Showing 1 words to 3000 words out of 79746 words
Chapter 1 - ABARI YA HUCE BOOK Complete Book by Sumayya Abdulkadir Takori.pdf
: *DANDANO DAGA ABARI YA HUCE*
*MAIRO A GIDAN YAYA HABIBU!!!*
© *Sumayyah Takori*
Litinin babbar rana, ko bature yana tsoronki. Habibu ya yi shirin ofis cikin _suit_ din ma'aikatan
bankin _Barclays_ , da jibgegiyar rigar sanyi, hand-socks da leg-socks, yana so zai fita aiki. ga
yara sunyi shirin makaranta tsaf, misalin karfe bakwai daidai na safe. amma babu hanya, domin
kuwa tashi sukayi suka tarar kankara ta rufe kofar gidan ruf, da tagogi bakidaya.
Dina ma ta fito cikin nata shirin cikin kayanta na lauyoyin banki, tana ta korafi akan 'snow'. Dole
Habibu ya fiddo waya ya kira ma'aikatan sare kankara, nan da nan suka zo cikin minti goma,
suka bambare kankarar sannan suka samu hanya suka fita.
Mairo ta fito daga dakinta ta yiwa sanyi mugun shiri, baka ganin komai nata sai shacin
kayatacciyar fuskarta kai ka ce balarabiyar *Morocco* ce. Tasa yaran a gaba suka fito tana
dauke da little Mairo, suka zo bakin hanya suka tsaya tana rike da hannayensu, tsayuwar minti
biyar sukayi motar makarantar su ta iso ta sanya su ciki suka tafi, suna daga mata hannu itama
tana daga musu. Kasancewar ita bata da karatu a yau sai ta kama hanya cikin nutsuwa ta koma
gida.
( _Wannan shine tsarin rayuwar gidan Yaya Habibu a kullum. Duk wayewar gari kowa abinda
yake yi kenan)._
Mairo na karantar Zamantakewar Dan adam (Sociology ) a jami'ar Michigan (Michigan State
University) tun bayan dawowar ta gidan Yayanta Habibu. A yammacin ranar tana zaune a
_study-room_ da farin gilashin karatu a idanunta tana nazarin littafin 'Haralarambus and Holborn
( _Sociology_ , _Themes and Perspectives_ ) domin wani assignment (aikin gida) mai matukar
wuya da aka basu akan *hedonism* zasuyi _submitting_ a washegari.
Aunty Dina ta murda kofar ta shigo fuskarta dauke da murmushi, sassanyan kamshin ta na
turaren (yves saint laurent) shi ya fara bakuntar hancin Mairo kamar koyaushe, Dina mace ce
mai darajja kamshi a jikinta ta dade da sanin wannan. Ta ja kujerar dake fuskantar Mairon ta
zauna sannan tace "Mairo dan rakiya nake nema, London zan je gobe ko zan samu ki raka
ni?"Mairo ta shiga girgiza kai da sauri "inada aiki mai yawa a makaranta goben, kuma zanyi
submitting assignment dina, me zaki je kiyi?"
Ta ce "kallon 'film-fare award' na wannan shekarar, gara in gani _vivid_ fiyeda a talabijin
nafi gane komai. Tun wancan satin ake ta sanarwa za'ayi".
Mairo bata san kallon Indian na Aunty Dina ya kai matsayin haka ba, da zata ni ki gari
kasa-ya-kasa tun daga birnin Michigan har babban birnin Birtaniya don kawai ta ga GALA! Da
sauri tace "sai kin dawo. Ni kam, bazan samu zuwa ba".
Habibu da taya bera bari ya yankowa Dina tiket ta tashi a washegari, gidan ya saura sai su
kadai. Tun safe Mairo na makaranta tana fama da ayyukan gaban ta itada kawarta Ir'eesh
Tawheedah 'yar asalin kasar Somalia. Bata dawo gida ba sai yamma lis, ta tarar tuni Yaya
Habibu ya riga ta dawowa. Zaune suke a falon shi shida yaran suna aikin makaranta yana nuna
musu. Mairo tayi sallama ta shigo suka yi tsalle suka daneta suna yi mata "oyoyo".
