilham".
Ilham ta ce "Ba komi Maryam, yadda Yaya Junaid ke ba ni labarinki sai na dauka zan ga wata
babbar budurwa, ashe kamar Sagir ce Maryama?"
Ya mike yana cewa "Ki tabbata ta ci abincin, kuma ba ta yi kewar kowa nata ba, I know you
Ilham. Zan dawo nan da awa daya mu tafi".
Ta ce "To Yaya Junaidu". Tana murmushi.
Ilham ta ce "Amma ko kannenki ba su zo ba Maryam?"
Ta ce "Ba ni da kanne, ni ce auta a wurin Innata".
Suka ci gaba da hira, Ilham na kokarin cika umarnin Yayanta na ganin cewa, ba ta bar Maryam
da kewa ba kamar yadda dan uwanta ya umarce ta. Ta zuba mata abinci mai rai da motsi cikin
filet da kirjin kaza ta mika mata tana cewa "Ci maza kamin Yaya Junaidu ya dawo ya tuhume ni
da barinki da yunwa". Dariya ta yi, da ta lotsa kumatunta, tana tambayar kanta ko wane matsayi Uncle Junaid ya ba ta
haka a wurin 'yan uwansa? Girmansa da kimarsa ya karu a zuciyarta. Tana ganin bayan Baba
da Inna da Yaya Habibu ba ta da kamar Uncle Junaidu.
Ya dawo da wata leda mai dauke da ruwan (Faro) roba uku masu sanyi ya mikawa Ilham. Suka
sha dukkansu sannan suka yi haramar tafiya, Mairo ta ji babu dadi.
Cikin 'yan awoyin da ta yi da Ilham sun saba sosai. Ta bude baki cikin al'ajabi tana kallon Uncle
da ya ce duka wannan kayan nata ne. Abinci kuma daga mahaifiyarsu ne sai ta rasa irin godiyar
da zata yi wa Uncle din nata.
Bayan tafiyarsu ta kinkimi kayanta daya bayan daya ta nufi hostel. Cikin ledojin ba komi ba ne
sai biskit na kwali kala-kala da crackers na shan shayi irin wadanda ta ke ganin su Kausar na ci,
dayar kuwa alawoyi ne, cakulet kala-kala masu dan karen tsada da katon na irin taliyar da ta ga
dalibai suna jikawa (indomie), sai katon na lemon gwangwani (Rani). Baki ta bude cikin matsanancin firgici, ba ta taba tsammanin wai ita Mairo zata taba cin irin
wadannan abincin ba a rayuwarta. Cikin kulolin kuwa bayan abinci akwai soyayyun kaji
wadanda suka soyu rakau yadda za su jima ba su lalace ba, cin-cin mai nama (meat pie), cake
da sandwitch masu yawa sosai. Kenan godiya ga Uncle Junaid wadda ba ta karewa. Mutanenta suka shigo, wani abin mamaki kulolinsu duk iri daya ne da nata, sai kala da ta
banbanta. Suka yi kasake! Cikin mamaki ganin irin garar da ke gaban Mairo wadda ko a
mafarkinsu ba su zata ba. Abin da suka dauka shi ne, ramar da ta ke kwadawa mai tsamin tsiya
da kanzo su za a karo mata. To sai ga sabani ga tunaninsu, ina ruwan Allah Mai azurta bawa. Mairo dai jeren kayanta ta ke a loka, ba ta kula su ba. Nabilah ta kasa shiru ta ce, "Kausar yau
billager ta shigo gari".
Kausar ta ce "Ke ina jin 'charity' ne daga (MSS), ba ki san ta shiga MSS ba? Kungiyar 'yan a
bamu saboda Allah?"
Ita yaran sai suka koma ba ta dariya sabida yadda suka sa mata ido babu gaira babu dalili, ko
mai ya yi masu zafi da ita? Allahu A'alam.
Bayan bisiting da sati biyu, rannan Mairo ta fito domin yin fitsari da daddare a lokacin Kausar
ma ta fito ta tsugunna a bakin rariyar hostel tana goge bakinta domin ta kwanta. Mairo na daga
bandaki ta hangi wani mulmulallen abu mai sheki da tsayi na sanda ya nufi Kausar. Ta ware
idanunta gabadaya sai ta gane katon maciji ne wanda ake rade-radin akwai a makarantar. Ta yar da butarta ta sheko da gudu dai-dai sanda macijin ya fasa kai, ta angije Kausar tun