Showing 12001 words to 15000 words out of 80879 words

Chapter 5 - Inda Rai B1 True Books Available Rubutawa Aisha Aliyu Garkuwa .pdf

matsayikin ba zata wulaƙantaki
ba”.
Wohoho ina wuta Ruƙayya ta Abka,Maryam cikin Tsananin hargowa da hayagaga tace.
“Ke ƙaramar alhaƙi, ke akayan miya mecece na rantse da Allah zaki gane kin zageni, nayi miki
alƙawarin sai na farraƙa tsakaninki da Yayan naki.
Cikin matsanancin bugun zuciya Aysha ta runtse idanunta hawaye Masu masifar ɗumi na
tsatstsafo mata.
Ruƙayya kuwa cikin hargowa tamkar zata fasa Speaker wayar ta cigaba da faɗin.
“Ita kuma wannan Mara aikinyi ki faɗa mata in dai Barrister take jira tayi aure, to in sha Allah a
bazawararta zata mutu. Mijina nan gani nan bari awar mayya ga yaji ga albasa Amman ba
daman ci, in kuma ta kuskura tayi taurin kan shigowa gidan mijina, duk abinda ya sameta tayi
kuka da kanta.” Cikin mamaki Garkuwa ke cigaba da sauraron ɗaɗɗatan maganar dake fitowa daga bakin
Ruƙayya tabbas wasu matan haukar kishi na shirin zautar dasu...
Aysha kam tuni hawayen da take ƙoƙarin riƙe wa suka fara silalomata.
Wannan dalilin nefa, yasa take tsoron aure, Shiyasa tunda suka zo makka sau uku ta yarda
suka haɗu da Barrister, tunda tasan yazo da matarsa, kuma bata son ta shiga haƙƙinta, shike
nan ita kuma ƙaddararta kenan?.

Da sauri Garkuwa ta zare wayar a kunnen Maryam tare da katse kiran kana tace.
“Yin mgna a cikin fushi kuskurene,domin duk sanda mutum yayi fushi bashi ke magana ba
shaiɗan ne keyi ki bari sai kin huce, kuma ai bada kema ya kamata, tayi wannan haushinba,
mijinta zata tara tayi idan tana tunanin tana da ikon hanashi Aure.”

Haka dai tayi ta tausar Maryam da Aysha da tai Murmushin mai haɗe da hawaye kana tace.
“Idan har aurena da Barrister alkhairi ne to ya Allah ka tabbatar in kuma ba alkhairi bane, Yah
hayyu ya ƙayyum bi rahamatika astagis, ya fito min da wani mafi alkhairi a gareni”.
Da Amin suka amsa baki ɗayan su.
Daga nan suka kwanta kowa da tunanin da yake aransa.
Barrister kuwa baima san abinda matarsa tayi ba bare yayi yunƙurin ɗaukar mataki

Ƙarfe uku dai-dai suka tashi suka tafi Harami acan suka wayi gari har zuwa ƙarfe, goma lokacin
da suke ɗawafin ban bakwana.


Duk da yanzu dubban ɗaruruwan mahajjata sun ragu amman hakan bai hana ka'aba cikaba.

Cike da kuzari da yaƙini Aysha keyin ɗawafin, tana mai nanawatawa mahaliccinmu buƙatunta.
Ɗawafin takeyi tana kuma kutsawa cikin dubban al'ummar tana kara kusanto ka'aba dan so
take ta jita a jikin ka'aba.
Cikin yardar Allah kuma ta samu ta ƙutsa ta gefen hajarul Aswad.
Wani irin matsa taji taro jama'a sunyi mata har numfashinta na kwabcewa Amman hakan bai
hanata kutsawa ba, zuwa yanzu ji take kamar sawunta baya taka ƙasa, tana makalene a
tsakanin kafaɗun manyan matan Chaina mutane masu kama da aljanu dan ƙarfi.

