Showing 21001 words to 24000 words out of 80879 words
Chapter 8 - Inda Rai B1 True Books Available Rubutawa Aisha Aliyu Garkuwa .pdf
shi ke ja mishi baƙi.
Wata Shida Baya Malam da Uncle Jibirin suka haɗa auren Taj da Meymey ɗiyar Uncle Jibirin
ɗin wacce taci sunan kakanta, wanda bisa dole suka datse soyayyar da Meymey keyi da wani
Dr da suka shafe cekara biyu suna soyayya.
Taj kuma baima saniba kawai dawowa yayi ya samu Meymey, wai ai an aura mishi ita, wannan
al'amari yayi misifar hautsuna mishi lissafi ya watsa mishi dukkan wani ƙudirinsa.
Toh Amman su kansu dan sanin biyayyarsa da haƙurinsa ne, yasa sukayi mishi haka, koda ya
dawo kuma Malam da kanshi ya kaishi gidan da aka shirya mishi matarshi kuma take can.
Ita ko Meymey ta lashi tokobin sai ta kashe auren ko ta wacce hanya.
Tayiwa kanta alkawarin babu abinda zai rabata da Dr Zakariyya, domin shi takeso, ta shirya ko
ta wacce sigar sai ta rabu da Taj.
Wanda shi baima san tanayi ba domin ya lura Meymey makirace, bata saniba shima bawai
sonta yakeba, Amman kuma bazai tozartata ba.
A hankali ya tura ƙofar falonta,
Tare da kutsa kanshi cikin Parlour.
Sassayan numfashi ya fesar ganin yadda Parlour ke hargitse bisa dukkan alamu ba ita da
Laylah kaɗai bane a cikin gidan.
Cikin ɗan ɗaga sautin murya kaɗan ya fara kiran Laylah ƙawar Amininshi Irfan Imran dan
Palastine ɗinnan.
Wace take cike da marci gaba da baya.
“Laylah Laylah Laylah!!!”.
Ya ƙare kiran sunan nata da ɗan ƙarfi.
Wanda hakan yasata fitowa daga kitchen a guje ta nufoshi.
Sai kuma ta tsaya turus a gabanshi.
Tuni idanunta na tsatstsapo da hawaye, tuno yadda Irfan keyi matansa yasashi buɗa mata
hannayensa.
Da gudu ta ruggume ƙafafunsa.
Cikin kula da jinta cikin tsatson jinkinsa tamkar yar da aka haifesu ciki ɗaya a tausashe yace.
“Me kikeyi a kitchen?”.
Ya ƙare maganar yana Binta da ido ganin yadda ta rame har ta ƙanƙance.
Cikin murmushi tace.
“Indomei zan dafa inci yunwa nakeji”.
Kanshi ya ɗan jujjuya tare da kallon tsakiyan Parlour.
“Ina Antynki?”.
Da yatsa ta nuna mishi bedroom ɗin Meymey.
Kafaɗunta ya ɗan riƙe tare da ɗan matsar da ita gefe, kana ya nufi inda ta nuna mishin.
Tura ƙofar yayi a hankali tare da shiga da sallama a bakinsa.
“Assalamu alaiku....”.
Sai kuma rogowar sallamar ta maƙale a tsakiyar maƙoshinsa bata koma cikiba kana bata fito
wajeba.
Sai kuma ya tsaya tamkar an dashi idanun sa kuwa sai neman rufewa sukeyi da kansu, saboda
sai ƙanƙamcewa sukayi, ya kuma hanasu rufuwan ya saitasu, kan Meymry dake ruggume da Dr
Zakariyya!
Wani irin tsuma da tashi yaji tsikar jikinsa nayi.
Wanda yake da yaƙinin bakwai na kishi bane, sai na tsananin mamaki da jin tsoron lalacewar
Meymey, eh ya sani makirace, Amman bai taɓayin zato ko tsammanin cewa lalacewarta har ta
kai matsayin tayi wannan muguwar ɗabi'a da kuma igiyoyin aurensa a tsakiyar kantaba baisan
cewa rashin tsoron Allah ta ya kai wannan mata kinba ta shigo mushi da gardi fasiƙi mazinaci
har cikin gidansa,.
Dr Zakariyya kuwa, wani irin fitinenne fitsari tsorone ya tsinkomishi.
Saboda kwarjini da haibar Taj ya tsinka mishin hanjin ciki da zuciya.
Wannan yasa tuni fitsarin ya fara ɗiso mishi cikin sauri yayi ƙasa da kanshi domin bazai iya
kallon tsarkakkun idanun Taj da nashi ƙazanrattun idanunba.