Yaya Habibu ya daga ido ya kalle ta yana mamaki cikin ransa wai wannan Mairo ce, MAIRON
GURIN-GAWA, MAIRON-HURE! Abu daya ya tuno a wannsn lokacin yayi murmushi (goruba
daga kan bishiya a kauyen GURIN-GAWA) ya ce "Mairo 'yan makaranta.... Mairon Dina. ...
Mairon Yaya Habibu...!" Ta yi dariya har fararen jerarrun hakoranta suka fito. Kirarin da yake
mata kenan idan ya so nishadi. Ta wuce dakinta rungume da jakarta don ta kimtsa.
Bayan tayi sallar magriba tayi wanka ta canza kayan jikinta ta fito falon ta zauna tare dasu.
Zuwa can Yaya Habibu ya fito daga dakinsa cikin shiri, sai kamshi yake. Ga dukkan alamu cikin
sauri yake. Ya dube tayace "maza a shirya dinner, amma _African-Dish_ . Inada babban bako
anjima kadan. Babban abokina Amiru zai sauka yanzunnan daga Washington D.C zan je filin
jirgi na dauko shi". Yadda yake maganar cikin rawar jiki kadai zaka fahimci wannan bakon mai
muhimmanci ne da matsayi na musamman a gareshi. Ba tun yau ba Mairo na jin sunan Amiru
a bakin Yaya Habibu da Dina. Zata iya cewa rana bata fitowa ta fadi wani cikinsu bai ambaci
Amiru ba.
Ta amsa da ladabi "toh, sai kun iso".
Yana fita ta mike ta nufi kicin, Lynder na goge-goge ta bata hanya ta wuce, ta bude
_deep-freezer_ tana tunanin me zata dafa musu? Daga bisani zuciyarta ta tsaya akan tuwon
shinkafa miyar danyar kubewa tunda dai suna da Okora (danyar kubewar gwangwani).
Nan da nan ta dora sanwa, tayi amfani da _dried fish_ da _mushroom curry_ cikin miyar, duk
kicin din sai ya dau kamshi. Sunada zobo, don haka ta tafasa shi ta tace, ta markada abarba ta
hade da zobon da fulebo din abarba ta juye a _jug_ ta sanya a firji don ya yi dan sanyi ba
tareda ta sanya sukari ba. Ba tun yau ba ta san Yaya Habibu da son Danwanke, kai shi duk wani abinci ma na Africa to ya
bi bayan dan wake. Don haka nan da nan ta jika kanwa ta kwaba ta jejjefa cikin tafashashshen
ruwan zafi, cikin dan lokaci ta kammala komai.
******
Ta kashe wayar ba tareda ta baiwa Nabilah amsa ba. Jikinta a sanyaye matuka, maganganun
Nabilah kullum irin na Anty Dina ne, ko maiyasa? Alhalin basu san juna ba, basu taba ganin
juna ba ko a hoto, balle tace sun hada baki ne suna _sharing idea_ don su kalubalanceta!
Dai-dai lokacin taji shigowar Yaya Habibu da bakonsa. Da alama ba su biyu bane don tana jin
muryoyin maza daban daban. Ta sake kudundunewa a cikin bargonta sama-sama take jiyo
tashin muryarsu anata turanci kamar tashin duniya. Kira ya shigo wayarta, daga kwance ta mika
hannu ta amsa a kasalance.
Dina ce.
Tace "yaya kuke Mairo? _Hope_ ba matsala, ina nan tahowa gobe insha Allah, mai zan sayo
miki?"
Mairo ta ce "munyi kewarki ne kawai Anty, duk gidan ba dadi da baki. Bana bukatar komai sai
dawowar ki lafiya". "Nima haka Mairo, ji na nake kamar nayi shekara ban ganku ba. Me ya
samu wayar Habib ne? Na kasa kama shi".
Tace "yana falo, yayi baki ne".
"Su waye?"
