Showing 39001 words to 42000 words out of 79746 words
Chapter 14 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf
daga cikin manemanki ki aura
mana?"
Ladidi ta ce "Na tuba, na bi Allah na bi ki. Wallahi daga yau bazan sake ba..."
"……Ki ma sake din mana don ubanki".
Suka juya a razane, Habiba ce tsaye a kansu, ashe ta dade da shigowa ba su ankara da ita ba.
Ta kwance dankwalinta ta yi damara, ta yo kan ladidi ta hau ruwan cikinta ta soma kirba mata
naushi tana ihu tana "Na tuba Mama, wallahi bazan sake ba".
Wannan bai ishi Habiba ba, sauka ta yi ta nufi kicin ta dauko tabarya ta yo kanta tana fadin,
"Gara na kashe ki kafin kanjamau ta kashe ki, kibar mana abin fadi cikin zuri'armu".
Ganin ta yo kanta da tabaryar Ladidi ta yo waje da gudu don tserar da rayuwarta, wannan ya
janyo hankalin kafatanin jama'ar gidan yara da manya, suka fito tsakar gida har Dina da Habibu
da Baffa. Ganin Ladidin zata yi waje da rigar bacci, kafarta ko takalmi babu, kanta ko dankwali,
Habibu ma ya rufa da gudu ya kamota tana ta kuka, tana "Na tuba wallahi ba zan sake
ba…….."
Habiba ta fito tana sharar hawaye, ta ce, "Ni fa ince, wannan aman da wannan kwanciyar nakin
na Ladidi, ba na lafiya ba ne, na zama shashashar Uwa, yanzu Mairo da kunnawana ba su jiye
min ba, haka zaki biye mata ku binne mu?"
Mairo na kukan tausayin Ladidi ba ta ce komai ba.
Baffa ya ce "Mai Ladidin ta yi ne?" Ya tambaya yana kallon Mairo.
Ta yi tsuru-tsuru ba ta yi magana ba. Ya sake tambayarta, ta ki magana. Habiba cikin kuka ta ce
"Ciki suka je aka cire mata, wai wannan shi ne na biyu, na ji su tana yi wa Mairon godiyar ta rufa
mata asiri".
Baffa ya ce "Mairon? Da ita aka je aka cire cikin?"
Mairo ta girgiza kai cikin kuka ta ce "Wallahi ba ni na rakata ba, ita kadai ta je abunta. Ni asibiti
na kaita ta ga likita".
Dariya ta kama Habibu, wai asibiti ta kaita, sai ka ce wata uwarta? Habibu ya ce "Ke ma sai mu
je a duba ki, don abokin barawo ai barowo ne".
Ya hankada Ladidi da ke hannunsa ya tankado keyar Mairon, ya ce, "Oya! Lets go, har gwajin
kanjamau duk za a yi muku tunda kun zama karuwai".
Mairo ta soma rantsuwar, wallahi babu ruwanta, ba ta da saurayi, ba ta taba yin zance da namiji
ba. Babu wanda ba ta baiwa dariya a wajen ba. Baffa ya kamo hannunta ya ce
"Share hawayenki Mairo. Babu inda za ki, kanwarshi ce karuwa ba ke ba".
8/1/21, 9:30 PM - Kawata: Mairo
Little Mairo tana ta murnar ganin mamarta da ta kwana biyu ba ta gani ba. Shi kanshi Yaya
Habibun idan ka lura zaka ga annurin fuskarshi ya karu sosai. Oh! Ashe haka auren so yake?
Mairo ta ce a zuciyarta. Kai ka ce sun shekara ba su ga juna ba.
A otel din da Amiru ya sauka (Best Western) suka ajiye shi, da alkawarin sai ya shigo da
daddare yin dinner. Kuma Mairo yake so ta yi mishi girki. Dina ta yi murmushi ta ce "Ban fa
gane ba, kada ka sa Harrit ta bindige min kanwa".
Ya yi murmushi ya ce, "Allah babu wasa cikin maganata Aunty Dina, don ni yanzu kin zama
Auntyna, alfarma nake nema ku yi min ke da mijinki, kokon bara na yana gidanku, duk da mijinki
is not hundred percently agreed (bai yarda gabadaya ba) sabida wasu hujjojinshi marasa
makama. Nasan ke za ki dube ni da idon rahma. Zan ba ku mamaki, zan nemi soyayyar Mairo
ba campaign nake so ku yi min ba".
