Showing 51001 words to 54000 words out of 80879 words
Chapter 18 - Inda Rai B1 True Books Available Rubutawa Aisha Aliyu Garkuwa .pdf
mai girma. Aka ɗaukesu kai tsaye gidan Sheykh Isa Ali Pantami
suka wuce.
Taj yaga kara da mutumci iyaka a wurin wannan Bagombe ya nuna mishi kuma lallay Gombawa
ɗiban farine, ba'a kwana dasu ba a tashi dasu.
A dare ranar yaga karrama.
Washe gari da safe, cikin mutuntawa Sheykh Isa Ali Pantami ya shiga masauƙin baƙon nasa.
Shi kuwa Taj a dai-dai lokacin waya yakeyi da Ummeey ya kuma haɗa comfrence call ne da
Ishmah sai dai Ummeeyshi bata saniba.
“Babana wai sai yaushe zaka dawo ne? Ko ka mance cewa ka tafi ka bar mararka ne, yau fa sai
nan tazo muka kwana, tace gaba ɗaya ƙasar Ethiopia batayi mata daɗi in baka nan”.
Sai kuma ta ɗanyi shiru.
Shi kuwa Taj a hankali ya gyara tsayuwarsa tare da ɗan gyara zaman hular kansa yana mai
nazari kan wasu ababen sauye-sauyen Meymey da sam a zuciyarsa bai aminta da itaba.
“Hello Babana kayi shiru, ɗazu munyi waya da Laylah tace wai bakusa ranaba me haka ke
nufi?”.
Cikin sanyi murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Yanzu ina Abuja gobe Thursday zan koma Yola. In sha Allah ranar Sunday zan iso Ethiopia
domin in samu in ɗan huta dan inada tafiya ranar Tuesday, kuma Ummeey malam ƙasar ne
suka ɗan riƙeni shiyasa.”
Ya ƙare maganar cikin Yaren Amharic wanda shine asalin Yaren Ummeeyshi, yayi mgnar cikin
sanyi tare da juyowa jin sallar Sheykh Isa Ali Pantami.
Da sauri ya sallami Ummynsh tare da katse wayar.
Ruggume juna sukayi shida Sheykh Isa Ali Pantami.
Yayinda PA'nsa keta ɗaukarsu hoto, gami da ɗan video.
Bayan sun gaisa ne suka wuce wurin taronsu da manyan malam Sunnan.
Inda suka bashi kyautar murya kira'a mafi daɗi da soyuwa a shekarar.
Washe gari da safe jirginsu ya tashi daga Abuja zuwa Adamawa Yola
Cikin farin ciki da jin daɗin mutumtaka da kima daya samu daga Manyan Malamai da kuma
jama'ar Nigeria.
Yah Abubakar ne ya ɗaukoshi a Airport ɗin.
Awaje suka haɗu da Abba wanda ya fito daga Masallaci bisa alamu yayi walaha ne.
Cikin so da kulawa Abba ya ɗan ruggumeshi tare da cewa.
“Barka da sauƙa lfy”.
Sai kuma ya kalli Adam daya buɗe but ɗin motar ya fito da jakarsa yana ɗan ja.
“Masha Allah isa daga ciki, ka samu ka huta, kasha zirga-zirga a titunan ƙasarmun nan da ba
cikekken kyaune da suba bare tsaro”.
Kai ya ɗan jinjina domin Allah ya sani a gajiye yake, ga yunwa dake kwaƙular cikinsa haka Allah
yayinsa baya iya cin abincin kirki in ba matsa mishi akayi ba, so yake yayi wanka yaci abinci
yayi bacci.
Shi yasa yana shiga BQ ɗin kai tsaye bedroom ya wuce.
Adam kuma jakar tasa ya ajiye mishi kana ya nufi cikin gida.
A kitchen ya samu Ishmah tsaye cikin wani tattausan lace pink and sky blue collar mai ɗan
ratsin Royal blue.
