Showing 48001 words to 51000 words out of 80879 words

Chapter 17 - Inda Rai B1 True Books Available Rubutawa Aisha Aliyu Garkuwa .pdf

da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa
basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo
musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 08069423567
muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan
baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._



sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,



NA
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/10, 3:23 PM] Leematu: ✈️

*INDA RAI*

*BOOK ONE PAGE 10*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*



*LITTAFIN INDA RAI NA KUƊINE, 1k ne cal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki
turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853278, ku kuma mutane Niger 1000fc jaka

ɗaya kenan rak zaku biya ta wurin Mommy +22790899076, ku biya mu tafi tare domin mun kusa
gama free pages*

Tsaya-tsaya fa kiji yar uwa.
Zuwa yanzu na gama nazari da fahimtar ƙorafe-ƙorafen wasu daga cikinmu mata da kan zomin
da kukansu ire-iren haka.

Garkuwa mijina baida kuzari!
Garkuwa mijina yana fin sati biyu ko uku bai buƙaceni ba!.
Garkuwa mijina baya gamsar dani in an fara 2 minute yakeyi.
A'a Garkuwa wlh abin oga yana ƙanƙancewa.

To ku taho ku kuma yi shiru.
In sha Allah, da yardar Allah da kuma izininsa da faɗinsa bai sauƙi ko wanne ciwoba Saida ya
sauƙi maganin cutar, sai dai in ba'a ganoshi ba.
Yar uwa kizo da yaƙini da yarda in Sha Allahu kukanki ya ƙare.
Domin akwai haɗin maganin maza.
Na basir da sanyi.
Domin mafi akasari matsala biyun nanne ke sasu wannan matsalar.
Bayan maganin matsalar kuma, akwai zazzafan haɗin maza.
Mai magance matsalar ƙanƙancewar gaba, mai ƙara masa kuzari, da girma, gami da iya juriyar
daɗewa lokacin raya sunna, da samawa iyali gamsuwar da zata ƙara zaman lfy da inganta farin
cikin dararen ma'aurata.
Akwai maganin na gargajiya da kuma na Bappa Nasara...


“Laylah najin daɗin garin nan fa, ita cewa ma tayi wai in koma in bar mata ke”.
Murmushin tayi tare da ruggume Laylah data faɗa jinkinta.
Cikin sanyi ta ɗan lumshe Idanunta tare da cewa.
“Toh Allah ya kaika lfy y dawo da kai lfy ni ina nan tare da Laylah na”.
Ameen ya amsa. Yana mai kallon Minat da saboda kamar ta da Ishmah yasa yake jinta har
ransa.

Washe gari da Asbah can cikin bacci Ishmah ta fara jiyo sanyayyan sautin muryan sa na ratsa
dodon kunnenta daga Masallacin ƙofar gidansu yana karanta Suratul Juma'a.
Cikin sauri ta buɗe idanunta tare da miƙewa zaune sai yanzu ta tuna ashe fa yau juma'a ce jin
yana karanta suratul juma'a miƙewa tayi tare da tashin Laylah da Minat, kana taje tayi alwala,
suma sukayi.
Bayan sun idar da sallah sukayi Azkhar sai kuma ta kalli Laylah dake gaisheta amsawa tayi
kana ta riƙe hannunta.
Yayinda hannunta ɗaya kuma ta shafa kan Minat tare da amsa gaisuwar ta, daga nan suka fito
falo hannunta na dama na riƙe da Carbi tana Istigfari...

Acan gefen Taj tare da Abba da Yah Muhammad suka fito daga Masallaci suka nufi gefen Abba
da kullum suke zuwa shan tea cikin nutsuwa Abba ya kallesa kana yace.
“Muje mu duba mutuniyar taka dan jiya da daddare tana ta rakin cewa hannunta ya ƙone”.
Da damuwa Taj yace.
“Subhanallah amma da dare sosai ko?”.
Kai Abba ya gyaɗa suna cigaba da tafiya yace.
“Eh kusan ƙarfe goma sha ɗaya Naji tanata raki anzo wajena karɓan Zam-zam ta ƙone kasan
Ishmah da raki sai da naje nayi mata tofi kafin ta samu bacci, yanzu ma muje nayi mata”.
Ɗan murmushi yayi tare da cewa.
“Toh Abba”.
Kana sukayi gaba su Yah Muhammad na biye dasu bakinsu ɗauke da sallama suka shiga falon
zaune a tsakiyar Parlour suka samesu...