Mairo ta ce "Na dai ji yace Amiru ne"
Dina tace "wow! Amiru yau a gidanmu? Maza kaiwa Habib wayar inason magana da shi".
Ta mike rike da wayar ta fita, shaf ta manta ko kanta bata rufe ba tsabar yadda Dina ta matsu
tayi magana da mijin nata, a haka ta isa falon. Ta karasa kusa da Habibu ta mika masa wayar.
Juyowar nan da zatayi sai idonta cikin na Amiru, wanda ke zaune gefen Habib cikin _Italian
Suit_ bakake wul, ya sassautama wuyanshi ruwan tokar _tie_ dake jikinshi. Suka samu kansu
cikin matsananciyar faduwar gaba a lokaci guda. Ga ita Mairo, kwarjini ne da kyawun Amirun ya
haifar mata da faduwar gaban. Amma ga AMIRUN, bazan iya cewa ba!
Habibu yace "Amiru *meet my beloved sister MAIRO* , da nake baka labari...".
Yana mai kokarin saita lumsassun idanunsa akan Habibun, don kawar dasu daga nacewar da
sukayi akan Mairon yace "itace Mairon??? Mairo zo mu gaisa....". Amiru dai Hausa yayi, amma
wani _accent_ ne da Mairo bata taba jin mai gardinsa cikin kunnuwanta ba. Kamar yadda bata
taba ganin mutum mai kyau da kwarjininsa ba, ilhamomin dake tare da shi bata taba haduwa da
mai irin su ba! Wannan shine AMIRUN Yaya HABIBUN???
( _The beginning of everything_ kenan)
*****
Mairo data koma daki kwanciya tayi rigingine cikin nadama. Kai tsaye ka dubi kwayar idon
mutum mai kima kamar Amiru, kace baka sonsa ai ya zama wulakanci da cin fuska. To amma
ita a ganinta daidai tayi, don bata iya karya ko yaudara ba. Amma dai duk da haka ta san bata
kyauta ba. Saidai a ganinta gara hakan, da dai tayi irin auren da zuciyarta ta raya mata akansa.
Dina tayi sallama ta shigo tana fadin "tashi, abincin da kike gudu ne na biyo ki da shi. In dai
Amiru ya dade da barin gidannan. Ta tashi ta zauna sosai ta karbi farantin ta soma ci. Dina na
kallonta, can kuma tace "Mairo me kika ce da Amiru ne? Ya shigo cikin walwalarsa, ya fita a
yanayin da bamu taba ganinsa a ciki ba. Ina laifin wanda ke son ka?". Ta cira kai daga cin abincin tamkar wadda aka katse wa gudun jini a cikin jikinta, sai kuma ta
sunkuyar. Can kuma ta dago ta dube ta tace.
"Yana magana ne kan wai yana so na, so kuma na aure, yana burin na zama uwar iyalinsa.
Nikuma na gaya masa kai tsaye cewa "bana son sa!".
Dina tayi murmushi, daga jin kalaman Mairo da yanayin maganarta kasan kuruciya na
dawainiya da ita. Cikin sanyin murya tace "sabida me ba kya son nashi Mairo? Gashi
kyakkyawa son kowa kin wanda bai samu ba, gashi da dimbin ilmi kamar Yaya Habibun da kike
cewa yana burge ki. Yanada matarshi baturiya zallah amma ya tsallakota yazo yace ke Mairo
yana son ki. Zai iya rabuwa da ita saboda ya aureki. Gashi da kirki ga addini, ke kuwa Mairo me
kike nema a da namiji da ya wuce wannan?"
Sai Mairo tasa kuka, ta kwantar da kai a cinyoyin Dina, ta shiga kuka mai tsuma zuciya.
"Na kasa mance *Uncle Junaidu* ne Anty Dina! Na kasa mance dimbin alherin da yayimin a
rayuwa. Shine tsanin duk wani matsayi da matakin dana ke kai a yau. Idan na auri wani ba shi
ba na ci amanar sa.......!"