Ɗinkin doguwar rigace da Idris ɗinta ya watsa mishi ɗinki na alfarmar, sosai ya zauna a jinkinta
ɗas da ita.
Sai wani irin fitinenne ƙamshi take zubawa, ta murza daurin a setta tayi kyau sosai a ciki.
A hankali take motsa gas meat and Emargency Sultan chips da yaji naman kaza ziryan ɗinta ba
ƙashi ko kaɗan sai ɗan Vegetables kaɗan.
lashe baki yayi tare da cewa.
“Uncle Taj ya iso fa”.
Da sauri ta juyo dan bata san ya shigo ba.
“Ya Salam to miƙo min Food flack' and mug ɗinnan”.
Ta ƙare maganar tana jawo trayn.
Miƙo mata yayi tare da ɗan jawo plate ya miƙa mata kana yace.
“Toh nima a saka min a nan”.
Tana juye Gas meat ɗin a wani kekkyawan food flack's dan madaidacin tace to.
Sai kuma ta juyo Sultan chips ɗin ma.
Kana duk ta jerasu a kan tray ɗin.
Sai kuma tasa plate, bowl, mug, sai spoon and fork.
Duk ta jerasu kana ta miƙa mishi tray tare da cewa.
“Yauwa gashi ka kai kan Dinnin table na BQ sai ka dawo ka amshi naka.
Sannan ka ɗauko min Laylah a gidansu Minat, tun juya suka tafi basu dawoba gashi ya dawo
bata nan”.
To kawai yace kana ya ɗauki trayn ya juya ya fita dan sauri yake ya samu ya dawo yaci wannan
haɗin.
Ita kuwa Ishmah da sauri ta buɗe fridge Yoghurt fruits data haɗa mishi ta ɗauka tare da faro
water ta sasu a tray tare da glass cup.
Kana ta fito, a Falo ta samu Rahman bisa alamu da Khadijah take waya dan jin tana cewa.
“Tunda kika komafa nake ta cewa ki haɗani da Maamah amman kinƙi, Maamah ɗiyar Khadijah
babbar kenan”.
Tana fita ne tace mata.
“Please ki gyara kitchen nan, kuma ki maida tukunyar danderun nan kan gas”.
Tana miƙewa tsaye tace to.
Shi kuwa Taj a hankali yake feshe jikinsa da turare, lokacin da ya gama kimtsa kansa cikin
tattausar jallabiyarsa Black collor.
Ɗan gajere tsaki yaja tare da gyara robar boxer ɗin jikinsa.
Allah ya sani shi baya son takura, musamman ma Taj ɗinsa dake fama da tsaurin ido, shiyasa in
a gidansa yake baya iya zama da Boxers dan bazai iya takura kansaba Allah bai takurashi ba.
A hankali ya ɗan shafa cikinsa jin yadda ya ɗanyu ƙugin yunwa.
A hankali ya fito Parlour.
Dai-dai lokacin kuma Ishmah ke ajiye trayn hannunta bisa Dinnin table ɗin kana ta kalli Khairat
ɗiyar Yah Abubakar wacce saboda Laylah bata nanne yasa ta biya ta ɗaukota suka taho tare.
A tare suka sauƙe numfashi mai nauyi kamar da sauri ya kuma rumtsa idanunsa saboda jin
alamun zaiyi loosing confidence ɗinsa aiko tuni ya gaza control ɗin bakinsa kamar a fizge yaji
yace.
“I miss you so much Ishmah”.
Wani tattausan murmushi ta sakar mushi tare cewa.
“Miss U to my friend”.
Ɗan kwaɓe fuska yayi tare da shafa kan Khairat kana ya ɗan kalli bayan Ishmah yace.
“Laylah fa?”.
Kujerar dinnin table ɗin ta jawo mishi tare da cewa.
“Bismillah zauna, Laylah tana gidansu Minat yanzu Adam zai ɗaukota”.
Cikin sauƙe numfashi gaji ya zauna tare da juya gajiyayyun idanunsa murya a gajiye yace.
“Im tired my heart”.