Har suka iso gida, Dina na jinjina kalaman Amiru a zuciyarta. Ta sanshi, ta san halinshi kamar
yadda tasan mijinta. Karya ko joking ba sa cikin halayyarsa, idan ya ce yes, to da gaske yana
nufin yes din babu gudu babu ja da baya. Babu kuma abin da zai sa shi ya janye abin da ya sa
gaba. Wani irin mutum ne mai nasara akan duk abin da ya sa gaba, wato dai irin mutanen nan ne
masu ra'ayin kansu, ba masu fadin karya don wani ya ji dadi ba. Hakanan ba sa iya boye abin
da ke zuciyarsu.
Ta dade tana addu'ar zuwan ranar da Allah zai nuna mata mijin Mairo, ta sha kissima yaya mijin
Mairo zai kasance? Domin ita din 'yar baiwa ce kamar Habibu. To amma ba ta taba tunanin
Amiru ne zai ce yana so ba. Kololuwar ilmi, nasaba, arziki, kyau, nagarta duk shine. Bankin
duniya yana hannunsu, kudin Najeriya gaba daya yana hannun ubansa, sai ya rattaba hannu a
kansu za a yi amfani da su, ko 'yar shugaban kasa yake so zai aura. Duk kalar macen da yake
so da gudu za a ba shi, amma ya ce; MAIRO, a ganinta wannan abin alfahari ne a gare su, ita
da Habibu domin Amiru ba zai yi karya ba, ba zai yaudare su ba. Ba zai fadi abinda ba haka
yake a zuciyar shi ba. To mai yasa Habib cogewa?
Ta san abin da yake gudu ba zai wuce Harrit da 'yammatan Amirun ba, domin iyayenshi
mutanen kwarai ne, 'yan jiya, bana yau ba, kuma Habibu kamar Da ne a wajen Abudrrahman
Gaya. Da irin wanda ya tsugunna ya haifa. Shi ya dau nauyin karatunshi tun daga master har
PhD da sauran kwasa-kwasan da ya halarta. Yasan kuma amintarsu da Amiru ba tun yau ba,
don haka ta ke ganin ta wannan fannin ba za a samu matsala ba.
Idan ma akwai matsalar ta fannin Harrit ai shi Amirun ba yaro ba ne, yasan yadda zai tsarawa
kanshi rayuwa.
Suna kicin ita da Mairo lokacin da Amiru ya iso. Dina ba ta ce mata komai ba, sai ta yi ma
kamar ba tasan zancen ba. Shi da Raymond ne sakatarenshi, suna hira kan harkokinsu shi da
Habibu, amma duk hirar ta gundire shi, sai baza ido yake don ganin ta inda Mairo zata bullo,
amma shiru. Habibun na hankalce da shi, yau surukuta sosai yake nunawa, duk sai dariya ta
kama Habibu, sabida wani ‘respect’ na musamman da ya lura Amirun na bashi. Ya yi fes cikin
ta-zarce, na farar shadda excellencior duk da kullum cikin kwalisarshi ya ke amma Habibun bai
taba ganin ya yi mishi kyau irin yau ba, to ina ga 'yammata?
Wadanda ke jin kamar su ja shi ta karfi, to amma fa banda kanwar Habibu 'Mairo', wadda kallon
fuskarshi ma ba zata iya yi ba idan ba dole ba.
Hakurinshi ya kare, tare da duban agogon hannunshi. Shi dai kawai so yake ya ganta, ko
hankalinshi ya kwanta, amma Habibu ya share shi kamar bai san halin da yake ciki ba.
Cikin ikon Allah sai ga Dina ta fito daga kicin ya ce "Wai Dina ina kanwarkin nan ne?"
Ta murmusa ta ce "Tana aiki ne".
Tsam! Ya mike, kanshi tsaye ya doshi kicin din. Ta juya baya tana yayyanka fruits cikin wata
katuwar silba, daga bakin kofa ya tsaya ya tokare hannunshi a kofar. Ya shagala sosai a cikin
kallonta har ya manta abin da yake yi, bai san kuma iyakacin mintunan da ya bata a tsayen ba.
