Showing 27001 words to 30000 words out of 95576 words

Chapter 10 - YAR LESBIAN COMPLETE BY Nadiya Muhammad Ahmad.doc

ka koyamun yanda Ake Kiran budurwa Awaya, tun 4days dasuka wuce na karba numbern ta nakasa kira. dafe Kai yazeed yayi yace Amma ka Raina ma kanka wayo Wlh, So koba wannan yarinyar Zaka kiraba bazan iya bata lokacina Akan ka ba. toh yayi inda budurwa Kace bazakace Haka ba Ai. Wani tsakin Yazeed yakara ja ya juya yacigaba da Aikinshi. Yusuf wayanshi ya ciro yashiga dialling numbern Kausar, Saida kira ta katse ba'a daga ba, cije baki yazeed yayi dan Shi haushin Yusuf yakeji yanzu baga irintaba ka kira yarinya ta Raina ka bata daga ba, ba ruwanka yusuf yace yakara dialling numbern Saida takusa tsinkewa Aka daga, HELLO! Kallon yazeed yayi Alamar ya gayamai Abinda Zaice, juyar dakai yazeed yayi be tanka ba. Hello waye ne? Am....Kausar am Yusuf, ya gida. Lfy tace kawai, Shiru nadan lokaci Yusuf yace "dama magana Zamuyi Kausar, tun Ranar damuka fara haduwa dake gidan kawarki Minal naji......bigeshi yazeed yayi Ahankali yace wawa da gaske Saika Zubda girmanka gaban yarinya karama, juyar dakai Yusuf yayi yana mai Alama da ba ruwanshi. Yacigaba Wlh Kausar tun Alokacin naji Kinzama Wani Abu Acikin Raina,pls Kausar ki karbeni Amtsayin mijin Aurenki nayarda Zan jiraki har lokacin dakika Shirya,fatana kibani waje Acikin Zuciyarki Mugudanar da Soyayya mai tsafta. Kausar daskarewa tayi daga bangarenta yayin da wani Murmushi ya Subucemata Cikin Ranta wani Nishadi take ji domin dama Mamy takira Hajiyarsu ta Sanar da Ita Halin da Kausar tashiga Sanadin kin Bata Hakkinta dasukai, Alokacin kuma Hajiyar Kausar tayi nadama kuma dayake tana karbar Shawarar Aminiyarta Mamyn Leemah Shiyasa ta Sami kausar tace ta fiddo miji Ayi mata aure, Amma duk dahaka Saita karasa Karatun ta tunda 1yr ya Rage mata. Kausar taji dadi Alokacin tayima Hajiya Alkawarin ta daina Yin lesbian har Abada kuma Zata Samo miji, toh yau Saigashi Yusuf din da tunda tafara ganinshi taji ya kwanta mata Arai Kuma yau Shine yazo mata da maganar yana Sonta, murna tarinkayi bangare guda tana tsoro kada Yasan ta taba Aikata lesbian yace baya Sonta.....Kausar kinyi Shiru ba Amsa Yusuf ya katse mata tunaninta. Shiru tayi daga bisani tace mishi Zatai Shawara, pls Kausar nabaki Zuwa Nan da gobe Kinga Zaku koma Skul, ok tace ta kashe wayar, tacigaba da tunanin Wayyo gashi naji mamyn Leemah tace budurci Shine martabar diya Mace Toh Anya nidin Virgin ce ma kuwa, Nashiga Uku Wlh lokacin khady har yatsa tana Saka Mun, gashi Ran nan A grp naji Ance Saka yatsa yana Maida mutum dis Virgin, Wayyo ni Kausar dole Yusuf Yasan Abunda na Aikata Abaya khadija ta cuceni Allah ya'isa harta So na cutar da wasu,Allah yasa Su feenah basa yarda dasaka yatsa da yanzu Suma Saisun koka,kai Innalillahi haka kausar tayita tunanin mafita. Shiko Yusuf Murna yarinkayi harda yar Rawa, Kafin ya juya dan yafada ma yazeed yanda Sukai da Kausar yaga wayam ba kowa Awajen,tabe baki yayi yafita Shidai Sai Murna yake.

