Showing 60001 words to 63000 words out of 80879 words
Chapter 21 - Inda Rai B1 True Books Available Rubutawa Aisha Aliyu Garkuwa .pdf
tare dani, in nayi nesa
dake ji nake bani da farin ciki, bayan iyayena ba fuskar da nake gani inji daɗi sai taki.
in gani gaki sai inji ina farin ciki ya mai sabuwar amarya”.
Ya ƙare maganar lips inshi na rawa tamkar maijin sanyi.
Ita kuwa Ishmah tuni jikinta ya saki rawa.
Da sauri ta janye hannunta kana ta naɗeshi cikin gyalenta.
Shi kuwa Taj a hankali ya buɗe marfin motar kana ya fita.
Binshi a baya tayi, suna shiga yayi sallama da Yan Muhammad da yaran kana ya kama hannun
Laylah suka shiga inda zai sadashi da wurin jirgin.
Su kuwa suka juya gida cike da kewar Laylah da Uncle Taj ɗin.
Ƙarfe ɗaya dai-dai jirginsu ya tashi zuwa Abuja.
Biyu saura 13 minute suka sauƙa a Abuja.
Sallan azahar sukayi tare da cin pepper chicken da Ishmah ta haɗa musu, tare da shan Yoghurt
fruit data haɗa musun.
Biyu dai-dai jirginsu ya fara ƙugin tashi.
A hankali yace.
“Maeesha yanzu jirgin zai tashi zan bar ƙasar Nigeria cike ƙuncin zuciya domin ji nakeyi tamkar
na bar dukkan farin cikina a ƙasar”.
Cikin sanyi tace.
“Taj nima ji nakeyi tamkar ka tafi da dukkan farin ciki na, rashin Daddy na ya dawo min sabo”.
Daga nan dai sukayi sallama kana suka tashi sai Ethiopia.......
Washe gari Ranar Monday zaune yake gaban Yah Abana da Ummeey sai kuma Mom Amal da
Yah Hafiz yana basu labarin yadda ƙasar Nigeria take da irin karrama da ƙaramcin daya samu a
wurin mutanen ƙasar More especially malam izala da ɗarika.
Numfashi mai nauyi Malam ya sauke zuciya cike da saƙa yace.
“Babana wanne state da wanne kaje?”.
Gyara zansa yayi tare da cewa.
“forko dai Abuja Adamawa, Borno, Zamfara, Kano, Bauchi”.
Da sauri yace.
“Har Bauchi!!?”.
Kai Taj ya jinjina mishi tare dare da cewa.
“Acan na samu wani dottijon malami Sheykh Tajuh Usman Bauchi.”
Sai kuma duk ya basu labarin yadda sukayi da kana ya daura da cewa.
“Yah Abana harda sandarsa ya bani yace in kawo maka, ni kuma ya bani alkyabbarsa harda
rawaninsa”.
Tunda ya fara bashi labarin Malam ya tsuke fuska tamkar bai taɓa dariya ba, babu wannan
annuri da nuna soyayyar cikin sanyi Ummeeyshi kuma tace.
“Babana kaci abinci mana”.
Yana kallon sauyin fuskar mahaifin nasa yace.
“Ummeey daga gidan Addawa nake fa, acan nayi breakfast”.
Sai kuma ya kalli Mom Amal dake cewa.
“Ya baka zo mana da Laylah ba?”.
Ta ƙarashe cike da makirci, yana ɗan gyara zamansa yace.
“Har zamu taho tare to, kuma ashe da zazzaɓi ta kwana, na bata magani na barta tayi bacci”.
Wani irin makirin murmushi tayi tare da cewa.
“Da alama dai Laylah itace ta biyunka, gashi tun kan ayi aure ta zama jakar ratayawarka!”.
Cikin ƙyamata da nesanta da kalmar da tazo mishi a bazata, zuciya cike da girman matsayin da
ya tsayawa Laylah na uba uwa dangi, da iyakar gsky yace.
