Showing 15001 words to 18000 words out of 80879 words
Chapter 6 - Inda Rai B1 True Books Available Rubutawa Aisha Aliyu Garkuwa .pdf
sosai suke zumunci haka Yah Usman auren ne dai Allah bai sauƙar da shiba.
Shaƙuwarsu da Taj ya wuce dukkan zaton ma zato da nazarin mai nazari, domin halattacciyar
shaƙuwace wacce babu saɓon Allah ko kuma gurɓacewa wanda mafi yawan Samari,Ƴan mata
da kuma Zaurawa keyi Abota ce da aka gina ta saboda Allah mai cike da sanya zukata
nutsuwa.
Zuwa yanzu kuwa, karatuttukan Taj da muryarsa sun zaga duniyar social media,
Musamman,Tik-tok,Instergram, Facebook, WhatsApp da sauran Man hajojin sada zumunta
domin salon Muryasa tana da maganaɗisu na musamman ga zukatan musulmai koda kuwa
baka san mai ake faɗa ba Muryarsa nada wani irin ƙwarjini mai tafiya da hankalin mutum da
samar da cikakkiyar nitsuwa da cika zuciya da shauƙin ƙaunar jin karatun ƙur'ani.
Yau ta kasance ranar jumma'a ce.
Ƙarfe ɗaya dai-dai jirginsu ya sauƙa a Addis Ababa bole intranational Airport.
Jim kaɗan da sauƙarsu, bayan an gama gwada dukkan lafiyarsa.
Da sassarfa ya fito ya shiga motar da tuni aka tanadar masa da driver'nsa da tafiya gida.
Yana shiga motar yacewa driver.
“Dan Allah kayi gudu na gasken-gaske domin so nake, in samu jami'in sallan jumma'a a
matsalacin. Grand Anwar Mosque nadan Ya Abana na jin daɗi in jashi jam'i”.
Ya ƙare maganar yana kallon Driver da sam baya sauri yadda yakeso, kuna shi sauri yake
domin so yake ya samu ya kasance a sahun forko bayan Yah Abana domin shine yake limancin
masallacin.
Wayarshi ya zaro tare da kiran Aysha tana ringing kuma bata ɗagaba.
Tsaki mai sauti yaja, domin badon sanin cewa, dokar sune pilot bazasu jan motaba, saboda
zasuyi gudu na fitan hankali kasan cewar sun saba da gudun jirgi, badan haka ba da tuni ya
amshi tuƙin nan.
Damin cike yake da begen ganin shi cikin ahlinsa, dan yanzu a ƙalla wata uku kenan bai zo
Ethiopia ba, kuma duk saboda Meymey ce.
Sake kiran Aysha yayi a karo na uku, numfashi mai sanyi ya fesar jin ta ɗaga.
Cikin aminci yarda shaƙuwa mai zurfi yace.
“Ina kika shiga inata kiranki bakya ɗagawa??”.
“Ina shafawa Dadeey maganine”.
Tayi mgnar tana nazartar muryarsa sai kuma tace.
“Kamar kana hanya ko?”.
Cikin sauƙe numfashi yace.
“Eh shine na kiraki ai muyi tafiyar tare, yanzu na sauƙa cikin Ethiopia”.
Tana gyara kwanciyarta tace.
“To muje in rakaka”.
Hannunsa yasa yana shafa tattausan sajensa mai masifar sulɓi da sheƙi, kana yace.
“So nake in samu jami'in sallan bayan Yah Abana, kuma sam driver nan baya sauri, ji nake
zanfa karɓi tuƙin”.
Da sauri ta ɗan ware manya idanunta alamar tsoro sai kuma ta langwaɓar da kai cikin sanyi
tace.
“Please kada ka amshi tuƙin nan, bana so”.
Cikin zu bawa tarin motocin da ya hango a gabansu bila adadin idanu yace.
“Toh yadda kika ce za'ayi”.
Ya ƙare maganar yana leƙa gefe da gefen hanyar ya gane, sun iso Ousman Ibn Affan Tero
Masjid ne, kuma shima masallacin jumma'a ne, duk da ya hana subi kan manyan titunan ne
saboda sanin, zasu samu an rurrufe hanyoyin yasa yacewa driver subi tsakiyar anguwannin,
cab yama mance da wannan masallacin. Bisa dukkan alamu kuma ana gab da tada iƙamane, gashi hanyar an rufesu tako ina.
“Yah Salam”. Shine abinda yace a dai-dai lokacin da yaga ta bayan nasuma motoci sunfi
takwas.
