Showing 3001 words to 6000 words out of 79746 words

Chapter 2 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf

to Detroit-Metro".

Hankalinta yayi mummunan tashi. Saboda ita ne Amiru zai bar kasar da haihuwarsa ne kawai
ba'ayi cikinta ba? Da sauri ta jefar da wayar. Da gudu tayi daki ta dauko mukullinta. Dina na kira
amma bata juyo ba take fadin.

"Shima zai tafi ya barni, kamar yadda Junaid ya gudu ya barni. Bayan sun kimsa min
soyayyarsu. Banaso in samu wannan _heartbreak_ (karyewar zuciyar) a karo na biyu".
Dina tace.
"Bi shi Mairo. Shine ZABIN ALLAH!!!"

Gudu take shararawa a kan titin da zai kaita _airport_ din Detroit. Cikin kankanuwar motarta
*GMC Terrain.* Hawaye na sauka akan kundukukinta. Da gaske Dina ta ke; wannan itace
SOYAYYAH! Da gaske Dina ta ke Amiru shine ZABIN ALLAH! Da gaske Dina ta ke da tace ta
kama mai sonta, ta rabu da *JIRAN TSAMMANIN WARABBUKA!* Ta karbi *soyayyah* a
hankali zata rikide ta zama *kauna* . To ga shi soyayyar ma zata gudu ta barta da tsammanin
warabbukanta wanda bata fata. .........................!!!

Koda Ta iso airport din ko kulle motar bata yi ba, a jikin motar ta bar mukullin. Da gudu ta shige
cikin _reception_ tana dube dube. Babu Amiru babu ko mai kama da *AMIRU* ! Ta karasa
_terminal_ bayan ta hankade ma’aikacin dake kokarin hanata shiga. Daidai sanda anka rufe

kofar jirgin ( _Lufthansa_ ) wanda zai tashi zuwa kasarmu mai dimbin albarka. Ba da jimawa ba
kuma ya soma ruguginsa mai gigitarwa bisa kwaltarshi, kafin ya daidaita sosai a sararin
samaniya.

Mairo ta durkushe anan tana kuka. Kukan da ta dade batayi irinsa ba tun bayan rashin
BABANTA da INNAR TA. Fita yake tun daga karkashin zuciyarta. Amiru ya tafi tareda dukkan
farin cikin data samu cikin *Michigan* wanda Yaya Habibu ya dade kafin ya assasa. Bai shigo
rayuwarta da sauki ba ashe! Ashe ya shigo ne ya kara rusa komai. Ya tafiyar da sauran karfin
zuciyarta. Ya dawo da rayuwa *unbearable* kamar kamar uncle Junaidun? Me yasa ita bata da
sa'a a soyayya komai kankantarta???
Ji tayi kamar an tsugunna a gabanta, kamin ta dago kuma an kai hannu a hankali an
dafa kafadarta. A sannu ta dago idanunta jage-jage da hawaye, don ganin ko wanene
wannan???

*A BARI YA HUCE* . ......
Littafin
*_Sumayyah Abdulkadir Takori*_

_Wannan littafi tukuici ne ga masu sha'awar ganin rubutun TAKORI a yanar gizo. Ga mai son
cikakken labarin (book 1-4) ya biya N1000 ga wannan account number_
*Sumayyah K Kabara*
*Zenith bank*
*2089357770*

_Sannan sai ya turo screenshot zuwa 07030137870_



NAGODE
7/28/21, 10:59 AM - Buhainat: KAUYEN GURIN-GAWA, 1988

Gurin-gawa karamin kauye ne mai tsohon tarihi da ya kunshi al'umma masu sana'o'i
daban-daban, amma duka tushensu daya. Galiban malamai ne da manoma, kuma kauye ne da
manyan malaman da a halin yanzun suka barwa duniya abin da ba za a mance da su ba suka
fito. Gurin Gawa na nan cikin karamar hukumar Kumbotso, yankin Fanshekara ta jihar Kano.
Karamin kauye ne, wanda ya samu tallafin gwamnati ta hanyar wutar lantarki, ruwan sha mai
tsabta, da takin zamani, wanda ke taimaka musu kwarai wajen bunkasa harkar nomansu.

