Showing 9001 words to 12000 words out of 80879 words

Chapter 4 - Inda Rai B1 True Books Available Rubutawa Aisha Aliyu Garkuwa .pdf

haɗa da cewa.
“Wannan ku ajiye ne, Amman na sayayyar da zakuyi, in kun gama kawai kuyi min mgn”.
Cikin jin daɗi Maryam da Aysha sukayi ta godiya tare da yimishi addu'a.

Da sauri Aysha ta maida hankalinta kan wayar jin, an amsa kira na huɗu data sakeyi.
A takaice yace.
“Kina ina?”.
Da sauri ta ɗago kanta ta kalli rubutun gaban saman wurin tace.
“For naw dai Ina Riyal Abaya shop, kaifa kana ina?”.
Yana mai dudduba jallabiboyin dake gabansa yace.
“Oriental Abaya House”.
Jin haka yasa tayi sauri ta kalli Uncle Ali tare da cewa.
“Ayyah Uncle dan Allah ta ina Oriental Abaya House yake”.
Kai ya dan juyo ya kalleta tare da cewa.
“Can kuke son zuwa ne”.
Da sauri tace.
“Eh Uncle dan zan amshi wayata ne a wurin wani yace min yana can”.
Kai ya gyaɗa kana yacewa.
Driver su tafi can.
Ita kuwa Aysha da sauri tacewa Taj cewa, gata nan zuwa yanzu ya jirata, toh kawai yace tare da
katse kiran.

Tafiya kaɗan sukayi suka isa bakin shop ɗin da yaci uban wancan da girma da cika da
ƙasaitattun kaya harma da tsaruwan wajen.

Cikin kulawa Uncle Ali ya kallesu bayan sun fita yace.
“Ku kulafa, kada ku tsaya har ku rasa jam'in sallan azahar.
Kada ku tsaya sayyaya ku mance Ibadar data kawomu.
Ni zan wuce, dan zamuyi gaba dan duba ingancin tantunan mu na wurin arfa”.
Cikin girmamawa sukayi mishi godiya kana mota taja ta tafi.
Da ido suka rakashi suna jujjuya kuɗaɗen da ya basu suna kiyastasu da kuɗinmu na nan gida
Nigeria ya kai kimanin Naira dubu ɗari da ashirin da biyar biyar harda burbushi canji.
Ga kuma cewa da yayi su ɗau duk abinda suke so zai turo Usman.

“Bismillah mu shiga, dan nasan Yah Usman yanzu zai fara ƙorafin lokacin salla yayi bazai
zoba”.
Garkuwa ta faɗi haka tana gaba, suna biye da ita Maryam tace.
“Waye Usman ɗin kuma?”.
Suna shiga cikin wurin Garkuwa tace.
“Yayana ne, kuma shine PA ɗin Uncle Ali”.
Kai suka jinjina kana suka ƙarasa kutsawa cikin shop ɗin.

Suna tafe suna dubu tsala-tsalan Abayoyi na alfarmar waɗanda suke da farashi na musamman.
Cikin yabawa Aysha ta kai hannunta kan wata Black blue ɗin Abaya da ta amsa sunanta, tace.
“Wow Masha Allah, kinga wannan Abayar”.
Jinjina kai Maryam tayi tare da cewa.

“Kai tayi kam sai tsada kalli kuɗinta fa, in an juya da kuɗinmu kusan dubu dari uku da hamsin
nefa”.
Cikin kula Garkuwa tace.
“Laa ba matsala wlh, ku ɗauka, kema Maryam in kinga kalar da tayi miki ki, ɗauka.”
Cike da poolaku Aysha tace.
“Kai Garkuwa haba, ai sai kuma abin yayi yawa, ai akwai kuɗi a hannunmu, kin manta jiyama
Barrister ya bamu kuɗi ai wannan sai musa Uncle Ali ya samu matsala a kan kujerarsa”.
Da sauri tace.
“Wlh da kuɗinsa halal ɗinsa ne zai mana hidima ba da kuɗin ƙungiya ba, kada kuji komai ai shi
yace mu ɗauka”.
Haka dai tai ta basu baki har suka ɗauka kana suka fara duba Vails kuma.
Sai kuma gefen bags da takalma.
da sauri Aysha ta zaro wayarta jin, tana ringing.
Tana amsa kiran taji yana cewa.
“Please dan Allah kefa nake jira, na gaji da zaman wurin ga lokacin salla na ƙara towa,
kizooohhh”.
Wani irin yam taji saboda yadda ya ƙarashe mgnar da wata iriyar gajiyeyyiyar murya kana
kasalalelliya”.
Murya a tausashe tace.
“Ta wanne side ɗin kake”.
A takaice yace.
“Side ɗin Dubai jallabiya na maza”.
Jin haka ne yasa taja hannun Garkuwa Da Maryam suka nufi can.
Tare da ce mishi.
“Gamu nan ma kusa da wurin”.