Cikin sanyi yace.
“Dole inyi salla anan fa Ishmah”.
Cikin son amintar mishi da hakan a zuciyarsa tace.
“Eh ba matsala ai Tajj kayi a wurin, ana idarwa sai ka tafi, ka samu ayi liyafar family na yau da
kai, tunda kana garin”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Toh in kashe ko in bari, zakiji sautin sallanmu”.
Cikin yanayin shaƙuwa tace.
“Bari inji karatun limamin ko zai samu rabin maki naka”.
Murmushi yayi sai kuma ya ɗan jin-jina kai kana yace.
“To an gama”. Sai kuma ya kalli Dottijon driver nashi tare da juya harshe zuwa Ethiopia's
language *Amharic* yace.
“Abu Hashim mu tsaya muyi salla a nan, kana da al'wala ko?”.
Cikin alamun tarin mutunta juna Abu Hashim ɗin yace.
“Na'am”.
Daga nan suka fara kutsawa cikin masallacin.
Kasancewar babban masallacine kuma a ɗan luƙu yake a tsakiyar anguwannin Shiyasa baya
irin cika da batsewar nan.
Cikin hikima suka samu suka shiga a har ciki, cikinma sahun farko saboda shiɗin ya kasance
mutum sanne a duniya ma baki ɗaya bare kuma ƙasarsa ta haihuwa, duk wanda aka cewa
Sheykh Afif Muhammad Taj dole zai sanshi, domin Ethiopia baki ɗaya tana alfaharin
kasancewarsa ɗan ƙasar tasu. Ahankali ya zuro ƙafarsa daga cikin mota wanda ke sanye cikin wani sau ciki baƙi mai masifar
kyau da sheƙi yayin da jikinsa ke sanya cikin wani yadi mai sulɓi da taushi Army Color daya
haska fatarsa yayin daya ɗaura Farin Suit asama Kansa na sanye da hula yayin da kwantaccen
sajensa ya sake ƙawata kyawun fuskarsa cikin sassarfa ya ƙarasa shiga harabar masallacin. Suna isa ana data iƙama.
Bayan an idar da salla an sallame, kowa yayi addu'o'insa da tasbihansa.
Shima haka Taj, a hankali ya zaro wayarshi tare da karawa a kunne murya a sanyaye yace.
“Kinji mun idarko yanzu zamu fita”.
Murmushi mai ɗan sauti tayi tare da cewa.
“Naji karatun limamin Amman bai kai naka daɗiba fa.”
Yunƙura yayi da niyar tashi sai kuma yaji ana sanarwar akwai ɗaurin auren da za'ayi yanzu ana
roƙon mutanen su ɗan dakata.
A hankali ya koma ya zauna bayan Abu Hashim.
Kana yaci gaba da mgn da Aysha.
Da sauri ya ɗago kanshi ya kalli mutumin dake sanarwar cewa.
“Dangin angofa sun fasa auren bisa wani dalili mai girma da kuma tuburewar ango na cewa ya
fasa aure.
Innalillahi wa innalillahi rajiun.
Shine abinda wani kamilin dottijon mai cikar kamala ya fara nanata wa, yayin da lokaci ɗaya
jikinsa ya ɗauki kerma tuni idanunsa suyi jazir.
Da sauri ya kuma kalli tawagar dangin angon da suka ɗauki, kayan ɗaurin aurensu irin Goro,
Dabino, cingam, da dai sauransu, sun juya sun fara fita.
Da sauri ya kuma maida ganinsa kan dottijon nan da yaga ya fara rarrafawa, ya isa gaba Abu
Hashim, wanda dai-dai wurin dangin Angon suke, cikin wata iriyar matsoracciyar murya mai
nuna dottijon bashi da ƙoshin lfyma, ga kuma gigita, hawaye na kwaranya a idanunsa ya riƙo
sawu, ɗaya daga cikin dangin angon murya na rawa cike da raunin neman alfarma yace. “Innalillahi wa innalillahi rajiun, dan Allah da son Manzon mu Muhammad (S.A.W) ku rufa min
asiri. Ayi auren nan wlh bani da wani buri da fargaba da ya wuce in aurar Adaya kafin barina
duniya.
Nayi muku magiya da girman Allah, ku bari ayi auren nan”.
Sai kuma ya fashe da zazzafan kuka.
Wanda har Aysha najin duk abinda ke faruwa, cikin sanyi tace.
