Showing 3001 words to 6000 words out of 80879 words

Chapter 2 - Inda Rai B1 True Books Available Rubutawa Aisha Aliyu Garkuwa .pdf

class suka, ta gaba-gaba basu da nisa da gefen matuƙan.
Sai hoto da video sukayi ita da Maryam, Murmushi Aysha dake gefen wata ƴar duma-dumar
mata mai matsakaici shekaru wacce ke riƙe da wayarta bisa alamu karatun ƙur'ani takeyi cikin
suratul Khaff kasan cewar yau ɗin jumma'a ne.

Ganin alamun ta dire ayar ƙarshen surar ne, tayi addu'a ta shafa a jinkinta, sai kuma ta ɗan

kallesu a fakaice ganin alamun kamar dai baƙin shiga jirgine saboda yadda suke ta kabta selfee
ba ƙaƙƙautawa ɗan gajeren murmushin dake nuna alamun sakin fuskantar tayi tare da ɗan
jingina kanta da kujerar ta kalli gefen dama inda Aysha take, tana kallon baiwar kyau da haiba
da Allah yayiwa Aysha ga tarin kwarjini, haka nan taji tana burgeta saboda Aysha mutunce mai
shiga rai lokaci ɗaya, ga kwarjini tana da yanayin nan da in mutum bai san taɓa zauce tana da
girman kai, sai dai bawai girman kai bane, girmama kaine in an zauna da ita kuma zaka gane
nagartar halayyar masu sawa a sotane.
Cikin mutuntawa Aysha ta kalli Kamilar matar da har zuwa lokacin fuskarta ke dauke da
sanyayyar murmushi kana tace.
“Hi”.
Still da murmushi afuskar matar ta ɗan gyara zaman wayar ta tace.
“Assalamu alaikum”.
Cikin lumshe ido Aysha tace.
“Afwan madadin inyi Miki sallama nace, Hi”.
Tana mai kallon Aysha tace.
“Ba komai dama nayi Miki hakane dan tunasarwa”.
Kai Aysha ta jinjina tare da gyara zamanta, kana tace.
“Sunana Aysha Abdullahi Matawalle”.
Itama matar Murmushin tayi tare da cewa.
“Ni kuma Aysha Aliyu Garkuwa”.
Cikin sauri Maryam ta ware Idanunta tace.
“Laah Aunty Garkuwa, , kai yau gani ga Garkuwa, duk da muna ƙasa ɗaya gari ɗaya Amman
ban taɓa ganinki ba, sai gashi cikin ikon Allah yau tafiya ta haɗamu”.

Murmushin Garkuwa tayi wanda ke nuni da karamci da kula ga duk wani Masoyinta tare da
kallon Aysha da ta fara yi musu video tana cewa.
“Bari inyi mana video”.
Tafin hannunta tasa ta ɗan kare fuskarta tare da cewa.
“Ya isa haka, muyi addu'a za'a tashi yanzu”.
Kai Maryam ta jinjina.
Ita kuwa Aysha Matawalle wani sabon video ta fara cikin nitsuwa da maɗaukakin jin daɗi take
mgna.
“Hi Barrister wannan video en nakane, kaga yanzu zamu tashi, ance 6:00 pm zamu tashi yanzu
saura One minute mu tashi, ka samu a addu'a Allah ya kawomu lfy muzo mu sameku lfy”.
Sai kuma tayi saurin juya wayar ta gefen window sit ɗinta.
Tare da zurawa harabar Airport ɗin ido.
A ranta take cewa.
Laaa ashe jirgima kamar mota yake tafiya, da tayoyisa a ƙasa yana fesa gudu, ikon Allah.

Ita ma Maryam window sit ɗinta take leƙawa.

Haka dai kowa da abinda yake yi cike da farin ciki zasu ziyarci ƙasa mai tsarki.

