Showing 30001 words to 33000 words out of 79746 words
Chapter 11 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf
wai fushi ta
ke da Momi da Daddy. Ranar lahadi aka kai amarya gidanta da ke Nassarawa GRA. Tana kuka,
Mairo na yi suka rabu, don wata irin kauna ce shakikiya Allah Ya hada a tsakaninsu.
Mairo ta dawo gida, ta kwanta a yagulalliyar katifarsu. Ta runtse idonta tana tunanin al'amuran
rayuwa. Yau dai ga Nabilah ta yi aure ta barta, ita kuma ko sai yaushe ne Allah Zai kawo mata
nata Mr. Right din? Tunda Uncle ba ya sonta? A zahiri aure ta ke so, ba kuma da kowa ba da
UNCLE JUNAIDU. Karatun ya fice mata a rai, tunda babu Junaidu mai karfafawa. Tana daga
cikin halittattun mata masu tsananin bukatar da namiji, amma ba da kowa ba, da wanda ruhi,
zuciya da gangar jikin su ke so. Haka kawai tunanin unguwar GALADANCHI ta fado mata a rai.
Idan har ba kuskure ta yi a tunaninta ba, Uncle ya taba gaya mata shi dan unguwar Galadanchi
ne, da ke cikin birnin Kano. To idan ta je Galadanchi ta ce tana neman waye? Alhalin ma an ce
Uncle Junaidu yana Russia? Zata je ta nemi gidan su Uncle, iyayenshi da 'yan uwanshi
musamman Ilham, wai an ce Gaida mai gaisheka...!'
Zumbur ta mike, ta jona ruwa a heater tana jiran ya yi dumi ta yi wanka, sabida sanyin da ake
cikin watan Junairu.
Daga can gefe Ladidi ta tashi tana yatsina fuska, ba a jima ba kuma ta soma kelaya amai a
tsakar dakin. Mairo na yi mata sannu amma ko kallonta ba ta yi ba. Ta gama aman ko kurkure
baki babu ta koma ta kwanta. Mairo ta dauko tsintsiya da abin kwashe shara ta soma gyara
wajen don tasan idan ta Ladidi ne, to a bar wajen a haka,. Ta dauko tsumma da omo klin ta
goge dakin tas! Ta kunna turaren wuta na tsinke.
Idan ba ta manta ba wannan aman Ladidi na shidda ke nan cikin kwana uku, amma ko tunanin
ta je asibiti ba ta yi. Ta matsa jikinta a hankali, abinki da dan uwa, ta ce, "Ladidi ki shirya na
rakaki asibiti mana, ko magani ne a baki, wannan aman ya tsaya?"
Ta yi shiru ba ta ce uffan ba, kuma ba ta kalle ta ba, can kuma ko mai ta tuna? Ta ce "Mu je".
A gurguje ta yi wankan ta fito, Ladidi ko wanka babu suka fito. Habiba na tsakar gida ta daga
ido ta dube su. Wani irin kishi da bakin-ciki ya tushe mata a kahon zucci, ganin irin kyau da
kwarjini na musamman a fuskar Mairo tamkar diyar larabawan Turkiya. Ladidi kuwa kamar a
rufe ido don muni da rashin tsafta. Ta ce "Ke Ladidi, ina zaki je da wannan mai kama da kabewar?"
Ta kyabe baki kamar yadda ya ke a al'adarta, ta ce "Asibiti wai zata kai ni".
"Ciwon me kike da za a kai ki asibiti?"
Ta sake kyabe bakin ta ce "Wai don ina amai, ko ta gaji da kwashewa ne? Oho!".
Ta gallowa Mairo harara ta ce "Kin ga ni bana son kinbibi da son nuna iyawa, waye ba ya amai
idan ya ci abin da ranshi bai so ba? Wuce da Allah ki ba ni waje, ke kuma ungo goro ki ci tashin
zuciyar zai lafa".
Mairo ta koma daki tana jinjina hali irin na Habiba. Karfe biyar na yamma ta ji karar motar Baffa
tabbacin ya dawo. Sai da ta ba shi lokaci ya kimtsa sannan ta je dakinsa, ta same shi yana cin
abinci ga Hajara da autarta Umma a gefe, ban da harararta ba abin da Hajara ke yi, amma ita
ba ta kula ba, tsugunnawa ta yi har kasa ta gaida Baffan, ya amsa cikin walwala, ya ce "Yaya
dai Mairo, babu wata matsala ince ko?"
