Showing 54001 words to 57000 words out of 80879 words
Chapter 19 - Inda Rai B1 True Books Available Rubutawa Aisha Aliyu Garkuwa .pdf
yace.
“Bakomai Abba in Sha Allahu watarana zai wuce kamar bai faru ba”.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya Abba ya gyara zamansa tare da cewa.
“Haka nake fata shiyasa nake so ka taimaka min da wani abu saboda naga Mamana tana
fahimtar maganar ka tana kuma jin shawararka”.
Ahankali Taj ya sake sunkuyar da kansa ƙasa yana mai sauraron bugun zuciyarsa dake
tabbatar da mgnar Abba haka take, yasan Ishmah na bin shawararsa sosai yasan akwai good
understanding a tsakaninsu.
Abba kuwa cikin sanyi da yaƙinin Taj zai fahimtar da Ishmah ya cigaba da cewa.
“Kaga ga Mahaifin Yaranta nan yana sonta yana ta ziryan zuwa zai maida ita itace taƙi bada
haɗin kai, bamu sani ba wala Allah Rabo ta dashi ne yaketa kauda sauran Mutanen da suke
zirya wurinta.
Zuwa yanzu Yayana Muhammad Bello, ya fusata a kaina, baya ƙasar ne shiyasa baku gabana,
ya tafi Uhmra dashi da iyalansa, kuma da yake su a Gombe suke da sauran ƙannena zaman
aiki ne ya kaisu can duk mafiya akasarin Family na suna Gombe, babban yayan mu ya fusata
sosai a kan Aysha yace min kusan dominta ya tafi umra zai roƙi Allah yayi mata zaɓi da mafi
alkhairi, ya tabbatar min wlh muddin ya dawo zai ɗaura mata aure da duk wanda yaga dama ko
tana so ko bata so.
To dan Allah ka tayani bata baki sannan ka nuna mata amfani da muhimmanci yin auren da
kuma muhimmancin komawa kan ƴaƴanta saboda ɗa sai da Uwarsa kuma itama uwa saida
ƴaƴanta, ka sanar mata yadda mukayi da ɗan uwana in fa ta sake har ya dawo ya huta gajiya
ya taho daga Gombe zuwa nan tofa tayi kuka da kanta a kan duk abinda yayi mata ta sanshi
tasan halinshi zai aikata duk abinda yace, gashi suna tare da wasu manemanta a can Gombe”.
Lokaci ɗaya yaji zuciyarsa tana bugawa yayinda zufa ya shiga tsatstsafo masa duk da sanyin
da ake yi ga kuma sanyin AC.
Haka nan yake ji kamar wani abu mai masifar nauyi ne Abba keson ɗaura mishi, ji yake yi
kalaman Abba na firgitashi kana suna sauƙa a kan jiki da zuciyarsa tamkar rushi yake watsa
mishi, shiru yayi batare da yace komai ba saboda lips inshi sun mishi nauyi...
Abba kuwa ganin yanayinsa ne yasashi sauƙe ajiyar zuciya tare da faɗin.
“Tajuddeen Shiyasa nace maka al'farma nake nema saboda na san zakayi tunanin idan kasa
baki acikin maganar zata yi fushi da kai ko wani abu amma koda tayi fushi da kai nan gaba zata
fahimci gaskiya ka faɗa mata tunda dama ai ita gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata”.
Kai Taj ya jinjina ba tare da ya iya motsa lips inshi ba.
Abba na gyara zama yace.
“Toh ka nuna mata muhimmanci haka idan kuma tace.
Dr Nafi'u zata jira toh ta cigaba da jiranshi amma Dr Nafi'u bazai Aureta ba ka gani tun yaushe
ake abu daya sai abu yazo sai yaja kwanaki”.
Runtse Idanu Taj yayi cikin tsananin bugun zuciya daya baibaye shi.
Abba kuwa cigaba da cewa.
“Ko yaushe sai jan kwanaki yake yanzu haka ya dawo yace wai akwai wani course da zai je
Indi'a yayi na wata shida sai dai ta jira idan ya dawo daga course ɗin sannan ya ƙara da cewa
wai idan ta samu wani tayi Aure ta kawai.
Toh kaga wannan alama ce ta ya janye hannunsa akan neman Aurenta kuma ga Alqasim
mahaifin ƴaƴanta yana bibiyarta tayi haƙuri ta koma kan ƴaƴanta ta riƙe ƴaƴanta ta bawa
ƴaƴanta tarbiyya da kanta shi yafi mata Al'khairi ”.