Akwai sanannen hadin kai tsakanin al'ummar garin mazansu da matansu. Sai dai kuma babu titi
mai kyau a Gurin-Gawa. Idan mota ce zata shiga kauyen sai ta yi futuk da kura, mutanen cikinta
sun gwaggwara kawunansu sabida rashin kyawun birjin.
Duk da haka wannan bai hana al'ummar cikinta jin dadin zamanta ba, motar haya ba ta shiga
cikin kauyen, sai dai ta aje ka a titin ka hau achaba ko bayan akori-kurar Rake ta mutanen garin

ka karasa ciki. Don haka da wuya ka ga mutanen birni na shiga kauyen, don a ganinsu ba su ga
mai zasu tsinto cikin wannan kalataccen kauyen ba.
Samarin garin Gurin-Gawa kan fita cikin Fanshekara da wajenta domin neman kwabo, ta
hanyar ga-ruwa, sayar da rake, dukanci, dako da sauransu. Don kalilan ne suka damu da
makaranta wadda dama idan dai ta boko ce, to ba a zancenta cikin garin Gurin-Gawa.
Makarantun allo da na Buzu su ne Allah Yai yawa da su a garin.
Malam Bedi, yana daya daga cikin dattawan garin Gurin Gawa, haifaffen nan ne iyayensa da
kakanninsa. Sana'arsa shi ne noma, yana da gonar rake da gyada, sannan yana nome dankalin
Hausa, makani da gurjiya.
Bedi da matarsa Hure, fulanin Gurin-Gawa ne na usul. Mutanen kwarai ne da duk Gurin Gawa
ba wanda bai sansu ba, tare da yi musu kyakkyawar shaida. Babban dansu shi ne Habibu,
wanda tun yana karami Malam Bedi ya dankawa kaninsa mai bi masa a haihuwa ya ke taya shi
sana'ar fataucin goron da yake yi daga Shagamu zuwa Kano, wanda daga baya shi Habibu ya
shiga makarantar horas da malamai (SAS) tun daga wancan lokacin kuwa ya koma Kano
kwata-kwata. Shi da Gurin-Gawa sai dai yazo da yawo idan ya zo gaida mahaifansa wanda
yakan dauki dogon lokaci bai yi hakan ba.
Su ma su Malam Habibu ba su wani damu da shi ba, don ba wata cikakkiyar shakuwa ce a
tsakaninsu ba. Duk wani burinsu na duniya yana kan 'yar autarsu “MAIRO”, wadda ba su samu
ba sai bayan shekaru sha takwas da haihuwar Habibu. Don haka idan ya zo a tura mai kujera
ya zauna, ana lale da shi, idan bai zo ba ma falillahil hamdu.
Inna Hure ce duke tana faman firfita wutar iccenta, domin ta samu ta kammala abincin rana
kamin Malam Bedi ya dawo daga gona. Idanunta sun yi jawur sai zuba suke, ga dukkan alamu
irin azababben itacen nan ne Allah Ya hadata da shi. A gefe 'yar lelen ce zaune bisa tabarma
tana dandasawa 'yar bebin karanta kwalliyar juma'a da wani tsalelen yankin yadin
mamar-mamar da ta tsinto a shagon tela. Ta daga 'yar bebin tana cillawa tana cafewa tana
wakarta cikin nishadi, ga dukkan alamu babu yarinyar da ke cikin farin ciki a gidansu a gaba
dayan kauyen Gurin Gawa kamarta, sabida daurin gindin sangarta da cikakken gata da ta ke
samu daga Innarta.

"Ke kam 'yar gata ce, Ta-Ummule.
Ni uwarki “MAIRO” na tsaya miki.
A taba ki a tabo bala'i,
A duke ki, in rama miki.
Innata ta tsaya min,
Ni kuma na tsaya miki........"

Sallamar Habibu ce ta katse ta daga wakar da ta ke rerawa 'yar bebinta, cikin zazzakar
muryarta kamar gyare. Ta yi cilli da Ta-ummulen ta kwasa da gudu ta makalkale shi, tana cewa,

"Yaya Habibu oyoyo!"

