Showing 18001 words to 21000 words out of 80879 words

Chapter 7 - Inda Rai B1 True Books Available Rubutawa Aisha Aliyu Garkuwa .pdf


“In sha Allah nan kusa, mijinta da kanshi zai zo ya ɗauke, tunda naga gida ai komai yazo da
sauƙi”.
Cikin gamsuwa dottijon da sauran duk suke gyaɗa kai domin haka nan, sukeji sun aminta
dashi”.
Shi kuwa dottijon gyara zama yayi tare da cewa.
“Toh muna nan muna tsumayinku”.
Daga nan suka ɗan tattauna.
Daga bisani suka fito.
Taj dake zaune cikin motar tasu, yana mai ƙara tsare gidan su Adayan da idanun yana kallon
lungu da saƙo na sashin wurin,

Rakiya sukayi wa Abu Hashim har gindin motar, wanda basu ga Taj a cikiba kasancewar glass
ɗin motar tintek ce.

Ma'aruf ne da kanshi ya buɗe mushi marfin gaba, da sauri ya shiga tare da cewa.
“Toh sai kunjini”.
Fatan sauƙa lfy sukayi mushi.
Tare da raka motar tashi da idanun, har ya ɓacewa ganinsu kana suka koma cikin gida.

Taj kuwa har yanzu wayarsa, na maƙele a kafaɗarsa, domin bai katse kiransa da Ishmah ba.

“Uhmmmmm”. Ya sauƙe numfashi, jin tana cewa.
“Taj kayi mgna mana, Please kayi mgna menene matsalarka?”.
Cikin ƙarfin hali ya buɗa lips inshi a hankali, kana ya haɗesu tare da rumtse idanunsa murya
can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Ishmah! Meke faruwa dani ne? Wai me nayi ne? Me zan cewa Ummeyna, Ishmah Yah Abana
bazai ɗauki wannan wargin bafa”.
Cikin ɗaurewar kai ita kanta take nazartar kalamansa.
Wanda kamata yayi suyi wannan tunanin kafin mai abkuwa ta abku, domin wannan ya zama
tamkar hikaya, ko mafarki mara tushe cike da kullewan kai tace.
“In sha Allah, komai zai zo da sauki Malam zai fahumceka, Ummeey zata zame maka hasken
da zai gamsar da malam, Please ka kwantar da hankalin ka kaji Bestie”.
Ta kiranshi da sunan da tasan, in ta gaya mishi yake rufeta da faɗa dan ya tsami sunan, ita
kuwa so take yayi faɗan ko zaiji sassaucin damuwar da ta fahimci tayi silar shigarsa ciki, domin
tafi kowa sanin zurfin cikinsa.
Shi kuwa Taj cikin rumtse idanunsa yace.
“Sai anji ma”.
Yana faɗin haka ya katse kiran.
Ido ta zubawa wayar kamar ta samu, abin kallo a jiki.

Shi kuwa Taj murya a ɗimauce yace.
“Abu Hashim gida zamu wuce”.
Yayi mgnar da yaƙinin yasan zuwa yanzu Mahaifinsa da yayunsa maza, duk sun koma gida.

Cikin girmamawa Abu Hashim ya amsa mishi, kana ya ɗauki hanyar gida.

Cikin kulawa Abu Hashim yayi parking a farfarjiyar wani, ƙaton gida da yafi kama da fada,
Sai dai ba fadan bane, kawai tsarin gininne alfarmar wanda kallo ɗaya zakayiwa gidan ka gane
cewa.
Babban gidane na babban mutum mai tarin zuriya, ƴaƴa da jikoki.