Numfashi mai nauyi yaja kana ya ɗago idanunsa tare da cewa.
“Abba nayi al'ƙawari zanyi mata magana kuma in Allah yaso ya yarda zaka ga sauyi”.
Cikin jin daɗi da samun sassauci Abba yace.
“Toh Allah yasa adace”.
Cikin sanyi da rauni ya sake sunkuyar da kansa tare da cewa.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.
Abba kuwa Idanu ya zuba masa yana mai tuna mafarkin da Dadeey ta faɗa masa tsakanin Taj
da Ishmah cikin sauri ya kawar da tunaninsa Aransa yace.
“Ai mafarki ba gaskiya bane”.
Nan dai Yah Muhammad ya shigo sukayi hira dashi.
Bayan an idar da sallar Isha'i Ishmah da Tajuddeen ne aharabar gidan agarden amma ba
ainihin cikin garden ɗin ba suna daga farko ƙasan Bishiyoyin ayaba yana zaune tana masa
Video fuskarta ɗauke da Murmushi kana tana mai jujjuya fararen idanunta acikin nasa tace.
“Kayi karatu mana kayi karatu”.
Ƙwayar idanunsa ya juya kamar yanda takeyi yace.
“Toh wace surah zan karanta Miki?”.
Tana mai gyara wayar tayi Murmushi tare da cewa.
“Ni kowanne ma ka sani ina so in dai acikin muryar kane tana yimin daɗi”.
Ɗan murmushi yayi tare da faɗin.
“Toh Bismillah”.
Camerar ta saita akansa tana mai cigaba da Murmushi dake bayyanar da fararen haƙoranta.
Shi kuwa Taj anutse yake kallonta tare da motsa lips inshi yace.
“Dawo nan kusa dani”.
Sai kuma ya maida kallonsa kan Laylah Minat dake can gefe tare da cewa.
“Laylah!, Laylah!! Zo ki riƙe wayar”.
Da sauri Laylah tazo ta amshi wayar video ta fara.
Miƙewa yayi tare da ɗan gyara tsayuwarsa, a hankali itama Ishmah ta mike ta matsa kusa dashi
kaɗan.
Sai kuma ta kallesa shima kallon ta yayi kana ya ɗage mata girarsa ɗaya tare da faɗin.
“Ya dai?”.
Tana tura baki tace.
“Ashe dai ka fini tsawo?”.
Murmushi yayi wanda ke sake fitar da kyawun fuskarsa yace.
“Ohhh dama ke tunani kike dama tsawon ki ya kai matakin da zaki iya kamani atsawo?”.
Narkar da Idanu tayi kana tayi Murmushi tare da cewa.
“Aini nayi tunanin baka fini tsawo ba”.
Hannunsa ya ɗan ɗaga kana ya ɗaura saman akanta..
Laylah kuwa murmushi take tana cigaba dayi musu Video Minat ma murmushi takeyi.
Shi kuwa Taj kuwa murmushi yayi cike da aji yace.
“Kalli fa zan iya daura plate akanki inci abinci”.
Ware idanunta tayi tare da faɗin.
“Lallai dai kam haka kace amma idan na sa hill ai bazai yi ba”.
Lallausan sajensa dake ƙyalli da sheƙi ya shafa kana yace.
“Um-um ai ko kin sa bazaki gagareni ba dole dai kece a ƙasa na”.
Sai kuma ya gyara tsayuwar sa tare da yin Bismillah Laylah kuwa cikin sauri tayi serving
wannan video ta sake farawa daga farko wanda ba ƙaramin kyau sukayi ba.
Ita kuwa Ishmah shiru tayi tare da tsura mishi ido, tana mai sake mishi lallausan murmushi.
Kallonta yayi tare da faɗin.
“Wacce surah kike so in karanta Miki?”.
Sanyayyan numfashi ta fesar kana tace.
“Aini kasan cewa kowacce surah ce ina jin daɗin saurara”.
Murmushi yayi cikin jin daɗin yanda take son muryansa yace.
“Ok bari in karanta Suratul Rahman”.
Cikin jin daɗi tace.
“Masha Allah Ubangiji ya mana Rahma arayuwar duniya da kiyama”.
Ameen ya amsa kana ya fara karanta Suratul Rahman.
_“Alrrahman”_
Ahankali Ishmah ta lumshe Idanunta tana mai motsa laɓɓanta.
Shi kuwa cikin sanyayyan sauti mai sanya nutsuwa azukatan dake saura ya cigaba da cewa.