“Allah tsarki, meyasa zasu fasa, dan Allah Taj ka tayashi basu haƙuri ayi auren nan”.
Ta ƙare maganar da iya gskyarta da kuma sanin irin ciwon da mahaifin yarinyar da ita kanta
yarinyar zataji, saboda ita tasan zafin dake cikin fasa aure, in ba mai ƙarfin zuciyaba, sai ta
buga ya mutu.
Shar-shar taji hawaye na kwaranyo mata, lokacin da taji sautin muryar dottijon nan ya saki
raunatacce kuka yana cewa.
“Ma'aruf ka gani ko, yan zuma a karo na uku kenan ɗaurin auren Adaya na watsewa. Ma'aruf
zuciyata zata buga saboda matsalar Adaya,
Zatayi ajalina, Ma'aruf ka bisu ka roƙesu da girman zatin Allah su cika min burina kafin wa'adina
ya cika, nasan idan na mutu nabar Adaya batayi aureba, ruhina bazai samu salamaba”.
Ya ƙare maganar da kife kanshi a jikin filar masallacin ya saki maraitaccen kuka, wanda aka kira
da Ma'aruf ɗinma kuka yaleyi.
Tajj kuwa lip inshi na kasa ya jiza da ƙarfi, sai yake misalta da ace Yah Abananshi ne ke kuka
hakan ya zaiji a cikin ransa,
Yasan ji zaiyi kamar zai suma, ya kuma tabbatar sai yayi duk yadda zai yi ya tsaida mishi
hawayen nan.
Sai kuma ya maida hankalishi kan Ishmah dake mgna cikin tausayawa.
“Dan Allah Taj ka taimakawa tsohon nan, Please ka tsayar mai da zuban hawayensa”.
Cikin sanyi murya yace.
“Please Ishmah kada kiyi kuka, kin san cewa kukanki na ƙona min zuciya ko, gaya min wanne
irin taimako zan mishi”.
Da sauri tace.
“Ka tayashi basu haƙuri ayi auren!”.
Cikin jin kukanta na hautsuna mishi lissafi yace.
“Ai har sun riga da sun tafi”.
Da sauri ya zazzaro idanunsa jin abinda tace, murya a kaɗe yace.
“eyeh hello mai kikace”.
Cikin rauni da kuma iya gskyarta kana da shesh-sheƙan kuka mai cike da rauni tace.
“Tajj ka aureta!!!”.
Da ƙarfi ya koma ya jingina da jikin gini, sai kuma ya kalli Dottijon nan da yake kuka harda
majina yana bin.
mutane yana kama hannunsu yana cewa.
“Dan Allah ka auri ƴata Adaya na baka ita.”
Mafi akasari sai su kauda kai.
A haka har ya iso gaba Taj.
Riƙe hannayensa yayi duka biyu, murya na rawa yace.
“Dan Allah dan soyayyarka da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, dan tsarkin Alkur'ani
da yake kanka a haddace, da kimar iyayenka Afif ka auri ƴata Adaya na baka ita duniya da
ƙiyima ka aureta ka amintar da ita domin irin kane mijin daya dace da ita.”
Jin kalamansa ne yasa jikinsa wani irin saƙewa yayi luƙus sai kawai ya zauna dirshan.
Kana a sashin Ishmah kuwa cikin taya dottijon nan magiya tace.
“Taj! Taj!! Taj!!!”. Sai a kira na ukun ne ya iya furta.
“Uhmmmmm”.
Cikin tausasa lafazi murya na rawa tace.
“Dan Allah dan Annabi da darajar Yah Abana da kuma ƙaunarka da Ummey da Amincinmu, da
gskyar abotarmu, da mutuntakarmu, ka aureta ka tsaida hawayen dottijon nan”.
Ya ilahi ya mujibat da'awati, yah hayyu ya ƙayyum bi rahamatika astagis, innalillahi wa innalillahi
rajiun”. Sune iya ababen da yake iya furtawa a bakinsa sai kuma yayi saurin cewa.
“Shiru Ishmah na amince zanyi wannan taimakon saboda Allah da Manzonsa da ke”.
Yayi mgnar da Yaren Hausa da zama shi da itane yasa ya fara iyawa kaɗan kaɗan.
Kana yayi Hausanne saboda yasan da wuya a samu wanda zai gane a cikin mutanen wurin,
Amman in fillancin Ethiopia yayi wasu zasu iya ganewa.
Sai kuma ya saki wani irin sassayan numfashi tare da kallon kamilin dottijon nan mai cike da
kima kamala da rauni da yake ta zubda hawayen da magiya.