Shi kuwa a hankali ya zaro ɗaya wayar tashi ya amsa kiran da kakarsa Addawa keyi mishi.
“Tajuddeen wai ina kake ne mun gamafa kai muke jira.”
Cikin sanyin Muryasa yace.
“Afwan Addawa gani nan zuwa ina duba wata jallabiya ne”.
Kai ta jinjina kana ta fara nufo inda take zaton nan yake dan ta lura in ba ta jawoshi ba fitowa
zaiyiba, ta rasa menene ya tsai dashi.

Maryam ce a gaba sai kuma Aysha yayinda Garkuwa ke baya,
Kusurwowin ciki, Aysha da Maryam suka fara lelleƙawa.
Da sauri Aysha ta juyo jin Maryam na cewa.
“Aunty Aysha gashi nan”.
A tare Aysha da Garkuwa suka nufi inda yake, tsaye wani daga cikin ma'aikatan wurin biye
dashi a gefe yana tura cart da ya zuba abubuwan da ya tsitstsinta.

Kasan cewar yana fuskantar ta inda Aysha ta shigone, yasa sukayi ido cikin ido.
Wani irin ɓoyeyyen numfashi mai sanyi ya fesar tare da ɗan buɗe lips inshi kaɗan.
Kana ya ƙanƙamce amintattun idanunsa, tare da ɗan kawar da fuskarsh gefe, kamar ba ita yake

kalloba, sai kuma yayi ƙasa da kwayar idanunsu, daga kan rumfar sawunta ya fara bi, da kallon
dake da ɓoyeyyen manufar da yake tuhuma da neman dalilin daya watsa mishi nitsuwarshi a
darare biyu da suka shuɗe.

Ita kuwa Aysha bisa takunta mai cike da nutsuwa take tafiya.

Ba tare da ya ɗauke idanunsa daga kantaba ya amsa gairsuwar da Maryam keyi mishi, kana ya
gaida Garkuwa.
Dai-dai lokacin kuma Aysha ta iso gabansa. Nannauyan ajiyan zuciya ya ɓoye cikin ƙahon
zuciyarsa tare da sauƙeshi a hankali, kana ya fara ware idanunsa tare da yin sama dasu, har
zuwa kan 0 face ɗinta da ya fito ras cikin tarhan da tayi.
A hankali ya lumshe idanunsa kana ya buɗe su a hankali jin, tana ce mishi.
“Sunana Aysha Abdullahi Matawalle”.
Kai ya jinjina tare da maimaita sunan a ranshi a fili kuwa a hankali yace.
“Afif Muhammad Taj”. Sai kuma ya ɗan kalli gefen hagunshi da wannan ma'akacin yake, tsuke
fuska yayi cike da wani irin ɓoyeyyen yanayi yayi mishi nuni da ya wuce gaba yana zuwa.
Da sauri Balaraben ya ɗan rusunar da kanshi kana ya ɗan raɓa gefen Aysha ya ɗan yi gaba
kaɗan.
Garkuwa da Maryam jallabiyoyi suka fara ɗan tsitstsinta ba tare da sun matsa daga wurin ba.

A hankali murya can ƙasan maƙoshinsa tamkar mai raɗa yace.
“Yah jiki basu sake tashi ba ko?”.
Ido ta ɗan jujjuya tare da cewa.
“Nifa lafiyata Lau, kawai tsoro naji”.
Ɗan ware idanunsa yayi alamar kin tabbatar?
Da sauri tace.
“Wallahi kuwa ni fa banda aljanu”.
Kanshi ya ɗan jujjuya tare da zira hannun sa, cikin aljuhun jallabiyar tasa.
Ita kuwa a hankali ta fara taku tare da ƙara matso inda yake, wayarsa ta miƙa kishi tare da
cewa.
“Ga wayarka, bani tawa!”.
Hannunshi na dama yasa ya amshi wayar tare da zurawa a aljihunsa na dama.
Har lau kuma idanunsa na kan fuskarta,
Sai kuma ya ɗan matsa saboda wasu matasan India da suka zo wucewa ta gefensu.
Sai kuma aka fara kallon kallo, domin su matasan sun shagala da kallon Aysha musamman
yadda take ta moi-moi da bakinta tana mgna ƙasa-ƙasa da fillanci.
“Haka kawai dan na tsorata a jirgi, sai ka liƙamin aljanu to ni dai Allah ya sani bani da aljanu,
masu shima Allah ya rabasu dashi, ni kuma Allah ya ƙareni da wannan fatan naka”.
Sai kuma ta juya ta kalli gefentan saboda ganin yadda ya tsuke fuska yayi kici-kici, ganin
samarin nanne na gefentan dake kallonta yakeyiwa wani irin hantarerren kallon da dole yasa
suka wuce.
Sai kuma tayi saurin yin baya kaɗan ganin yana raɓawa gefentan zai wuce sanda yazo dai-dai
da itane kuma a hankali yace.