Da sauri Abu Hashim ɗin ya fito tare da buɗewa Taj marfin motar.
Cikin mutuwar jiki ya ziro ƙafarsa waje, ba tare da ya miƙe tsayeba, ya kamo hannun Abu
Hashim, wanda hakan yasa ya sunkuyo, cikin sanyi murya yace.
“Afwan Abu Hashim, duk da nasan kai mutum ne mai amana da riƙe sirri. Amman zan kuma
roƙonka da girman zatin Allah wannan al'amari ya zama sirri dagani sai kai, sai Allah, Please
kada ka gayawa kowa, har sai na samu mafita”.
Cikin bayyana cikar amana da sirrantaka Abu Hashim yace.
“Nayi maka al'ƙwarin duk duniya babu maijin wannan mgnar a bakina, in sha Allah”.
Cikin gamsuwa ya miƙe tsaye, tare da nufar asalin cikin gidan.

Cike da girmamawa Mai aikata gidan duk suka nufo garesu.
Driver Malam ne ya amshi jakar dake hannun Abu Hashim tare da cewa Taj.
“Barka da isowa Abban Abba”.

Cikin ƙirƙiro murmushi dole ya kallesu tare da amsa gaisuwar da suke masa.

Tafiya mai ɗan tsawo sukayi kana suka, isa tsakiyar gidan,
Da gefen hagu da dama suke ɗauke da tsala-tsalan part guda bibbiyu komai nasu, iri ɗaya
wanda 3-3 bedroom ne sai 2 Parlour, and dinning area, sai kitchen, kana da sito,

Sai kuma wani babban part da yake tsakiyarsu yana fuskantar alƙibla wanda shima 3 bedroom
ne, sai kuma Parlour manya guda uku, sai ta bayan shi dake shimfi da wani ni'imtaccen gardin
wanda yake ɗauke da nau'wukan itatuwan kala daban da ban, sai kuma wani ƙaton Parlour da
yafi kama da holl wanda aka ƙawatashi da kayan ƙawa na alfarmar kuma shine falon forko.
Sai kuma can bakin gate da ɗauke da BQ babba 2 bedroom sai babban falo, sai kuma sashin
ma'aikata.

Suna isa tsakiyar harabar cikin gidan wasu ƴan dugui-dugui ɗin yara suka fito daga part ɗin
dake kusa dashi wanda, suke gab da bakin ƙofar sai, cikin tsananin jin daɗi babbar cikinsu da
bazata gaza shekaru takwas ba, ta buɗe murya da iyakar ƙarfinta tare da faɗin.
“Oyoyo Uncle Afif”.
Ta ƙarashe kiran sunansa da masifar ƙarfi tare da nufarsa da gudu.

Cikin abinda bai gaza one minute ba, sai ga yara na fitowa ta ko wanne part a ƙalla sun kusan
goma, gaba ɗaya sun ruɗa gidan da kiraye-karayen sunan.
“Oyoyo Uncle Afif.”

Cikin jin farin cikin ganin yaran ya ɗan rusuna ƙasa, tare da ware hannayensa.
Kamar tattabaru haka duk sukazo sukayi mushi zobe,
Yarane masu shiga rai da samar da farin ciki.

Murmushi Ummeey dake cikin kitchen dinta ita da babbar ƴarta Maryam.
Cikin tsananin jin daɗi tace.
“Alhamdulillah Babana ya iso”.
Cikin Murmushin Maryam tace.
“Bari in tafi nasan wurin Malam zai wuce.
Rashida ce wacce ita ke bin maryam ta shigo yayin da Halima ke biye da ita a baya, wacce ita
Taj ke bi.
Cikin murmushi da bayyanenne jin daɗi tace.
“Ummeyy albishir.
Cikin murmushi tace.
“Naji ai yadda ƴaƴanku suka cika gidan da ihun Uncle Afif ya iso”.
Da sauri Zakeeya ƙanwar Taj mai binshi duk da tsakaninsu kusan shekaru goma ne, kana itace
ƴar autar Ummeey, shigo kitchen ɗin fridge ta buɗe tare da ɗaukan Apple, Grapes, cherry,
strawberry. ta ɗaurayesu tare da goran ruwa mai sanyi tana fita tace.
“Ummeey Uncle Afif fa ya iso”.