“Ka taimakeni ka auri Adaya Afif kayi min wannan taimakon, in kayi min haka ka gama min
komai a aduniya, Dan Allah ka auri Adaya”.
Wayarshi ya zaro tare da rubutawa Abu Hashim text message ya tura mishi.
Da sauri Abu Hashim ya zaro wareshi jin alamun saƙo ya shigo.
Sai kuma ya jinjina kanshi tare da zaro kuɗin daga aljihunsa, kana ya irgasu, dubu 1,22000 ne
kuɗinsu na can.
Da sauri ya miƙe ya nufi mall da ke cikin harabar masallacin.
Dabino da sweets ya seyo katon bibbiyu
Kana ya dawo da sassarfa ya zauna gefen. Dottijon da har yanzu yake riƙe da Tajj yanayi mishi
magiya hawaye na ɗiga bisa tafukan hannun Taj ɗin.
Gyara zama Abu Hashim yayi tare fuskar Dottijon nan da yake gab da sumewa, cikin yarensu
Aromo yace.
“Ni Oumar Ibarahim ina nemawa, ɗana Tajuddeen auren yarka Adaya ga sadaki mu, naira dubu
100”.
Wani irin dogon numfashi Dottijon yaja tare da juyawa ya fuskanci alƙibla yayi sujudushukur
kana ya juyo ya kalli Taj tare da cewa.
“Alhamdulillah kayi haƙuri kaga na takuraka duk da na fahimci baka so. Toh Alhamdulillah gashi
mun samu wani zai aurawa ɗansa ita”.
Yayi mgnar tare da juyowa ya fuskanci Abu Hashim da ba wanda ya sanshi a cikin masallacin.
Ma'aruf ne ya kalleshi cike da son gano wani aibu ko naƙasu tare dashi.
Amma. Ina babu saboda Abu Hashim yana samu albashi mai gwaɓi a hannun Taj Shiyasa in
kan ganshi bazaka gane sana'arsa ba, to driving ɗinma da sai Taj na garine haka yasa a
wadace yace gashi mutun ne shi kamili mai haiba.
Kuma in kaga yanayisa dole yana da ɗa kamar Tajj.
Nan take kuwa a wurin aka ɗaurin auren.
Adaya da T.....
*Shi wannan littafin salon sa na dabanne ni kaina yana tsumani, ki biya koyi karatu cikin aminci
1k ne kacal fa 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta
wannan number 09097853276, ku kuma mutane Niger 1000fc ne jaka ɗaya kacal kenan
+22790899076 Zaku biya ta wurin Mommy*
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/4, 12:58 PM] Leematu: ✈️
*INDA RAI*
*BOOK ONE PAGE 4*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
*Littafin INDA RAI na kiɗine yanzu free pages ne mukeyi ku biya in saku a group, ku karanta
cikin aminci ba haƙƙin kowa bisa kanku, 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa,
sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276. Gareku mutanen Niger 1000fc
ne zaku biya jaka ɗaya kenan ga number wacce zakuyiwa magana +22790899076 Please a
mutunta shekarunta babbar macece.*
*Haɗin amarya budurwa mai ƙarancin shekaru da mai matsakaicin shekaru da kuma mai ɗan
yawan shekaru, kana haɗin amarya bazawarar da take da ragowar ƙuruciya, da mai
matsakaicin shekaru da wacce shekaru sun ɗan ja, hadi dai-dai da halittarki ƴar uwata, ƙawata,
ƙanwata, ƴata, ƴaƴata, kai harma da ke kakata, akwaisu masu maida tsohuwa yarinya, duk
mutuwa da sakewar fatar nan zata tattare da tsuke ta katse ta rayu da ni'imtaccen yayyafin
gyaran zaman aure. To wai ke mai jego ina kike akwaisu fa naku haɗin, in ma yawan* *haihuwa
yasa wurin ya sake ya kuma ƙafe, barden goyo ko ɗanyen goyo, akwai haɗinku Zaki min
bayanin me matsalarki! Sakewa ne? Rashin ni'ima ne? Rashin feeling ne, ko rashin kuzari ne
Duk fa akwai haɗinshi haɗin uwar gida ko tsakar gida duk akwai, set ɗin na hawa hawane, duk
ƙanƙantar kuɗin Customers na baya zuwa ya koma baya, ƙananan set ɗin daga 40k ne zuwa
ƙasa 35k 30k 25k 20k 15k ƙaramin haɗina ɗan autan 12k sai haɗin robor ƙasaitacciyar macen
5k. akwai manyan set ɗin daga 50k 60k 70k 80k 90k sai sha kunɗum ɗin 100k. Sai maganin
infection set 10k rabin 5k Maliƙi 5k daɗi har maɗiga 5k akwai haɗin kazar 12k akwai zabuwar
20k in dai a shirye kike ga 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, ta wannan number zaki
turo min shaidar biyanki 08069423567 itace ta Customers ɗina na kayan ɗa'a*
Tajuddeen Muhammad Tajuddeen, (Afif)
kenan saboda sunan kankanshine yaci.