Cikin sauri Aysha ta tasa wayarta a Airplane mode, saboda jin ɗaya daga cikin Hostess ɗin na
ce mata, ta kashe wayarta.
Haka yasa ta ɗan kife wayar bisa cinyarta tare da gyara zamanta kana ta gyara saƙala Aepeace
ɗin dake kunneta, tana mai jin waƙar IN DA RAI, na sani akwai rabo yana zuwa.
Haka yasa ta gyara zamanta tare da sauƙe sassayan numfashi tana mai hamdala a ranta tare
da tariyo dukkan tarin buƙatunta domin wakar kan sosa mata taɓon ƙaddararta.
Yess ai dama in dai da rai akwai rabo duk zafin ƙaddaarka bazaka cire tsammanin warakaba,
numfashi mai sanyi ta fesar tana mai mgnar zuci tace.
“Alhamdulillah oh Yah Allah na gode maka, yau nice Aysha zan tafi maka, Yah Allah ka isar
damu lafiya, in ganni gaban ka'aba, in ruggumi Ka'aba, in faɗi tarin ƙaddarorina da jarabbobina
masu zafi da ɗawainiya da rayuwata inyi addu'a in sha Zam-zam inyi tawassali dashi, in har
akwai jinnu ko wata cutar dake tare dani dake hanani samun salama da zaman lfya a rayuwar
zaman aurena.
Rabbi ka yaye minshi.
Ka sauƙaƙa min. Jarraba mai zafi, domin Jarrabawar Aure itace Jarrabawar mafi ciwo a zuciyar
ƴa mace ba Jarrabawar data fita ciwo sai na cuta.
Yah Allah kasa inyi Hajj Mabrooq Allah ka amsa min addu'o'in da zanje, inyi.
Yah Allah ka takaitamin matsalar rashin nagartar aure kasa in nayi aure da Barrister sai mutuwa
zata rabamu.
Yah Allah in dai aurena da Barrister alkhairi ne, Allah ka tabbatar dashi, Yah kasa shirin aurena
da Barrister ya tabbata, ko dan farin cikin Mahaifiyata da Mahaifina, ko dan in tsira da zargin
mutane dake ganin cewa, nice naƙiyin aure.”
Wannan sune maganganun zuci da Aysha takeyi.
Dai-dai lokacin kuma tayoyon gaba na jirgin ya fara rabuwa da ƙasa, alamun yanzu zasu ɗaga
kenan.

A can gaba kuwa wurin pilots ɗin, cikin natsuwa da tsanantan bugawar da zuciyar da Taj keyi,
yaci gaba da saita komai na tafiyar, yadda kawai zai zauna ne, yana kallon na'urorin ba tare
daya taɓa komai ba, muddin sun ɗaga sama.

A can bayan kuma wurin passingers ɗin.
Cikin sauri sababbin fara shiga jirgi duk suka rurtufe idanunsu kowa da addu'ar da yakeyi.

A gefen First class kuwa.
Da sauri Aysha ta matso gaban kujerar tare da kife kanta da jikin kurejar dake gaban tata
kujerar wanda Maryam ce a kai.
Cikin tsananin kaɗuwa da tsoron da mafiya akasarin mutane sukeji a shigan su jirgi na farko.

Rumtse idanunta tayi da masifar ƙarfi lokacin da taji jirgin ya rabu da ƙasa baki ɗaya, ferfelan
sun fara aiki na musamman damonin tare iska dan saita hancin jirgin wanda , haka yasa jirgin
ke marisa irin dai ƴar marisar nan da manyan jirage keyi in sunzo tashi, dan nasu baya kai na
ƙananan jirage irinsu...

Saurin ƙanƙame saman kujerar da Maryam ke kai Aysha tayi tare da riƙewa saboda wani
zuuummmmm da taji jirgin yayi tamkar zai rikito ya faɗo ƙasa, wanda hakan yasa taji zuciyarta
ta bada sautin zummmm ɗin har takeji kamar hanjin cikinta na barazanar ɓarewa, ya Salam
Aysha Farar kura ga tsoro ga ban tsoro. Wani irin karkarwa jinkinta ya fara yi tamkar mazari, saboda azabebben tsoro da tsinkewar
zuciya.