Ita kuwa Meymey cikin wani irin tsaurin ido da tson ɓoye ainihin firgita da gigitar da tsoron
idanun Taj daya sakar Mata, tasa hannunta da sauri da nufin kamo hannun Dr Zakariyya daya
janye jikinsa da nata, yayinda gaba ɗaya jikinsa yake ta rawa tamkar mazari.
Sai kuma ya nufo hanyar fita yana wani irin yin fiki-fiki da munafukan idanunsa.
Shi kuwa Taj a hankali ya ɗan jungina da gefen ƙofar tare da harɗe hannunsa a ƙirji kana ya
ɗan ɗaura ƙafarsa ɗaya bisa ɗaya.
Kululu'ulllllllluuu. Cikin Dr Zakariyya da Meymey suka bada sautin a tare.
Shi kuwa ido ya kafe Meymry dashi ba ko kebta wannan ne kuma ya sakar mata da rawan jiki.
Shi kuwa Dr Zakariyya cikin fellewa a guje ya raɓa gefen Taj ɗin ya wuce.
Yana matse da hantsar wonɗonsa da tuni ya jiƙe da fitsari.
Da wani irin kallon da yasa hantar cikin Meymry kaɗawa ya raka Dr Zakariyya dashi.
Sai kuma ya dawo da lannsa kanta, ko ƙala bai ce mata, sai irin kallon nan.
“Ke najasace, kuma ke baki da amincin da zuciyata zata aminta dake bare inji kishinki, sai dai
inji kishin saɓawa Allah da kikayi a cikin gidana”.
Duk da ba mgna yayi da bakiba Amman idanunsa sun nuna mata kallon ƙazantacciya kuma
ƙasƙantacciya yakeyi mata.
Wani irin rumtse idanunta tayi da ƙarfi lokacin da taga ya juya ya fita.
A Parlour ya samu Laylah riƙe da plate ɗin indomei.
Hannunta ya kamo kana ya juya suka fito.
Ganin ya shiga Motane yasa Abu Hashim shigowa ya ja motan tare da cewa.
“Ina zamuje?”.
A taƙaice yace.
“Gida”.
Koda suka isa cikin gidan, kai tsaye part ɗin Malam Laylah ta nufa, shi kuwa part ɗin
Ummeynshi ya shige.
Laylah na shiga Halima ta buɗe mata hannun da gudu tazo ta, ruggume sai kuma tayi saurin
sake Halima ta ruggume Ummeey tare da cewa.
“Ummeey yunwa nakeji”.
Cike da tausayin tarin maraicin dake dabai-baye da rayuwar yarinyar Rashida tayi sauri sa mata
abinci.
Maryam kuma kama hannunta tayi ta zaunar da ita.
Nan take ta faraci, hannu baka hannu ƙwarya, fes ta cinye ganin haka Rashida ta ƙara mata.
Shima tas ta cinye, za'a ƙara mata ne, tace a'a ya ishe ta.
Cikin kulawa Halima dace.
“Laylay kin rame kinyi doshe da yawa”.
Kai kawai ta jinjina tare da ɗaukar Iman suka fita, ta nufi gardin ɗin gidan.
Ganin lokacin sallan la'asar ya ƙaratone yasa.
Malam da Uncle Jibirin da suke ɗaya Parlour suka fita suka tafi masallaci kamsussalat dake
cikin gidan.
Haka yasa suma duk mazan suka fita.
Su kuwa mata hira suka ɗan ci gaba dayi saboda da ɗan sauran lokacin.
Sai da suka ji an kira sallane, kana duk suka miƙe suka yi sallan la'asar ɗin a nan Parlour
Malam, bayan sun idar ne kuma duk suka miƙe suka nufi sashinsu.
Maryam da Halima ɗakin da Haliman ta sauka suka nufa, Rashida kuma bayan Ummey tabi,
dan zata kimtsa mata durowarta.
Cikin wani irin yanayi mai wuyar fahimta Ummey ta ke kallon Taj dake zaune bisa alamu yanzu
ya dawo daga masallacin.
Zaune yake a ƙasa yayinda ya kife kansa bisa gadon, tare dasa hannunshi duka biyu ya rumtse
kanshi dake mishi wani irin fitinenne sarawa, sam shi lamarin Meymey baya cikin kansa, sai
wannan gangancin da yafi kama da wasan kwaikwayon da ya aikata ne, ke gab da fasa minshi
kai, a hankali ya ɗan murza kanshi kaɗan ya gyara wayar dake manne da kunnenshi. “Uhmmmmm”. Ya fidda wani sauti mai kurman baƙi.