“Wa'iyazubillah Laylah bata cikin sahun matan da ya kamata ace kun siffantasu da haka, ni
Laylah a matsayin ƴar cikina na ɗauketa, kuma jinta nake a jikina tamkar ni na haifeta, ni zan
zame mata uba da uwa da yayun data rasa. Dan Allah Mom karki na kamanta wannan a
zuciyarki!”. Ya ƙare maganar da iyakar gskyarsa.
Ita kuwa Mom da sauri tace.
“Toh ya haramta ne?”.
Hannu Malam ya ɗaga mata tare da cewa.
“Haba tunda yace abar mgnar ai sai mu barta ko”.
Sai kuma ya kalli Taj ɗin tare da cewa.
“Kace yau kana da tafiya zuwa Qatar ko?”.
Kai ya jujjuya tare da cewa.
“A'a American Passingers zan dauka, in na sauƙesu ne zan ɗauki na Qatar, daga Qatar ɗin zan
juyo nan”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Allah ya taimaka, ya batun aikin Asbitin da sa mishi suna”.
Yana amsa Apple ɗin da Ummeeyshi ke miƙa mai yace.
“Eh anyi komai an gaba duk abinda ya dace, an kai sabbin kayan aikinma”.
Ya ƙare maganar yana dan murza Apple ɗin alamun da sauran abinda yake son faɗi.
“Sunan fa Tajmuh hospital aka sa ko?”.
Mom Amal ta tambaya.
Ba tare da ya kalleta ba yace.
“AL-AHLI AFISHA HOSPITAL”.
Ya bata amsa a takaice.
Da sauri tace.
“To me yaci sunan Malam ɗin, kuma waye Sha ɗin kuma”.
Yah Hafiz ne ya gyara zama tare da cewa.
“Sobada wannan Hospital ɗinsa ne, na kanshi bana Malam ba babu ko asin malam a ciki, batun
wani Sha kuma ai sirrinsa ne, tunda kin gane Afi ɗin firkon sunansa ne”.
Wani mugun kallon ƙasa-ƙasa ta watsa Yan Hafiz ɗin.
Shi kuwa Taj gaba ɗaya hankalinsa na kan sauyin mahaifinsa.
Ummeeyshi kuwa murmushin jin daɗin bayanin Hafiz tayi yoh ai gwara su sani kada su
ɗaurawa ɗanta jakar tsaba kaji su bishi su tsatstsageshi suce mahaifinsu na fifitashi, ita a
burinta ma tunda Kabeer ya gama karatunsa tunda shina likita ya karanta zata sa Taj ya bar
mishi ragamar Asbitin.
A gidansu Adaya kuwa, cikin tsananin damuwa Abpu ya kalli Ummin Adayan tare da sauƙe
numfashi mai nauyi kana ya kalli Ma'aruf tare da cewa.
“Zuwa yanzu dai na fara tsinkewa da lamarin mutumin nan fa, yasa an ɗaura auren Adaya da
ɗansa, yanzu mako huɗu cib har an shiga na biyar Amman shiru bashi ba alamarsa bare
ɗansa”.
Sai kuma ya kalli Ummin Adayan dake sauke ajiyan zuciya alamun tasha kuka.
“Shiyasa ni banso ayi irin wannan aurenba, da barinta akayi ta zaɓa da yafi mana”.
Ta faɗi tana zubda siraran hawayen.
“Kayya Ummi ai dole ce tasa Abpu yiwa Adaya irin wannan bauɗeɗɗen auren saboda gudun
lalacewarta da raye-raye nan data sawa ranta”.
Cewar Ma'aruf.
Cikin sanyi Ummin tace.
“Toh yanzu me daurin auren ya hana, tun jiyafa data fita da Asina Izzin gata har yanzu bata
dawoba”.
Cike da damuwa Abpu yace.
“Kema da laifinki, kin sake mata fuska yasa bata tsoron fita”.