_“AAallamal Ƙur'an”_
Ahankali ta buɗe idanunta dake lumshe ta zuba masa tana jin wani irin nutsuwa na ratsa ko
wani ɓargo da tsokar da jinin dake gudana asassan jikinta.
Kallon gefen Idanu ya mata tare da faɗin.
_“Khalaƙal Insaan”_.
Wannan karon kam kasa jurewa tayi haka nan taji alamar idanunta nason tsatstsafo da ruwan
hawaye yayin da wani irin salama da aminci ke baibaye ta...
Haka ya riƙa jero ayoyi dake ratsa zuciya.
Dai-dai lokacin kuma Aunty Nana ta fito harabar gidan da alamu zasuje unguwa ne dan ga
Khalid da Yah Muhammad har zata shiga mota ganinsu yasa tayi Murmushi tare da kallon
mijinta da yake gaisawa da Taj ɗin.
cikin girmaman darajarsa da kwarjin hasken Alqur'ani tace.
“Barka da dare Sheykh”.
Cikin sanyinsa cike da kamala ya ɗan risinar da kansa yace.
“Aunty Nana Barka da fitowa”.
Tana murmushi tace.
“Barka dai al Sheiky bari muje Unguwa”.
Yana kallon Ishmah yace.
“Sai kun dawo”.
Kai ta gyaɗa kana ta shiga mota, da sauri Minat ma tabi bayansu .
Ahankali ya maida kallonsa kan Ishmah tare da cewa.
“Gobe in Allah ya kaimu da safe zaki rakani gidan Hajja Umma in gaisheta, da Aunty Hawwa,
Aunty Aysha, har ma da gidan Garkuwa inje in gaishe su ko”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Toh Allah ya kaimu lafiya”.
Ameen ya amsa kana sukaci gaba da hirarsu.
Washe gari da safe tsaye Ishmah take a kitchen ta jingina jikin sink ɗin kitchen numfashi ta
fesar tana tunanin mai zata girkawa Taj na breakfast.
Fridge ta buɗe ta ɗebo naman rago zallan tsoka ta wanke kana ta yanka albasa tare da saka
maggi, garlic, curry, seasoning, sai ruwa kaɗan gass ta kunna ta daura tana tsaye ya tafaso
kwashewa tayi ta zuba man gyaɗa cikin ƙaramin lokaci ya soyu bata barshi ya soyu sosai ba ta
kwashe kana ta ɗauko plantain data yayyanka ta zuba acikin man cikin mintunan da baza su
gaza uku zuwa huɗu ba ya soyu kwashewa tayi ta zuba wani shifter kana ta rage yawan man
daidai yanda zai mata ta saka Tafarnuwa, Citta, albasa, jajjageggen attarugu da tattasai da ya
wadatu da albasa ta zuba, sai kuma ta zuba curry, Maggi, da sauran spieces sama-sama ta
soya kana ta kawo soyeyyen plantain da soyeyyen naman ta zuba bayan ya ɗan fara soyuwa ta
kawo ruwan data tafasa naman kaɗan ta zuba sai kuma grean beans da Carrot ta zuba kaɗan
sai ta ɗan watsa kifin data gyara a ciki tare da zuba yankekken albasa mai ɗan dama a ciki...
Da sauri ta juya jin Aunty Nana da Aunty Maryam suna haɗa baki wurin cewa.
“Masha Allah me ake girka wa wanda ya cika gidan da ƙamshi haka?,tun ina Azkhar ƙamshi ke
barazanar toshe min hanci”.
Murmushi tayi ita kanta tasan cewa source ɗin yayi masifar daɗi ga ƙamshi na musamman dake
fita.
Tana sauƙe tukunyar tace.
“Laaaa Aunty Nana ba wani abu bane mai wahala bafa sai daɗi na yiwa Taj source da farar
taliya kinsan bai fiye son abu mai nauyi ba”.
Ta ƙare maganar tana zuba source ɗin cikin warmer me kyau wanda tuni ta juye farar taliya data
fara da fawa acikin ɗaya Warmers ɗin murmushi Aunty Maryam tayi tare da cewa.
“Aikam dai yayi kyau sosai ni kuma da har nayi mishi Chickensandwich da ɗan Yam balls.
Ta kai ƙarshen maganar tana ajiye mata food flack's ɗin a gefentan.
“Eh ai bai ɓaci sai ya ci abinda yakeso”.
Ta faɗa tana kallonsu ganin yadda suke mata wani irin kallon tuhuma.
“Kallon nan fa to?”.
Kai Aunty Nana ta jujjuya tare da cewa.
“Wai ku yarda cewa son juna kukeyi. Amman kunƙi yarda, sai randa so ya fasa muku zuƙata
zaku gane”.
