Showing 63001 words to 66000 words out of 80879 words

Chapter 22 - Inda Rai B1 True Books Available Rubutawa Aisha Aliyu Garkuwa .pdf

ce zaune kusa da Meymey a dinning table, magungunanta ta ɓare ta bata tare da miƙa
mata ruwa.
Amsa tayi tare da shansu.
Fitowan Taj ne yasa ta ɗan zuba mishi ido cike da alamun da yafi kama da tsoro.
“Masha Allah Laylah ya jikin”.
Ya ƙare maganar yana sa hannunsa a wuyanta.
Cike da tsananin tsoro ta sunkuyar da kanta murya na rawa tace.
“Da da dasauƙi”.
Cike da kulawa yace.
“Ya dai Laylah me haka jikinki yake rawa?”.
Da sauri tace.
“B.. ba... Bab.. babu”.
Ita kuwa Meymey idanu ta zuba mishi cike da alamun son gano wani abu.
Dai-dai lokacin kuma kiran Ishmah ya shigo wayarsa.
Amsa kiran yayi yana kallon Laylah da duk ta takure jinkinta.
“Jikin Laylah da sauƙi Maeeshah”.
Ya faɗa tare da motsowa kusa da Laylah kana ya miƙa mata wayar da faɗin.
“Gata”.
Wani irin kallon mai cike da tarin manufofi Meymey ke liƙa mishi.
“Hello Aunty Ishmah”.

“Na'am Laylah ya jikin naki?”.

Cikin sanyi kasala da ya zame mata jiki tace.
“Da sauƙi sosai ma”.

“Masha Allah to Allah ya ƙara sauƙi kina cin abinci kiji ko”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“To Aunty ina Minat?”.
Cike da kulawa tace.
“Tana gidansu”.
Daga nan dai sukayi sallama.
Amsar wayar yayi tare da ficewa.
Ya wuce Tajmuh hospital.
Yana isa ya fara aikin CS ɗin da zasuyiwa kusan mata biyar, da taimakon Dr Farida da Dr Adey
sukayi komai.

Kwanan Taj goma da dawo kana ya sake wata tafiyar zuwa Bangaladash daga can ya wuce
India
Kwana shi biyar ya dawo Ethiopia.

Yau tun safe kuma Laylah ta kuma tashi da amai da zazzafan zazzaɓi.
Haka yasa ta ɗauketa tayi gida da ita.
A Parlour Malam suka samu, mafiya yawan mutanen gidan.

Bayan sun gaisa ne Meymey keyiwa Ummeey bayanin jikin Laylah, cikin taɓe fuska Mom Amal
tace.
“Na rantse da zatin Allah ƴannan cikine da ita, in kunƙi kuma kuje ayi muku gwajin cikin zakusha
mamaki wlh.
Cikin fara jin tsoro da ganin alamun gskyar Mom Amal Ummeyn tace.
“Gsky dai nima ina gafa gwara aje”.

Dai-dai lokacin kuma Taj dake shigowa yace.
“Ba wani ciki a jikin Laylah dan Allah Ummeey ku daina faɗar hakan, hankali na tashi innaji
kuna batun Laylah”.
Ya ƙarashe maganar tare da zira wayar shi cikin aljuhun ba tare da ya katse wayan da yake yi
da Ishmah ba.
Kusan duk a tare suka juyi suka zuba mishi idanu.

Malam kuwa wani irin kallon cikin ƙwayar idanun Taj ɗin yake tamkar mai son karantan wani
abu.

Ita kuwa Meymey cikin tsoro tace.
“Gsky dai nima zanso ayi mata gwajin cikin nan, dan abin ya fara bani tsoro ayi kawai hankali
na ya kwanta”.
Maman Yah Hafiz ne ta jawo hannun Laylah tare da cewa.

“Laylah meke damunki ne?”.
Laylah da batama san menene suke mgn a kaiba jiki cike da kasala ta juya ta fita, yawun
bakinta ta zubda kana ta dawo.
Ita kuwa Maman Yah Hafiz cikin sanyi tace.
“Dan Allah ku daina alaƙanta ƴariyar dake da alaƙa da gidanan da wannan mugun abun da
bazamu iya ɗaukaba”.
Ta ƙare maganar tana kallon Malam da ya kafe Laylah da kallon dake nuna tsananin tsana da
ƙyamar da zata iya fuskanta a tare dashi, domin tasan yadda zuciyar mijinta yake farin sani.