Ya ce "Ke da Allah kazamar banza, cika ni, dubi bakinki damale-damale da busasshen koko,
hanci duk busasshiyar majina, sannan kalli hannunki duk bakin tukunya, kin zo kin goge su
duka a jikina. Wallahi duk sanda na doso garin nan cikin fargabar cakumon da zaki yi min da
kazantarki nake, shashashar banza an girma ba a san an girma ba". Ya rabata da jikinsa ta karfi, ita ko ko a jikinta, dariya ma ta ke abinta kamar ba da ita yake ba.
Inna Hure ta cika fam, kiris ta ke jira ta sauke mishi kwandon bala'in da ke cike taf a bakinta,
sabida wannan tijara da yake yiwa autarta.
A ganinta Habibu ya tsani Mairo ne kawai, don shi yana birni, ita tana kauye, duk da
matsananciyar kaunar da Mairon ke masa. Babu ranar Allah da zata fito ta fadi, Mairo ba ta
ambaci sunan Yaya Habibu ba. Shi kuma da zarar ya zo irin tarbar da yake yi mata ke nan, ita
kuwa kamar dada tunzura ta yake ta yi masa oyoyon, da dukkan zuciyarta.
Ya matsa gaban Innar ya kai gwiwoyinsa kasa, ya ce
"Inna barkanku da gida, mun wuni lafiya?"
Ba ta juyo daga fifita wutarta ba, haka ba ta kalle shi ba, ta ce "Lafiya kalau". Cikin danne bacin
ranta.
Ya yi shiru cikin zargin kansa. Ya san tabbas ya tabo Innar, don ta sha ce masa idan ba zai
daina kyarar mata auta ba, to ya daina zuwa, babu dole.
Cikin kasada ya ce "Amma Inna ga wannan katuwar yarinyar ki zauna kina hura wuta, ita tana
wakar 'yar bebi? Duk wani dan arziki kamarta ai yanzu ya dawo ne daga makaranta, yana
haramar tafiya islamiyya, amma ban da wannan, ban da karare ba ta san komai ba, shi yasa
duk wasu abubuwa na yara masu hankali, ba ta san shi ba............" A fusace ta juyo ta zuba masa jajayen idanunta, ta ce "Kai saurara. Wai me ye gaminka da
yarinyar nan ne? Me ta tare maka? In don oyoyon da ta ke yi maka ne ba ka so, zan hanata,
amma wannan sababin da kake yi mata ya ishe ni. Ka zo gidan su ka uzzireta babu gaira babu
sabar? Ba ta zuwa makarantar, idan kai ka haife ta sai ka dauketa ka kai ta". Ya sunkuyar da kai ya ce, "Allah Ya ba ku hakuri Inna, Inna Allah Ya huci zuciyarku".
Ta ja tsaki, "Tsuuuu!" Ta ci gaba da aikinta tana ta sababi, shi kuma bai kara tofawa ba, bai
kuma tashi daga durkuson shi ba. Malam Bedi ya yi sallama ya shigo, rataye da fartanyarsa da
alama a gajiye ya ke likis, sai gumi ke disa daga wuya da goshinsa. Yana ganin Habibu sai ya
fadada far'arsa, amma jin Inna Hure na ta sababi sai ya maida fuskarsa ya dinke. Ya dade yana
sauraronta ba ta san ma ya shigo ba, tana ta fadan idan Habibu ba zai daina tsangwamar mata
Mairo ba, to ya daina zuwa, don ba ita ta kirawo shi ba.
Malam Bedi ya yi gyaran murya, sai a nan tasan da tsayuwarsa. Ta ce "Ai gara da ka zo, dama
binka zan yi yanzun, ka ja wa yaron nan kunne ya sakar wa diyata mara ta yi fitsari, tunda ba a
gidansu ta ke zaune ba, balle ya ji kunya don an ce kanwarsa ce".

