Showing 72001 words to 75000 words out of 80879 words

Chapter 25 - Inda Rai B1 True Books Available Rubutawa Aisha Aliyu Garkuwa .pdf

cikin kid’ima had’i da gigituwa suke kallonsa
hawaye na zuba a idanunsu.

Yah Abana kuwa kallonsa ya mayar kan Meymey dake zaune cikin tsukakkiyar fuska yace.
“Meymey me kika ce ranan?”

Baki ta bud’e cikin zubda hawayen munafurci tace.
“Abbah wallahi Yah Afif shi yayiwa Laylah ciki”.
Cikin sauri Hajiya Babba tace.
“Toh me hujjarki Sannan menene Shaidar ki?”

Cikin shesh-sheƙa ta yi wa Taj da kansa ke ƙasa wani irin kallo kana tace.
“Ina da hujjoji da yawa da kuma shaidu”.

Lokaci d’aya Yah Abana cikin rashin walwala had’i da tsuke fuska yace.
“Menene shaidun ki?”
Tana goge hawayen dake zubo mata tace.
“A tambayi ita Laylah ɗin”.
Da sauri Yah Abana ya juya ya kalli Laylah sai kuma ya maida kallonsa ga Taj.
Taj kuwa juyawa yayi yana kallon Laylah haka zalika duk wanda ke cikin Falon Laylah yake
kallo.

Sabanin Momyn Meymey data zubawa ƴar Tata Idanu tana mai Binta da wani irin kallon
tuhuma.
Laylah kuwa kanta ta sunkuyar ƙasa.

Cikin murya mai cike da damuwa da tsantsar tashin hankali daya bayyana asaman fuska Yah
Abana ya kalli Laylah tare da cewa.
“Laylah”.
Kanta a ƙasa tace.
“Na'am”.
Sake kiranta yayi amsawa tayi batare data ɗago kanta ba.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya ya sake kiranta akaro na uku tare da cewa.
“Ɗago kanki ki kalleni”.
Ahankali ta ɗago kanta ta kallesa.
Yana mai jin bugun zuciya yace.
“Kinsan akan me ake magana?”.
Kai ta gyaɗa.
Ɗan muskutawa yayi tare da faɗin.
“Magana zakiyi”.
Cikin shesh-sheƙan kuka tace.
“Eh”.
Yana mai runtse idanunsa yace.
“Kinsan cewa ance kina da ciki a asibiti?”
Jikinta na tawa tana me kokarin danne kukan dake taso mata tace.
“Eh”.
Cikin sanyi gami da tsoro had’i da fargaba Yah Abana yace.
“Laylah waya Miki ciki?”.
Kusan baki ɗaya zukatan mutanen dake Falon bugawa yake musamman ma masoyan Taj.

More especially Ummey zuciyarta yafi na kowa bugawa.
Laylah kuwa cikin sanyi da rawar murya tace.

“UNCLE TAJJ NE!!”

Lokacin ɗaya Taj yaji baki ɗaya ilahirin jikinsa yana narkewa kamar an shanye jinin jikinsa ji
yake tamkar yana zama yashi yana narkewa jin yanda kalmar ya daki ƙoƙon zuciyarsa cikin
sauri ya juya ya kalli Laylah sai kuma ya juya ya kalli Meymey da ta saki wani Murmushi wanda
daga shi sai Ubangijin daya haliccesa suka san manufarsa.
Da sauri Aunty Halima da jikinta ke rawa ta matsa kusa da Laylah’n cikin tarin damuwa da kuma
tashin hankali tace.
“Laylah kiji tsoron Allah ki faɗi gaskiya Uncle Taj ɗinki nefa”.

Kai Laylah ta jinjina cikin zub da hawaye tana me ci gaba da sakin shesh-sheƙan kuka tace.
“Wallahi shine kullum in ya dawo gari aɗakina yake kwana kuma yace idan na faɗa zai
yankani…”

A yanzu kam baki ɗaya ilahirin jikin Taj karkarwa yake da tsuma idanunsa sunyi jajur sun kada
tamkar wuta, yayinda yake jin kamar ana kwara masa narkakkiyar dalma tun daga tsakar kansa
har zuwa k’asan k’afafunsa, tabbas aduk rayuwarsa bai tab’a ganin tashin hankali da masifa irin
wannan ba. Yah Abana kuwa baki daya idanunsa ne suka rikice tare da sauya launi suba farare ba haka
kuma su ba jajaye ba, kar-kar-kar haka jikinsa ke rawa.
Laylah’n kuwa kuka ta ci gaba da rerawa batare data kuma yin magana ba.