Kanta a kasa ta ce "Babu Baffa, ina so in je Galadanchi ne".
Bai tambayi wajen wanda zata ba, ya dauko naira dari biyu a aljihunsa ya mika mata, ya ce "Ga
shi ayi kudin mota, amma kada ki bari dare ya riske ki waje".
Ta ce "Insha Allahu Baffa".
Mairo tana tafe tana tunanin rigima irin tata, ya za a yi ta nemi gidansu Uncle alhalin ba tasan
komi a kanshi ba? Ace ma ta sani, me zata je ta ce, kuma me zata je ta yi? Wata zuciyar ta ce
"Gaida mahaifiyarsa kamar yadda yake gaida naki". Wannan tunani ne mai kyau.
Ta fito daga Yakasai zuwa Bakin Rimi, ta tari tasi ta ce "Galadanchi". Ya bude mata kofa ta
shiga.
Ba a fi minti goma ba ya sauke ta a unguwar Galadanchi. Ta fito ta ba shi dari biyun Baffa ya ba
ta canji, ta gangara dai-dai makarantar gidan Galadima ta tsaya nan tana rarraba ido, ta rasa
wanda zata tambaya.
Daga can gefe wajen masallaci dandazon matasa ne a zaune suna haramar shiga sallar
magriba, ba zata iya shiga cikin wadannan samarin ba don haka ta ci gaba da tsayuwa cikin
rashin sanin abin yi. Tana nan tsaye wani saurayi ya zo gittawa ta gabanta ta yi mishi sallama,
ya juyo ya amsa, ta ce "Don Allah Yayana tambaya nake". Ya ce "Allah Ya sa na sani kanwata".
Ta ce "Gidan su Junaid nake tambaya".
Ya ce "Junaid? Ya ya sunan maigidan?"
"Gaskiya ban sani ba".
"Babba ne ko yaro ne?"
"Babba ne, don zai girme ka".
Ya yi dan tunani "Kwatanta min shi".
Nan ta shiga kwatanta mishi, ya ce "Ke ko gidan Justice Atiku kike tambaya?"
Kwarai ta taba jin sunan Chief Justice Atiku Galadanchi a bakin Kausar mai rasuwa,
(Alkalin-alkalai) na Jihar Kano. Ta ce "Ina jin nan ne".
Ya ce "Mu je na nuna miki".
Abinka da karamar unguwa, kowa yasan kowa. Ya yi mata nuni da gida ginin manyan 'yan
bokon da, mai malalen suminti, dakali biyu sun sa gidan a tsakiya, ko ina a share tas ko tsinke
babu. Ta yi wa saurayin godiya ta sa kai zauren gidan.
Ashe yadda wajen yake ba haka cikin gidan yake ba, cikin gidan gini ne sosai na zamani, mai
ban al'ajabi, sabida yadda aka kwalmada karfe da rodi aka yi irin wannan ginin ba kasafai ake
samun irinshi cikin Nijeriya ba. Ko'ina gilashi sai daukar ido yake hatta kofar shiga falon gidan ta
gilashi ce. Ta tsaya a kofar falon tana sallama. Wata dattijuwa da alama mai aiki ce, ta fito tana mata kallon rashin sani. Mairo ta tsugunna ta
gaishe ta, ta amsa, ta ce "Yammata wa kike nema?"
Ta ce "Babar su Ilham".
Ta bude mata kofar falon, ta ce "Zauna a nan, Hajiya tana zuwa yanzu".
Ba ta zauna a kujerar ba, a kan wani tattausan kilishi da ke tsakiyar dakin ta zauna. Talabijin na
ta aiki cikin tasoshin tauraron dan Adam. In banda kamshin turaren wuta na (Bakhour) ba abin
da ke tashi a falon, gauraye da ni'imtaccen sanyin na'urar sanyaya daki duk da sanyin da ake
fama da shi kuwa. Ta daga kai a hankali zuwa gabas maso kudu na dakin. Tangamemen hoton Uncle Junaidu ya
yi mata sallama, yana murmushi. Wata matsananciyar faduwar gaba ta same ta, ta kura mishi
ido ba ta ko kyaftawa. Dai-dai lokacin da ta ji muryar Hajiyar tana yi mata sallama.