Tajuddeen Shiyasa akayi masa laƙani da Afif.
Sai Afif ɗin kuma ya danne Tajuddeen ɗin.
Shiya sai na kusa da shine kaɗai suka san hakan.
Hakan yasa ko mutum ɗaya bai gane cewa dashi Afif aka ɗaura aren Adaya ba.
Shi kuwa Taj ana gama ɗaura auren bisa sunan da ƙa'idar addinin musulunci.
Yaja wani ɗimautaccen numfashi tare da zurawa, Abu Hashim idanu, ganin Dottijon nan ya
jawo hannunshi tare da cewa.
“Bismillah ko Malam Ousman muje, kaga gidana, yana nan gefen masallacin, muje in danƙa
maka hannun Adaya ka kaiwa ɗanka.”
Da sauri Abu Hashim ya juyo ya kalli Taj domin kalaman dottijon sun zo musu a bazata.
Shi kuwa Taj wayarshi da yayi mishi text message dashi ɗazu, ya kumayi mishi wani text ɗin.
Da sauri Abu Hashim ya zaro wayatarshi daga aljihu, tare da duba saƙon.
Murmushi ya ɗanyi tare da miƙewa tsaye tare da fara gaisawa da mutanen dake ta miƙa mishi
hannun daga bisani suka fita.
Taj kuwa yunƙura yayi tare da tattaro ragwar ɗan kuzarinsa ya miƙe tsaye tare da binsu a baya,
tafiya yake yi tamkar babu laka a jikinsu, tarin ƙalubalen dake gabansa a lamarin yake
hasasowa yadda zai fuskanci mahaifinsa yayi mishi wannan bayani mai kama da tatsuniya ko
mafarki, ko hikayar cikakkun marubuta mai cike da sarƙaƙiya.
Numfashi mai nauyi ya sauƙe tare da rumtse idanunsa, ya sani ko Ummeynshi bazai iya
fuskanta ido da ido wai yace mata, yayiwa kanshi aure ba, bare kuma Yah Abananshi da ya san
halinshi farin sani, baya ɗaukan wargi,
yatsunsa biyu yasa ya sharce zufan dake tsatstsapa mishi bisa goshinsa.
A hankali ya jingina jikin motarsu, tare da rumtse idanunsa, ya sani Ko babban yayansu, Hafiz
bai isa yayi aure mahaifinsu bai saniba, wanda shima yana da yaran da sun kusa aurema bare
shi, ya Salam shine abinda ya furta a tsakanin lips inshi, runtse idanunsa yayi tare daci gaba da
mgnar zuci dake tabbatar mai da cewa Ishmah na juya tunaninshi da kwanyarsa ta yadda baya
iya ƙin yin duk wani abinda zai sata farin ciki, Allah ya sani ji yake rayuwarsa bazata samu
cikakkiyar nasarar in har bai sata farin ciki ba.
Ido ya zubawa Abu Hashim da Dottijon nan da wasu mutane da basasu, gaza huduba, sunka
nufi wani gate, da yake fuskantar harabar masallacin.
Lunshe idanun yayi kana ya buɗesu, ganin sun shiga wannan gidan, wanda bisa dukkan
alamun nanne gidansu Adaya.
A wani matsakaicin Falo suka zauna,
Cikin hikima Abu Hashim ya gyara zama da bin mgnar da Taj ya rubuta mushi, ya kalli Dottijon
tare da cewa.
“Toh Alhamdulillah yanzu dai naga gidan, zan koma nawa gidan kuma in shaidawa mahaifiyar
yaron da shi kanshi yaron, dan a kimtsa inda zata zauna a kuma shirya mata, tarbar da ta
dace.”
Cikin jin daɗi Dottijon yace.
“Kai Alhamdulillah naji daɗin jin haka kuwa, amman yaushe za'azo ɗaukarta”.
Cikin sauri yace.