“Ni ba fata nake mikiba”.
Ya bata amsar da fillancin Ethiopia wanda ta ɗan fahimci abinda ya faɗa, sai dai kuma ta cika
da mamakin jin yana fillancin.
Shi kuwa a hankali ya tsaya
Dai-dai wurin Cart ɗin kayanshi da Balaraben nan ke tsaye, hannunshi ya sanya a ciki ya ɗauko
ƴan wasu abubuwa baƙaƙe masu taushi,
Gabanta ya dawo ya ɗan tsaya, saboda ta juyo ganin kamar zai tafi kuma bai bata wayartaba.
Ɗaya daga cikin abubuwan daya ɗaukon ya miƙa mata tare da cewa.
“Kisa wannan, ki kuma kiyaye hukunci sheriya ki daina fita haka”.
Cikin rashin fahimta tasa hannun ta amshi ɗaya, ga mamakinta Niƙab ne, ganin hakane yasa ta
fahimci manufarsa.

Wareshi tayi tare da kaishi kan fuskarta, kana tasa hannun ta ta baya ta ɗaurashi.
Shi kuwa hannunsa ya harɗe a ƙirji tare da jingina da jikin kantar yayi irin tsayuwar nan ta gefe
ɗaya, ya zura mata idanunsu.
Kasancewar bata iya ɗaurawa ba yasa ya ɗan karkace, hakanne yasashi, ɗagowa daga jinginar
da yayi tare da matsota kana yasa hannun dai-dai saman hancinta, ƴan tsunsa biyu yasa ya
ɗan kamo ɗan saman niƙab ɗin, bai bari ko farcensa ya taba fatartaba.
Dai-dai lokacin kuma Maryam da Garkuwa suka juyo kansu a tare.
Cikin nazartar yanayin Garkuwa ta zuba musu ido tana nazartan su.
Maryam kuwa cikin sauri tace.
“Aunty Aysha Yah Barrister nefa, ya kira wai in baki, waya zai tambayeki wacce iriyar waya
kikeso ya saya Miki.
Toh Amman nace, mishi ai mun gane wacce ta ɓatanma, gashi har munzo amsarta”.
Ta ƙarashe mgnar tana kallon Taj da yake miƙa wa Aysha sauran niƙab ɗin.
Sai kuma ya kauda kanshi gefe ganin, kallon da Maryam ɗin keyi masa.

Ita kuwa Aysha numfashi ta fesar tare da cewa.
“Nifa abunan ɗauke min numfashi yakeyi”.
Yana mai miƙo mata wayarta yace.
“Idan kin saba zaki daina ji”.
kai ta gyaɗa mishi tare da amsar wayar.
Sai kuma ya juyo da sauri jin muryar Addawa na cewa.
“Tajuddeen!”.
Sai kuma ta zuba mishi ido dake nuna mgnar zuci da takeyi.
Ikon Allah Tajuddeen yau kuma, kaine a gaban mace, har kana gyara mata niƙab.
A zahiri kuwa sai cewa tayi.
“Wannan ƴar wacce ƙasace? Kuma me sunanki?”.
Cikin Murmushin Aysha tace.
“Suna Aysha Nigeria ce ƙasata”.
Kai ta jinjina tare da amsa gaisuwar su Maryam.
Shi kuwa Taj ido ya ɗan tsurawa Aysha jin tana cewa.
“Dan Allah ya akayi kake iya buɗe wayata”.