Da yake itama haka take kiranshi.
Kusan a tare ita dasu Rashida duk suka fito.

Shi kuwa Taj tuni ya ya shiga Parlour Malam tare da zugan ƴaƴan yayunshi da kuma ƙannensa.

Suna shiga Parlour, Malam ya saki wani irin murmushin dake bayyana tsananin so da ƙaunar
da yake yiwa Taj ɗin.

Shi kuwa Taj cikin sauri ya dire wata yar kekkyawar baby da bazata gaza shara ɗaya ba, ɗiyar
Yah Hafiz ce.

Yana ajiyeta, kuwa ta saki ihu, haka yasa yayi saurin ɗaukarta,
Tare da ruggume Yah Hafiz ɗin.
Wanda shine babban ƙab gidan nasu, sai Kuma Yah Sulaiman da Yah Yusuf suka ruggumeshi a
tare.

Suna mai ɗan bubbuga kafa ɗarsa, tare da sumbatar gefen kuncinsa.
Shi kuwa murmushi dake bayyana irin tsananin yadda yake son ƴan uwan nasa yayi tare, da
juyowa ya nufi Malam.

Hannun Mahaifin nasu ya buɗe mishi alamun yazo.
Da sassarfa ya ƙarasa gabanshi tare da durƙusawa bisa guiwowinshi.
Haka ya basu damar ruggume juna, hannunshi yasa ya tallabo fuskantar Taj da farin cikin
ganinsu yasa ya fara mance kitimurmurar daya haɗawa kanshi.

Sassayan sumbata ya direwa Taj ɗin a tsakiyar goshinsa, kana ya daura hannunta tsakiyar
kansa tare da cewa.
“Marhababuka Yah Abana Barka da isowa lfy Allah ya Ubangijin yayi maka albarka”.
Cikin tsananin jin daɗi ya ɗaura hannunsa bisa hannun mahaifin nasu tare da cewa.
“Amin ya Allah.
Yah Abana ya ƙafa?”.
Ya ƙare maganar yana kallon Yah Abduraham dake ta murmushi, sai kuma ya maida kallonsa
kan Yah Aryan dake yiwa mahaifin nasu masaj.

Sai kuma ya juyo ya kalli Yah Aryan ɗin dake zaune gefe, yanayi mishi wani kallon dake cike da
kishin irin tsananin son da mahaifinsu ke nunawa Taj ɗin.
Sai kuma ya kalli Kabber wanda shine yaro na miji ƙarami a gidan nasu baki ɗaya.
Shi kuwa Kabbir janye jikinsa ya ɗan tare da matsawa gefe.
Da sauri Malam ya rike hannunsa tare da cewa.
“A'a Kabir ina zaka je zauna nan kusa dani”.
Ya ƙare maganar dayi musu murmushi dake nuna sonsu a ranshi dan baya ƙaunar su zargi
cewa, yafi son wani a cikinsu.
Hakan kuma yasa Kabir ɗin jin daɗi sai ya koma ya zauna a inda yake, shi kuwa Malam sai ya

jawo hannun Taj ya ajiyeshi a gefen damansa.

Maganar zuci Aryan ya fara yi.
“Uhmmm ai dole dama shi Taj a gefen damanka zaka ajiyeshi, Kabir da shine ƙaramima kullum
a gefen hagu kake ajiyeshi”.
Yayi kalam cike da kishi.

Shi kuwa Taj cike murmushi ya ɗago hannunsa tare da yafito yaran.
Ɗuuu haka duk sukazo gabansu suka zauna.
Mahira ɗiyar Yah Yusuf da kuma Iman ɗiyar Yah Hafiz ya ɗaura bisa cibiyoyinsa.
Sai kuma ya jawo Islam ɗan yayarsa Maryam gabanshi.

Yayinda saura kuma duk ya ajiyesu a ganshi.