Kar-kar haka jinkinta ke rawa cikin tsananin kiɗima ta fara.
Karanto duk addu'o'in dake zuwa zuciyarta da bakinta.
Da tsananin ƙarfi ta rumtse idanunta lokacin da jirgin ya danyi juyin ɗaukar asalin hanyarsa.

Kiɗimarta da diriricewarta ta tsananta ne saboda jiyo wata babarbariyar dake sit ɗin gaba da na
Maryam ta zurma wani irin gigitaccen ihu, da addu'o'i cikin harshen barbarci take cewa.
“Wayyyo Allah hanjina wayyyyyoohhhh zamu faɗi fa”.

Garkuwa kam murmushi mai ɗan sauti tayi, saboda tuno yanayin da ta shiga lokacin forko da ta
fara shiga jirgi.
Sai kuma ta kalli Aysha dake wani irin karkarwa jinkinta baki ɗaya tsuma yake.
Hakane yasa ta yunƙura da sauri alamun zata tashi, sai kuma tayi maza ta koma ta zauna
saboda Hostess ɗin dake nufosu da tayi mata alamar ta zauna.
Zaman tayi tana mai kallon Aysha yayinda ita kuma ƴar matashiyar balarabiyar ta tsaya gaban
babarbariyar nan, tare da zama gefenta ta ruƙo hannunta tana mai kwantar mata da hankali.

Aysha kuwa zuwa yanzu ta saki duk inda ta riƙe saboda jin yadda suke marisa a sama yasata,
fara fuzgar numfashinta dake kubce mata.
Shike nan ashe tsananin son zuwanta Makka da takeyi, shine silar rayuwarta, tunda gashi a jirgi
zuciyarta zata buga ta mutu, ashe burin iyayenta bazai cikiba, ashe abinda take tsoron mutuwa
ba igiyar aure a kanta shi zai sameta, Allah sarki Barrister yana jiran mu isa ashe ni kam
bandani. Sai kuma maganganun zuci da takeyi suka kafe mata, saboda wani zuuummmmm da taji kamar
jirgin ya tsinko ya taho ƙasane.
Wannan yasa ta ƙara ƙanƙame sit ɗin da Maryam ke kai, wacce itama gaba ɗaya tayi zuru-zuru
da idanunta.

Ita kuwa Aysha ji takeyi tamkar ta ɗaura hannunta bisa tsakiyar kanta, ta rinƙa kwarara ihu da
shelanta, a sauƙeta ta fasa tafiyar, toh Amman ta hani kanta da yin hakan saboda sanin ko tayi
tasan baza a sauƙanba.
“Yah ilahi ya mujibadda'awati.”.
Ta faɗa da ƙarfi lokacin da taji jirgin ya harba can sama ya lula alamun ya saita hancin sa bisa
da'irar taswirar hanyarsa.

Da sauri Garkuwa ta ɓalle sit belt dinta tare da miƙewa, tsaye ta nufi kan Aysha saboda ganin
duk jinkinta ya ɗebi karkarwar tamkar wacce aka jonawa wutar lantarki, kana numfashinta nayi

off and dawn, bisa alamufa ta kusa suma.

Da sauri ta riƙo hannunta tana faɗin.
“Hostess help help”.
Jin hakane yasa Hostess biyu dake bayansu saurin isowa kusa dasu.
Ita kuwa cikin kulawa take jijjiga Aysha dake karkarwa gaba ɗaya jinkinta sai ƙirjinta dake
ɗagawa sama da ƙasa.

Ɗaya hostess ɗince tayi saurin ɗaga sautin muryata tare da juyawa ta nufi, side ɗin inda suke
tana cewa.
“Abata ruwa”.
Da sauri ɗaya daga cikin waɗanda ta haɗu dasu suna turo, ruwan da zasu fara rabawa
passingers ɗin ta miƙata goran ruwar, amsa tayi kana ta juya da sassarfa.