Kamar yanda Abba ya sani tana riƙe da hannun tana hura masa iskar bakinta kana tana ɗan
yarfewa.
Anutse ta ɗago kanta tare da amsa sallamar sai kuma tace.
“Yawwa Abba ayi min tofi hannun raɗaɗi yake min ya hanani bacci”.
Sai kuma ta maida kallonta kan Khadijah dake cewa.
“Ummm”.
Ashagwaɓe tace.
“Toh me zakice wani ce Ummm?.
Keda kike ta baccin ki baki sani ba ya hanani bacci da kyar na samu nayi bacci”.
Murmushi Abba yayi cike da kulawa yace.
“Shiyasa ma naxo na Miki Tofi Mamana”.
Ya ƙare maganar tare da zama kan kushin kasancewar tana kasa ya kamo hannunta yana mata
Tofi su Yah Muhammad sai dariya suke suna faɗin rakinta yayi yawa Taj kuwa kallonta yake cike
da tausayi da kuma yanda take shagwaɓe fuska kallonsa tayi sai ta sake kwaɓe fuska shima
fuska ya kwaɓe kana ya ɗaga mata girarsa ɗaya. Abba kuwa bayan ya gama yace.
“Toh ki matso mana Taj ma ya Miki addu'a kinsan kowa da dafa'in bakinsa”.
Juyawa tayi ta kallesa sai kuma ta miƙa masa hannu ya mata tofi tare da cewa.
“Toh Allah ya sawwaƙa”.
“Ameen”.
Ta amsa tare da gaishe da Abba kana ta gaishe da Yayunta da Taj.
Har zasu fita tace.
“Abba in zo musha shayin tare”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Zo mana Mamana”.
Mikewa tayi tabi bayansu

Atare suka sha shayin da ita.

Ƙarfe sha ɗaya dai-dai Jirginsu ya tashi daga Yola zuwa Maiduguri borno birnin kanuri bayinmu

Fulani.
*Sirati sirta moɗa, toh saldori tagga moɗa* kasancewarsu bayi ne a garemu yasa suka koyi
karamci da martaba bako, Borno gidan karamci da girmama baƙi tarba na musamman Taj ya
samu daga Manyan Malamai Tabbas yaga karamci awajen Kanurai A jiddari aka sauƙe sa
bayan ya huta yayi wanka yaci abinci kana akayi masa jagoranci zuwa babban Masallacin
Jumma'a Al-Ansar.
Kusan a tare suka shiga yana tsakiyar
Al Sheiky Zharma..
Imam Muchmah. Da kuma Al Sheiky Idee sun sashi a tsakiya yayinda. Dubban musulmai ke
dandazon shiga ciki masallacin
shi yayi musu limancin Sallar juma'a na wannan ranan.
Koda aka idar tuni matasan Borno suka zagayeshi nan sukayi ta gaisawa dashi tare da yin
hotuna da vidios suna yaɗawa a social media, tuni Nigeria ta ɗauka cewa Sheykh Afif
Muhammad Taj na cikin ƙasar.

Washe gari Asabar bayan an idar da sallan asuba ya wuce garin Zamfara, nan ma yaga
karamci.
Kamar yadda ya alƙawaranta haka ya limamcesu kamsusul salawat.
Daga Zamfara ya wuce Kano ta dabo tumbin Giwa.
Jallabar hausa. Ya Salam shine abun da yake faɗa a lokacin da ya dira a malam Aminu Kano
international airport, sabida ganin taron masoya mabiya karatuttukan.
Bisa jagorancin Malam Aminu Ibraahim Daurawa da tsaron hukumar Hisba suka tarbeshi har
zuwa masauƙinsa na musamman da aka tanadar.
Taj yaga karamci iya ka wurin kanawa.
Dole kwanan sa biyu a Kano.

Ishmah ce zaune bisa kujera riƙe da cup ɗin da da Khadijah ta dama furar mata ta kasa sha,
ɗan kwafe fuska tayi lokacin da ta kurbi damun, domin ba daɗi kam to Amman akan ya lalace ai
gwara ta shanye musamman in ta tuna gargaɗin Garkuwa gyara riƙon da tayiwa wayarta tayi
tare da cewa. “Yanzu dai ai yau zaku wuce Bauchi ko”.