Sisto kin Shirya kifito mutafi Nazeer Kema Feenah magana, Nashirya big bro Naga kafini dokin Zuwa gidan Su Leemah dinma, "Aa" Feenah Sabida dare ne, toh muje Nashirya,fitowa Sukai Suka Samu Mumy dasu mubeen tana koya musu homework dinsu, mum mun fitofa, my feenah kin Shirya komai ko? "Eh mumy Nashirya" Zomuje Akwai maganar da Zan miki tashi mum tayi feenah Nabinta Abaya Zuwa Room dinta, Zama sukai mum ta kamo Hanunta,my daughter Kinga Nasihar da mamynku tayi muku koshi kadai ya isheku, Zan kara Miki da nawa Kadan,feenah Abunda kuka Aikata Abaya inaso yazama Labari,na hadaki da girman Allah kada Ki kara aikata makamancin irin Abunda kikai Abaya, Nasan wanchen ma Sharrin Shedan ne ba Halinkin bane,Amma kinsan wajibine Dan Adam yayi yaki da Shedan A Rayuwanshi,kusan duk Abinda mutum ya Aikata na Zunubi Son Zuciya ke Angiza Shi,pls Feenah banason kara jin kin Aikata Abu makamancin wanchan badan niba Dan Allah. Sa'annan game da Sha'awa wannan wani Abu ne da yake damun duk wani baligi ko baliga mai lafiya, Inason kisani Aduk lokacin dakikaji zaki iya Samun natsuwa ta Wajen karanta aur'an,Azkar da yawan yin Azumi, Insha Allah dakin gama karatunki kin dawo Za'a fara maganar Aurenki da kabeer inhar kinasonshi kinji my daughter kimun Alkawarin bazan ji kin Aikata wani mummunan Abu ba koda Aboyene. Rungume mum feenah tayi tana kuka tace Mumy nadau maganarki Bazan kara Aikatawa ba da izinin Allah Koda Chan ma ba halina bane Sharrin Shedan ne! ( wai komai Ace Sharrin Shedan Zaku hadu dashi masu aikata Abu da gangan kuce Sharrin Shedan=??) Allah yamiki Albarka yata, Amin mumy ta! Ki kara Maida Hankali A Skul kisamu Abunda kikaje nema, insha Allah mum. Tashi muje Toh kigaida mamyn Leemah din, toh tace Suka fito atare palon Suka dawo Nazeer har ya karasama Su Mubeena homework dinsu. Yaya Nazir muje Ko, ok Sister muje. Su Mubeen ne Suka tashi suma Zasuje, mum tace kunga Auntyn kuce ba lfy Allura Zasuje Ayi mata,duk maiso saiya bisu. Ai da Sauri Suka koma Suka Zauna feenah da Nazeer Suka fita Suna dariya.