Ya ƙarashe mgnar can ƙasan maƙoshinsa saboda shi kansa baisan ta fitoba, hakazalika itama
bataji ƙarshenba.
Cikin tausayawa da kulawa tace.
“So sorry sun gajiyar da mijin Meymey ko”.
Ganin kallon da yayi mata ne yasa tayi saurin yin ƙasa da kanta, kana a hankali ya jawo trayn
nan Yoghurt fruit ɗin ta zuba mishi a bowl mai ɗan girma kana tasa mishi table spoon tare da
miƙa mishi tana faɗin.
“Gashi fara da wannan kafin in zuba maka abinci, so nake ka shanye kafin in zuba maka”.
Amsa yayi tare da ɗan lumshe idanunsa su huɗune kacal suke mishi haka a duniya.
Ummeeyshi, Yah Abana, Addawa, da kuma ita, sai kuma Aunty Rashidansa.
Ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe lokacin da ya kai Yoghurt fruit ɗin bakinsa ya Salam, garɗin
madara Apple Banana da kuma zaƙin inabi ne suka haɗu suka sashi fara sha.
Murmushi tayi tare da kallon Khairat dake cewa.
“Goggo Ishmah bani wayarki”.
Miƙa mata wayar tayi kana ta ɗauki plate gefe kaɗan ta sa mishi farar shinkafa, tare da ɗan
ɗaura yankakken lemun tsami daya a kai, sai kuma gefen tasa Sultan chips ɗin ɗaya gefen
kuma tasa gas meat ɗin da yake zuba ƙamshin da kan iya tada yunwa.
Cikin kulawa ta ɗan jawo bowl ɗin gabanshi ganin ya shanye saura kaɗan,
Table spoon da fork ta sa mishi a gefe da gefen, kana ta miƙa mishi.
Da sauri ya fidda idanunsa waje alamun yayi yawa.
Ita kuwa kwaɓe fuska tayi cikin yanayin da bata san tana shigaba tace.
“Please ka cinye”.
Ta ƙare maganar tana sa mishi ruwa a glass cup ɗin.
Shi kuwa Taj kanshi ya ɗan longwaɓar yana yi mata wani irin amintaccen kallon dake fita daga
wani sirri daga can cikin ƙahon zuciyarsa yana cusa shi cikin tata zuciyar a sirrance.
Ganin ta tura bakine yasa ya fara ci.
Ya salam ya gamsu Ishmah ƙarshece a komai.
Yanayin yadda ta haɗa mishi abincin kawai ya ishe ka sha'awa.
A hankali ya fara ci suna ɗan hira.
“Uhmmm kasan yanzu naga an buɗe TikTok da IG da sunanka sosai, har Channel aka buɗe a
You tube da sunanka. Suna ta saka karatuttukanka.”
Murmushin yayi tare da tauna tsokar kazan da yasa a baki yace.
“Da haka suma zasu samu lada”.
Ruwan ta miƙa mishi tare da cewa.
“Harma da kuɗi ai ƴan You tube kam zasu samu”.
Kanshi ya jinjina tare da zuba mata ido jin tace.
“Wannan trolling fa, naga bada shi ka tafi ba”.
Ruwan ya ɗan kurɓa tare da cewa.
“Gomnan Borno ne zulum yayi min irin kyautar da kikayi min, da naje Bauchi kuma Sheykh
Tajuh Usman Bauchi shima ya bani tsala-tsalan alƙyabbu guda uku, harda rawaninsa”.
Cikin murmushi tace.
“Basu dai haɗa maka da mata ba kam ko? Dan naga yadda suke ta ribibinka nace wannan dai
da alama zasu baka mata biyu ka cika ta huɗunka a Nigeria”.
A hankali ya ture plate ɗin tare da jawo Tissue box.
Ita kuwa plate ɗin ta kalla yaci yafi rabi, tunda yazo ma baici abinci mai yawa kamar hakaba,
hakanne yasa ta ɗauki ɗaya plate ɗin ta rufe abincin kana ta tura trayns ɗin gefe.