Dai-dai lokacin kuma Zakiya ta shigo da sallama Rashida da Maryam na biye da ita a baya.
Rusunawa sukayi suka gaida mahaifin nasu da yayunsu. Kana Aryan da Kabeer suka gaida
Rashida da Maryam dan sune manya a kansu.
Gefenshi suka je suka zauna.
Da sauri ya sa hannunsa ya amshi Trayn dake ɗauke da plates ɗin dake cike da fruit.

Inabin ya fara sinka yana danƙawa yaran ɗaya bayan ɗaya,
Tare da kallon Zakiya cikin sanyisa yace.
Akwai jakar tsarabarsu, tana hannun Baba Abu Hashim, kije ki kwance kowa da sunansa a jikin
nasa, ki basu, akwai kuma Chocolates insu, yana mota kije ki dauko duk ki basu”.
To tace tare dasa hannun ta dauki Mahira da Iman.
Haba su kuwa ƴan manyan jin haka keda wuya, duk sukayi ɗuuu suka bi bayan Zakiya suna
faɗin.
“Aunty Zakiya a fara ɗauko mama Chocolate ɗin”.

Daga nan duk suka fice.
Kusan duk Parlour da ido da murmushin suka rakasu.

Shi kuwa Taj gyara zamansa yayi tare da kamo ƙafar Malam ɗin cikin sanyin sauti da halinsa
yace.
“Yah Aryan bari in karɓeka tausar nima in samu ladan”.
Murmushi duk sukayi, shi kuwa Taj kafar mahaifin nasu ya daura bisa cinyarsa ya fara yi mushi
tausa mai cike da iyawa a matsayinsa na likita.

Sai kuma ya kalli Maryam dake cewa.
“Ba abinda kacifa”.
Sai kuma suka kalli Rashida da tayi saurin miƙewa tare da cewa.
“Yauwa kin tuna min na, dama yau nace in sha Allah abincina Malam zai faraci”.
Da sauri kuma suka kalli ƙofar shigowa jin muryar babbar yayarsu mai bin Yah Yusuf tana cewa.

“Ai kuwa bamu yardaba”.
Su dai sai murmushi suke haka ƴaƴan Malam matan da suke cikin Ƙasar Ethiopia a birnin Addis
Ababa suka rinƙa shiga wanda yayanshi mata 13 ne cib maza kuma 7. Haka yasa yaranshi 20
ne cib.

Sai kuma mata shi Huɗu, Hajia Halisa itace babba uwar Hafiz, sulaiman, Sai kuma Anty Khaulat
sai autarta Hajara, sai kuma Hajia Sumayya itace mahaifiyar Yusuf da Aunty Ni'imatullah da da
Aryan da Abdurahan.
Sai kuma Hajia Muhibbat.
Uwar Salma, Madina, Ruƙayya, sai Kabir, da , sai kuma Amal,
Su ukun nada yaya 15 sai kuma Ummeey dake da biyar, Maryam, Rashida, Halima, Taj,
Zakiya.
Sune 20 cib.

A irin ya wannan rana yakance da matansa, yau ranar ƴaranshi ne dan haka kada su matsa
mishi.
Dan duk ranar jumma'a ta ƙarshen wata duk ƴaƴanshi a tare suke wuni.