Wani nannauyan ajiyan zuciya mai tafe da raunataccen kuka ta saki lokacin da taji ta jikin
ka'aba.
Fuskar ta ta manna da jikin Ka'aba murya na rawa ta fara jero tarin addu'o'inta da buƙatunta
cikin raunatacciyar Muryar da tasa makusantatan juyowa suna kallonta.
Wanda gefen damanta Ummeyn Tajj ne, gefen hagunta kuma Addawa ne sai Tajj ɗin dake
tsakanin kafaɗarta data kakar tashi domin itace ta kutsa ta shiga tsakanin nasu, jin yadda ta
kutsone yasa ya ɗan janye jikinshi duk da bai ga waye bane.
Jin sautin kukanta da muryarta ne yasa ya juyo ya kalleta cike da mamaki.

Ita kuwa Aysha cikin raunatacciyar murya da sassayan kuka take addu'o'in da yaruka uku
Larabci, Hausa, fillancin. Kusan duk take haɗesu waje ɗaya.
”Yah Allah ka sauƙaƙamin ƙaddarata, ka juya min ita izuwa kekkyawa mai daɗi, Alhamdulillah
Allah na gode maka ka bani rai da lfy, da damar zuwa wannan tsarkakekken wuri, Yah Allah
kaine kace mu roƙeka.
Ya Allah ka tabbatar min da alkhairi tsakanina da wannan bawa naka Barrister Kamal, idan har
aurena dashi alkhairi ne ya Allah ka tabbatar mana dashi, ka tausashi zuciyar matarsa, ka bamu
zaman lfya, ka hanani samun damar cutar da ita, itama ka hanata samun damar cutar dani.
Yah Allah idan har ba alkhairi tsakanina da Barrister Allah ka sauya mana da abinda yafi alkhairi
a garemu. Ka fito min da mijin aurena na alkhairi ka bayyana minshi akan alkhairi kasa mana
dangana tsakanin zuƙatanmu ya Allah in dai Barrister ba alkhairi bane a gareni, ka alaƙanta
wanda yake alkhairi a gareni ka kuma nuna min ranar aurena. Ka kuma sa mana haƙuri nida Barrister.
Ya Allah kayi min kekkyawar rayuwa ka bani kekkyawar ƙarshe ka shafe zunubaina.
Ka haskaka duhun zunubaina da hasken gafararka. Yah Allah ka raya min yarana kayi musu
al'barka, ka shirya minsu bisa tafarkin gsky.
Yah Allah ka bawa Mahaifiyata lfya mai ɗorewa.”
Sai kuma ta kakare saboda kukan da ya taso mata daga can ƙasan zuciyarta, wanda yake son
fizge numfashinta ta, da kyar ta iya jawo numfashi kana taci gaba, da jero bukatar ta, na nan
gidan duniya da ƙiyama.

Yayin da Ummey da Addawa da Yah Abana, duk suka zame daga wurin dan bawa wasu damar
samun kusantar ka'aba, ita kuwa Aysha ji take yi tamkar wahayin buƙatunta akeyi mata Shiyasa
suka ƙi ƙarewa.

Tajj kuwa, tsintar kansa yayi, da shiga lamurran addu'o'inta, more especially yadda take yawan,
mai-maita Allah ya bawa mahaifiyarta Dadey ta lfya ya yaye mata cutan dake damun, kawai ji
yayi yana mai kwaranyowa Dadeey addu'o'in samun, lfya tare da ambaton babban sunanta
Fatima kamar yadda yaji Aysha nayi. Sai kuma ya ɗaura da tayata, Addu'ar shirya ga ƴaƴanta, da take kira.
Mahmood, Minat, da Khalid.
Ya tsinci zuciyarsa da tayata, Addu'ar.
Kana ya ɗaura dayi mata addu'ar da ta buwayi kunuwansa da ita.
Samun miji na gari, da fatan in dai tsakaninta da Barrister ba alkhairi to Allah ya sauya mata.
A ƙarshe suka shagala da neman rabauta na duniya da ƙiyama, da neman tsari da azabar
ƙabari, da wutar jahannama, suka cike gurbin du'anin da neman jannatul Firdausi.
Yayin da gaba ɗaya kwayar idanunsa ke kan ƴan yatsunta da Maryam ta watsa mata
mashahurin lallen amarci.