Da sauri tace.
“Wallahi Allah kenan ba yadda banyi da itaba kada ta fita, Adaya ta fetsare wai tana cemin
dolefa ta fita wai yanzu saura watannu su tafi gasar rawan da aza'ayi dan haka duk watannin
nan na yin rihazal ne”.
Cike da takaici Abpu ya miƙe ya fice daga Parlour.
A hankali ya shiga Parlour Addawa, cikin sanyi ya zauna bisa kujerar 3 sitter, ɗan kishinƙida
yayi tare da rumtsa idanunsa.
Yau tunda gari ya waye yake ta kiran Ishmah bata amsa kiranshi yayi mata text message ba
amsa, yayi mata mgn ta Whatsapp ɗin da tasan domin ta kaɗai yake yinsa ta buɗe ta kuma gani
ba amsa.
Ɗan gajeren tsaki yaja tare da juyawa rufda ciki yana lumshe idanunsa haka nan yake jin wani
irin sassayan yanayi na gameshi a kanta.
Addawa kuwa wacce tun amsa sallamarsa da tayi bata kuma cewa, komaiba haka shima bai
kuma ce mata ko ƙalla ba.
Shi yasa ta zira mishi idanu.
“Lfy kuwa!?”.
Kake ta faman jan tsaki”.
A hankali ya ɗan yunƙura zaune tare saurin jawo wayar tashi jin kira ya shigo, a zatonshi itane,
sai kuma yaga Aunty Rashida ne, cikin sanyi ya amsa kiran tare dayin sallama kana ya ɗaura
da cewa.
“Afwan Aunty Rashida jiys da dare muka iso, yau kuma kin san ranar Ummeyn da Yah Abana
ne”.
Shiru ya ɗanyi sai kuma yace.
“In sha Allah zan zo, Amman yau zan tashi zuwa American, sai na dawo zanzo sai muje gidan
Aunty Maryam ma”.
Daga nan dai suka ɗanyi hira kana ya katse kiran, tare da tashi zaune jin Addawa tana ta mita.
“Ba wanda ka rainawa wayo sai ni, ka ɗebo damuwa kazo kaƙi gaya min me matsalarka ka sani
a damuwa, kaje ka tasa iyayen ka mana, wlh ina jiye maka tsoron shege zurfin cikin kan nan
zai jaza maka matsa a rayuwar ka, yanzu menene kake yiwa tsakin?”.
A hankali yace.
“Ishmah ce”.
Wani fahimtaccen murmushi tayi tare da cewa.
“Me kuwa tayi maka”.
Shafa sajensa yayi tare da cewa.
“Yau tunda gari ya waye naketa kiranta, bata piking call ɗin na nayi mata text no raspond. Tun
jiya da darefa da muka sauƙa ta kirani bata kuma kirana ba”.
Numfashi mai sanyi ta fesar tare da cewa.
“Toh da nake ce maka, bazaka iya rayuwa ba tare da itaba, ai gani kake kamar shirme tsufa ne,
gani wuni ɗaya rak ne baka jita ba duk ka damu, sonta kakeyi sonka takeyi kuna ta yaudarar
zuƙatanku in na faɗa gani kake bansan soba, alhalin kuma kaine nan baka san soba”.
Kwaɓe fuska yayi tare da cewa.
“Toh in ana son juna kuma sai aƙi ɗaukar wayan juna, Kinga ai da tunaninki hakanne da baza ta
ƙi amsa kirana ba”.
Da sauri tace.
“Wata ƙil rashin nuna kana sonta ne yasa tayi fushi da kai, tukun nama daya kuka rabu ko ka
mata wani laifi”.
A hankali ya fara mgnar zuci da baisan tana fita ba.
“Ni ba laifin da nayi mata, kawai dai nayi mata nasihar tayi aure ko dan sa mahaifinta farin ciki,
domin ya shaida min baya jin daɗin zamanta haka”.