Dina ta katseta "akwai hanyoyi da yawa da zaka sakawa mutum Alherin da yayi maka ba dole
sai ta hanyar aure ba. Misali shine ki dinga bin shi da kyakkyawar addu'a ba tareda shi din ya
sani ba. Wannan addu'ar Ubangiji yayi alkawarin karbar ta Mairo. Kada ki yi mamaki zuwa
yanzu shi Junaidun ya samu wadda yake so ya aura ya manta da ke. Ni na kasa gane kan wannan soyayya da kike yiwa Junaid maras dalili. Kin ce bai taba cewa
yana son ki ba! Kince ba kuyi alkawarin aure ba! Kince ya san gidan Baffa amma bai nemeki ba!
To Mairo gaya min wace hujja gareki da zata tabbatar da cewa yana son ki?
Bakisan akwai masu taimako sabida Allah ba? Ba don a aure su ko a saka musu da soyayya
ba? Haba Mairo, kiyi tunani mana, kiyi amfani da hankalinki, ki so mai son ki a zahiri da badini.
Kiyi aure saboda Allah da raya sunnar Ma'aiki amma ba don abinda zuciyarki ta afu a kai ba.
Ina tabbatar miki Amiru in kin nutsu, kin bude zuciyarki a hankali zaki so shi wallahi har ma
fiyeda son da kike ma Junaid. Iyakar soyayya ta gaskiya kin yiwa Junaid, ko baki aure shi ba
Allah ya shaida! Yayi alkawarin sanya masoyan gaskiya da suka mutu ba tareda sun auri juna
ba a gidan aljannah. Ina tunanin Junaid yayi abin nan ne da hausawa ke cewa ABARI YA HUCE
SHI KE KAWO DA RABON WANI!"
Ta dubi Dina da sauri har tsakiyar idanunta tace.
"Idan hakane Aunty Dina, kema kin yarda Uncle Junaid yana so na, furtawa ne baiyi ba kamar
yadda _Inna ta_ da Nabilah ke cewa???"
Gyada kai Dina ta yi. "EH, yana son ki, amma ya bari YA HUCE! Don kuwa a zahiri babu wata
mu'amala ta mutunci da tausayi tsakanin mace da namiji sai 'SOYAYYAH'. In ma mutuncin ne
da farko, to daga baya rikidewa yake ya koma soyayya. ...
Ke dinnan Mairo har wata soyayya kika sani ko halarci? Wallahi HALACCI kike yimawa ba
soyayya ba. Amirun shi kike so da gaske; na gani a kwayar idon ki, na gani a gangar jikinki.
Kina jin abubuwan da kike ji kan Amiru a Uncle Junaidun? Kina neman Junaid ya aureki ne don
ya tallafi rayuwarki a wancan lokacin da kike neman matallafi ido rufe, amma ba don kinsan
hakikanin me aure ya kunsa ba.
Mairo kinaso ki ramawa Junaid halaccin da yayi miki ne ta hanyar 'aure' don da shi kika saba,
ya sanki, kin san shi, a tunanin ki wannan shine karshen soyayya, to ba shi bane! Soyayyar
aure daban take, Allah ke hada ta, kuma bata fassaruwa.
Ita zuciya an halicce ta ne da son mai kyautata mata, wannan shine tsakaninki da Junaid ba
soyayyar aure ba! Idan kuma mata sun fara zuwa neman aure ne to sai muyi shirin tafiya Kano,
unguwar Galadanchi gidansu Uncle Junaidu, mu nemeshi mu kai kudin aure... mu gaya masa
yadda kike son shi, har kina duban tsakiyar idanun masu son ki da aure na hakika kina gaya
musu ba kya son su. ......sabida kawai kada ki ci amanar soyayyar shi da ya baki a makaranta.
......" .
Ala dole ta murmusa, ta san _zambo_ ne Dina take mata. Duka wannan bata lokacin da yawan
bakin da Dina ta share tana bayani, ba duka abinda tace ne Mairo ta yarda dasu ba.