Dina ta dawo ta ce "Ba ni hanya malam".
Ya matsa, ta wuce ciki tana murmushi kasa-kasa, a sannan ne ma Mairon tasan da mutum a
tsaye. Ta cira kai ta dube shi, shi ma duban nata yake cikin lumsassun idanunsa. Bai san me
zai ce mata ba ta fahimci masifar sonta da Allah Ya dora masa. Yana daga cikin mutanen da
harshensu bai iya bayyana abin da ke karkashin zuciyarsu. Sai dai action da emotion dinsu ya
nuna. Da Mairon zata daure ta dube shi, da ta gane yadda ya yi laga-laga cikin SOYAYYAH. To
amma ta ki, kallo daya ta yi mishi ta dauke kanta, bata sake marmarin maimaitawa ba.
Ya karaso ya karbi wukar da ke hannunta ya ci gaba da yanka mata gwanda (paw-paw). Dina ta
dau abinda zata dauka ta fita. Ta mika hannuwa cikin sink ta wanke hannu ta juya zata fita.
Ya dago a galabaice, muryarshi har ba ta fita sosai, ya ce "Idan kika fita zan yi miki Allah Ya isa
ne…, tunda Manzo ma ya ce, "BAKONKA, ANNABINKA..." Idan kika fita kin wulakanta ni, shin
ma mene ne gare ni da kike guduna? Na yi miki kama da dodon da zai cinye ki ne?"
Ta ja turus, ta tsaya, ita ba ta fita ba, ita ba ta juyo ba. Ya ajiye gwandar ya sha gabanta sosai
har tana jin hucin numfashinsa. Wanda ke sauka da sauri-da-sauri. Kwayar idanun sun rikide,
sun haukace da soyayya. Ban da alkawarin da ya daukarwa Habibu, da wallahi rungumeta zai
yi, sannan ne yake jin zai iya gaya mata ko mene ne ke cin ransa, zuciyarsa da gangar jikinsa a
kanta. Amma a haka ba zai iya bata bakinsa ba, ba zai iya ce mata komi ba. Da kyar ya daure
ya langabar da kai, ya ce "Yi min magana mana, don Allah, Mairo? Mairo ko ba kya SO na?"
Nan ma shiru, kai ka ce da gunki yake magana. Don ita jin abin ta yi banbarakwai, wai namiji da
suna Hajara, tunda dai babu wanda ya taba tararta da wannan kalmar, wai….. Ya katse
tunaninta da cewa, "Mairo Allah Ya jarrabce ni da sonki, tun daga lokacin da Allah Ya dora
idanuna a kanki. Duk wani saukar numfashina a yanzu da sunanki yake fita, duk wani tunanina
a yanzu na yadda zan mallake ki ne a matsayin matata, uwar 'ya'yana.
Sunana Ameeru Abdurrahman Gaya, ni kadai ne da namiji a wurin iyayena, ina da kanne mata
goma sha biyu. Na yi dukkan karatuna tare da Habibu. Iyayena ‘yan Gaya ne suna zaune a
Abuja, amma mu 'yan asalin garin Gaya ne da ke cikin jihar Kano, ina aiki a Washington, sai dai
kwanan nan zan bari in koma gida. Ina da mace daya da 'ya'ya zero. Duk wani abu da kike son ji game da ni, ki tambayi Habibu,
zan samu karbuwa Mairo? Mairo ko ba kya so na?"
Ya tsare ta da wani irin kallo daga can karkashin kasan lumsassun idanunsa.
Mairo ta rasa inda zata sa kanta. Ga kunya da ta baibaye ta, ga jin nauyi, don ganinshi ta ke
kamar Yaya Habibu. Idan ta ce ba ta sonshi ta yaudari zuciyarta, haka idan ta ce tana sonshi ta
yi karya. Mutum daya ta ke wa 'SO' na hakika, wato UNCLE JUNAIDU. To amma shi wannan
jinsa ta ke har cikin kasusuwa da bargonta ba zuciya kadai ba, da wani al'amari mai ban
mamaki da ba zata iya fassarawa ba.