Kanshi ya ɗan kauda daga kallon ƙwayar idanunta kana yace.
“Da fingerprints nake buɗeshi”.
Fuska cike da mamaki tace.
“Toh ya za'ayi finger ɗinka ta iya buɗe wayar tunda dai da iya finger ɗina kawai na sai tashi”.
Cike da kamala da kwarjini da sanyinsa na nutsuwa yace.
“Toh nima ban san ya akayi hakaba”.
Da sauri ta jujjuya wayar tata, tare da matsa gefe, haskenta ya ɗauke, ta kuma shiga key, miƙa
kishi tayi tare da cewa.
“Dan Allah sa mu gani.”
Kai ya ɗan juya tare da danna kan babbar yatsarsa.
Ga mamakinta sai gashi ya buɗu.
Da sauri tace.
“Ikon Allah ya buɗufa”.
Sai kuma tayi sauri ta shiga Settings, ta sake dubawa da kyau yatsa ɗaya ce, sake canza yatsar
tayi tasa ta hagu, kana ta miƙa mishi tare da cewa.
“Please sa mu gani dan Allah”.
Manna yatsar yayi amman sai bai buɗuba.
da sauri ta kalleshi lokacin da taga yasa yatsarsa ta hagu saiga waya kam ta buɗu.
“Ikon Allah kenan zanen yatsunku iri ɗaya ne?”.
Cewar Garkuwa.
Maryam kuwa da sauri tace.
“Haka dai na fahimta, Amman abinda bada mamaki kam.
Kanshi ya ɗan jinjina tare da miƙa mata wayar sabodo Addawa datasa hannun ta kamo
hannunsa tana tafiya.
Ba musu ya bita saboda ganin ma'aikatan wurin nata firfita dan lokaci salla ya ƙarato.
Sauri-sauri gudu-gudu suka zo wurin biya.

Koda aka haɗa lissafi Garkuwa na saurin kiran Yah Usman.
Ɗaya daga cikin ma'aikatan yace musu.
Taj ya biya musu ai.
Ya ƙare fadar hakan da miƙawa Aysha wata jaka mai kyau, tare da ce mata Taj ne yace a bata.
Ikon Allah gashi tuni shi ya fita, basuma sameshi a wurinba, bare suyi mishi godiya.

Suna cikin haka Yah Usman ya iso, da mota da driver nan suka kwashi duk kayan da suka
saya.

Da gudu-gudu suka shiga gida ruwa suka ɗan watsa tare da yin al'wala hakama Yah Usman da
driver.
Daga nan kuma suka taho harami ya Usman na bin Aysha da kallon da yasa ƙanwarsa fahimtar
ya ƙyasa ne.

Alhamdulillah anyi arfa lfy, aikin mahajjatan ya cika, sai waɗanda suka fara sauƙa Makka ne

suke da sauran ziyara Madina birnin ma'aiki. (S.A.W) haka dai akayi ta gudanar da aikin wanda
zuwa yanzu har mahajjatan ko wacce ƙasa da suka fara zuwa sun fara komawa.

Alhamdulillah su Aysha ma duk sun gama ziyar bankwana.
A hankali suke fitowa cikin Rauda, cike da bege da son Manzon Allah Sallallahu alaihi
Wasallama.
Da jin ƙunar barin inda yake kwance shi da sahabbansa.

A hankali Aysha ke sharche hawayenta da fingers ɗinta, da suka sha jan lalle, dan yau zasu
koma Makka, kuma jibi laraba jirginsu zai tashi in sun koma Laraba kuma, al'hamis jumma'a
za'a ɗaura aurenta da Barrister Kamal Mubi yayan Maryam kenan.
Haka nan take jin tsananin so da ƙaunar Madina, duk da wani sashi na zuciyarta na cike da
kewar ƙasarta Nigeria.

Ji take kamar ta ɓuya, katta koma Nigeria.

Jiki a mace suka fito, kamar ko yaushe, da sauri, ta tsaya jin Garkuwa na gaisawa da muryar
Taj.
Ido ya zuba mata cike da tarin tambayoyi ganin tana zubda hawaye, ganin kamar bazata yi
mgna bane yasa yace.
“Lfy kuwa ko dai jikin ne?”.
Cikin sanyi murya na rawa alamun kuka na iya kwabce mata tace.
“Ji nakeyi bana son inyi nesa da Rauda, ji nakeyi Madina tafi min ko wanne wurin daɗi a
duniya”.
Sai kuma tayi shiru saboda sassayan kukan daya kwabce mata.
Zuwa yanzu ya fahimci cewa.
Ita macece mai rauni, da saurin kuka, ga kuma shagwaɓa da gwaurayen sakalci-sakalci.
Garkuwa kuwa, tuni itama idonta ke zubda hawaye, shi kuwa Taj a hankali ya kalli.
Side ɗin da su Ummeynshi suke bisa alamu Zam-zam suke sha.
Cikin sanyi yace.
“Ayyah toh kuyi addu'a Allah ya lamunce Miki duk shekara ki samu zuwa mana”.
Da sauri tace.
“Inayi kuma, in sha Allah zan ƙara gobe ma a ɗawafin ban kwana.”
Kiran da Ummeynshi tayi mushine yasa ya sallamesu, ya nufi inda su Ummeyn suke su kuma
suka tafi suka shiga motocin su, zuwa makka.