Aysha kuwa gyara zamanta tayi, tare da gyara wuyan ɗan ƙaramin baby hijjab da su Doctors
suke yawan ta'ammali dashi.
Sai kuma ta lunshe idanunta tare da gyara riƙon wayar d takeyi da Taj ɗin, cikin sassayan
murya tace.
“Please ka daina wannan damuwar, in sha Allah ba wata matsala da zata faruwa, yadda ka
tsaida hawayen dottijon nan, Allah zai cika maka rayuwarka da farin ciki ya tsaida ma
hawayenka, na sani yanzu ko abinci baka ciba”.
Sai kuma ta buɗe idanunta jin muryar Dr Nafi'u Kabir Katsina ya turo ƙofar Office ɗinta tare da
cewa.
“Hi Sweetheart me kikeyi ne, har yanzu baki tafi gidaba?”.
Wani ɗan gajeren tsaki Taj yaja saboda jin Muryar Dr Nafi'u Kabir Katsina.
Sai kuma yayi saurin sakin sassayan numfashi tare da mgnar zuci.
“Wai kai Taj meyasa kake tsanan kusancin Dr Nafi'u ne, da Ishmah duk da kasan cewa ta
tsaidashi a matsayin mijin aurenta, wanda yau saura wata ɗaya ne rak aure nasu”.
Sai kuma yayi saurin buɗe idan shi jin Muryar Ummeynshi.
Zama tayi gefenshi kanshi ta ɗan ɗago tare da ɗaurawa bisa cinyarsa, cike da kulawa tace bani
wayar.
Ba musu ya miƙa mata
Katse kiran tayi domin bata san da waye yake mgna ba, sai kuma ta kalli Rashida data zuba
musu ido.
“Jeki duba a fridge din Dinnin area akwai fruits salat da na haɗa, ɗazu ki kawo min”.
To tace tare da juyawa ta fita.
Jim kaɗan da fitanta ta dawo hannunta riƙe da wani bowl mai ɗan kare kyau, da spoon a ciki,
amsa Ummeynshi tayi tare da ɗan janye guiwowinta, kana ta fuskanceshi da kyau, ɗiba tayi tare
da kai mishi baki.
Kai ya ɗan jujjuya sai kuma ya miƙa mata hannun alamu ta bashi, zaisha da kanshi.
“Ka tabbatar?”. Ta tambaya cike da so ƙauna kulawa irin na uwar, uwarma da shi kaɗaine ɗanta
na miji.
Ganin ya gyaɗa mata kaine yasa ta miƙa mishi.
A hankali ya kai spoon ɗin bakinsa.
Spoon biyu yayi sai kuma ya ajiye, ganin haka ne yasa Ummeynshi amsa ta fara bashi, dole ya
fara amsa saboda ganin alamun rashin cin abincin nashi na damunta.
Saida ta bashi kab kana tace.
“Zuwa yanzu zurfin cikinka, ba damuna yakeyi ba, cutar dani yakeyi, Afif ina cutuwa da zurfin
cikinka da haƙurinka.
Zuciyata na ƙuntata a duk sanda naga tarin damuwa tare da kai, Amman sai kaƙi faɗa.
Har kwanan gobe nasan cewa ba son Meymey kakeyi ba, Amman tsananin haƙurinka da zurfin
cikinka yasa mahaifinku gaza gane abinda kakeso da wanda baka so, har ya aura maka matar
da ranka bayi so.
Still yanzu kuma naga tsananin tashin hankali a cikin ƙwayar idanunka da ɗimuwa, Amman kayi
shiru ka binneshi a ranka ya kakeso inyi ne Afif?”.
Wani makararren murmushi ya ƙaƙalo ya ɗaura bisa fuskar da bata taɓa riskar irin yanayin
damuwa da yake cikiba sai lokacin da aka aura masa Meymry da kuma yau.
Cikin son kwantar mata da hankali da gudun ɓacin ranta yace.
“Ummey na ba abinda ke damuna fa, kwai gajiya ce, so nake nayi bacci”.
Da sauri tace.
“Toh me ya dawo da kai bayan ka tafi gidanka”.
Cikin sanyi yace.
“Laylah ce na samu, bata ci abinciba Ummey shiyasa na taho da ita taci abinci in kuma yi sallan
la'asar da Yah Abana”.