Yana mai ɗan sunkuyar da kansa kasancewar wayar na aljihunsa ne domin rashin samun
lokacin kansa yace.
“Eh yanzuma zamu tafi”.
Cikin kula tace.
“Taj anya kuwa kana cin abinci yadda ya kamata Allah naga videos ɗinka ka ɗan rame, gashi
kanawa nan yan al'barka sun zagaye min kai yadda kake ta musabaha da mutane a gajiye”.
Yana ɗan lumshe idanunsa dake cike da tarin gajiya yace.
“Suna da karamci Amman yawan su da yawan son da suke min yasa sun kasa barina in huta”.
Cikin sanyi tace.
“Bari in Barka dan naji yanzuma cikin mutane kake”.
Cikin sanyi yace.

“In sha Allah jibi zan dawo dan yau in munje Bauchi da dare zamubi jirgi zuwa Abuja.
Duk zaman da zamuyi gobe zamu gama a Abuja jibi da sassafe zan iso Yola”.

“Toh Allah ya kawoka lfy Amman Please ka kularwa Meymey da kanka da Adaya”.
Da sauri ya rumtse idanunsa tare da katse kiransa saboda tsinkewa da zuciyarsa keyi a duk
sanda ta kira mishi su more especially Adaya.

A ranar suka wuce Bauchi.

Sha biyu dai-dai suka isa Bauchi Yakubu.
Kai tsaye suka wuce gidan, Sheykh Tajuh Usman Bauchi, dottijon malami kuma sannane a cikin
ƙasar mu da kewaye baki ɗaya, Shekh Tajuh Usman Bauchi dottijon mai tarin limin addini da
yawan shekaru kana da zugar zuriya ƴaƴa da jikoki da jikokin jikoki, malami ne na Ɗarika
tsakakkeyiyar ɗarika. Wanda yake da good understanding da manyan malaman kasarmu na sunan, shiyasa tafiyar
ma dasu akayi suna shiga harabar gidan Taj ya lumsh idanunsa tare da sauƙe wani irin
amintaccen ajiyan zuciya da fesar da sassayan numfashi kana ya buɗe idanun a hankali yana
karewa tsarin gidan da yafi dacewa da a kira shi da fada ko masararuta ilimi isilam domin
girmanshi ya wuce ace dashi gida, tsaruwarsa kuwa yafi karfin ace dashi ko sangaya sai dai
masarautar.
Isarsu ba wuya akayi musu iso cikin asalin sashin Sheykh Tajuh Usman Bauchi.

Kusan a jere a jere suke tafiya cike da kamala da nitsuwa da ilimi addinin Musulunci ya sakar
musu, yayinda yan agajin da kuma jami'an hukumar Hisba ke zagaye dasu.

Kusan duk a tare suke sauƙe sassauke numfashi a hankali da tsuka ratsa tsakiyar wani
mashahurin Parlour na alfarmar.

Sai kuma duk suka ɗan tsaya saboda, ganin ɗaya daga cikin masu yi musu jagoran ya ɗan
buɗe musu wata babbar ƙofa tare dacewa Bismillah.
Manyan malaman sunan a gaba, yayinda suka sa Taj a tsakiya sai yan agajin dake baya, kusan
duk a tare sukayi sallama
Ya Salam.
Shine abinda Taj ya faɗa a lokacin da suka iso tsakiyar Parlour da yafi dacewa da a kira shi da
holl, sai kuma ya lumshe idanunsa saboda hango Sheykh Tajuh Usman Bauchi dake zaune a
tsakiyar ƴaƴansa da jikokinsa gami da kuma amintattun ɗalibansa duk sun zagayeshi tamkar
sarki a tsakiyar waziransa. Haka nan sai yanayin yayi mishi kama da yadda suke sa Yah Abana a tsakiyar duk ranar
jumma'ar ƙarshen ko wanne wata, komai na zaman da tsarin gidan yayi mishi tuni da gidansu.

A hankali ya buɗe idanunsa tare da diresu kan kekkyawan farin dottijon.
Kusan a tare shi da Dottijon suke rufe idanunsu Saboda wani irin fitinenne bugun zuciyarsu da
yayi a tare.

Yayinda sauran kuwa duk sun zube a tsakiyar Parlour a gaban dottijon da duk ya girme su,
yana haifesu wasuma yayi jika dasu.
Yayinda sauran yaransa kuwa duk suka juyo suna kallon inda mahaifin nasu ke kallo.