Yah Hafiz kuwa cikin wani irin yanayi na tsoro da kiɗima jikinsa na rawa yace.
“Meymey kiji tsoron Allah kisan abinda kike faɗa”.
Sai alokacin Uncle Jibril ya dago Kai ya kalli Yah Hafiz tare da cewa.
“Hafiz Mamana bata ƙarya tun tana ƙarama ban shedeta da ƙarya ba”.
Cikin takaici da wani irin yanayi Momyn Meymey ta katsesa da cewa.
“Ɗan Adam yana iya sauya hali akowani lokaci Alh ka daina shaidar Meymey”.

Cikin sauri Yah Abana ya karɓi maganar da cewa.
“Kamar yanda kuma shima Afif dan Adam ne da zai iya sauya halinsa akoda yaushe ba.”

Ummey kuwa cikin tashin hankali marar misaltuwa take kallonsa kana murya na rawa cike da
tarin d’imuwa had’i da karyewar zuciya tace.
“Babana kayi magana! kayi magana Afif ka wanke kanka kace wani abu!!”

Me zaice? Bazai iya cewa komai ba, bazai iya ba, kansa juyawa yake yana jin kamar mafarki
ne, zuciyarsa tayi masa mugun nauyi, yana jin kamar ana caka masa mashi akan k’ahon
zuciyar nasa, komai ya riga da ya k’wace masa, baida wani abunyi sai kansa kawai da yake

girgizawa, again ya kasa magana jikinsa ne kawai keta karkarwa.

Mom Amal kuwa cikin wata murya me ɗauke da wasu irin manufofi da ita kaɗai tasan ma'anar
su tace.
“Wannan ma bai isa hujja ba Meymey idan kina da wasu hujjojin sai ki fito dasu mugani ”

Cikin sauri Meymey ta ciro wayarta ta bud’e tare da shiga Gallery bayan ta shiga kan abunda
take son shiga ta juyo da screen d’in wayar zuwa fuskar Yah Abana.

Da sauri Yah Abana ya rumtse idanunsa sai kuma ya miƙe tsaye yayin da numfashinsa ke fusga
yana ƙoƙarin ɗauke wa.
Sakamakon ganin hoton Taj da yayi tsaye tsirara Laylah na durƙushe ta riƙe gabansa.
Da wani irin firgita had’i da gigita mai tsanani ya fara cewa.
_“Auzubillahi minarshaiɗanir rajim Auzubillahi da kai Tajudden Subhanallahi da kai Tajuddeen
ka ƙazanta ka barranta daga zuri'ata ka barranta daga ahalina.“_

Taj kuwa kansa ya soma girgizawa cikin son yaga abinda Mahaifinsa ya gani da ya kiɗimashi
haka.

Uncle Jibril kuwa cikin sauri ya miƙe ya karbi wayar daga hannun Meymey yana kallo cikin
tashin hankali yace.
“Innalillahi wa inna ilaihirraju’un! Afif ka zama guba ka zama ƙazanta acikin al'umma wannan
wani irin nasiface Tajudden wace rayuwa ka zaɓawa kan ka”.
Ya ƙare maganar tare da sake wayar ta faɗi ƙasa, haka yasa ta ɗan sule zuwa gaban Taj ɗin.

Shi kam Taj ya kasa tantance yanayin da yake shin araye yake ne ko ko kuma amace? Saboda
ganin tabbas shine a hoton kuma tabbas tsirara yake, kuma tabbas Laylah ce gabansa
durƙushe tana riƙe da al'aurarsa, so yake ya rufe ƙwayar idanunsa ya buɗe ko zai daina ganin
ɗigon tawadan Allah da yake a saman mararsa wanda yasan duk duniya banda iyayensa da
suka raineshi a ƙuruciya babu wanda yasan dashi.

Cikin kuka Meymey tace wlh gashi in ba shi bane ya faɗa.
Cikin wata iriyar muryar dake cike da hargitsi Yah Abana yace.
“Tajjuddeen wai kaine a hoton nan!?”.
Cikin jin ƙahon zuciyarsa na gaba da faso ƙirjinsa murya na rawa yace.
“Eh Yah Abana ”.
Yayi mgnar da iya kar gskyar sanin cewa yess tabbas shi ɗin ne.

Ummey kam kuka mai tsanani ta fashe dashi ta kasa magana haka zalika sauran ƴaƴanta da
mafi akasarin Mutanen falon...