Kai tsaye Suna Shiga gidan parlon Sama Suka haura Anan Suka tarar da Mamy da Leemah Suna fira,Sallama Sukayi da gudu Leemah ta tashi Suka Rungume juna da Feenah Suna dariya. Mamy ce ta Amsa Sallaman tana Allah ya Shiryamunku yaran nan. Mamy Sannu da gida. yawwa my Son, yasu Hafsa din?Suna lfy Mamy tace A gaidaki, ina amsawa. Karasowa Feenah tayi ta durkusa tana gaishe da Mamy,jawota Mamy tayi tana Amsa gaisuwan,my daughter Shine baki kara Zuwa ba tun Rannan ko har Mum ta koya miki Rashin Zumunci ne? Girgiza kai tayi tace Aa Mamy ba Haka bane. Kin kayuta tunda ba Haka bane. Nazeer ne yace mamy Ina yazeed? Yazeed yana part dinshi inaga bacci yake kokuma bakin Ran yake. dariya Sukayi banda feenah data kauda kanta gefe, tashi Nazeer yayi yace Bari naje wajenshi kamun na wuce gida,toh yarona dan Albarka. Leemah jan Feenah tayi Suka Shige dakinta Ya rage saura Mamy A parlon. Kwance ya Sameshi yana waya da Yusuf da Alama fadan nasu Dasuka Saba Suke. Yazeed yana ganin Nazeer ya kashe wayan. Captain kaine A gidan namu? Murmushi yayi yace nine Dr yazeed na kawo Sister dina ne, gemtse fuska yazeed yayi yajawo wata fira Sunayi, Nazeer jiya Nasamu wata baby ita nakeson Aure, kai dacter ina kasamota? Wajen Malali take jiya naje wucewa ta wajen muka hadu, namaka Murna Amma zatakai Shekara 30 din ko? Tace Shekarunta 28 kaga kadan ya Rage, mun fahimci juna da ita tabani phone number dinta, bari kaga picture dinta, kai yazeed ina Zaka Kai Wannan katuwar macen dan Allah?kalletafa kamar.....katseshi yazeed yayi nidai Ahaka nagani Kuma Naji inasonta, Allah yabada Sa'a. Amin yazeed yafada yace bari naje wajen Mamy. Ok Saika fito. Waya Nazeer ya daga yashiga Kiran feenah,bugu daya Ta daga.....big bro tafiya Zakai? No sister turo Leemah ta karbi tsarabanta, ok bro. da ker Feenah tasha kan Leemah tukun ta yarda da tace saidai Suje tare. Tura dakin tayi da Sallam Cikin Siririyar muryanta. lumshe ido Nazir yayi yanajin Wani bugun Zuciya besan meyasa duk lokacin da yaga Leemah saiyaji hakanba tare da Nishadi Aranshi, Azuciyarshi yace tabbas maganar Yusuf Gsky ce Sonta nake, Amsa Sallaman yayi,Leemah ta nimi waje ta Zauna Agefe, Sister nazo baki bani Ruwa ba, Sorry yaya Nazir nazata....kinzata Nasha ko? Eh Hakane Nasha kamin nazo miki,dago kai tayi, yace "umm" yana daga mata gira danke Nazo, wannan na kawo miki ya daura mata Karamar back Kan cinyarta, Sannan Don namiki Sallama,pls Leemah kikula Mun da Kanki, Zaro ido tayi tace "why"? So kike kiji kawo kunnanki tashi tayi da gudu tabar dakin,tana Murmushi, karo taci da yazeed dake kokarin Shigowa,kallonta yayi ya tabe baki yashiga dakin. Leemah nashiga ta Zauna tana nishi, kekuma lfy? Bakomai besty. Toh naga kindade, eh yabani wannan ne. Bude muga,wlh bazan budeba tunda kema banga nakiba. Shikenan Feenah tafada ta juya bacci ya dauketa. Leemah daren Ranar kasa bacci tayi datayi juyi Yaya Nazeer take gani lokacin dayake mata magana.


=ؖ?=؋?=؋?=؋?=ؖ?=؋?=؋?=ؖ?
YAR LESBIAN CE
=ؖ?=؋?=؋?=ؖ?=؋?=؋?=؋?=ؖ?
By
Nadeeya Muhammad Ahmad

dedicated to
Xaynab Ummu mahbub

*this whole page is for you dear (khaleesat haidar) My love to you d'd' May Allah give you a happiness and Successful in your life Always "Amin"*

Page....21

Yau takama Ranar Sunday Ayau Su feenah Suka Shirya komawa Skul. Zaune Suke kan bed Suna hira Leemah ce tace besty yakamata Ki kira Haruna driver yazo ya Kaimu, kinsan fa munce da wuri Zamu tafi. "Oh Leemah sau nawa Xance miki Haruna baya nan" wai Ina Ya tafi ne? Wai daddy ya Aike Shi fa. Yanxu waye Zai kaimu kenan? Muje Mu hau taxi feenah ta fada tana Ware hannuwa. Chaf Wlh badaniba Aje Asiyar dani Ahanyar Abuja Leemah ta fada tana kokarin fita. tabe baki feenah tayi tacigaba da hada kayan dake gabanta. Mamy! Mamy! Oh Leemah idan kina kira kamar makauniya, Mamy dake fitowa daga bed Room dinta ta fada. Mamy drivern Su feenah baya gari waye Zai Kaimu ne? Ai Saikije kice brother dinki ya kaiku "Zaro ido Leemah tayi tace Mamy pls Kije kice mai" Naji Kije kishirya. "Toh Leemah ta fada tayi hanyar dakinta" part din yazeed Mamy tanufa, tura dakin tayi tashiga, yana kwance yana waya juyowa yayi ganin Mamy ce yatashi yana Sosa Kai! Mamy Sannu da gida. "Yawwa Son" Mamy dakin kirani ma nazo Ai, Sabida kada naji firar taka ko? Murmushi yayi bece komai ba. dama So nake katashi kashirya ka Kai sisters dinka Abuja. Mamy....! daga mai Hannu tayi tace Umarni nabaka daga Haka tafita tabar part dinshi. dafe Kai yayi Cikin Ranshi yace wannan mai idon mujiyan itace Zatasa Ayi Hakan, Xanje! but Wlh Leemah nashiga Xanja motan nayi gaba, Kwafa yayi yafara Shiryawa Cikin Manyan kayanshi.