Sai kuma yayi saurin kallon Addawa jin tana cewa.
“Hmmm Allah ya kyauta, in tayi tsami ai kwa fitar da ita in kunji yana gab da kasheku”.
A hankali ya miƙa mata hannunsa tare da cewa.
“Bani wayarki”.
Miƙa mishi wayar tayi tare da miƙewa ta nufi kitchen.
Shi kuwa number Ishmah yasa tare da kiranta bugu ɗaya ana biyu ta amsa kiran.
“Assalamu alaikum Addawa”.
Cikin sanyi ji murya a narke yace.
“Kiyi haƙuri dan Allah kada ki hukuntani, da nesanta kanki dani, kada ki hanani jin muryarka
Please abotarmu bata cancanci hakaba Maeeshah”.
Sassayan numfashi ta fesar tare da cewa.
“Taj kainefa ka bani shawarar inyi aure ko?”.
A hankali yace.
“Ehhhh”.
Tana mai rumtse idanunta tace.
“Toh shiyasa na fara nesanta da kai domin in nayi auren ai bazai yiwu muci gaba da abotarmu
ba”.
Cikin wani irin damuwa yace.
“Kin mance cewa, kince ni dake ba abota bace ƴan uwantaka ce”.
Da sauri tace.
“Amman ai duk da haka in dai nayi aure mgnar da mukeyi zata haramta”.
Cikin sanyi murya yace.
“Dan Allah ki bar mgnar nan Maeeshah ki bari in kinyi auren nayi miki alkawarin nida kaina zan
nesanta dake, irin nesantar da bazaki sake jina da ganina ba”.
Yayi mgnar da jin cewa kamar nesanta da ita zaisa ya nesanta da rayuwa.
Jin yadda yaketa mgnar cikin sanyi ne yasa tace.
“To ba matsala yanzu dai lokacin salla yayi sai anjima zamuyi waya”.
Da sauri yace.
“Kinyi al'ƙawari”.
Cikin jin bazata taɓa yi nesanta da shiba tace.
“Eh Taj nayi al'ƙawari zanci gaba da yin waya da bestie na”.
Daga nan sukayi sallama.
Ganin lokacin salla Magrib yayi yasashi yin al'wala ya wuce gidansu.
Domin in yana gari shike limancin a masallacin kamsusul salawat na ƙofar gidansu.
A daren ranar jirginsu Taj ya tashi zuwa America.
Washe gari da safe, Meymey ce zaune a Parlour tallabe da kafaɗar Laylah daketa kwaza amai
gaba ɗaya jinkinta yayi luƙus.
Cikin nuna tsantsar kulawa tace.
“So sorry, tashi mu tafi Hospital aman nan ya isa haka”.
Cikin galabaita da muguwar kasalar da ta kwana dashi tun randa suka dawo Nigeria ta yunƙura
ta miƙe.
Da taimakon ta suka tafi Aabet Hospital.
Bayan awa ɗaya da zuwansu ne suka fito kai tsaye gidan su Taj ta wuce da ita.
A Parlour Ummeyn suka zauna.
Bayan ta gaida Ummey cikin girmamawa tace.
“Malam yana cikine”.
Cikin kulawa da jin daɗi Ummey tace.
“Eh yana ciki muje ko”.
Ta ƙare maganar tana kallon Laylah dake kwance tayi luƙus sai kuma ta bita da ido ganin ta
miƙe da sauri ta nufi Dinnin area.
Yawu mai yauƙi ta ɗan tofar a washing hand baby dake Dannin area ɗin.
Sai kuma ta dawo ta zauna, ita kuwa Ummeeyshi cike da mamakin irin wasu sauye-sauyen da
ta gani tare da yarinyar ta miƙa mata hannun tare da cewa muje ku gaida malam.”
Miƙewa meymey tayi tana mai ɗan latsa wayarta.
A Parlour suka samu Mom Amal da Aryan sai Kabir.