Ido kawai ta tsura mishi tana son nazartarsa, Amman ina shi har idanunsa kan iya ɓoye ainin
matsalarsa duk duniya ita ɗince ma kaɗai kan iya fahimtar yana cikin wani yanayi ma, sai kuma
Ishmah da ita ko muryarshi taji tana iya gane komai tare dashi.
Ajiyan zuciya mai tafe da raunataccen numfashi ta fesar tare da fara mishi addu'a.
“Yah Allah ka shiga lamarin wannan ɗan nawa Tajuddeen, ya Allah kaine ka halicce shi da zurfin
ciki, da haƙuri da jurayar da tasa baya iya fuskantar kowa na duniya ya faɗa masa matsalarsa
sai kai, mahaliccin mu, Yah Allah ka shiga lamurran sa ka yaye mishi damursa ka bashi sa'a da
nasara akan duk wani ƙalubalen rayuwa, yah Allah ka hana hawayensa zuba a inda bashi da
mai sharce mishi su”.
Murmushi nan dai na ƙarfin halin yakeyi yana mai amsa addu'o'in da take jere mishi, hakama
Rashida da Maryam da yanzu ta shigo.
Hannunshi ya miƙa Ummeeyshi tare da yin musabaha kana ya miƙe tsaye.
“Bari in tafi”.
Tana miƙewa itama tace.
“Toh Laylah fa?”.
Yana mai ɗan taune gefen lip inshi na ƙasa yace.
“Zamu tafi tare?”.
Ya ida mgnar suna fitowa Parlour, dai-dai lokacin kuma Zakiya da Laylah suka shigo, haka yasa
suka fita tare.
Suna isa gidan.
Ya wuce side ɗinsa.
Laylah kuwa cikin sanyi ta nufi bedroom ɗin Meymey dan zata isar da saƙon Halima.
Daga bakin ƙofar ta fara jiyo Muryar.
Amal ƙanwar Taj ƴar Hajia Muhibbat, uwar Kabir kenan wanda itama ƴaƴanta duk matansae sai
Kabir kaɗai
Cikin neman mafita da kuma saka gadar zaren da suke shiryawa Taj Meymey tace.
“Ai wallahi ko yaƙi Allah sai ya sakeni, ko shine ƙwai sai na sashi ya magantu, kuma zanyi
amfani da zurfin cikin nasa, da ya hanasa fitowa ya butulcewa iyayensa lokacin auren harfa
wani cemin yayi nimafa ba sonki nakeba.
Kawai kije ke ki butulcewa naki mahaifin nasan in kikace bakya so Malam zai janye”.
Ƙwaffa Amal tayi tare da cewa.
“Bana gaya miki tun lokacin ba, inda Yah Afif ne, wlh bazai taɓa yiwa Malam musuba, ko ya fito
da damuwarsa, haka Allah yayisa.
Shi yasa da wannan halin yasa Malam yakeyi mishi wani irin bayyannen son da bai san cewa
fuskarsa bata iya ɓoyewa ba, ke Yah Afif duk nacinka da jarabaar neman mgnarka bazaiyi ma
kamar yasan kanayi bare ya kulaka, domin da yana kula mutum da tuni shi da Yah Aryan ko
mgna bazasuyi ba, domin a fili yah Aryan yake nuna tsananin tsanar da yake yi masa. Kuma abin mamaki yanzu haka shi ya ɗauki nauyin karatun Arfa, ɗan Yah Aryan wanda pilot
yake karanta in kinji milliyoyin da yake kashewa sai ki riƙe baki.
Ya haɗa da Imran ɗan Yah Hafiz, duk shi yake musu komai suna karatu a Mexico”.
Sai kuma ta zuwa Meymey ido jin tana cewa.
“Uhmmm ai bai haɗu da kaidin macce bane, su mazane shi yasa”.
Da sauri Amal tace.
“Kaidin macce kuma ai in kinsan abinda Mom ke shiryawa a kansa tsawon shekaru yana
tsallake wa sai kinyi mamaki.
Kawai dai yanzu zamu haɗa ƙarfi da ƙarfe ne.
Zan gayyato Yah Aryan da Mom a cikin tafiyar.
In sha Allah sai mun tozartashi tozarci mafi muni, sai mun Ƙyamatar dashi a zuciyar Malam sai
mun rabashi da wannan soyayyar ta juye ta zama ƙiyeyya, uwarsa kanta da take jin daɗin ɗanta
mahaddacine sai ta fara kunyar amsa sunan uwarsa sai tayi nadamar haifarsa”.
Wani makirin murmushin Meymey tayi tare da gyara zamanta suna masu ci gaba saƙa gadar
zare.