Cikin sanyin jiki, ta fara kiciniyar juyowa.
Ido cikin ido sukayi dashi,
lumshe idanunta tayi, sai ga hawaye shar sun kwaranyo.
Kai ya jujjuya mata alamun tayi shiru, sai kuma ya zaro tattausa hankicib dinsa mai ni'imtaccen
ƙanshin ya miƙa mata, tare da juyawa yayi mata alamar su fito.
Ba musu ta amsa, tare da sharce hawayenta da kuka yasa idanun suka ɗan kumbura.
Da hanzarin ta fara bin bayansa, duk inda ya cire ƙafarsa nan take dire tata ƙafar, domin ya
zame mata Garkuwa daga cunkoson mutane ba dan shiba tana da yaƙinin wannan
gabza-gabzan Matan sun turmusheta.
Tafiya mai yawa sukayi, har suka fito can wajen harabar masallacin.

Shi bai tsayaba ita bata daina binshi ba.

Wani shago dake farkon titin da suka miƙa ɗin ya shiga,
ita kuwa a bakin wurin ta tsaya, jim kaɗan da shigansa ya fito, da wata ƴar leda a hannunsa.
Hannunshi yasa ya zaro, wasu tattausan safan hannun masu masifar kyau da taushi ya miƙa
mata.
Cikin ɗan tsura mata ido tare da tausasawa yace.
“Kisa wannan, in kinyi lalle ki dai yawo haka ba safan hannun, domin junnu suna saurin
shigarku ta wannan sigar, musamman ma irinki, da kike da ƙalwaya.
Kuma ko a sheriya ma bai halatta ki bayyana adonki ga ko wanne Tom and Jerry ɗin ba.”
Ya ƙarashe mgna da danne wani abun dake taso masa a ƙahon zuciyarsa.
Amsa tayi ta sanya, kana ta amshi ledan.

Daga nan suka fara tattaki, suka nufi masauƙinsu domin tsakaninsu ba nisa.
Nashi ne a forko, so a bakin ya tsaya tare da kallonta cikin fuskar aminci yace.
“Fatan Allah ya maidaku lfya, Allah yasa munyi Hajji Mabrooq.
Idan kin koma ki gaida min Dadeey da jiki, Allah ya bata lfya mai ɗaurewa, yasa wannan ciwo
nata zakkan jikine.
Allah yasa kuyi farar jinya ki gaida min su Mahmood kuma kiceea Abba ina gaidashi”.
Ya ilahi bazata iya hana hawayenta zuba ba, domin a duniya maiyiwa Mahaifiyarta da yaranta
da Abbanta Addu'a ya gama mata komai.
Kawai sai ji tayi hawaye na kwaranyo mata, kana tana amsawa da.
“Amin Amin Ameeeeeeeen Ya rabbil izzati ngd matuƙa da addu'o'inka garesu, ka gaida
Ummeey da Yah Abana, kace inayi musu fatan alkhairi Allah yasa ka kasance musu
al'wadussaliha”.

Cikin kauda kai yace.
“Amin ya rabbi”. Daga nan ya wuce ciki.

Ita kuwa Aysha ji tayi kamar an dasata a wurin, sai kuma ta juya da sauri jin Maryam na kiranta,
nan suka shiga ciki.

Alhamdulillah misalin ƙarfe.
Shida kamar yadda suka zo, haka suka taso.

Zuwa yanzu gaba ɗaya Mahajjata duk sun koma ƙasashensu, sai waɗanda jinya ta riƙesu, da
kuma ire-iren shugabannin mahajjatan da dole, in akwai ɗan yankin su da ba lfya suke tsayuwa
a kula da komai nashi.
Mahajjatan Adamawa duk sun dawo cike da farin ciki da jin daɗin irin karamcin, Amirul Hajj
ɗinsu yayi musu.
Gashi duk kayan mutane ya dawo kan lokaci.