Yusuf ne kwance yana tunanin Kausar Aranshi. Yakamata na kirata Naji menene matsayina Awajenta kamin ta Koma Skul yau! dialling number dinta yayi.......Saida ta kusa tsinkewa Aka daga "Shirune yabiyo baya" daga bisani Yusuf yace Hello "Sweetheart" wani farin Ciki taji Aranta tace "Na'am" Murmushin Nasara Yusuf yayi yace Hope kinyi Shawara din? Shiru tadanyi daga bisani tace Umm Nayi, Alhmdllh Menene matsayina Azuciyar ki for Now? Na Amince But Akwai Abunda Zangaya maka......katseta yusuf yayi my Kausar nariga danaji Abunda nakeson Ji kuma naji dadi, kuma nasan Nayi Sa'ar Matan Aure Tunda kika kasance Kawar Su Leemah bangare guda kuma Kawar Minal yabon da Dr Khalid yake Akan Minal ma kadai ya isheni Shedan kedin kamammiyar mace ce,pls Kausar ki Amince mun na nuna miki Soyayyata,ki yarda Kuma Zaki kasance matata Nan da Dan lokaci! Kausar gaba daya jikinta yayi Sanyi tanason ta gayamai Ainahin Halinta, tana tsoro Shiyasa tace, Na Amince Allah ya nuna mana lokacin, Amin Yusuf ya fada yana jin dadi har cikin Ranshi. Yaushe Zaki tafi ne? Yanzu nama gama Shiryawa, ko nazo nakaiki ne? "Um"um"basai Kazo ba. Kina mun Rowan ganinki ko, No ba haka bane. "Alright " my kausar kikula mun dakanki "I love you" Ok darling love you more. Wow me kikace Dan Kara fada Murmushi kausar Tayi tace Saimun hadu. Alkawari kikai! Na yarda bye ta Kashe phone din, Kai Yusuf Badai Surutu ba ta fada Cikin Ranta kuma tanajin dadin hirarsu. tashi tayi tashiga wajen Hajiyarta, Nafito Hajiya, Ai na leka Naga kina waya, Allah ya tsare kindai Ji Nasihar danakara miki kikula da Kanki,kuma Na Rabaki da khadija din nan idan har na'isa, Insha Allah Hajiya na Rabu da Ita....Allah ya miki Albarka. Amn Kausar tace tafita tashiga mota driver yajata.