Meymey ko gyara zama tayi tana matsar ƙwalla tace.
“Kuma har Video ma akwai”.

Cikin sauri Taj ya ɗago kansa jin yanda Yah Abana ya kira sunansa atsawace.
Ahankali ya ɗago raunatattun idanunsa da suka ciko da k’walla suna sheƙi ya kallesa jin yana
cewa.

“Afif ka tashi ka fitar min agidana kabar min gidana bari na har abada bana son ganinka.
Bana son sake kallon wannan ƙazantacciyar fuskartaka arayuwata Afif bana son ka sake
shigowa cikin gidana.
Wallahi Allah kenan idanka sake yarda mu kayi ido huɗu Allah ya isa tsakanina da kai!!!”

Cikin tsananin ruɗu mutanen dake falon ke kallonsa.
Passs sautin fashewar glass cup dake hannun Yah Abduraham dake bayan Taj ya ratsa
kunnuwansu.

Shi kuwa Malam cikin tsanar halayyar Taj ya cigaba da cewa.
“Kaje na sallamawa duniya kai Afif.
Na barrantarwa duniya kai na cireka daga cikin ƴaƴana daga yau ka fita acikin ƴaƴana.
Tajudden daga yau Allah ya isa idan har ka sake ambaton sunana a bakin ka matsayin
mahaifinka”.

Cikin tsananin kaɗuwa mai gauraye da ruɗani Yah Hafiz da Yah Yusuf suka runtse idanunsu
suna masu girgiza kansu Yah Abdurrahman kuwa wani sanyayyan kuka ya saki mai cike da
ɗimuwa ganin halin tashin hankali da ahalinsa ke ciki.

Su Aunty Maryam kuwa, tamkar an daskarar dasu da dusar ƙanƙara haka suka zama.

Ummu Aryan ko da Hajia babba riƙe kai sukayi.
Mommyn Meymey kuwa da ƙarfi tace.
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”.

Yah Abana kam cikin ƙunan zuciya da tsananin fushi ya cigaba da cewa.
“Daga yau ka yanke sunana daga cikin bakinka bana buƙatar ka acikin rayuwata na barrantar
da kai daga cikin zuri'ata ku kuma kuji ku shaida dalilin da yasa na taraku”.
Sai kuma ya dire maganar yana kallon ƴaƴan nasa.
Rai cike da ƙunci ya sauke ajiyar zuciya tare da juyawa falon yana kallon ƴaƴansa yayin da
numfashinsa ke sama da ƙasa alamar yana son barin gangar jikinsa yace.
“Ku kuma kuji ku shaida duk wanda ya sake mu'amala da Tajudden Allah ya isa ban yafe masa
ba, na kuma tsine masa duk wanda ya sake mu'amala dashi bani bashi, ku kuma Matana duk
wacce ta kiramin sunan Tajuddeen zata ga fushina, kai kuma Tajuddeen ka tafi kai bazan tsine
maka ba, kuma bazan maka baki ba, dan laifin da kayi ya isheka tsinuwa, kawai ni sharaɗin
tsinuwana idan ka sake yarda mukayi ido biyu da kai to akan igiyar auren mahaifiyarku kuma
bazan yafe maka ba muddin kayi sanadin rabani da Fatima”.

Wani irin kuka mai gunji Aunty Halima, Aunty Maryam, Aunty Rashida suka sake suna masu

shiga ɗimuwar jin abinda mahaifin nasu ya faɗa.
Haka ma sauran Matan Mom Amal kuwa fuskarta ba yabo ba fallasa baza ka gane shin farin
ciki take ko akasin saba.
Tajudden kuwa kansa na ƙasa ji yake tamkar almara ne ji yake shin mafarki yake ko ko afarke
baki daya ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa sun gaza auna kalaman Yah abanansa...