Malaman Sunnan kuwa da sukazo cike da girmamawa suke gaida Sheykh Tajuh Usman
Bauchi.
Amman ina hankalinsa baya kansu.
Ido ya zuba wa Taj tamkar zai mannesu a jikinsa.
Shi ma Taj idon ya zuba mishi yana mai ɗan matsowa kusa da abokan tafiyar tasa.
Sai kuma duk taron jama'ar da suka samu a Parlour suka juyo da sauri suka zubawa Dottijon
idanu jin yana mgna cikin muryar girma da nitsuwa da tsufa mai nagarta yace.
“Inajin Ƙamshin Mahmoudu na, ƙamshin Mahmoudu nakeji”.
Ya ƙare maganar da miƙawa Taj hannunsa tare da cewa.
“Afif Muhammad Taj ne yau a sangayata”.
Da sauri Taj ya miƙa masa hannunsa.
Jawosa kusa dashi,
Da sauri Taj ɗin ya ɗan rusuna tare da direwa bisa guiwowinshi,
Shi kuwa Sheykh Tajuh Usman Bauchi, kan Taj ɗin ya ɗaura bisa cinyarsa, sai kuma ya sunkuyi
tare da cusa hancinsa cikin sumar kan Taj, tare da shaƙar ƙamshin jikinsa.
Numfashi mai sanyi ya fesar tare da ɗago kanshi ya kalli baƙin nasa tare da cewa.
“Izala ƙanwar ɗarika yau kun kawo min baƙo na musamman, bakon da nake jin jini da zuciyata
sun aminta dashi”.
Sheikh Jabeer sani Maihula ne yayi ɗan murmushi cikin sokkotancinsa yace.
“Malam ai ayanzu Sunnan ce abbabba ɗarika ce aƙƙarama, kawai kui mubaya'a ku yarda mune
ag gaba gareku”.
Murmushin Dottijon yayi tare da cewa.
“Yoh aiko ɗan hodiya mancewa yayi a sauka Sokoto da Bauchi zaizo”.
Dariya sukayi mai sauti sai kuma duk suka fara gaisawa, har lau dai Sheykh Tajuh Usman
Bauchi bai saki Taj ba, yayinda ƴaƴan da jikokinsa kuwa kab idonsu na kan Taj.

“To Alhamdulillah sannu ku da isa lfy”.
Sai kuma ya ɗan kalli gefen damansa tare da cewa.
“Ku isa kusha ruwa kuzo muyi muƙabala”.
Da sauri Sheykh Daurawa yace.
“A'a Malam zafa kayi mubaya'ar nan da baka sonyi in mukayi muƙabala”.
Sai kuma suka kalli Sheykh Janeer dake cewa
“Awoh haɗimai Gsky dai, domin hujjar aggaremu gaba gareku, kuna gani da ajjiyarku zaku
dawo baya garemu, ko ku zam kuna ɗumi”.
Dariya sosai sukeyi musamman sokotancin da Sheykh Jabeer ke zubawa.
A hankali ya yunƙura tare da fara kiciniyar miƙewa, da sauri Taj ya tallabeshi tare da taimaka
mishi ya miƙe, sai kuma yayi saurin amsar sandar da mutumin dake gefensa ya miƙa mishi.
Amsa yayi tare da bawa dottijon shi kuwa Sheykh Tajuh Usman Bauchi cikin tarin girma da isar

kamala yace.
“Ni bana gaisawa da baƙo har sai na bashi abin sha da ci yaci ya sha, dan haka Bismillah ku
iso nan ya ƙare maganar yana nuna musu Dinnin area.
Wani tamfatsetsen Dinnin table ne na alfarmar wanda ke da kujeru goma sha huɗu.
Yayinda saman table ɗin ke cike maƙil da kayan marmari da kuma manyan womers na alfarmar
sai plates, bowls, mugs, and spoons.
Sanin YESS bazai tsaya yayi mgn ba sai sun sha wani abune yasa suka nufi Dinnin area ɗin
bisa jagorancin babban ɗansa.
Sheykh Tijjani.

Ga mamankisu kuwa sai gani sukayi yaja hannun Taj.
Sun bi wata ƙofa ta musamman sun tafi.

Kusan duk yayansa kallon kallo suka farayiwa juna, fuskokinsu ɗauke da maɗaukakin mamaki.

Su Sheykh Jabeer kuwa.
Bayan sun ci sun shane, duk sukayi al'wala saboda jin an kira salla.