A dai-dai lokacin kuma a can cikin wurin su pilot Irfan Imran.
A hankali Taj ya ɗan juyu ya kalli abokin aikin nasa kuma amininsa ɗan ƙasar Palastine.
Murmushin Pilot Irfan Imran yayi saboda ya fahimci me aminin nasa ke nufi.
Haka yasa ya tashi daga inda yake, kana yazo ya zauna inda Taj ɗin ya tashi Taj.
Ɗan miƙa yayi tare da rumtse idanunsa, saboda tsananta da bugun zuciyar keyi, fuskarsa ya
ɗan shafa, kana juya ya nufi Bathroom ɗinsu saboda zaiyi al'walan sallan Magrib, dan yaga
lokacin sallan Magrib ne ya yayi a ƙasar Nigeria ɗin.

Jim kaɗan da shigansa, ya fito, da alamun yayi al'walan dan fuskarsa dake ƙellin ruwa, wanda
babu wani gashi ko ɗan tsilli a saman kekkyawar fuskar tasa face gashin girarsa dana ido.
Da ido ya ɗan zuba wani ɗan na'ura mai haska musu abinda ke faruwa a cikin wurin passingers
ɗin,
Hannun rigar jikinsa ya ɗan fara warwarewa saboda naɗewa da yayi kafin yayi salla.

Shiru yayi a tsaye ganin kusan Hostess nasu duk suna tare wuri ɗaya.
“Mitsss.”.
Ya ɗan ja gajere tsaki a saman lips ɗinshi, ganin sun bar passingers ba ko ruwa bare aje ga ɗan
wani abun ci.
A hankali ya ɗan daddanan wasu pins ya buɗe ƙofar dake tsakiyarsu da passingers ɗin fist
class, wanda kujerar babarbariyar nane firko sai ta Maryam kana ta Aysha.
A gefen dama kenan.

Ganin shine yasa duk Hostess ɗin mimmiƙewa tsaye, cikin tsananin girmamawa da kiyaye
tsarin aikinsu.
Maida hankalinsu, a hankali ya haɗe lips inshi da ya buɗe tare da cewa.
“What happened?”.
Cikin sauri ɗaya daga cikinsu tayi mishi bayanin abinda ke faruwa.

Yayin da Maryam da Garkuwa kuwa duk sun kiɗime sai kiran sunan Aysha daketa karkarwar

tamkar mazari suke.

Juyowa Garkuwa tayi ta kalli bayanta jin ana ce mata ta matsa ga Dr Taj zai duba Aysha.
Jin haka ne yasa tayi saurin matsawa, tare da jan hannun Maryam, suka bashi fili.

Shi kuwa Taj da sauri ya lumshe idanunsa kana, a hankali ya ɗan sunkuyo kanta, sai kuma yayi
saurin datse lip inshi na ƙasa da haƙoransa na sama, saboda wani irin masifeffen harbawa da
zuciyarsa tayi tamkar zata ɓallo ƙahon zuciyarsa tayi waje.

Ita kuwa Aysha zuwa yanzu dai saura ƙiris tsoro ya sumar da ita, duk da jirgin ya dai-da ta kan
hanyarsa.
Shi kuwa Taj cikin ƙarfin hali ya buɗe kwayar idanunsa ya tsaidasu kanta, alamunta da yanayin
yadda take yi yafi kama da na mai iska.
Domin karkarwar da salatin yasa ta sule tayi ƙasa.
A hankali yasa hannunsa na dama ya riƙo hannunta na dama.

Rumtse idanunsa ya kumayi da ƙarfi kana ya jawota ya zaunar da ita kan kujerar.
Kana ya zauna gefen hannun kujerar, tata ba tare da ya saki hannunta ba.
Cikin gamsuwa da yaƙinin aljanune a kanta ya ɗan juyo ya fuskanceta da kyau
tare da yin auziya kana yayi basmala.
Ya buɗe lips inshi a hankali tare da ɗan ɗaga sautin muryarsa ya fara karanto mata ƙebantattun
Ayatush shifa na Alkur'ani.