Sai kuma ta kalli Maryam dake cewa.
“A haka dai nasan ba wani ɗa na miji da zai iya samun zuciyarki muddin kina tare da Taj, na
kuma tabbata shima ba matar da zaiso sama dake, mutumin da shine ya Kore min Yah Kamal
ɗina”.
Fuska ta kwaɓe tare da cewa.
“Ba dama ayi abota da aminci sai mutane sunce soyayya ake, ni da Taj fa ba wannan mgnar.”
Haranta kawai sukayi kana suka fice.
Ita kuwa cikin nutsuwa ta haɗa masa kunun madara wanda yayi masifar kyau da daɗi kana yayi
fari bata sa sugar da yawa ba tana saukewa ta koma bedroom wanka tayi kana ta shafe jikinta
da Humra da kuma Kolaccar da Garkuwa ta bata towel ɗin ta since kana ta shirya kanta cikin
wata atamfa mai golden dark green da ratsin maroon,sai kuma ratsin fari-fari da golden sosai
rigar ya zauna ɗass ajikinta ɗauri mai V tayi kana ta ɗan ja ɗankwalin baya hakan ya bawa
tattausan sajenta na gefe da saman goshi damar fita. Maroon gyale da plat shoes shima
maroon ta sanya sosai tayi kyau duk da cewa ba tayi wani makeup ba amma asalin kyawunta
ya bayyana baza kace ta Haifo ƴaƴa uku ba.
Anutse ta ɗauki Basket data shirya ta nufi BQ da yake bakinta ɗauke da sallama ta shiga Falon.
Zaune ta hangosa kan 3sitter kunnensa maƙale da waya.
Ishmah kuwa cikin tsananin yaba kyawun da yayi ta motsa laɓɓanta tare da faɗin.
“Masha Allah jinjina ya tabbata ga Ubangiji daya tsara wannan halitta mai cike da tsantsar
nutsuwa da kamala sosai ta shagala da kallonsa sanye yake cikin wata Gezner Fara ƙal anyi
masa ɗinkin riga da wando ƴar ciki da gariya irin na samarin zamani kansa na sanye da hula
Mai mala yayin da ƙafarsa ke sanye cikin wani takalmi mai yatsa irin ratsin hular sajensa ya
kwanta sai sheƙi yake alamar yana samun gyara yayin da jikinsa ke fitar da sanyayyan ƙamshin
turare sosai ta shagala da kallonsa.
Agefen Taj kuwa tun lokacin daya ji Sallamar ya katse kiran kasancewar ya gama magana yayin
da ƙamshin Humra da Kwallaccar ya daki hancinsa yana masifar son ƙamshin jikinta sosai
kwalliyarta ya ƙawatar dashi...
Cikin sanyayyan Muryarsa yace.
“Wa'alaikum Salam Ishmah”.
Dogon numfashi taja kana ta janye idanunta daga kansa tace.
“Taj sorry na Barka kana jira”.
Ta ƙare maganar tana ajiye Basket ɗin kan dining sai kuma ta zauna a lokacin shima ya karaso
zama yayi kan kujerar dake facing ɗin ta.
Mikewa tayi ta ciro Warmer tare da ɗaukan plate ta zuba masa farar taliya da source, sai kuma
ta ɗan sa mishi yam balls and chicken sandwich a Plata ɗaya cikin sauro ya lumshe idanunsa
kana ya buɗe tare da cewa.
“Masha Allah Ishmah wannan ƙamshin girkin ma kaɗai zai wadatar dani ba tare da naci ba”.
Ware idanunta tayi tana Murmushi tace.
“Um-um kadai ci”.
Ta ƙare maganar tana ajiye masa plate ɗin gabansa sai kuma ta ɗan kalli fuskansa jin ya cewa.
“Mu da muka zo gaisuwa, Amman duk kin kiwacemu mun zama kamar kajin gidan gona, naga
Laylah tayi ƙiba sosai, ni ma ɗin so kike in zama ƙato ko?”.
Murmushi tayi tare da
Ciro Flaks ta da mug ta zuba masa kunun madara kana tace.
“Eh ai banso Meymey taga gazawata mijinta ya koma a rame”.
Kai ya jinjina yana tunanin wayar da yayi yanzu da Uncle Jibirin, dake cemai Meymey nata kuka
wai ya tafi ya barta ya ɗauki Laylah ya barta da kewa.
Sai kuma ya ɗan ɗauki fork ɗin, jin tana cewa.
“Kaci mana”.