Daga nan suka wuce masallacin sangayar.
Murmushin Daurawa yayi lokacin da suke tsaye a sahun forko sai kuma ya kalli Sheykh Musa
Yusuf Asadussunah na faɗin.
“Toh yau maji ma gani wa zai limamce, izala zata limancin ɗarika ko ɗarikace zata limancin
izala”.
Murmushin Sheykh Isa Ali Pantami yayi tare da cewa.
“Mu mun basu dama”.
Da sauri Sheykh Janeer yace.
“Anya ko munefa gaba garesu”.
Murmushin Sheykh Tijjani yayi yana kallon mahaifinsa ganin yana jawo hannun Sheykh Afif
Muhammad Taj.

Ga mamakin duk al'ummar Annabi dake cikin yankin jin Dottijon yana faɗin.
“Yau ba ni zan ja sallaba
ya faɗa tare da ɗan matsawa gefe kana yaci ga da cewa.
“Alhamdulillah dai ga Afif Muhammad Taj, a ƙasar Nigeria a kuma jahar Bauchi a tsakiyar
tsagayata a kuma sahun limamcin masallancimu.”
Ya ƙare maganar yana jawo hannun Taj ya tsaida shi da'irar limancin kana ya koma ya tsaya a
sahun forko.
Shi kuwa Taj zuwa yanzu al'amarin dottijon ya daina bashi mmki kawai dai yana jinsa har cikin
jini da tsoka ƙashi da bargo jiki da zuciyarsa, wani irin son dottijon yakeji yana game jiki da
zuciyarsa.
Cikin sanyi ya gyara tsayuwarsa tare da gyara maek ɗin cikin nitsuwa gami da cikir kamala ya
ɗanyi gyaran murya tare da cewa.
“Sahoohhhh! Sahoooohhh!! Sahooooooohhhhh!!!”.

Kusan gaba ɗaya mamun nasa lullumshe idanu sukayi saboda yadda sautin Muryasa yake
ratsadu, sai kuma duk suka gyaggyara tsayuwar sahun.
Ajiyoyin zuciya suka rinƙa sauƙewa tare da bubbuɗe kwayar idanunsa lokacin daya fara tada
iƙama.
Da yawa sunso ace jam'in sallama Magrib ko Isha ko asuba zai jasu dan suji zaƙin muryasar.

Bayan an idar da salla suna sake koma ciki.

Nan suka tattauna duk abinda ya kawosu.
Kasan cewar Sheykh Afif Muhammad Taj da Isa Ali Pantami da Sheykh Jabeer Sani Maihula da
wasunsu Abuja zasu wuce, kuma sai tara na dare jirginsu zai tashi ne yasa suka kai dare.
Saura kuma tun bayan la'asar suka juya suka koma Kano.

Sit kakaji masallacin da lokacin da yake jansu sallan Magrib babu abinda ke tashi sai sautin
muryarsa bayan ya karanta suratul Fatiha kana ya ɗaura.
Daga forkon Suratul Yoosuf
“(Aliflamrah tilka ayatu alkitabi almubinu)”.
Daga nan yaci gaba da kawo ayoyin har yaje aya ta 10 kana sukayi sujjadar forko, kana suka
miƙe dan.
Cikin aminci ya karanta suratul Fatiha kana ɗaura da Suratul Yusuf ɗin ya ɗauka daga aya ta
11.
(Qaloo ya Abana ma laka la tamanna Aaala Yoosufa wainna lahu lanasihoona”.)
Wasu irin tafassasun hawayene suka zubawa Sheykh Tajuh Usman Bauchi, Dottijon mai cike da
wani miki a zuciya, yayinda shi kuwa Taj haka nan yaji tsoro na diro mishi cikin danne rauninsa
ya kawo aya ta 12.
“( Arsilhu ma'AAana ghadan yartaAA wayalAAab wainna lahu lahafithoona”.
Numfashi mai nauyi ya fesar a hankali tare da baddashi cikin taƙib kana yaci gaba da kawo
ayoyin Saida yaje aya ta 20. Kana suka tafi ruku.

Haka dai sukayi sallan cike nitsuwa da amcin mu'ujizar Alqur'ani mai girma.
Koda suka idar basu fitaba sai da sukayi isha, anan ma duk a Suratul Yusuf ya jasu, wanda duk
aya goma goma ya rinƙa kawowa haka yasa aka samu ayoyi 40 kenan

Ƙarfe tara dai-dai jirginsu ya tashi zuwa Abuja.

Cikin alfarmar darajar Alqur'ani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login