Malam Bedi ya ce, "Anya Hure? Kina kyautawa abin da kike yi wa Habibu? Ina laifinsa don ya
zo gaishe ki? Wannan yarinya da kike ta tada jijiyar wuya akan an gaya mata gaskiya, wane ne
majibincin al'amarin ta nan gaba a bayan mu? Wannan din dai da kike cewa ya fita harkarta shi
ne ba wani ba. To idan ya fita harkar tata ranar da babu mu, wane ne zai shiga? Shin ma me ya yi mata da zafi? Don kurum ya ce ta dinga wanka? To ki yi hakuri, Habibu ya
daina cewa 'yar ki ta yi wanka, don Allah ta shekara ba ta yi ba. Kai taso mu tafi masallaci kar

mu rasa jam'i".
Ai jin haka ta yi daki da gudu ta yayibo mayafinta da takalmin robarta, a gujen ta sake fitowa,
"Yaya Habibu ni ma zani masallacin, dama tun jiya ban yi sallah ba".
Wani takaici ne ya sake kama shi, ya hadiye ya ce, "To mu je, amma sai ki tsaya a wajen
masallacin daga gindin bishiya kina bin jam'in, don mata ba sa zuwa masallacin maza".
Ta ce "To idan mun fito zaka rakani mu je mu tsinko wa Inna tsamiyar kunu? Dama Rabe shi
yake dora ni, kai kuwa ka ma fishi tsawo".
Ya kama baki, "Yanzu Mairo bishiyar tsamiya kike hawa?"
Cikin son ta burge shi, da alfaharin hakan sosai a kwayar idonta, ta ce
"Mu hau tsamiya mu sauko, mu hau magarya, mu hau dinya, mu tsallaka goba. Rannan Lanto
ta fado tim! Ta karya kashin baya, ni kuwa idan na makale a jikin reshen bishiya kamar 'yar
Birrai nake. Bana fadowa, sai dai in ciko bujena da goba da tsamiya........."
Ya yi gaba ya rabu da ita don takaicinta kamar ya amayo zuciyarsa, amma sai ya yi tunanin to
ita me ye laifinta? Innarta ce ta daure mata gindi.

Habibu saurayi ne dan kimanin shekaru ashirin da biyar. Ya kammala kwalejin horas da
malamai ta Kano, wato (SAS), yana jiran sakamako ne ya wuce babbar makaranta, kodayake
ma abin da ya kawo shi Gurin-Gawa kenan yanzun, wanda yake son su tattauna da mahaifinsa.

Alhaji Abbas Mai goro kanin Malam Bedi ne ciki daya, uwa daya uba daya, shi ke rike da
Habibu da hidimar karatunshi, ko da yake morar juna suke tunda kuwa duk wahalar
kasuwancinsa na goro, a wuyan Habibun ta ke, wadda ya ke gudanarwa idan ya dawo daga
makaranta da ranakun karshen mako. Suna zaune a unguwar Yakasai a cikin birnin Kano. Yana da matan aure biyu da 'ya'ya bila
adadin maza da mata. Saidai ‘ya’yanshi kanana ne da ake haifa akan idon Habibu. Cikinsu
duka babu mai shekaru goma. Babbar diyarshi Ladidi sa’ar mairo ce. Don haka Habibu tamkar
wani jigo ne ga iyalin Alh. Abbas wanda duk suke kauna sabida zumuncinsa da rikon amana. A rayuwar Alh. Abbas bai taba ganin yaro mai kwazon neman na kai da amana irin Habibu ba.
Tunda ya ke tare da shi, kwandala wannan bata taba bata cikin lissafinsa ba, kimanin shekaru
ashirin ke nan. Watau tun Habibun yana dan shekara biyar. Wannan ne dalilin da ya sa ya
maida Habibu dan cikinsa ba Dan dan uwansa ba. Taimako dai-dai gwargwado Alh. Abbas na yi ma yayan shi Malam Bedi, kamar ta samar mai
ingantaccen takin zamani, da taimaka mai da motocin noma a yayin girbi, wadanda yake dauko
masa haya daga KNARDA.
Bayan wannan sallah da azumi shi ne sutturarsu, haka ta fannin abinci lokacin azumi, tun daga
kan sukari, lipton, madara, da su taliya ba abin da ba ya taso Habibu ya kawo musu, sai dai
idan suna nomansa a nan Gurin-Gawa.
Zumunci ne mai karfi a tsakaninsu, wanda iyayensu suka dora su a kai, har gida Alh. Abbas ya
sayawa Mal. Bedi a Yakasai ya ce ya dawo su zauna tare, inda shi kuma ya ce shi da rabuwa
da Gurin-Gawa sai dai mutuwarsa. Ko ita ba ya fatan a fitar da gawarsa daga Gurin-Gawa, su je
can su tsinci abin da suke tsinta a birnin, shi kam a gareshi kwanciyar hankali shi ne komai.
To amma wannan zumunci na mazan ne banda matan. Babu shiri ko kadan tsakanin Inna Hure