Da daddere bayan sunyi wanka sun ɗan huta gajiyar hanya daga Madina zuwa Makka, ne suka
ɗan fita shopping Malls dake kusa dasu, suka ɗan tsitstsinto ƴan ƙananan abubuwan da ba'a
rasaba.

Bayan sun dawo sun gama harharda kayansu, Yah Usman yazo ya kwashi, dan za'a sasu a
tawaga ta musamman ne dan jirginsu gobe da Magrib zai tashi.

Nan suka zauna suna ɗan hira.
wayar da Maryam keyi da Ruƙayya matar Barrister Kamal ne yasa duk sukayi shiru, saboda
suna ɗan iya juyo me take cewa cike da tsananin fusata da ƙunan rai da makantar zuciya da
kishi yake dirar wanda ke maida wasu mata tamkar zautattu tace.
“Dan.....!


By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/3, 5:15 PM] Leematu: ✈️

*INDA RAI*

*BOOK ONE PAGE 3*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*



*Littafin INDA RAI na kiɗine, yanzu free pages ne mukeyi, ki biya kafin a gama, 1k ne kacal zaki
turo ta 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan
number 09097853276. Gareku mutan Niger 1000fc zaku biya wato jaka ɗaya kacal kenan ga
number da zakuyiwa magana ku biya ta wurin Mommy +22790899076*

Yauwa matan alkhairi ku matso kuji, wani sabon haɗi na musamman mai huce mana
haushinmu, ya magance mana matsalarmu. Mata da yawa na koka min matsalar Basir da sanyi
ya kashe musu mazanjensu, har basu iya bya msu bƙtrsu bare aje ga gamsar dasu a tarayya,
wasu kan ce abin ya ƙanƙance. To kuzo da kekkyawan yaƙinin Ubangijin ya sauƙar da maganin wannan ciwon tun kafin ya
sauƙi cutar.
Inada haɗin na musamman na mazane ras. Hajia matsalarki tazo ƙarshe da izinin Ubangiji in
kina buƙatar ƙarin bayini, kin kuma tabbatar zaki saya ne to kiyi min PC haɗin Rabin set 5k set
ɗin kuma 10k akwai kuma mgni infection sadidinan shima haɗin rabi 5k set 10k..

“Dangin miji dangin shaiɗan, su Maryam manyan munafukai dangin shaidan, ashe da karuwar
Yayan naki, kuka taho Makkan ban saniba?, da yake ke makirace, munafuka, baki gaya min
cewa da karuwar shi ya biya manaba, ke kan ki kin sani wallahi da nasan da wata macce
karuwa a cikin jerin waɗanda ya biya wa hajjin bana, wlh da bazan zoba, domin itace baƙuwar
zuwa Makka, ki gaya mata cewa, ni wannan karon zuwa na bakwai kenan ina zuwa da mijina.
Dan haka tun wuri kice mata ta nemi nata mijin Barrister mijin Ruƙayya ce ita ɗaya, domin
Ruƙayya aka halicci Barrister ita kaɗai saboda haka ki faɗa wa wannan Karuwar banza karuwar

wofi Ni Ruƙayya nafi ƙarfin haɗa miji da ita”.
Ta dasa ayar mgnar cikin tsananin zafin kishin da kansa wasu mahauka tan mata iya yin komai
a kan mazansu.
Ita kam Aysha rumtse idanunta tayi, tare da sunkuyar da kanta ƙasa zuciyarta na wani irin
suya...

Garkuwa kuwa cikin mamaki take sauraren kalamanta da taci gaba da faɗa tana mamakin
tsananin kishin jahilcin hauka da wasu mata keyi.
Sai kuma Maryam tayi sauri katseta ta hanyar cewa.
“Aunty Ruƙayya, inafa mutuntaki,Ina ganin kimarki so dan haka ki daina kirana munafuka,
yadda kike matar yayana, shine ya haɗamu dangantaka, itama yayan nawa ne zai haɗamu
dangantaka, kuma Aysha ba karuwa bace, ina mai kyautata nats zaton har a wurin Allah ta fiki
kima, tunda ta fiki tsoronshi da bin dokokinshi domin da itace a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login