Ta daga kai ta kai dubanta ga mahaifiyar Uncle Junaidu. Nan ta ga inda Junaid ya debo kyau,
tsurarsa. Mace ce ma'abociyar zati da kamala gami da gogayya cikin zuzzurfan ilmin boko. A
idanunta farin gilashi ne (medicated). A kiyasce zata yi shekaru hamsin. Amma a idaniyarka ba
zata fi shekaru talatin da biyar ba. Ta zauna a kujera fuska cike da annuri, Mairo ta duka tana gayas da ita. Ta amsa cikin
murmushi ta ce, "Yammata daga ina? Ban gane ki ba".
Itama Mairon sai ta rasa abin da zata ce. Wata zuciyar ta ce "Akul! Kika ce danta kika zo nema,
wannan ba mutumcin diya mace ba ne. Kin zo ki gaishe ta ne sabida Allah, da kuma soyayyar
danta da Allah Ya dasa miki. Amma ba don kamun kafar neman soyayyar ba".
Hajiyar ta sa mata ido tana nazarinta, ta rasa inda ta san fuskar. Haka kawai Allah Ya sanya
mata kaunar yarinyar a zuciyarta. Duk inda ake neman kyau da nutsuwa, haiba da kamala to
wannan yarinyar ta zarce, ga shi da alamunta ilmi ya ratsata ta ko ina. Amma shirun da ta yi
mata ya sanya ta diga mata ayar tambaya (kuestion mark?). Ta sake maimaita mata tambayarta
"Yammata daga ina kike ban gane ki ba?"
A sannan ne Mairo ta cira kai, wasu irin fararen idanu, gauraye da wani irin blue-blue suka
haske Hajiyar, ta yi wa Allah sarkin halitta tazbihi, ta tsarkake Shi, ta tsarkake iko da iyawarSa.
Cikin sassanyan sautinta ta ce "Na zo wurin Ilham ne".
Ta ce "Ke kawarta ce halan? Don na ga kamar nasan fuskarki".
Ta ce "Eh". A takaice.
Ta ce "To amma kuwa na yi mamaki da ba ta kawo miki katin bikinta ba, an yi bikinta watanni
uku da suka wuce. Suna zaune a Wales din kasar Ingila inda mijinta ke karatu".
Mairo ta ce "Allah Sarki, Allah Ya yi ba zamu hadu ba".
Ta sake juyawa ta dubi hoton Uncle. Ta sake juyowa ta dubi mahaifiyarsa, wata irin soyayya da
kauna na sake mamayar zuciyarta. Ba ta ki ta zauna a nan tare da Hajiyar Junaidu ba, tana yi
mata bauta, har karshen rayuwarta koda Junaid ba zai aure ta ba. Wannan ita ce kauna ta
hakika, wadda ba a samunta a wannan zamanin. Da gaske Junaid ya yi mata nisan da ba tasan
ranar da zata kamo shi ba.
Tsigar jikinta ya tashi, ganinta ya dushe, wani duhu ya gilma mata ta daina ganin abin da ke
gabanta na wucin gadi.
Hajiyar ba ta lura ba, don a lokacin hankalinta ya tafi ga amsa kiran wayar da ya shigo mata
yanzu-yanzu. Ta mike tana gyara lullubinta ayayinda ta fuskanci da Uncle Hajiyar ke magana.
Hajiyar ta yi mata alama da hannu ta jirayeta. Sai da ta gama wayar ta ajiyeta akan centre table,
ta ce da Mairo "dan jiraye ni ina zuwa". Ta koma matattakalar da ta fito, jim kadan ta dawo da leda mai tambarin shagon country mall ta
mika mata. Mairo ta girgiza kai alamar ba zata karba ba, don tasan ko ta karba rabon su Ladidi
ne, dama ace za su gode ne, to a'a, zagi da bakar magana ne zai biyo baya.
Hajiyar ta ce "Ni ba babarki ba ce? Ba zan yi miki ihsani ki karba ba?"