Laylah da tazo da niyar, isar da sakon Halima na ta cewa Meymey gobe zatazo ta wunin musu.
Jin kalaman da sukeyi ne, yasata tsayawa a bakin ƙofar tamkar an dasata.
Duk da ƙaramcin shekarunta.
Abun ya bugeta, haka nan tsoron Meymey ya ƙara rufeta.
Jin motsinsu alamun zasu fitone yasa tayi saurin fara yin Knocking.
Dai-dai lokacin kuma suka iso bakin ƙofar Amal ce a gaba, ganin Laylah ne yasata ɗan suƙe
fuska tare da cewa.
“Lafiya”.
Cikin yin ƙasa da kai ta isar da saƙon Halima, da sauri ta juya da baya saboda tsawar da
Meymey ta watsa mata.
“Ke matsa daga nan shegiya ƴar ta'adda ɓacemin daga nan”.
Da sassarfa ta wuce ɗakinta.
Shi kuwa Taj yana shiga al'wala yayi tare zama bisa sallaya, idanunsa ya lumshe tare da fara
karanta suratul Khaff.
Sai da ya dire ayar ƙarshe sai kuma, ya saita Camera wayarshi.
Ya karanta aya ta 67-70, ya tura a shafinsa na TikTok
Tare da ɗanyin ɗan guntun rubutu a saman video.
Don't forget to read, suratul Khaff on Friday, Jumma'at Mabrooq to all Muslims Ummah.
A ƙalla yayi kusan stsawon shekara ɗaya da fara hakan, domin tunasar da al'ummar musulmi.
Yanayin Update ɗin video in 5 minutes a ƙalla mutum sama da 1,700 sukayi mishi like, a
comment kuma sama da mutum 1000 ne sukeyi, mafi akasari su addu'o'i garesa da jinjina
baiwar zazzaƙar muryar da Allah ya bashi.
Follower's kuwa duk ta inda al'ummar musulmi suke a duniya waɗanda ke TikTok ɗin suna biye
dashi.
Misalin ƙarfe sha biyu na dare.
Ishmah ce ke kwance bisa gadon ta, tayi da take riƙe da wayarta tana bibiyar comments ɗin da
ake yiwa Taj, wanda dama ita ke bibiyar masa comments inshi, duk abinda ta gani na tambaya
ko yabawa ko neman haske, takanyi screenshot sai ta tura mishi ta Whatsapp.
Washe gari ranar asabar. Cikin Ethiopia, gidansu Adaya.
Daga bakin ƙofar Parlour wani, irin kiɗinema mai cike da salon kiɗin su na Ethiopia na Damm ke
tashi.
Zirya takeyi a tsakiyar Parlour tare da rawa da juyi tamkar mazari, irin rawarsu nan dai na wuya
da kafaɗu.
Cikin burgewa da so, ganin sabanin kwarewar ta a rawar, ƙawarta Asina da abokinsu Izzin,
suke kallonta, dayi mata video tare da liƙi, jujjuya kanta takeyi, tana tsawo dashi, kamar barewa,
sai kuma tayi guntu dashi kamar, kwaɗo tana jujjuyashi kamar maciji, sai kuma fara karkaɗa
kafaɗarta na hannun hagu, kai kace jikinta ba ƙashi bane, robace, pantsama-pantsaman
nononta kuwa sai rangaji sukeyi cikin yar rigar data matsesu, tamkar zasu bulluƙo waje dan
girma da cika, sunyi tumsu tumsu.
Izzine, ya kalleta cike da sha'awa domin yana masifar gigita da yadda take kaɗa rusa-rusa
nonon.
Sai kuma ya haɗiyi yawun , saboda ganin yau ɗin tana cikin tsananin fushi da hatsala tana
rawan ne domin shine kaɗai ke sama mata nitsuwa, cikin haki ra
Fuskan cesu, cike da yanayin ƙunci mai gwauraye da tsiwa da gausin baki dake bayyana
shagalarta da duniya, ta dawo ta zauna gaban Step Mom ɗinta.
Tare da rumtse idanutan da kukan data kwanayi yayi sanadin kumburarsu cikin yaƙini da ƙarfin
aniya cikin harshen Yaren Omoro tace.
“Wallahi tallahi auren nan bai ɗaur....
Wasan da yanzu aka soma, toma me akayi ki biya ki karanta cikin salama.
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/7, 12:14 PM] Leematu: ✈️
*INDA RAI*
*BOOK ONE PAGE 5*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
*Littafin INDA RAI na kiɗine wannan free pages ne, muna gama free page kuma ko kin ganshi a