Shi kuwa Taj ruwa yasha, sassayan gyatsa yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
Ita kuwa Ishmah a hankali tace.
“Ɓoye min zakayi dan an baka mata a ƙasarm..”
Sai kuma tayi shiru tare da ɗan zuba mishi idanunta saboda ganin yadda ya longwaɓar da
kansa kana idanunsa sukayi jazir, lip inshi na ƙasa ya ɗan ciza murya can ƙasan maƙoshinsa
yace.
“Ai dama kafin in samu matar aure a ko ina a faɗin duniya a Nigeria na fara samu, damace da
ban samuba, da ƙaddara dake ta ɗawainiya da rayuwata yasa bamu kasance a tare a inuwar
aureba”.
Da sauri tace.
“Taj a Nigeria kuma? Wacece ita? Me sunanta? Yaushe kuka haɗu? Meyasa baka gaya min
ba?”.
Kafe kwayar idanunsa yayi cikin nata, itanma shi ta tsare da idanunta tana jiran amsarta cikin
sanyi ya motsa lips inshi a hankali yace.
“Ita na fara sani kafin ko wacce mace, bayan Mahaifiyata kakata da yayuna mata. Rashin ta ne
yasa ƙaddara samun damar juya rayuwata, domin da na aureta bazan taɓa auren wata ɗiya
mace ba a duniya, ita kaɗai ta isheni, inada yaƙini zata kula dani kulawar da mata huɗu zasuyi
min, shiyasa a kanta na ajiye burina na auren mata huɗu, domin da wannan burin na tashi a
rayuwata Inyi mata huɗu kamar Yah Abana, ko wacce ta haifa min yaya 12 ko 6-6 Kinga in na
samu ƴaƴan sha bibbiya zan samu yaya 48 in kuma shida shida na samu kinga 24, Inyi musu
irin tarbiyyar da Yah Abana yayi mana, domin Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallam
yayi alfahari dasu a ranar goɓe ƙiyama.”
Sai kuma ya fesar da wani irin raunataccen numfashi mai cike da dafin so kana ya juya
gajiyayyun idanunsa cikin nata.
Hakan yasata kasa janye idonta cikin nata.
Shi kuwa Taj murya can ƙasan maƙoshinsa yaci gaba da cewa.
“Tun randa na ganta naji na janye wannan burin domin nasan zatayi min duk abinda mata huɗu
zasumin, kuma bazan iya yi mata kishiyaba dan inayi mata kishin kaina da kaina, dan nasan in
na aureta ta isheni ko yaya 6 ko biyu ta haifa min sun isheni kai ko bata haihuba zan rayu da ita,
kin mance ina gaya miki in na auri wacce rai da zuciyata keso bazan mata kishiya ba”. Ya ƙare maganar da iyakar gsky zuciyarsa, da sauri tace.
“Taj ashe akwai wani abu naka a duniya da kake ɓoye min ban saniba, toma me yasa baka
aureta ba Taj?”.
Cikin sanyin halinsa da murya yace.
“Ɓoyeyyiyar ƙaddara, bata buƙatar namiji irina, gashi kuma Kinga yadda ƙaddara ta kawo
Meymey cikin rayuwata, ke kuma kika liƙo min Adaya a rayuwata, so yanzu bani ba ƙara aure a
duniya, domin zan bar gurbin wacce nakeso, shiyasa bazan taɓa cika mata huɗuba, dole zan
bar gurbin da duk randa ta soni so na aure zan aureta”. Ido kawai ta zura mishi tana mamakin kalamansa.
Sai kuma tayi saurin cewa.
“Yauwa ya batun Adaya ma yaushe zata tare”.
Da sauri yace.
“Kiyiwa Allah ki bar brain ɗina ya huta”.
Ya ƙarashe maganar cike da alamun tarin bacci da gajiya.
Da sauri tace.
“Toh amman wai meyasa baka haɗani da Meymey ba, ko ta'aziya baka bari tayi min ba”.
Yana miƙewa tsaye yace.