Ta sake kai dubanta ga Uncle Junaid da ke cikin hoto yana murmushi. Sai ta ga kamar ya
turbune mata fuska, cikin rashin jin dadi. Ta maido ga dubanta ga Hajiyar, kallonta ta ke
tsakaninta da Allah da matsananciyar kauna cikin kwayar idanunta.
Ji ta yi kamar ta kwantar da kai a kafadunta ta yi kukan da ke cin ranta, ta gaya mata
matsananciyar kaunar danta da Allah Ya dora mata. Ta ji dumin da Junaid ya ji, a jikin wannan
nagartacciyar UWA, ganin hawaye na neman tona mata asiri ta yi hamzarin karba ta ce "Na
gode".
Har ta kai bakin kofa zata fita, Hajiyar ta kirata jikinta a sanyaye, don daga dukkan alamu akwai
abin da ke damun wannan yarinya, ta ce "Har za ki tafi, ba ki gaya min sunanki ba, idan Ilham
din ta yi waya in gaya mata".
Mairo ta ce
"Ki ce mata Maryam ce".
"Maryam-Maryam!" Tana ji a bakin su Ilham, amma a wannan karon Allah bai bata ikon ganewa
ba.
Har yarinyar ta fita, ba ta motsa daga inda ta ke ba, ta dade tana tunanin inda tasan yarinyar.
Mai yasa ba ta tambaye ta daga inda ta ke ba? To akan me zata tambaye ta? Don kwaita zo
wajen Ilham? Amsar shi ne, don zuciyarta tana sonta. Ta koma falon ta zauna cike da tunani.
Sai ana kiran isha'i ta iso gida, Baffa na alwalar sallah a nan kofar gida, ta tube takalminta
sannan ta wuce shi, zuciyarta cike da jin haushin dadewar da ta yi. Ya ce "Ban ce kada ki kai
dare ba Mairo?"
Cikin matsanancin ladabi ta rausayar da kai tace "Ka yi hakuri Baffa, mota ce ban samu da wuri
ba".
Ya ce "Ni dai duk inda za a je aje ido na ganin ido, amma bana son ayi dare. Idan kin shiga ki
turo min Lawan".
Ta ce "To".
Habiba na kwasar tuwon dare sanda ta shigo, ta dago kai ta dube ta a ranta ta ce, "Kai wannan
yarinya da kashin arziki ta ke, kullum ta fita ba ta dawowa haka nan, sai bakin jini har yau babu
wanda ya taba sallama da ita, duk kyawun nan nata. Ladidi kuwa kullum idan mutum biyu ba su
yi sallama da ita ba, hudu za su yi".
Ta dubi Lawan wanda ke bin ledar hannunta da kallo, ta ce "Ka je Baffa na kira".
Ya ce "In an ki fa?"
Ba ta yi magana ba ta wuce wajen Habiba ta durkusa ta ce "Mama Na dawo, sannunku da aiki".
Lawan ya ce "Wani feleke wai 'Baffa', mu 'Baba' mu ke cewa Babanmu, ba wani Baffa ba. Wai
mama yarinyar nan ta fara bin maza ne ta ke shigowa gidan nan da manyan ledoji?"
Habiba ta ce "Idan ta bi sun ina ruwanka, ko mace ba don namiji aka halicceta ba? Me muka
samu ne Mairo? Miko nan in gani".
Ta mika mata ledar ta tusa karkashin kujerar da ta ke zaune kada Hajara ta fito ta gani, ta ce sai
an raba da ita.
Ta dauki tuwon da ta saka mata a wani kwano duk lamba, ta zuba miyar karkashi akai ta mika
mata. Ta karba ta wuce daki cike da takaici.
Ashe wani takaicin ke jiranta. Tana sanya kai dakin wani mugun karni ya dake ta. Ladidi ta
kelaya amai tun daga bakin kofa har bakin katifarsu. Tana kwance a katifa tana barci kamar
mushe ba abin da ya dame ta. Ta fita ta dauko tsintsiya da abin kwashewa ta soma aikin aman
kamar zuciyarta ta yo waje don bakin ciki. Tuwon da ba ta iya ci ba ke nan sabida karnin da
dakin ke yi, haka ta kwana da yunwa.