Bayan wata ɗaya da, dawowarsu.
Garkuwa ce zaune a Parlour'n Dadeey yayin da Aysha ke miƙa mata cup ɗin data zuba mata,
Juice mai sanyi.
Amsa tayi tare da ɗan kurɓa kana ta ajiye, tare da yiwa Dadeey sannu da jiki.
Cikin yanayin alamun sauƙin jikin tace.
“Yau dai ga Garkuwa a Parlour'na, tunda kuka dawo kullum sai Aysha ta bani labarinki”.
Murmushin Garkuwa tayi cike da girmamawa tace.
“Ayyah Dadeey ai kullum ina son zuwa Allah bai nufaba sai yau.”
Murmushin Aysha tayi tare da cewa.
“Maryam jiya uwar haka muna tare ai, Yah Abubakar ne ma ya maidata”.
Gyara zaman Garkuwa tayi tare da cewa.
“Ayyah Maryam nima last two weeks taje min, ita ce ma ke cemin Barrister baya ƙasa ko?”.
Kai Aysha ta jinjina tare da kallon Dadeey dake cewa.
“Uhmmmm Allah dai ya kyauta, Garkuwa lamarin Aysha akwai buƙatar addu'a kigafa irin

hidimar da Barrister yayi mata, da yadda yake sonta, Amman batun aurensu ya shiririce.
Ko an mishi mgna sai yace.
Su bari sai gaba akwai abinda yake damunshi.
Ya fito ya faɗi damuwar kuma yaƙi, abinda da kuna dawowa da kwana biyu nefa za'ayi bikin”.
Cike da jimami Garkuwa tace.
“Bakomai Dadeey in sha Allah, wata rana zai wuce kamar ba'ayi ba Dadeey ke dai muyi ta
matta addu'a _INDA RAI to da RABO_”.
Cikin danne ƙunan dake zuciyar Aysha tace.
“Kayya Aunty Garkuwa ni na fara karaya da lamarina fa, hakafa duk wanda yake sona sai mgna
tayi zurfi tayi nisa na gama duk shirin biki, sai abu yazo ya watse, kuma ka rasa dalili,
Hakafa mukayi da Mukhtar Garkuwa naso Mukhtar har raina, Babanshi yayan Sarkin Gombe
ne, lokaci ɗaya abun ya lalace, Garkuwa haukane kawai banyiba lokacin da mgnata da Mukhtar
ta watse nayi kuka har na rasa hawaye, Abin takaici kuma haka ma ya faru da Yah Muhammad
wani dan Kaduna, abin har ya zame min jiki yanzu kuma ga wasu ma neman sun tasoni gaba
basu saniba Ni tsoro suke bani”.
Abba dake shigowa ne dan duba jikin Dadeey yayi ɗan gyaran murya tare da cewa.
“Ba komai Aysha in sha Allah komai zai zo da sauƙi, addu'armu gareki ba zata faɗi ƙasa banza”.
Da sauri Garkuwa ta ɗan zame ƙasa tare da gaida shi,
Cike da kulawa ya amsa kana ya tambayi Dadeey ya jiki, kana ya juya ya fita.

Yana fita sukaci gaba da hirar, tsoron Aysha a haka har mgnar tazo kan abinda tayi a jirgi.
Nan sukayi ta hirar Garkuwa na bawa Dadeey labarin yadda tayi, da yadda Taj ya taimaka daga
nan sukayi ta hirarsa.
Cikin kwaɓe fuska tace.
“Shifa da gaske gani yake aljanu gareni”.
Cikin dariya Garkuwa tace.
“Yoh ai koni lokacin kallon mai aljanu nayi miki.”
Tana gyara zamanta tace.
“Ai baki sani ba, rana ita yau iwar haka, kawai sai naga, kira naso in gane number Amman sai
na sha'afa.
Ina ɗagawa naji shine!”.
Da sauri Garkuwa tace.
“Ke haba dai dan Allah”.