Yayinda duk sauran kuma suka zurawa Laylah ido murya a raunace tace.
“Nima ban saniba, bana iya cin abinci kuma yawuna ba daɗi in na haɗiye amai nakeyi”.
Da sauri Mom Amal tace.
“To me kikeson ci?”.
Tana zamewa kwance tace.
“Abu mai tsami”.
Yah Salam shine abinda Taj ya iya faɗa zuwa yanzu shima tsoro mai yawa ya rufeshi
musamman da ya ƙura mata idanu a matsayin sa na likita ya gano alamun ciki.
Cikin sauri duk suka kalli Malam da yaja wani firgitaccen numfashi tare da cewa.
“Kai Hafiz ɗauketa ka kaita a gwada min ita yanzun nan nake jiran amsa”.
Ya ƙare maganar cikin tsananin tafasowar fusatar zuci
Da sauri Yah Hafiz ya miƙe.
Meymey miƙewa tayi tare da tallabe Laylah kana suka nufi waje.
Cikin so da kulawa Malam ɗin ya kalli Taj daya juya da nufin zai bisu.
“Zo Babana ka huta, yayanka zai kaita, yanzu ka dawo ko ruwa baka sha ba”.
Wani irin mugun kallo Mom Amal da Aryan suke mishi ƙasa-ƙasa.

Mamin Aryan kuwa da ido ta tsare ɗan nata ganin kallon da yakeyiwa ɗan uwan nashi, cikin
mmki da tsanan hali irin na Aryan ta miƙe ta bar Parlour.

Nigeria Abba ne zaune a Parlour shi bisa dukkan alamu waya yakeyi da Yayanshi Bello.
“Ya gajiyar ibada kuma”.

“Alhamdulillah ai yanzu kam gajiya tabi lfy, yau wata ɗaya gudafa kenan da dawowarmu, in sha
Allah ma nanda mako biyu dai ina nan tafe zan shigo Adamawa, ɗazu nayi waya da Ishmah
nace mata ta shirya”.
Cikin girmamawa Abba yace.
“To Masha Allah, Allah ya kawo ka lfy, ba ruwana
Kaida ɗiyarka”.
Ya ƙare maganar cike da kara.
“Ɗazuma ma Adam ke cemin wai ashe Dr Nafi'u ma, yabar ƙasar jiya ko?”.
Yana gyara zaman hularsa yace.
“Eh yace wai ta ɗan jirashi in ya dawo zasuyi auren”.
Cikin faɗa Uncle Bello yace.

“Bamuyi wannan alƙawarin ba, wlh ina zuwa Adamawa zan ɗaura mata aure, da duk wanda
yake buƙata, idan kuma Mukhtar yace yana sonta wlh aura mishi ita zanyi.
Dan yaron yana da mutunci dan koda na dawo Umrah yazo min sannu da zuwa”.
Kai Abba ya jinjina domin ya sani tabbas.
Mukhtar (Bappa Kawu) yana da mutunci da Kamala ko shi bazai ƙi aurenta da Mukhtar ba.

A cikin gida kuwa.
Cikin tarin damuwa Ishmah ke jin duk maganganun da akeyi a Parlour Yah Abana ta wayar Taj
dake cikin aljihunsa.

Ganin kiran Bappa Kawu ya shigo wayarta ne yasata katse kiran Taj ɗin kana ta amsa cikin
sanyi tace.
“Assalamu alaikum, Bappa Kawu”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ni dan Allah na tuba a dena cemin Bappa Kawu nan ko Hamma ki kirani ba sai kince my price
ɗin ba”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Wannan ai tsohon suna ne”.
Da sauri yace.
“Ni kuma so nake a sabunta minshi, To my princess, ai ni so nake ki aminta dani fiye da amincin
da kikayi dani a baya domin a yanzu da yaƙinin aure na dawo da ƙarfi na”.
Cikin sanyi tace.
“Bappa Kawu ka dawo ka kuma yin wasa da zuciyata kenan ko?”.
Ta ƙare maganar tana jin son da tayi mishi a baya na tasowa.
Allah ya sani taso Mukhtar rabuwan su haukane kaɗai batayi ba.
Cikin salon so ya rinƙa isar da soƙonsa.

Ethiopia.

Kusan duk ma zauna Parlour ido suka zubawa Yah Hafiz da ya zauna gaban Malam yayi ƙasa
da kansa hawaye na kwaranya a idanunsa.
Ganin haka ne yasa Taj yin mutuwar zaune saboda koma menene yasan ba labari mai daɗi
bane.
Kana ga Meymey a durƙushe a gaban Malam ɗin tana sakin shesh-sheƙan kuka.
Laylah kuwa jikin Ummeeyshi ta faɗa tana karkarwa.