Washegari Ladidi da kanta abin duniya ya ishe ta, ta rarrafa katifar Mairo ta tashe ta, misalin
karfe bakwai na safe. Mairo ta bude ido tana kallonta, yawu ya ciko mata baki ta juya bayan
kofa ta tsartar ta ce
"Zo ki raka ni asibitin don Allah, na kasa gane abin da ke damuna, amma da gaske ba ni da
lafiya".
Sai Mairon ta ce "Ki fara zuwa ki tambayo mama tukunna, idan ta amince sai na rakaki".
Ta ce "Rabu da ita kawai, zo mu fice tana daki".
Mairo ta ce "A'ah, ba za a yi haka da ni ba".
Ba da son ran Ladidin ba ta fita ta tambayo Habiba za su je asibiti. Habiba ta dubi diyarta ta ce
"Bana so ku dinga jerawa ne kada a ga muninki".
Ladidin ta kyabe baki, ta ce "Lallai ma Mama, ni ce ma mummunar?"
Habiba ta ce "Sai idan ba ku jera da wannan mai kama da aljannun ba".
Ladidi ta ce "Ke wannan ya dama, ni da munin nawa dai ai na fi ta farin jini, kin taba jin ko bera
ya aiko yana sallama da ita?"
Ta ce "Haka kuwa, ku je sai kun dawo".
Suna tafe a gefen hanya har asibitin Murtala, Mairo ta yanko mata kati suka hau layi. Suna nan
zaune har aka kirasu
7/30/21, 10:24 PM - Kawata: 98
Likitan yana rubuce-rubuce a file lokacin da suka shiga, Mairo ta tsaya ta harde hannuwa a kirji
a bakin kofa. Ladidi ta karasa ta zauna a kujerar da marasa lafiya suke zama. Ya gama ya dube
ta ta karkashin gilashinsa ya ce "Me ke damunki?"
Ta ce "Ina fama da haraswa, zazzabi da ciwon kai mai tsanani, ga wani yawu da yake taruwar
min a baki, bana jin dadin bakina".
Likitan ya dau abin awonsu ya sanya a hannunta yana sauraro, sannan ya yi rubutu a wata 'yar
takarda ya ce, su je laboratory su kawo masa result. Suka fita suka tambayi lab aka nuna musu.
Nan aka bai wa Ladidi robar fitsari aka ce ta je toilet ta yi ta kawo. Nan da nan result ya fito suka
koma ofishin likita. Ita dai Mairo tunda ta ga an rubuta positibe hankalinta yai matukar tashi.
Likitan ya dube su bayan ya duba takardar ya ce da Ladidi, "Ina mijinki?" Ladidi ta ce "Ba ni da aure".
Ya kura mata ido na 'yan sakonni ya ce, "Amma you are pragnant,(kinada juna biyu) watanni
biyu cif?"
Ladidi ta fiddo 'yan idanunta gaba daya suka yi kuru-kuru, wannan bai damu likitan ba ya ci
gaba da aikin da ke gabansa bayan ya rubuta mata magani a wata 'yar takarda.
Suka fito jikin Mairo har rawa yake, saboda dimuwa da razana, ita kuwa Ladidi in banda kuka
ba abin da ta ke, wai likitan sharri yai mata, duk girman kan nan ta sauke shi tana rokon Mairo
wai su je wani asibitin a sake dubawa.
Mairo ta sa mata ido, ta ce "Wannan asibitin specialist ne, duk Kano daga Aminu Kano sai shi,
hakikanin gaskiya suka gaya miki. Don haka ni babu inda zan kuma zuwa".
Ta yi shiru hawaye na zubar mata. Ba tausayin Ladidi ta ke ji ba, tausayin Alhaji Abbas ne,
bawan Allah, Baffa bai cancanci 'ya'ya irin wadannan ba.
Sun kusa Yakasai Ladidi ta ce "Wallahi Mairo duk abin da kike so zan baki, ki rakani a zubar
min da cikin, in Baba ya ji wallahi-wallahi kashe ni zai yi".
Mairo ta ce
"Ni kuwa mai za ki ba ni Ladidi in rakaki a kashe rai? Tukunna ma ni ban san inda ake zubar da
ciki ba. Kin bata wayonki! Amma bana tausayinki, Baffa nake tausayawa. Iyakacin tarbiyya da
ilmi ya baku, daga boko har na Arabiyyah, ya tsare muku cinku da shanku, da suttura dai-dai
karfinshi. Bai cancanci