Tunaninta shi ne, ba zata iya hada rayuwarta da kowa ba, idan ba Uncle Junaid ba. Ta dauki
al'amarin da ta ke ji akan Amiru da BURGEWA da SHA'AWA, wato yana burge ta, yana bata
sha'awa, yana daukar hankalinta, yana bijiro mata da sha'awar tayi aure. Zata iya aurenshi don
ta mallaki gangar jikinshi, amma ba don so ba. Idan aure ne kadai hanyar da zata samu
mallakar abin da zuciyarta da gangar jikinta ke so daga gare shi, to zata iya aurenshi don ta
samu, amma SO guda daya na UNCLE JUNAIDU ne!
Wata irin kunya ta kamata, da ta yi wannan tunanin, don gani ta ke kamar ya hango abin da ta
ke sakawa da warwarewa cikin zuciyarta. Tana tunanin idan ta yi hakan kuma ai ya zama
yaudara. babbar yaudara kuwa, don haka ta soma tunanin yadda zata yi ta gudu, ba tare da ta
ce da shi komai ba. Yadda Uncle Junaid ya yaudare ta, ta san ciwon hakan, ko ba don komi ba don amintarsu da
Yaya Habibu da mutumcin da ke tsakaninsu kamar yadda Yaya Habibu ya gaya mata, mahaifin
Amiru shi ya dauki nauyin karatunsa daga masters har PhD. Sabida haka ba yadda za a yi ta
yaudari Amiru wata rana ta rabu da shi idan ta samu Uncle Junaidu. Haka nan idan ta ce ta yarda tana sonsa ita ma ta yi sallama da burinta na WATA RANA
zata hadu da Uncle Junaid su yi aure a lokacin da Allah Ya nufa. Gara ta ci gaba da dakon
soyayyarsa, don idan ta yi aure ya tabbata ita da Junaid kenan HAR ABADA!
BURGEWA da SHA'AWA ba tubala ne na kwarai da za a gina aure a kansu ba. Idan aka yi
hakan, ba da jimawa ba ginin zai rushe tamkar ba a taba ginawa ba.
Don haka gara ta hakura da rudin zuciya don shaidaniya ce, ta fuskanci gaskiya. Ta yi aure don
Allah, ba don kyale-kyalen Amiru da rayuwa bakidaya ba. Ta ci gaba da jiran Uncle ya gaya
mata da bakinsa cewa ba sonta yake ba, sannan ne zata hakura, ta yi addu'ar Allah Ya kawo
mata mijin da zata so da gaskiya, ta kaunata saboda Allah, kamar yadda ta ke yi wa Junaidu.
Ta daga kai a hankali ta dubi Amiru, wanda har zuwa wannan lokacin bai dauke kyawawan
idanunshi daga kanta ba, binta yake da ido, da zuciya. Idan Mairo ta ce ba ta sonshi, bai san
inda zai sa kanshi ba.
Ta ce (cikin kaskantacciyar murya) "Don Allah ka ba ni hanya in wuce".
Ya ce "Ai ba ki ba ni amsa ba, ko na yi miki tsufa ne Mairo?"
"Ni ban ce ba".
"To mai kika ce?"
"Cewa na yi ni ba sonka nake yi ba!".
Wannan ita ce kalma mafi muni da wani ya taba gaya mishi a rayuwarshi. Ji ya yi kamar ta soka
mishi mashi a kahon zucci. Hajijiya ta kamashi. Ta wani fannin kuma sai ta BURGE shi, sabida
kai tsaye ta gaya mishi kalmar da babu wata diya mace da ta taba gaya mishi. Wannan ya
tabbatar mishi da cewa, ita ta daban ce. Sai dai yadda ta yi maganar da yanayinta kadai zai nuna maka tsabar kuruciyarta karara. Don
haka bai yi fushi ba, ance wai, 'Mai nema yana tare da samu'. Ya lumshe ido ya bude su dukka
a kanta "Amma mai yasa Mairo?
Komi yana da dalili, kamar ni, na so ki ne sabida wasu abubuwa guda uku, wadanda bazan iya
gaya miki ba. To ke mene ne naki dalilin?"