da matan Alh. Abbas wato Habiba da Hajara. Tun sanda daya daga cikinsu ta taba cewa a bata
Mairo ta dinga taimaka mata hidimar ‘ya’yanta ta kulla gaba da su. Ta ce kuma wadda duk ta
kara tako mata gida, Allah Ya isa. Ta rasa dalilin da 'yar tata ta tsolewa kowa ido. Ba abin da ta
ke so a rayuwarta irin ta budi ido ta ga Mairo na wasan 'yar tsanarta a tsakar gida, suna
harkokinsu gwanin ban sha'awa.
Don haka ne ko makarantar firamare da ake sa yara a kauyen taki yarda ta sakata, ita dai su
zauna abinsu.
Sai da Mal. Bedi ya yi da gaske kamin Mairo ta dinga zuwa karatun allo a makwabtansu, daga
takwas na safe zuwa sha biyun rana. Nan din ma ba wani abin arziki ta ke tabukawa ba da ya
wuce tsokana, jan fada, surutu da guduwa idan Malam ya soma gyangyadi.
Abin da Mairon Hure ta kware akai shi ne hawa bishiya. Yadda kasan kadangaruwa koko Gorilla
haka ta ke makalewa a jikin bishiya. kusufa-kusufa ta iya kurdawa ta tsinko abinda ranta ke so
ta cika bujenta. Duk girman bishiya Mairo zata iya dafe ta, ko tsoron irin aljannun nan da ake ce
suna zama a bishiyoyi ba ta yi. Ta tsinko musu su ci abinsu, ita da Innarta, wannan ya fi komai
dadi ga Hure.
Mairo yarinya ce 'yar kimanin shekaru takwas cif. Amma kaifin bakinta ya fi na dan shekaru
ashirin. Kyau kam ba a magana, tsurarshi na Inna Hure, doguwa shafal-shafal da shafaffar
mara gami da lafiyayyen kugu, wanda tun tana jaririya haka yake. Sumar kai yalwatacciya,
yalo-yalo kamar ta hada jinsi da Larabawa. Sai dai fa dankare take da kwarkwata da amosani
wanda ya bi ya cinye rabin gashin.
Wani aiki sai Hure Innar Mairo, don tunda Mairo kukan kitso ta ke, aka shafe yi mata kitso a
doron kasa. Kai wata kila ma ta manta akwai suma akan Mairo, don kullum kulle ta ke tamau
cikin wani bakin dankwali mai masifar dauda. Sai idan kwarkwatar ta ishe ta da cizo ne ta ke
tube dankwalin ta samu gefe guda ta yi ta susa da hannu bibbiyu har sai jini ya bubbugo.
Wannan shi ne babban takaicin rayuwar Habibu, yana matukar bakin-ciki da tsarin rayuwar
kanwarsa tilo, wadda kuma Allah Ya sanya masa matsananciyar kaunarta da tausayinta. Ta
wani bangaren ba ya ganin laifin Inna Hure, domin haihuwar ce Allah Ya ba ta a tsufanta, bayan
ta riga ta fidda rai da samunta. Sannan yawan aiyukan gida da ke kanta ba zasu barta ta kula da irin wadannan kananun
abubuwan game da yarinyar ba.
Duk ba wannan ya fi damunsa ba, kamar jahilcin Mairo. A ganinsa Mairo jahila za a kirata kai
tsaye, ba arabi ba boko. A ganinsa da tana zuwa makaranta, wannan duk wani abu ne da ita
kanta zata yi wa kanta nan gaba, ba tare da kowa ya sata ba.

Bayan sun fito masallacin ya duba inda ya ce Mairo ta tsaya ta yi sallah, ba ta ba alamunta,
balle dardumar karauninta. Ya juya gabas da yamma, Kudu da Arewa babu Mairo. Ransa ya
sosu, ya kira wata 'yar yarinya mai tallan rogo, ya ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login