Ita kam Ummeeyshi tuni ta fara karkarwa.
Mom Amal kuwa cike da zaƙuwa tace.
“Hafiz mgn zakayi ba kuka ba, me likita yace?”.
Ta ƙare maganar da kallon Malam da fuskarsa ta sauya daga fara zuwa jazir kana idanunsa
sunka ƙanƙance suka kuma sauya launi daga fari zuwa fatsu-fatsi.
Cikin Muryar dake nuna tsananin fusata da tashin hankali yace.
“Hafiz me likita yace?”.

Cikin raunin murya Yah Hafiz yace.
“Dr yace tana da ciki har na tsawon wata uku”.
Wani irin masifeffen harbawa zuciyar Taj tayi lokaci ɗaya zufa ya karyo mishi.
Da sauri kuma ya rumtsa idanunsa jin Malam na cewa.
“Waye yayi mata ciki?”.
Kusan gaba ɗaya Parlour juyowa sukayi a kaɗe suna kallon Meymey da ta saki wani irin kuka
mai cike da shesh-sheƙan kuka.
Cikin tsananin tsoro kaɗuwa Yan Hafiz, Yah Yusuf, da Abduraham, kana da iyayensu mata suka
zubawa Meymey ido jin abinda take cewa.

Shi kuwa Taj dimmmm yaji kunnuwansa sun toshe zuciyarsa ta tsaya da bugawa idanunsa sun
daina gani a lokacin da yaji Meymey na cewa.
“Yah Afif ne yayi mata c....”




By
*GARKUWAR MARUBUTA*
✈️

*INDA RAI*

*BOOK ONE PAGE 13*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*




*Page biyu kacal suka rage mu gama free pages bayan wannan, ki biya ki karanta cikin aminci
da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki
ta wannan number 09097853276, kuma mutan Niger 1000fc ne rak zaku biya ta wurin Mommy
+22790899076.*


Cikin shesh-sheƙan kuka taci gaba da cewa.
“Yah Afif ne ya mata ciki babu wanda zai mata ciki a duniya bayan shi,shine ya maidata tamkar
matarsa”.
Wani irin karkarwa da rawa jikin Yah Abana ya ɗauka maganar tazo masa abaxata baiyi zato ko
tsammanin jin irin waɗannan kalaman ba.
Rawa zuciyarsa keyi domin sam bata yarda ba kuma bata amince ba lokaci ɗaya yaji jinsa na

ƙoƙarin ɗaukewa..

Yayin da Taj kuwa tunaninsa, nazarinsa da ƙwaƙwalwa suka tsaya daga bugawar da suke haka
zalika kunnuwansa sunyi dif daga sauraren abinda suke kana idanunsa sunyi dulum daga
kallon abinda suke babu abinda yake gani face duhu haka nan yaji numfashinsa na ƙoƙarin
barin gangar jikinsa fahimtar yana gab da sumewa In yayi garajene yasan ya ɗan gyara
zamansa cikin ƙarfin hali yayi saurin fisgo salati da tasbihi daga cikin zuciyarsa zuwa harshensa
duk da bai fito kan lips ɗin sa mutane sunji ba amma da taimakon kalmar _Innalillahi wa'inna
ilaihi rajiun Allahumma Ajirni Fii musibati Wa'alhlifli khairan minhaa_ da yake naimaitawa ya
bawa numfashinsa damar dai-dai-tuwa ya koma ya zauna kana ya bawa kunnuwansa damar
jin maganar da ake yi sai dai har zuwa lokacin zuciyarsa bata samu salama da sa'idar da zata
iya komawa bugawanta na aihini ba, sai wani irin bugawa da yake da azabebben ƙarfi da watsa
jini liter ɗaya acikin ko wani second saboda ɗinuwar daya shiga...