Yah Abana kuwa cikin wani irin kunci zuciya mai tafe da nadamar kasancewar Tajudden jininsa
ya cigaba da cewa.
“Idan ka sake yarda kayi ka nunani a matsayin mahaifinka Allah ya isa ban yafe maka ba idan
ka yarda ka sake shigowa gidan nan ko kuma ka sake magana da ɗaya daga cikin Ahalina ban
yafe maka ba kuma akan igiyar Auren Mahaifiyar ka...
A dai-dai lokacin da yake fadar haka kuma Ummey taja wani dogon numfashi mai nauyi take ta
fadi asume.
Lokaci ɗaya kukan Aunty Maryam Aunty Halima Aunty Rashida ya sake tsananta
Yah Yusuf da Yah Hafiz kuwa da rarrafe suka isa gaban Mahaifinsu kana suka riƙe ƙafafunsa
tare da cewa.
“Yah Abana kayi haƙuri Tajuddeen bai cancanci wannan abin ba,Wannan hukunci ya masa
tsauri kuma muma ya mana tsauri Yah Abana kayi hakuri kada ka yanke wa Tajuddeen hukunci
cikin fushi”.
Yah Abdurrahman kuwa da ƙarfi ya matso yana buga kafaɗar Tajuddeen tare da cewa.
“Afif kayi magana Tajudden ka wanke kanka Tajuddeen ka wanke zargin da Mahaifin mu yake
akanka Nasan cewa baka aikata ba”.

Taj kam ya kasa motsa laɓɓansa bare ya iya sarrafa harshensa wajen magana.
Aryaan da Kabeer kuwa duk da irin tsanarsa da kuma haushinsa da suke ji sai da hukuncin da
Yah Abana ya ɗauka ya girgizasu...

Cikin sauri Taj ya miƙe jin Yah Abana na cewa.
“Ba naso ka ƙara koda 5 minute ne acikin gidana idan ka ƙara ban yafe ba Tajuddeen in ka sake
kusanto inda mahaifiyarka take ban yafe ba kuma wallahi akan igiyar Aurenta su Maryam kuma
na rabaka dasu”.
Ya kai ƙarshen maganar tare da faɗawa kan kushin .
Cikin kifewar tunani da cushewar zuciya gami da rashin sanin abinyi Taj ya juya tare da ɗaga
ƙafarsa dan fita.
Kan glass cup ɗin da ya fashe a hannun Yah Abduraham ya dire ƙafarsa ta hagu.
Cikin sauri Ummu Aryan tace.
“Ya Salam Taj glass ka taka fa”.
Ina baya jinta bare ya iya tsayawa, hasali ma zogin zuciyarsa ya hanasa jin zogin sukan glass
ɗin.
A haka yaci gaba da takawa yayinda tuni jini yake meye gurbin shatin sawun nashi.

Da gudu Aryaan ya shiga ɗakin Yah Abana ya ɗauko maganinsa kana ya basa.
Aunty Maryam da Aunty Rashida kuwa Ummey suke jijjigawa.

Ganin haka yasa Yah Yusuf cicciɓan Ummey ya nufi asibiti Aunty Maryam da Aunty Rashida na
biye dasu.

Taj kuwa Ahankali ya ɗan kuma juyowa tare da zaro sandar da Sheikh Tajuh Usman Bauchi ya
bashi ya ajiye agaban Mahaifinsa tare da faɗin.
“Yah Abana gashi wannan saƙone daga wurin Sheikh Tajuh Usman Bauchi Nigeria daya bani in
baka ban samu na baka ba sai yau”.
Cikin tsawa Yah Abana yace.
“Ka fita daga nan bana son ganinka ka ɓace min da gani idan ka sake minti biyar acikin gidan
nan Allah ya isa ban yafe maka ba kuma zan tsine maka!!!”
Da sauri ya miƙe tsaye sai kuma ya tsaya jin Yah Abana na cewa.
“wannan ɗin kuma da kayiwa ciki kai zaka ɗauketa kasan yanda zakayi da ita,' saboda cikinka
ne bana uban kowa ba.
Kuma dama kai ka kawota cikin ahlina so yadda ka kwasota ka kawo haka zaka kwahseta ku
tafi tare da abin kunyarku.
Sannan ka saki Meymey ƴar Aminina ba zata zauna da ƙazamin mazinaci ba ka tabbatar a yau
ɗin nan ka saketa”.