Ta so ta ce da shi "Sabida ina da wanda nake so". Sai ta tuno alkawarin da ta daukarwa Yaya
Habibu, na barin soyayyar Junaid da mantawa da al'amarinshi. Don haka sai ta ce.
"Sabida wasu dalilan nima, da bazan iya gaya maka ba!!".
Sun dauki mintina uku shiru, babu wanda ya sake cewa da dan uwansa uffan. Kamin ya dauke
ido daga kanta, ya ce.
"Ni kuma na yarda ki aure ni ko da ba kya sona…!!!".
Ta ce "Ba zan yi hakan ba, idan na yi hakan na yaudare ka, na ci amanar kaunar da nake yi wa
Uncle Junaidu……....!!!"
Ta yi saurin kai hannu ta toshe bakinta da karfi, ba ta san yaushe furucin ya subuto daga
zuciyarta ba, ga shi an ce 'magana zarar bunu' ta riga ta fita.
Sai ya kauce da zafin nama ya ba ta hanya sabida wani masifaffen KISHI da ya taho ya tokare
masa a kirji. Ai tana samun hanya ta arce. Da kyar ya iya dago matattun kafafunsa bayan
mintina goma sha biyar, ya nufo falon inda ya tarar da Raymond da Habibu akan tebur suna cin
abinci, Dina na tsakiyar falon tana canza channel a talabijin. Abincin da bai ci ba ke nan, ya
zauna cikin doguwar kujera fuskarshi babu walwala, ya ce.
"Raymond idan ka gama sai mu wuce".
Habibu ya juyo ya dube shi yana nazarinsa, ya ce "Ba zaka ci abincin ba? Mairo ce ta girka
maka..........."
Ya dago idanuwanshi da suka canza launi luuuu! Yana kallon Habibu a kankance, ya ce "Ba zan
iya ba!!".
Dina ta ce "Haba don Allah Amiru? Ba ka ga wahalar da ta sha wajen girkin nan ba? Idan ba ka
ci ba bazata ji dadi ba".
Bai san lokacin da ya ce "Ba don ni ta girka ba, don Yayanta ne".
Daga haka ya mike ba tare da ya iya hada ido da kowa ba. Ya sake ce da Raymond, "If you
finish, meet me outside….".
Shima Habibu sai ya ajiye cokalin don jikinshi ya yi sanyi, don bai taba ganin Amirun cikin
kwatankwacin irin wannan halin ba.
Don haka ya mike ya bi shi wajen ya dafa kafadunshi da ya juya baya. Ya ce.
"Mai ya faru ne?"
Ya kalle shi kawai bai amsa ba, tambayar duniyar nan Habibu ya yi, amma ya ce "Babu komai".
Don ba burinshi ba ne a takurawa Mairo ta aure shi. So na hakika ya ke nema, ba da tallafin
wani ba.
Mairo da ta koma daki kwanciya ta yi, rigingine cikin nadama. Kai tsaye ka dubi kwayar idon
mutum mai kima kamar Amiru da ya ce yana sonka, ka ce ba ka son shi, ya zama wulakanci da
cin fuska. To amma ita a ganinta dai-dai ta yi, don ba ta iya karya da yaudara ba. Amma dai duk
da haka ta san ba ta kyauta ba, sai dai a ganinta gara hakan, da ta yi irin auren da zuciyarta ta
raya mata.
Dina ta yi sallama ta shigo, dauke da faranti tana cewa "Kin yi barci ne?"
Ta girgiza mata kai, alamar "A'ah".
Ta ce "To tashi, abincin da kike gudu ne na biyoki da shi".
Ta tashi ta zauna sosai, ta karbi farantin ta soma ci, Dinan na kallonta. Can kuma ta ce "Mairo
mai kika ce da Amiru ne? Ya shigo cikin walwalarsa, ya fita cikin yanayin da bamu taba ganinsa
a ciki ba. Ina laifin wanda ke son ka?"
Ta cira kai ta dube ta, sai kuma ta sunkuyar. Can kuma ta dago ta dube ta, ta ce "Yana magana
ne akan wai yana sona, ni kuma na gaya mishi cewa, bana son shi!"
Dina ta yi murmushi. Daga jin kalaman Mairo,