feenah da Leemah ne Suka fito Sai Mamy dake biye dasu Abaya, Oho Sarkin bakin Ran bema fito ba kenan, yawwa Mamy tun da befito ba Bari naje nakara duba back din inda Na ajiye Leemah ta fada. Saikiyi Sauri kamin ya fito yafara Harare Harare, toh Leemah tace tanufi Cikin gidan. daughter dakiyita tsayuwa naga Motan Abude take Zoki Shiga kamin Su karaso! Mamy ta fada tana kallon feenah yayin da take bude Mata gaban motar, Mamy Bari nashiga Nan ya'isa, Aa my daughter dawo nan din dai idan Leemah tazo Saita Shiga bayan, bata iya musu da Mamy dan haka kawai tashiga gaban. Mamy tace Bari naje Na turo Shi. Zuwa tayi ta tura dakin nashi ya Shirya yana Zaune yana danna waya" yayi Sarkin fadin Rai tashi ga Sister dinka Chan Amota kamin dayar ta fito kutafi. tashi yayi Mamy nagaba yana binta Suna Zuwa Mamy tashige Ciki tace Bari na turota, dadi yaji Aranshi yace Ai Kafin ta fito Naja mota ta. Shiga yayi be kalli wacece gaban motar ba Kawai yaja yafita da Sauri...... kiyi Sauri Leemah najifa Kaman ya kunnah Car din, Ok mumy nama gani Ai. fitowa Leemah Tayi bataga kowa ba,ta kara leka waje nan ba Kowa, juyawa tayi takoma Cikin gidan, Mamy ya tafi da Feenah, tasowa mamy tayi tace muje dai kiduba waje. Mamy Wlh na duba. Kai Nidai ban San Irin Halin yazeed ba Allah ya Shirya. Mamy ni yanzu waye Zai kaini daddy baya gari? Shine Ai dole na kawo driver Sabida irin Haka. Yawwa bani phone dina nakira Mum dinku. Mika mata Leemah tayi ta neme waje ta Zauna. Kiran mum mamy tayi Suka gaisa, Hafsa Nazeer yana Gidane? Yana nan. Nakai mishi ne? Aa dan Allah Leemah Zaizo yakai Abuja, wannan miskilin dan naki daga taje neman Abu kamin tafito yayi gaba da daughter dina. Ahhh Fatima Kodai Halimatun nawa ta tsaya ba! Eh keda bakison laifinshi cema Nazir yazo yakaita. toh bari namai magana.... part din Nazeer mum tayi tasameshi Akwance kamar mai Naxarin Wani Abun...My Son! Tashi yayi yace Mum. Me kakeyi ne?? Bakomai mumy dazun Aka kirani Ake gayamun Anmun transfer gaba daya Aikina ya dawo Nan. Kai Alhmdullah! Allah ya Amsa Addu'a ta dama ni yanzu banaso kuna nesa dani. Nima Nayi farin ciki mum, Allah yakara temakawa Amin mum. Kana free ne yanzu? Kina son wani Abu ne mum? Mamynku ta kirani wai Yazeed ya tafi da Feenah be dau Halima ba, Shine tace kaje ka kaita. Kara tashi yayi Zaune yace bana komai mum bari natashi, Murmushi tayi kawai tabar dakin ganin Yanda ya daburce farar daya.... tana fita yahau Rawa=؃?=؃?Alhmdllh yau Zan Sanar da ita Abunda yake Raina. Shiryawa yayi Sharp Sharp yafita,lekawa yayi yace Mum na tafi. Zo mana Ai tace Anfasa! turus ya tsaya lokaci daya face dinshi ta chanza dariya mumy tayi tace wasa nake Safe trip Son. Murmushi yayi yace Tnx mum yafita yayi gidan Su Leemah. Yana Zuwa Mamy ya kira ya gaisheta yace yakaraso. fitowa tayi Cikin takunta na kasaita yana ganinta yayi Sauri ya fito ya Amshi kayan hanunta yasa a booth ya bude mata gaban mota Saida ta Shiga ya mayar ya Rufe yashiga Yajasu.

Saida yayi tafiya mai tsayi kamshin turaren jikinta yake Shaka yana lumshe ido, Leemah waye yabaki wannan turaren? kinma Shigo bako gaisuwa. Shirun da yajine yasashi juyawa. Keeeyyyyy ya tsayar da motar yana kare mata kallo,itako ta Dan jinginar da kanta Jikin kujera tana bacci Kasancewar jiya basuyi wani bacci mai yawa ba. Gashi tashigo gaban motarshi kamshi da Sayin Ac ya dibeta tun tana tunanin Meyasa be dauko Leemah va har bacci yayi gaba da ita. Innalillahi ya fada Afili ni wai Wannan yarinyar meyasa take Shiga Mun hanci nane? Why? Meyasa duk lokacin da banason haduwa da ita Saina ganta? Mtswww yaja tsaki yakara dago da kanshi ya Zuva mata ido.....baccinta take hankali kwance, Cikin Ranshi yace Ashe tana da Kyau Haka? Daga kai yayi y Zuba ma pink lisp dinta ido,kan Siririn hancinta yakara kallo, ga idonta dasuke Alumshe Gwanin Sha'Awa,kumatunta ya kalla wanda yake dauke da dimple. Cikin Ranshi yakara maimatawa Kai gaba daya Mufeeda batakai Rabin kyan yarinyar Nan ba,kuma ita da kullum face dinta yake dauke da Make-up ma, Amma Ji Wannan bataima make-up dinba Kalleta mai Kyau....mtswww yaja tsaki Afili yace Amma Sai Rashin Kunya da fitsara "iri" "iri" Shiyasa nakeson Mufeeda ba Ruwanta da Rashin Kunya irin na yarinta din Nan......katsemai tuninshi tayi yayin da yaji hanunta kan Cinyarshi, take yaji wani Abu ya wuce mai tun daga Kai har Zuwa tafin kafarshi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login