Da sauri Rashida ta dauko womers ɗin ta da tazo dasu daga gidanta. Kana ta dawo gaban
mahaifin nasu ta zauna tare da zuba mishi abinci.
Halima da yanzu ta shigo hannun rike da womers ce tai ɗan murmushi tare da cewa.
“Allah sarki gida daɗi, kunkam da kuke aure a garina kunji daɗi ai, irina dasu Aunty Ni'imatullah
da Madina kam sai in munxo muke samun wannan ladan, dan haka tun da kan su tafi masallaci
nayiwa Malam abinda zaici don nima in samu ladan. Yau dai kuyi haƙuri ku bari yaci nawa”.
Murmushi mai cike da farin ciki malam keyi. Tare da kallon ahlin nashi, cikin fara'a Aunty
Khaulat tace.
“Gsky fa haka ne Halima to mun haƙura”.
Da sauri Maryam tace.
“Laah Aunty Khaulat ai wayo take mana, muda muke garin ai iya jumma'a jumma'a ne shima sai
na ƙarshen wata kaɗai muke samu yaci girkinmu, sufa ƴan nesan nan in sunzo har su koma
sukeyi masa girki.
Irin Halima gata nan har shara side dinsa in dai tazo ita keyi mishi mu muna samun wannan
damar ne”.
Dariya sukayi duka sai kuma suka kalli Amal dake shiga tana cewa.
“Kum tsaya mujadala gashi Aunty Rashida ta riga ta samu shi”.

Ita kuwa Rashida murmushi tayi cikin jin daɗi kasancewar mace mai fara'a yasa Malam kan
sake mata fuska sosai, cikin Murmushin ta mika mishi plate ɗin gashin da yaji Vegetables, da
sauri Yah Yusuf ya amsa tare da ajiye mishi a gabanshi, Amal kuma Fruit ta ajiye.
Mishi Aumty Khaulat kuwa sauran tarin womers ɗin dake kan Dinnin table nashi tasa su Halima
da da Maryam suka jido da tarin plates and spoon's da fork.
Nan duk ta zubawa, kowa.

Hafiz ne ya kalli Taj dake tayiwa maifin nasu, tausa a ƙafarsa dake kusa dashi yana ɗan jan
yatsun ƙafar, bisa dukkan alamu, yayi nisa a cikin tunani, domin ana ta mishi mgna yaci abincin
Amman bai tan kana.

Shi kuwa gaba ɗaya tunaninsa ya koma kan wancan al'amarin da ya faru tsakininsa da wacce
tsohon nan ya buwaye su da kiran sunanta Adaya.

Allah ya sani yana jin yunwa to Amman ina bazai iya cikin komai ba, domin cikinsa ya cika tib
da ruɗani.

“Afif me ke damunka”.
Yah Yusuf ya tambaya cikin kulawa, eh dama Taj ba surutaccen bane kuma baisan kwaramniya
Amman yanayinsa na yau ya nuna akwai wani abu tare dashi sai dai zurfin cikinsa ne bazai bari
a gane damuwa bace.

Cikin sauƙe nannauyan numfashi ya miƙe tare da cewa.
“Bari inje inga Ummeey na”.

Cikin kulawa Yah Hazif yace.
“Ka zauba muci abinci tu...”
Sai kuma yayi shiru ganin Mahaifinsu ya ɗaga mishi hannu alamun ya barshi, sai kuma yayi
mishi nuni da hanya alamun yaje.

Shi kuwa Taj ganin haka yasa ya fita, kai tsaye part ɗin Ummeynshi ya nufa.

A Parlour kuwa cikin Rahama Amal tace.
“Ke ma dai Aunty Maryam mutun da amaryarsa, kika san me ta shirya mishi, zaki wani da
mashu da abinci kisa yaci ya koma ya kasa cin nata, kin kuma san Meymey da taɓara.”
Kai Maryam ta jinjina ba tare da tace komai ba, sai mgnar zuci da tayi.
“Uhmmmm Meymey ai ba irin wannan matar bane”.

A can Parlour Ummeey kuwa zaune yake gabanta bisa kan Turkey carpet.
Yayinda kanshi ke kife bisa guiwowinta, cikin kulawa da so tace.
“Afif meke dumunka?”.
Yah Salam wannan tambayar da sukeyi kishi tana kara ɗugunzuma nitsuwarsa, suna tuno mishi
abinda ya faru.