Idanunsa dake gane masa duhu ya rumtse tare da mik’a hannunsa ya kamo hannun Laylah
suka fita.
Tafiya kawai yake amma baisan inda yake sa ƙafarsa ba, hasalima baya cikin hayyacin sa,
meye zaiyi ko ina zai dosa duk baisani ba, ahaka ya ci gaba da tafiya k’afarsa na zubar da jini
sannan yana rik’e da hannun Laylah dake ta kuka haka suka dinga tafiya da sawayen su har
suka k’araso gidan Addawa...
Cikin murya mafi rauni da sanyi yace.
“Addawa ga Laylah nan ance cikine da ita kuma ance wai ni nayi mata cikin kuma itama ta
tabbatar da hakan”.
Hankali atashe Addawa ta kalli Laylah murya na rawa tace.
“Laylah waya miki ciki?”.
Da sauri da kuma alamun tsoro Laylah ta matsa gefen Addawa, again murya na rawa tace.
“Uncle Taj ne”.
Cikin tashin hankali marar misaltuwa Addawa tace.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Afif meye gaskiyar maganar? menene gaskiyar lamarin”.
Kai ya girgiza kana cikin rauni, had’i da k’unan zuciya me tsanani yace.
“Nima ban sani ba Addawa, na dai san Ummey na bata da lafiya sun tafi da ita asibiti Yah
Abana yace idan na sake kusantar ta”.
Sai kuma yayi shiru yana jin wani abu mai ɗaci na toshe masa maƙoshi.
Dai-dai lokacin kuma Aunty Halima tashigo falon da kuka kana ta bawa Addawa labarin abinda
ya faru.
Hawayen dake zuba a idanunta Addawa ta share mata kana ta kalli Taj tace.
“Allah yana tare da mai gaskiya kada ka damu Tajuddeen komai yai farko zaiyi ƙarshe komai
yayi tsanani maganinsa Allah”.

Idanunsa ya lumshe batare da yace komai ba.
Bayan wasu mintunan kuma ya buɗe idanunsa ya kalli Laylah yace.
“Laylah ki daina tsorona”.
Dan ya lura da yanda yarinyar take tsoronsa abin har mamaki yake bashi.

Aranan anan gidan ya yini sai bayan maghariba ya kira Abu Hashim ya kaisa gidansa yana
shiga side ɗin sa ya shiga ya tattara duk wasu abubuwa nasa masu muhimmanci da na amfanin
yau da kullum ya haɗa.
Yana mai jin zamansa a Ethiopia yazo karshe Rayuwa''.
a Ethiopia tazo ƙarshe ahankali ya ciri paper guda biyu daga cikin jotter dake cikin Weldrop
ɗinsa ya dauki biro ya rubutawa Meymey ta kardan saki sai kuma a ɗayan yayi rubu mai ɗan
tsawo kana ya ninke yasa a aljuhu, kana ya cigaba da tattare duk wani abun bukatarsa sannan
ya fita.
Abu Hashim kuwa ya lura ubangidansa na cikin tashin hankali kai tsaye gidan Addawa suka
nufa.

Yana shiga gidan Addawa ya samu Aunty Halima da Addawa na zaune sunyi zugum-zugum.
Asanyaye yace.
“Addawa Ni zan tafi”.
Aunty Halima kuwa ganin yana juyawa tace.
“Taj ina zaka je?”.
Batare da yace mata komai ba ya kalli Addawa tare da cewa.
“Ki faɗa mata cewa Yah Abana yace idan wani ahalinsa ya sake yimin magana Allah ya isa bai
yafe ba ta kiyaye kada Allah ya isan Mahaifin su ya hau kanta”.
Araunane Aunty Halima ta fashe da kuka murya na rawa tace.
“Yanzu Taj ina zaka je”.
Baice mata komai ba ya juya ya fita ya shiga bayan mota Abu Hashim yaja tare da cewa.
“Sir ina zamuje?”.
Cikin sanyi murya yace.
“Gidan tsohon nan da yasa aka auri ƴarsa……”


*Wasa farin girki saidai ba a ma fara wasan ba, kar dai ku manta wannan book d’in na kudine
sannan daga page 15 free pages sun k’are saboda haka kar ku bari ayi babu ku, biya 1000
kacal domin samun daman karatu 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa.*





*BY*

*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/16, 8:56 PM] Leematu: ✈️

*INDA RAI*

*BOOK ONE PAGE 15*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*



*Last free page*

_LITTAFIN INDA RAI DAI NA KUƊINE 1K NE KACAL, 0661110170 GTBANK Aisha Aliyu
Garkuwa. MUTANEN KASAR NIGER KUMA 1000FC JAKA ƊAYA KENAN RAK ZAKU BIYA TA
WURIN MOMMY +22790899076_

*Last free page! Last free page!! Last free page!!! Daga wannan Page 15 ɗin na kaɗe na gama
free pages koda Kinga littafin INDA RAI a wani group ɗin ki wata ta tura miki to ba satane kuma
haƙƙin mallakarsa nawa ne, in kuma baki/baka biyaba kika/ka karantaba mgnar gaskiya haƙƙina
dai bazan yafe ba. Littafin INDA RAI na kiɗine ki biya ka biya ku karanta cikin aminci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login