Tana gyara wuyan rigarta tace.
“Wallahi kuwa, wai ya kirani yaji ya jikin Dadeey har na bata waya suka gaisa dashi, harda Abba
ma, sun gaisa”.
Da sauri tace.
“A'a Aysha ko dai? Ko dai?”.
Da sauri cike da gsky da gsky da ya ƙini Aysha tace.
“Yah salam ba wannan mgnar wlh, kin dai san ni nafi son babban mutum”.
Kai Garkuwa ta jinjina domin tasan yes Aysha tafi son babban mutum irin mai mata da yara
haka dai.

Ganin la'asar tayi ne yasa suka miƙe sukayi sallan la'asar.

Bayan sun isar ne, Garkuwa ta gyara zamanta tare da cewa Aysha.
Yayan ta Usman nefa ya aikota cewa yana sonta.
So sanin su waye su yasa tace, Allah ya tabbatar musu da alkhairi duk da Usman saurayine
Amman tasan ya girmeta nesa ba kusa ba, duk da dai tasan bata da ra'ayin auren saurayi
Amman ta nemi zaɓin Allah, daga ranar Usman ya shiga cikin jerin masoyanta.


Yau watansu biyu cib da dawowa, konce take a ɗakinta, tunda tayi sallan azahar bacci yayi
gaba da ita cikin, baccin ta fara jiyo ringing ɗin wayarta, a hankali ta ɗan motsa tare da buɗe
idanunta ta kalli Fuskar wayar, number Ethiopia ce kana ga sunan Tajj yana yawo a sama ne
yasa ta ɗauka tare da karawa a kunne. A hankali ta kuma lunshe idanunta saboda jin sassayan sautin muryarsa daya ratsa
kunnuwanta, cikin yanayin bacci tace.
“Assalamu alaikum Tajjj”.
Sai kuma tayi kasake jin yana cewa.
“Wa'alaikissala Afwan Ishmah bacci kikeyi ko na tadaki?”.
Kai ta ɗan jujjuya tare da cewa.
“Gwarama daka tada ni, ai lokacin salla ya ƙarato”.
Numfashi mai sanyi ya fesar tare da cewa.
“Toh yanzu dai ya jikin Dadeey”.
Murya a narke tace.
“Alhamdulillah jiki da sauki kwanan kuma ya sake tashi”.

“Allah ya ƙara mata lfy, ya Abba dasu Khalid suna lfya ko?”.
Cikin jin daɗin kulawarsa ga iyayenta da yaranta tace.
“Lfy Lau Alhamdulillah, Yah Ummey da Yah Abana”.
Cikin sanyi yace.
“Suna lfya. ki bawa Dadeey waya mu gaisa”.

Toh tace tare da kaiwa Dadeey wayar suka gaisa, kana tace.
“Ba kaƙi ka haɗani da Ummeey ba, sai Addawa sarkin rigima”.
A hankali yace.
“Kiyi sallan zan kiraki”.
Toh kawai tace kana ta katse kiran.

Bayan ta idar da salla kuwa ya kirata sukayi ta, hira wanda mafi akasarin akan abinda tai a cikin
jirgine.
Ya ƙara da cewa.
“Yau ne na samo wata passinger daga Jordan zuwa Palastine itama tai tayin yadda kikayi, sai ta
tuna min da ke, tunda na fara aikin ku biyu ne, naga kunyi haka”.
Cikin murmushin mai haɗe da kunya tace.