Ummey kam baki ɗaya daskarewa tayi ji take kamar tana yawo asararin samaniya takasa
fahimtar cewa araye take ko amace.
Mom Amal kuwa wani murmushin jin daɗi tayi tare da cewa.
“Uhum haba shiyasa mana ashe da dalili, shiya ko yaushe in akace aje ayi gwaji yake ta
lauye-lauye haba koda naji al'amarin nan da ban mamaki da ɗaure kai”.
Da sauri Yah Hafiz ya shiga girgiza kansa cikin tsananin mamaki yace.
“Noooo!,Noooo dan Allah kuyi shiru bana son jin maganar nan Mom Amal ki daina faɗa”.
Yah Yusuf kuwa hannunsa yasa ya toshe kunnuwansa duka biyu yana mai girgiza kansa yayin
da Hajiya Halisa Mahaifiyar Yah Hafiz ta juya ta kalli Meymer tare da cewa.
“Meymer kiji tsoron Allah kiji tsoron irin abinda kike faɗa Meymey kisan akan wakike
magana,Afif fa, Taj kike cewa wai shi yayiwa Laylah ciki ƴar daya ɗauka ya riƙe kana ya maye
mata gurbin Uwa, Uba,Yayu da ƴan Uwa yanda yake riƙe da ita yake rainonta tamkar ƴar
cikinsa”. Cikin matsanancin kuka Meymey ta rarrafo ta dawo gabanta cikin rawan murya tace.
“Wallahi Hajiya idan nayi mishi ƙazafi Ubangiji yana gani, idan na mishi ƙazafi Allah ya hanani
kwanciyar hankali.
Yanda ya maye mata gurbin uwa, uba haka zalika ya zauna a gurbin mijinta.
Kuna gani koda tafiya zaiyi da Laylah yake ya barni baya tafiya dani. ki gafa kwanan nan suka
dawo daga Nigeria kwana goma sukayi wallahi ba ƙazafi nake masa ba ai gashi nan suna
zaune yayi inkari mana ba gashi nanba, kawai shiru yayi ba tunda yasan baida gsky”.
Ta ƙare maganar cikin matsanancin kuka da gigita har kamar numfashinta zai yanke...

Ummey kuwa cikin tsananin kaɗuwa jikinta ya ɗibi wani irin karkarwa tamkar wacce aka tsoma
cikin ruwan ƙanƙara baki daya ilahirin jikinta ɓari yake numfashinta na kokowa da juna da ƙyar
ta samu ta fara fisgo kalmar _Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun Allahumma Ajirni Fii musibati
Wa'alhlifli khairan Minha_ sune abinda take iya maimaitawa wannan kalmar da take maimaitawa
shine yasa Taj ya fara ji da ganin ninsa ya dawowa ahankali ya fara kallon mutanen cikin falon
duk da cewa dishi-dishi yake ganinsu.

Ganin tana ƙoƙarin shiɗewane yasa cikin sauri Ummu Aryaan ta miƙe kana ta ɗauki roban
Swan dake gaban Malam ta balle murfin kana ta tallafe Ummey tasa mata goran abakinta cikin
sanyi tace.
“Kisha”.
Kai Ummey ke girgizawa tare da cewa.
“Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun”.
Ji take sam ba zata iya ba...

Yah Yusuf kuwa tun lokacin daya toshe kunnensa yake jujjuya kansa har zuwa yanzu bai bari
ba.
Yayin da Kabeer da Aryaan kuwa ido suka zubawa malam suna son karantar wani irin yanayi
yake ciki da kuma hukuncin da zai iya ɗauka.

Malam kuwa baki ɗaya ilahirin jikinsa tsuma yake yayin da idanunsa suka kaɗa sukayi jawur
tamkar garwashi kana jijiyoyin kansa sun tashi musamman babban jijiyan dake kan hancinsa ta
taso har tana harbawa tsaban tsananin tashin hankali da kiɗima kana da yanda kalmar ta dake
shi ji yake cikin gigicewa mai haɗe da ɗimuwa, fahimtar kamar yana gab da ɗimaucewa ne yasa
shi maimaita _Allahuma Ajirni Fii musibati Wa'alhlifli khairan Minha Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun
Lahaula walaƙuwwata illah billah_.
Jin yanda sautin addu'oin ke fitowa daga bakinsa ne yasa kowa dake cikin falon ɗaukar addu'oi
banda Kabeer, Aryaan da Mom Amal ko wannensu da tunanin da yake aransa.

Ita kanta Meymer batasan lokacin data fara maimaita _Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun ba_.
Laylah kuwa cikin rauni ta saki wani marayan shesh-sheƙan kuka mai haɗe, da ɗimuwa, tashin
hankali, gami da rauni ganin yanda baki ɗaya falon ya gigice wasu na kuka wasu sun ɗaura
hannuwansu akai zuwa yanzu ta fahimci duk akanta ne sosai kukan da take ya tsananta wanda
har ta kai matakin da numfashinta ke shirin barin gangar jikinta. Ganin halin da take cikin yasa Meymer yin saurin rarrafawa ta jawo ta jikinta ta rungumeta tana
shafa kanta kana itama tana cigaba da kuka.
Cikin shesh-sheƙan kuka tace.
“Kiyi haƙuri Laylah ba laifin ki bane ya cuceki ya cuci rayuwarki.
Nima ya cuceni ya wulaƙantani iyayena sun aura masani amma bai ɗaukeni matsayin mace ba
bai kalleni matsayin mace ba”.
Laylah kam kuka take tamkar ranta zai fita Meymer kuwa cikin tashin hankali ta cigaba da cewa.
“Baki da laifi dan shine ya cucemu ya wulaƙantar dani ya ajiyeni tamkar gunki bai taɓa kallona
Amatsayin matarsa ba ya ɗauke ki ya maye gurbina dake azuciyarsa da kuma jikinsa ya
maidake abar biyar buƙatarsa”.
Ta kai karshen maganar tana sake fashewa da kuka.