Ya Salam shine, abinda Garkuwa Da Maryam dama duk sauran waɗanda ke wurin sukace tare
da lumshe kwayar idanunsu, saboda jin wani irin amintaccen zazzaƙan sautin muryarsa da yake
rero karatun ƙur'ani cikin nitsuwa da cikekkiyar tajweed mai fidda amintaccen Ghunna, Qalqal,
iqlab da idgham hadida Ikhfa'a masu sa zuciyar ko wani muminin mutum da aljan samun
nitsuwa. Nitsuwar kuwa harda Babarbariyar nan ta nitsu.

Ita kuwa Aysha wasu tagwayen ajiyan zuciya masu nauyi ta fara sauƙe.
Lokacin da taji Ya Kawo ƙarshen.
Suratul Fatiha
Sai kuma taja dogon numfashi jin ya ɗauko,
Ayatul-kursy
A hankali wani nitsuwa ya fara diro mata, wanda yasa jinkinta fara mutuwa. jin ya fara karanta,
Aamanar-rasuulu sai kuma ya ɗauki.
Laqad ja'akum
A hankali tayi luuuh ta ɗan jingina da gefenshi jikinsa lokacin da taji ya fara karanta.
Wattaba'uu ma tatlush shayaɗeenu ala mulki sulaymaan.
Zuwa yanzu ta fara samun nitsuwa. Jinginar da tayi da jikinsa ne kuma ya sa wayarsa dake
cikin aljuhun rigarsa sulowa ya fito ya faɗi,
Dai-dai inda wayarta dake kan cinyartan ya faɗi gefen wayarta
Wani ni'imtaccen bacci ne ta fara jiyowa yana diro mata daga sama kanta, numfashin samun

nitsuwa ta shaƙa gami da ni'imtaccen ƙanshin turaren jikinsa mai sanyaya zuciya, a lokacin da
taji yana karanta.
Qulyaa ayyuhal kaafiruun
Sai kuma ya ɗaura
Qul huwallahu Ahad.
Qul a'uuthu bi rabbil falaq.
Qul a'uuthu bi rabbin-naas.
A hankali ta gyara jinginar ta da jikin kujerar tata yayinda rabin gefen kafaɗarta yake ɗan jingine
kaɗan da rabin kafaɗarsa wanda ko ya tashi ma bazata zameba.

Ganin hakane yasa Maryam da Garkuwa dama duk sauran kowa ya koma mazauninsa, ganin
tayi bacci.
Shi kuwa Afif Taj, cikeda taushin murya yaci gaba da kawo ayoyin wasu surorin kamar haka.
Suratul isra'i aya ta 81 zuwa 82.
Suratush-shu'ara aya ta 78 zuwa 82.
Suratus-sajadah aya ta 13 zuwa 14.
Suratu aali Imran aya ta 139.
Suratuz-zumar aya ta 18.
Suratul-ankabuut aya ta 41.
Suratul-ahazaab aya ta 22. Kafin yazo ƙarshen tuni baccinta yayi nisa, ta samu cikekkiyar
nitsuwa ta falalar Alqur'ani mai girma kenan.

A hankali ya ɗan kalli gefen fuskarta kana, ya ɗan yunƙura ya miƙe, yana mai ɗan shafa
aljihunsa, sai kuma ya kalli gefenta, hannunshi yasa ya ɗauki waya.
Dai-dai lokacin kuma hankali sa.
Na kan Hostess ɗin su dasukaci gaba da rabawa passingers ɗinsu abinci da sha.
Daga nan sukaci gaba da tafiya, suna keta hazo.

Ƙarfe goma dai-dai agogon Nigeria Niger Cemaroon da Chadi wanda yayi dai-dai da ƙarfe sha
biyu da minti uku kacal, jirgunsu yayiwa King FAHD international Airport dirar mikiya, dora kuwa
irin wacce ba zato ba tsammani domin duk da sun san da sauran jirginsu ɗaya a Nigeria bai
hanasu cuku-cukun rufe Airport din ba kamar yadda sukace. Shi kuwa Taj.
Da sauri ya kutsa kan jirgin bisa da'irar da suka bashi damar saukan 12:00 duk da kuma ganin
alamun gargaɗin da suke yi mishi, hakan bai hanashi sako kai gadan-gadan ba, wanda bisa
dole yasa suka fara shirin tarbarsa cikin gaggawa, domin da har sun fara datse na'urarorinsu.