Ta dauki Dina a matsayin mai campaign ga AMEERU! Sabida shi ta sani, shine mai irin tsarin
rayuwar su. Bata san komsi game da rayuwarta ta baya ba, batasan wanene Uncle Junaid a
rayuwarta ba. Ita kudin Yaya Habibu ma tsoro yake bata balle na Amirun da ta ji suna cewa
yana _World Bank_ karewar _Barclays_ . A karkashin inuwarsa rayuwar Habibu ta ginu
bakidayanta. Shi ya maida Yaya Habibu ko me yake a yanzu.
Ta yarda ta hakura da Uncle Junaidu sabida hujjoji kwarara da kowa yake gaya mata. Hatta
Nabilah tace da ita "lokaci yayi da zata manta da Uncle Junaidu tayi aure". Ta dubi irin auren da
ita tayi, amma daga baya ya zame mata ALHERI. Don yanzu ba abinda take so a duniya sama
da Ismael kuma shima hakan har ga albarkar haihuwa.
Ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta kwanta bayan fitar Dina. Ta ja bargo har kanta ta kudunduna.
Bacci take so ta yi amma ya ki zuwa. Al’amuran na neman tarwatsa mata kwakwalwa tareda
wargaza mata tunani bakidaya. Tana so ta yarda da Dina, halaccin dake zuciyarta na karyata
Dina. Amma abubuwan da ta zano ai duk haka suke; zata je neman auren Uncle Junaidu ne???
Ko kuwa haka zata kare a zaman jiran *tsammanin warabbuka* ???
Zata iya cigaba da zaman jiran ranar da uncle Junaid zai nemeta, ya bayyana mata
soyayyarshi, ya bata uzurin da ya hana shi yin hakan a lokacin da ya dace daga nan har gaban
abada! Amma bazata iya jure bukatar gangar jiki da zuciyarta ba irin na kowanne lafiyayyen dan
Adam. In hakane aure ya zama dole a gareta domin kare kanta daga _zina_ , da sauran
ayyukan alfasha, cikar mutunci a idon duniya da karuwar matsayi a fadar Ubangiji.
Wayarta dake karkashin filo ta soma dan kidi mai sanyi, alamar shigowar sako (text ). Cike da
mamakin wanda ya yo mata sako a daidai wannan lokacin karfe biyu na sulusin dare agogonsu
na can ta mika hannu ta lalubo wayar ta danna. Bata san lambar ba don kuwa bakuwa ce, ga
abinda ke rubuce;
".......... _When life changes, and we go our separate ways, you will still be in my heart till my
dying days...... my world has never meet a person like you!"_
(A yayin da rayuwa ta canza ni da ke muka bi hanyoyin mu mabambanta (muka rabu) zaki
cigaba da zama a xuciyata har karewar numfashi na. Duniyata bata taba haduwa da mutum irin
ki ba).
Haka ta sa sakon a gaba tana ta karantawa har akayi kiran Assalatu. Don ta tabbata ba kowa
bane; Amiru ne. Duk da bai saka suna ba ko wata alama mai nuna shi din ne. Allah sarki! Har
YA HUCE ne? Tana so ta bashi amsa bata san me zata ce masa ba.
Da safe take nunawa Dina a kitchen, ta karanta tayi dan miskilin murmushin nan nata. Tace "ke
kuma kika ce me?"
Ta zumburi baki "ni ko kula sa ma na yi?"
Dina tayi dariya tana kwaikwayon muryar ta tace "Haba Mairo! Yi hakuri ki dan kula sa. Kin ga
shi yayi fushin amma ya sauko, sabida ya fahimci Mairo ba sonsa bane bata yi, kawai ita din
mai *amana* da *rikon alkawari* ce".
Tayi murmushi har kumatunta ya lotsa. Dina kam akwai shegen wayo, kanwa ce uwar gami.
Tace.
"To me zan rubuta???"
"Ki ce kawai yazo yayi _joining_ dinmu _breakfast_ ".
Mairo ta rubuta ta tura. Amsar da ya bata ta sa ta yin murmushi, domin ya ambato
rabin ranta.
"A'ah kirawo JUNAID......"
" He's far away....!_ " (Amsar Mairo).
"And I'm not closer too.... I'm far away either, and I will not come back. On
my way