Cikin wani irin fusgar magana Malam ya kalli Taj akaro na farko a rayuwarsa yace.
“Tajuddeen”.
Cikin ruwan murya kana lips ɗin sa na karkarwa ya kira sunansa...

Taj kuwa cikin ruɗu ya rarrafo akan gwiwarsa yazo gaban mahaifinsa ya tsugunna.
Malam kuwa cikin tsira masa Idanu yace.
“Taj me nake ji?,Me ake cewa?,Me zaka iya cewa akai?”.
Ina ya kasa mgn sai kansa kawai yake jujjuyawa.

Cikin tsananin tsoro da kiɗima Ummey ta dafe hannunta aƙirji tsoronta ya hau-hauwane saboda
sanin shi mutum ne da baya taɓa iya kare kansa arayuwarsa, baya taɓa iya in kari kuma, baya
musu tafi kowa sanin yanda Taj yake tasan yanda ya tashi ko bashi yayi laifi ba muddin akace
shi yayi baya taɓa iya In-kari wannan tunanin da tayi yasa ta saki wani maraitaccen kuka mai
cike da ƙuna a zuciya.

Taj kuwa kansa kawai yake juyawa.
Malam kuwa cikin ɗimuwa da kaɗuwa ya cigaba da cewa.
“Taj ka buɗe baki kayi min magana me nake ji?.
Me nake ji Tajuddeen?”.
A kuma dai-dai lokacin Uncle Jibril tare da Momyn Meymer sukayi sallama jin kamar falon
Aruɗe ne yasa cikin sauri suka ƙara sa shiga Falon.

Momyn Meymer na shiga cikin sauri ta nufi kan Ummey kana ta tallafo ta jikinta tare da faɗin.
“Subhanallah Hajiya Fati meke faruwa?”.
Sai kuma tayi saurin juyawa jin Mom Amal na cewa.
“Menene ma bai faru ba Hajiya Ruƙayya babu abinda bai faru ba. Tajudden ya zubar mana da
mutuncin gida ya tozarmu ya wulaƙantamu ya tozarta tarbiyyar da ake gina wa tun daga kan
yayun sa har ƙannensa”.
Cikin tsananin mamaki Momyn Meymey ke kallonta tana jin tashin hankali Mom Amal kuwa cikin
tarin tsanarsa ta cigaba da cewa. “Tajuddeen ya tozartamu ya bamu kunya yaci amanar
hadddar Alkur'ani izu sittin dake kansa Tajuddeen yayi kwance kwance ya ɗibgawa Laylah ciki
ya rasa wacce zai yiwa ciki sai marainiya dan jarabar tsiya matarsa bata ishesaba sai ya ƙara
da yarinyar amana”.

Cikin sauri Ummey ta sake toshe kunnuwanta tare da cewa.
“Laaaa, la, laaaa, la No Noooo bana son ji bana son ji.
Da sauri Uncle Jabril ya ƙarasa gaban abokinsa ya zauna tare da cewa.
“Ya Salam Malam Muhammad kai ya kamata kayi control ɗin su amma sai kuma ka ɗimaucewa
ka ɗimautar dasu”.
Sai kuma ya juya ya kalli Yah Hafiz yace.
“Hafiz ka kwantar da hankalinka”.
Sai kuma ya sake maida kallonsa kan Yah Yusuf yace.
“Me haka kuke ɗinaucewa!?”.
Kallonsa ya kuma mayarwa kan Yah Abdurrahman wanda tunda Meymer tace Afif ne yayiwa
Laylah ciki ya buɗe bakinsa bai rufe ba sai hawaye dake ta kwaranyo nasa Aransa yace.
kenan mafarkin da nayi yana ƙoƙarin tabbata akwai, ƙalubale da masifa da zata saƙƙo acikin
family na, ta watsa mana farin ciki ashe kalubalen dana gaani akan Tajuddeen zai sauƙa!.

Yah Abana kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login