Murmushi mai sauti Balaraben dake can cikin dogon gidan da suke iya ganin gilmar koda
tsutsace aƙasan wurin ko sama.
Ya sani wannan aikin Taj ne, domin matashine mai jini a jika, wanda burin rayuwarsa na duniya
pilot, haka kuma babu abinda ke sashi karsashi da shauƙi sama da ya ganshi yana sarrafa jirgi.

Murmushin yayi tare da bashi umarnin dirowa,

Duk da yasan Taj ɗin zai fuskanci ƙalubalen tuhumar dalilinsa na wuce lokacin da aka bashi da
kuma yi musu kutse cikin Airport insu.
Sau ƙintama shi ma'akacinsu ne, Amman yasan duk da haka da wuya in bai fuskaci
dakatarwaba, bisa gargaɗi mai ƙarfi.

A nan cikin jirgin kuma Irfan Imran ne, ya saki wani zazzafan numfashi.
Jin gubbbb alamun tayoyin jirgin sun dira ƙasa.
Aysha kuwa wannan ƙugin shi yasata rumtse idanunta, tare da ɗauka wayar gefentan tasa a
cikin hand bag dinta, sabida jin Garkuwa nace.
“Alhamdulillah mun isa lfy”.

Murmushi tayi tare da buɗe windo gefentan tana kallon cikin Airport ɗin da yake tamkar rana
saboda haske.

Zururuuuuuuuuuuu haka jirgin ke fellawa da gudu, bisa da'irar da dama itace ƙarshen rufewa
saboda ana tsammanin sa.
Mamakin yadda jirgin ke gudu ya cika mata zuciya.

A hankali ta juyo ta kalli Hostess ɗin data ɗan daga kafaɗarta tare dace mata.
“Yau kinyi babban raɓo, lallai ke mai Sa'a ce Captain Taj Afif ke jan jirgin nan, kin samu taimako
na musamman badon shiba da suma zakuyi, tunda ko Doctors inmu sun dubaki matsalarki ta
junnuce”.
Cikin sauri tace.
“Kai nifa banda aljanu kawai tsorone”.
Murmushin tayi tare da cewa.
“Ke dai ki godewa Allah ki kuma godewa Captain Afif Taj.”
Ta ƙare maganar dai-dai lokacin da jirgin ya tsaya gis.

Daga nan duk passingers suka mimmuƙe Hostess na bubbuɗe musu durowowin jirgin suna
ɗaukan jakukkunamsu, ana buɗe musu ƙofa suka fara fita.

Bayan awa ɗaya da daƙiƙu arba'in da biyar, duk passingers ɗin, sun bar cikin Airport.


Ƙarfe biyu da minti goma dai-dai,
Su Aysha suka isa masauƙinsu.
Kamar yadda duk sauran majatta kowa ya isa masauƙinsa.

Tuni kuma sun ɗauki niyya kasancewar sunso a ƙurerren lokacin yasa cikin Makka suka dira.

A can Airport ɗin kuwa, cike da tsananin mamaki Doctors ɗin dake bincika lafiyar su pilot Irfan
Imran da Taj.
Suka zubawa Taj ɗin idanu.

Domin wannan shine karo na farko da bincikensu ya nuna musu cewa Pilot Afif Taj yana tattare
da matsalar matsananciyar sha'awa mai gigitarwa.
Dan ma kasancewarsa mutum mai tsananin haƙuri, juriya gami da zurfin cikine yasa sam a
zahiri babu alamar wannan matsalar tattare dashi ko kaɗan sai suda na'urori suka nunawa,
sirrin jikinsa.
Tsuke fuska yayi tare da kauda kanshi.
Da sauri Dr Yace
“Are you okay?”. Cikin takaicin yadda na'urar ke nuna ainihin yadda bukatarsa ke hauhawa
kamar farashi yace.
“Yesss! I'm okay!”. Ya ƙare maganar yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login