Ita kuwa Ummeeyshi ganin yadda jikinshi yake a mace ga idanunsa da su ɗanyi ja ga alamun
rashin nitsuwa, sai tayi tunanin ko begen matarsane, haka yasa cikin kulawa tace.
“Toh yanzu dai tashi ka tafi gidanka.
Ka dawo gobe muyi hira”.

Yes Allah ya sani so yake ya kaɗaice, ko zai samu damar da zai yi nazari.

Hakan ne yasashi ɗago kanshi a hankali.
Ido Ummeynshi ta zuba mishi tana nazartar yanayin tashin hankali da ɗimuwar dake cikin eyes
ɗinshi.
Ta sani bazai faɗa komai ba saboda tafi kowa sanin tsananin zurfin cikin ɗan nata.
“Babana meke faruwa ne ka gaya min mana”…
Cike da juriya ya ƙaƙalo murmushi dole wai dan ya kwantar mata da hankali cikin sanyi yace.
“Ummey na ba komai fa kwai gajiyace”.
Kai ta jinjina tare da ɗago hannunsa kana tace.
“Toh muje ka gaisa dasu Hajia Babba sai ka wuce gidanka ka samu ka huta”.
Ba musu ya bita a baya suka shiga sashin matan baban nashi sai dai basa ciki alamun sun tafi
wurin Malam haka yasa suka wuce can.
Bayan ya gaida su ne yayi musu sallama.
Kana Ummeey da da yayunshi Rashida da Maryam da Aumty Khaulat suka rakashi.

A bakin motar suka tsaya suna ɗan hira saboda, hango Abu Hashim dasu Baba Idi suna cin
abinci.
Shi yasa suka ɗan zauna suka jirasu.

Suna gamawa Abu Hashim yazo.
Kana su Ummeey suka koma ciki.

Motarsu na gab da fita motar Uncle Jibirin na shigowa.
Haka yasa Taj cewa.
“Abu Hashim tsaya”.
To yace kana ya tsaya shi kuwa da sauri ya fito tare da nufar motar Uncle Jibirin da tuni sunyi
parking har driver'nsa ya buɗe masa ƙofa ya fito, Dottijon ne da bazai gaza Malam ba.
Cikin tsananin sakin fuska ya nufi Taj yayinda shima Taj shi ya nufa.
Rusunawa yayi ya gaidashi.
Ya amsa a mutumce kana ya ɗaura da cewa.
“Amman Mamana bata san ka dawo bako Taj, dan yanzu haka can gidan naka na fito bata gaya
min cewa ka dawoba”.
Kai ya ɗan rusunar tare da cewa.
“Ai isowata kenan. Ko Malam bai san zan dawoba ganina kwai sukayi, yanzu zan wuce gidan”.
Motsawa Uncle Jibirin ɗin yayi tare da ɗan bubbuga kafaɗarsa kaɗan kana yace.
“Toh aje a huta”.
Daga nan shi yayi cikin gida, shi kuwa Taj ya koma cikin mota suka nufi gidansa da ba wani nisa
sosai dan kusan sashin layin wurin duk su ya sune, gidan babansu suka sa a tsakiya duk su
mazan gidajensu na zagaye da na babanne”.


Uncle Jibirin, aminine ga Malam wanda duk wanda yasan Malam a Ethiopia ya sanshi ne da
Jibirin, bashi da kowa a duniya da ya aminta dashi sama da Jibirin bashi da abokin shawara a

duniya sama da Jibirin.
Shine iya kar wanda Ƴayansa kab suka sani wai wani na jikin mahaifin nasu, basu san kowa
nashi a duniya ba.
Sai Uncle Jibirin, shine madadin Babpansu kakansu kakarsu. Wanda sunayensu kadai suka
sani, wanda Taj yaci sunan kakansu na mijin.
Halima kuma taci sunan kakarsu macen.

Wannan yasa komai na abinda ya shafi aure Uncle Jibirin keyi musu da kuma Sheykh Adam
wanda shine kuma amini na biyu a wurin Malam kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login