Lokacin daya Kai spoon ɗin farko bakinsa sai daya lumshe idanunsa saboda daɗi da dandano
daya ratsa harshensa Ishmah kam murmushi tayi jin yanda yake yaba girkin.
Lokacin daya sha kunun madarar kam dariya tayi sosai jin yace sai ta koya masa dan sosai
kunun yayi mishi daɗi.
Bayan ya gama suka fito farfajiyar gidan dai-dai lokacin wayarta ya ɗauki ruri anutse ta duba
ganin sunan Dr Nafi'u yasa tayi picking tare da kaiwa kunnenta bayan sun gaisa yace.
“Kina gida ne?”.
Kai Ishmah ta jujjuya kamar yana gabanta sai kuma tace.
“Eh amma kuma yanzu zan fita”.
Kai tsaye yace.
“Ina zaki je?”.
Tana gyara rufin gyalenta kana ta ɗan gyara zaman wayar akunnenta tare da faɗin.
“Zan raka Taj wajen Hajja Umma ne”.
Murya acun kushe yace.
“Ok fita da shi yafi jirana muhimmanci ne?”.
Ya ƙare maganar yanajin anya zai iya haƙura da ita kuwa, duk da baya son raɓa mata cutar
dake tare dashi yanajin kuma son ɗanɗanar jinkinta, a ranshi yake faɗin.
“Gwara a ɗaura mana aure mu tafi tare, tunda yanzu kwana arba'in ya rage in tafi, ai nima gani
ina raye, so itama bazata mutuba sai muyi ta shan magani a tare”.
Ya ƙare maganar zucin yana mai wassafo surarta a idon zuciyarsa.
Ita kuwa Ishmah
Ahankali ta juya ta kalli Taj.
Taj kuwa fuska ya tsuke kasancewar yana ɗan jiyo abinda Dr Nafi'u ke faɗa.
Ganin yanda Taj ya tsuke fuska ne yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa.
“Dr kamanta ance baƙonka annabinka”.
Da dan fusata a Muryarsa yace.
“Eh ban manta ba amma Allah da girma yake Miji da girma yake kin manta cewa Annabi
Muhammad (S.A.W)yace da zai umarci wani yayi wa wani sujjjada a duniya daya umarci mace
da tayiwa mijinta sujjjada”.
Sanyayyan numfashi ta sauke kana tace.
“To ai Dr ba'a riga da an ɗaura ba ko Dr?” .
Cikin fushi da kishi yace.
“Ohhhh gadarar da kike kenan ba'a ɗaura ba kin mance mungama komai har Sadakina yana
hannuki, ke nifa na tsani wannan Taj ɗin naki da wasu makiran idanunsa na jarababbun maza”.
Cikin sanyi da kuma son kawo karshen maganar tace.
“Dr idan ya tafi dai shikenan”.
Cikin fushi yaja dogon tsaki tare da cewa.
“Idan ya tafi shikenan?,Ba shikenan ba idan kina so ki bishi sai in tabbatar daya fini matsayi da
kima awajenki”.
Yana kai ƙarshen maganar ya katse kiran.
Cikin sanyi da rauni ta juya wayar nata ta kalla sai kuma ta kalli Taj.
Taj kuwa hannunsa ya buɗe alamar ko oho kana ya nuna mata hanyar tafiya anutse yace.
“Mu tafi mana”.
Araunane ta kallesa sai kuma ta langwaɓar da kai tare da faɗin.
“Taj fushi yayi fa”.
Idanunsa ya lumshe kana ya buɗe su akanta cikin nuna mata matsayi da kima da take dashi
awajensa yace.
“To sai me Ishmah? Idan yayi fushi dake ai ba Abba bane yayi fushi dake, kuma bani bane nayi
fushi dake, so kada ki damu, da ace duk duniya zasu juya Miki baya ni ina tare dake. Idan duk
duniya babu mai tsaya miki Ishmah! Ni zan tsaya miki Idan duk duniya zasuyi ƙoƙarin saka ki
hawaye Ishmah!Ni zanyi ƙoƙarin tsayar da hawayenki”. Lokaci ɗaya taji wani irin nutsuwa da farin ciki na maye gurbin da damuwar da Dr Nafi'u ya
sanya mata haka nan taji zuciyarta ta aminta da duk wani abu daya faɗa ta san shi mai gaskiya
ne bazai taɓa yi mata karya domin yasata farin ciki ba Taj kuwa Ahankali ya cigaba da cewa.
“Kisa aranki idan kina tare dani ba zakiyi baƙin cikiba ki kuma sa aranki kin ƙulla alaƙa