“Wai kai baka mantuwa ne”.
Kai ya ɗan rausayar tare da cewa.
“A dai naki kam bazan manceba”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Kwanan ma da Garkuwa tazo muna hirar mukayi ta dariya”.
Cikin kulawa yace.
“Me tazo yi?”.
Kamar a fizge taji mgna ta fito bakinta.
“Wai tazo ta gaya min wai yayanta Usman na sona, yana nan da fuskarsa kamar mace ba saje”.
Sai kuma tayi saurin rufe bakinta.
Shi kuwa Tajj a hankali ya ɗaura hannunsa bisa tattausar fuskarsa, da mafi akasarin ranaku sai
ya yaɗe sashensa da gemun.
Cikin nazari yace.
“Toh ina Barrister abin ya watse ne?”.
A hankali tace.
“Eh”.
Shiru sukayi baki ɗayansu, fahimtar kamar ya fama mata mikin rantane ya sashi cewa.
“Toh ke me ruwanki da rashin sajen na miji ai ba saje zaki auraba ko?”.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
“Ai fuskar namiji in ba saje da gemu, bata da banbanci da fuskar mace, ni bana son namiji ba
saje”.
Kai ya jinjina, tare da cewa.
“Ok yanzu dai bawa Dadeey waya inyi mata sallama”.
Miƙewa tayi ta shiga Parlour'n Dadeey bisa sallaya ta sameta a zaune, miƙa mata wayar tayi
tare da cewa.
“Tajj ne wai zai miki sallama”.
Amsa tayi, ita kuma Aysha sai ta zauna a gefe
Dadeey kuwa gyara riƙon wayar tayi jin, Tajj na cewa.
“Dadeey ya jikin da sauƙi sosai ko”.
Yayi mgnar cikin gyara fillancinsa na Ethiopia yadda zata gane sosai.
“Eh Alhamdulillah Tajuddeen jiki da sauƙi sosai ma”.
Cikin jin daɗi yace.
“Masha Allah haka nake son ji, Allah ya ƙara lfy Dadeey sai kina ɗan motsa jikin”.
Kai ta gyaɗa kana yana mai ci gaba da bata shawarwari irin nasu na Doctors.
Daga bisani sukayi sallama.


A hankali rayuwa taci gaba da juyawa, yanayi na sauyawa.
Kwanaki na tafiya makkoni na shudewa watanni na mirginawa izuwa shekaru.

Bayan tsawon shekaru huɗu kenan.
Abubuwa da dama sun faru cikin shekarun nan.
More especially tsakanin Aysha da Tajj, wanda suka gina wata tsabtacecciyar amintakar, dake

bisa wani ɓigiggiren, da su kansu basu san na menene ba, sun zama aminai na musamman
wanda duk motsin ɗaya, ɗaya na sani.
Sunyi wata iriyar shaƙuwa mai haɗe zuƙata tasa su bawa juna dukkan yarda, Tajj bai taɓa wani
abokiba a duniya sama, da marigayi pilot Irfan Imran wanda aka kashe a faɗar tsakanin
Palastine da Isra'ila.
Dashi da iyayensa baki daya sai ƙanwarsa Laylah yar shekaru sha biyu, wacce Taj ya ɗaukota
riƙonta ya dawo gareshi a Ethiopia a gaban Ummeeyshi. A rayuwar Taj ba abinda Aysha bata
saniba, haka shima, hatta denginta ba wanda bai sanshi ba, zuwa yanzu Abba da Dadeey kam
jinsa suke tamkar ɗansu, duk da bai taɓa zuwa sun ganshi ido da idoba.
Aysha kuwa Jarrabawar Aure har gobe, tafiyar bata sauya zaniba.

Shaƙuwarta da Garkuwa kuwa abin ya wuce ƙawance ya zama ƴan uwantaka babu abinda ke
ɗan sata faranci gami da ɗebe mata kewa kamar karanta littattafan Garkuwa domin a littafinta
take samun Darussan rayuwa Ilmantar, Faɗa karawa,kana da Nishaɗantarwa idan tana karanta
littafin ji take tamkar azahiri abubuwan ke faruwa...
Maryam ƙanwar Barrister kuwa, Yah Abubakar ɗinta ya aureta har su haihu, Barrister da kanshi
zumunci sukeyi sosai dan yana yawan zuwa duba jikin Dadeey da yake ɗan yawan matsa mata
ga kuma ƙarin zumuncin da ƴar uwarsa na gidan.

Hakama Mukhtar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login