Suna shiga Mom Amal ɗin ta zuba wa Laylah idanu tana ƙare nazartanta.
Ita kuma Laylah cike da azabebben kasalar data buwayi rayuwarta ta tsuke bakinta saboda
yawun daya sake cika mata baki so take ta sake tayi ta bawa Ummeey labarin Ishmah dasu
Minat da Rahma Amman ina duk ta rasa kuzarinta.
Gefen Ummeey ta zauna tare da lafewa a jinkinta.
Cike da tsananin mamaki Mom Amal tace.
“Ikon Allah bag ɗin Taj ya haka saikace mai laylayin ciki”.
Cikin tsananin sinkewar zuciya Ummeey tace.
“Subahallahi wannan wacce iriyar mgna ce haka Mom Amal”.
Ta ida mgnar tana kallon yadda Laylah ta sake.
Aryan ne yayi saurin cewa.
“Ai kam tayi kama da masu ciki”.
Sai kuma ya kalli Kabir dake cewa.
“Ni kuma gani nayi tayi ƙiba”.
Ita kuwa Meymey tsuke fuska tayi tare da cewa.
“Kai Mom ai sai kisa zuciyata ta buga in mutu da wannan mummunan hasashen naki akan, yar
amanan tamu, Malaria cefa ta kwatso a Nigeria wata ƙil harda taypot”.
Dai-dai lokacin Malam ya fito daga dakinsa bisa dukkan alamu yaji duk abinda suke tattaunawa
a kai saboda jin yana cewa.
“Toh kin kaita asibiti ne Mamana?”.
Cikin sauri Meymey tace.
“Eh Malam yanzuma daga Hospital ɗin muke, kuma ta samu magunguna”.
Cikin gamsuwa yace to Allah ya sauƙawa.”
Da Amin suka amsa baki ɗayan.
Bayan kwana biyar.
Adaya ce tsaye a tsakiyar babban hall ɗin da suke ɗaukan darasin rihazal na gasar rawan da
zasu tafi nanda watanni uku zuwa huɗu, wanda shine kaɗai babban burinta.
Wani irin shu'umin waƙa da kiɗi rawarsu na Ethiopia's Gerls aka sake mata, yayinda itace
jagorar tawagar shiyasa itace a gaba.
Asina agefen damanta sai kuma Bititi a gefen hagu wacce ita arniyace.
Sai kuma bayansu Izzin ne a gabanta sai wasu maza uku.
Wani irin rawa sukeyi na kafaɗa da kaɗa ƙirji.
Rawa sukeyi kai kace babu ƙashi a jikinsu.
Shi kam Izzin rawar yakeyi cike da ficewar hankali sabo yadda ƙirjin Adaya ke hautsuna mishi
lissafi, dan wani irin juyi da tsalle tantsama-tantsaman ƙirjinta ɗin sukeyi tamkar zasu rabu da
ƙirjinta su zube ƙasa.
Gigatashi da sukayi ne yasa ya sauya salon rawar tasu, da ƙara kusantarsu ta baya.
Kana yasa hannun damansa ya zagaye lafeffen cikinta, tare da ɗaura na hagunsa kuma saman
ƙirjinta.
Haka suma sauran sukayi.
Matse cibiyoyinsa yayi da masifar ƙarfi ya rinƙa tsalle da karya kafaɗarsa haka yasa itama bada
ƙaimi, burinta yasa ta gaza tantance abinda yake mata, ya saɓa tunanin.
Sauranma haka suke rawan.
Yayinda couch da sauran fara yi musu tafi da ihu. Haka dai suka kwana wannan jarabar rawar.
Koda garin ya waye a gajiye ta dawo gida.
“Yanzu kenan Adaya ki rantse lalata rayuwarki zakiyi a banza ki zubda kima da darajarki na ɗiya
mace kuma musulma”.
Cewar Umminta hamma mai cike da bacci tayi tare da cewa.
“Dan Allah ki bari in nayi bacci na farka zamuyi mgn”.
Ta ƙare maganar da sake video da sukayi a TikTok.
Sai kuma ta cilla wayar kan gado ta shigo Bathroom.
Ganin haka ne yasa Umminta fita rai cike da ƙuna.
Kwanan Taj takwas da tafi kafin ya dawo, gidansu ya fara wucewa kai tsaye saboda
Ummeynshi ta shaida mishi Meymey da Laylah suna gida.
Cikin mamaki yake kallon Laylah da tayi wani irin fari na fitar hankali har wani yellow-yellow tayi,
musamman goshinta da yake wani irin ƙelli, kana tayi wata ƙibar da bai santa da shiba.
Cikin mamaki yake lallonta sai kuma ya ɗan juyo ya kalli Meymey dake haɗa mata tea.
“Yah Salam wai me yake damunta ne?”.
Fuska a tsuke tace.
“Ni ya kamata inyi maka wannan tambayar, tunda ni ba likita bace”.
Cikin tsuke fuska yace.
“Bana son mgnar banza, ba kece kika kaita asibiti ba”.
Sai kuma ya ƙare maganar da jawo hannun Laylah yace.
“Taso mu tafi Hospital”.
Da sauri Ummeeyshi tace.
“Yanzu fa suka dawo daga Asbitin”.
Sai kuma ta kalli Zakiya dake miƙawa Laylah ɗanyen dabino irin mau gafin nan da tace tana so,
cikin tsoro Ummeey tace.
“Kai nifa al'amarin nan ya fara bani tsoro, duk fa abubuwan da Laylah keyi na masu juna ne”.
Bai fahimci mgnar Ummeyn ba bare ya damu.
“Zuwa yanzu dai nima na fara zargin da Mom Amal takeyi cewa Laylah nada ciki ne”.
Baima jitaba bare ya fahimci me take faɗa.
So kawai ɗaukar Laylah yayi suka tafi Hospital.
Yayi mata ƴan gwaje-gwaje kuma basu ga matsala tare da itaba.
Sai ɗan Malaria ɗin tsarabar Nigeria daga asibitin gidan Addawa ya wuce da ita.
Kusan ƙarfe goma na dare ne Meymey ta kalli Ummeynshi cikin sanyi tace.
“Hmmm kinga har yanzu bai dawo ba ko”.
Kai Ummeey ta jinjina tare da cewa.
“Bari in kirashi”.
3 miss calls tayi mishi Amman bai ɗauka ba.
Shi kuwa Taj tuni sun koma gida shida Laylah ta wuce ɗakinta.
Shi kuma ya wuce side ɗinsa.
A zatonsa ma Meymey ta dawo.
A Parlour ya zube woyoyinsa bisa senter table dake tsakiyar Parlour shiyasa baiji kiran
Ummeeyshi ba.
A hankali cike da alamun gajiya da kasala da nannauyan baccin da yakeji.
Mai ya ɗan shafa kana ya fesa turare, ɗaya daga cikin tattausan towel nashi da sune na
baccinsa ya zare tare da ɗaurawa a ƙugunsa.
Bakin gadon ya zauna tare da yin addu'a ya shafa kana ya kwanta kamar yadda ya saba a
rayuwarsa daga shi sai Towel ko jallabiya haka yake kwana.
Yana kwanciya bacci yayi awon gaba dashi.
Cikin sanyi Meymey tace.
“Ummeey asa ko Kaber ne ya maidani dan nasan Yah Afif in dai yana tare da Laylah baya tuna
komai”.
Ta ƙare maganar da alamun takaici.
Ɗan ƙwaffa Ummeey tayi kana ta kira Kabir ɗin yazo ya maida ita.
Alhamdulillah yanzu kasalar da sauƙi sosai tunda ya haɗa mata magunguna sai yawune dai har
yanzu.
Bayan kwana biyu da safe.
Laylah