“Nace miki bazan taɓa haɗaki da duk wacce akace matata bace”.
Da sauri tace.
“Wai dan Allah saboda menene?”.
Ba tare daya bari ta ƙarasa mgnar ba yace.
“Saboda kada wata rana suce, kin munafurcesu ko kin hancincesu koma suce kinci amanarsu”.
Da sauri itama ta miƙe tsaye.
Sai kuma ta tsaya ganin ya juyo ya zuba mata ido tare da cewa.
“Itama dayar shiyasa ban haɗaku ba”.
Ta buɗi baki zatayi mgna kenan akayi kiran salla.
Haka yasa tayi shiru.
Bayan sun gama bin kiran sallan da yin addu'a ne ya ɗan kalleta tare da cewa.
“Da jarida kika karanta dan shi ya dace dake ba aikin likitanci ba. Kin wani tsareni da tambayoyi
tuhuma, takaicina ma ba gane komai zakiyi ba, Ni bari inje inyi salla in na dawo kuma zanyi
bacci ne”.
Da ido ta rakashi har ya ɓacewa ganinta, daga nan itama ta kama hannun Khairat suka nufi
side ɗin Aunty Nana a falonta suka sameta tana salla, itama salla ta niyanta.
Azahar yana dawowa yayi baccinsa, kiran salla la'asar ne ya tada shi.
Suna dawowa su Laylah na shigowa da gudu suka nufi BQ ɗin ganin ya shiga, Mahmoud,
Minat, Khalid, da kuma Khairat cikin nitsuwar tarbiyya suka gaidashi daga nan suka fara kallon
Tom and Jerry da akeyi.
Shi kuwa Taj System nashi ya ɗauka ya fara duba shirye-shirye tafiyar da zayyi da ƙasashen da
zai jajje in ya koma ma sai yayi kusan mako biyu yana zirga-zirga in yayi hutun mako ɗaya
kuma zai sake tafiyar da zayyi kwana goma.
Yau asabar, ta kama gobe Sunday ne jirgin Adamawa to Abuja zai tashi da safe, na Nigeria to
Ethiopia kuma zai tashi da yamma.
Bayan an idar da sallan la'asar ɗin. tare suka shiga falon Abba cikin sauƙe numfashi Abba ya
kallesa kana yace.
“Tajuddeen ɗazu da muke shigowa naji kamar kana cemin yaushe zaka tafi?”.
Cikin girmamawa da mutumtaka ya gyaɗa kai tare da cewa.
“Eh Abba in Sha Allahu ina so gobe zan tafi Abuja daga nan zan wuce Ethiopia da yamma”.
Ajiyar zuciya mai nauyi Abba ya sauke kana cikin fesar da numfashi yace.
“Taju mun gode Ubangiji Allah ya saka da al'khairi”.
Kansa aƙasa ya amsa da.
“Ameen ya Allah Abba”.
Numfashi mai nauyi Abba yaja kana ya fesar tare da cewa.
“Taju akwai wata alfarma da nake nema awajenka”.
Cikin wani irin baƙon yanayin da zuciya ke ɗauka abaxata ya kalli Abba cike da girmamawa
yace.
“Abba Kace Umarni zaka bani ba alfarma zaka nema ba. Saboda kafi ƙarfin neman alfarma
awajena sai dai ka bani Umarni kamar yanda Yah Abana zai bani Umarni”.
Zama Abba ya gyara kana ya fuskancesa da kyau cikin gskyar zuciya da amincin da yakeji
akan Taj ɗin yace.
”Um-um Tajuddeen Alfarman dai nake nema”.
Cikin jin nauyi da ganin kimansa ya sake risinar da kansa tare da cewa.
“Abba idan kana faɗin haka kunya nake ji”.
Kai Abba ya girgiza cikin sauke ajiyar zuciya da sanin kiman da muntuncin Taj yace.
“A'a Tajuddeen dole ne ince haka”.
Manyan Idanunsa Masu haske ya lumshe Muryarsa dake cike da nutsuwa ya gyara tare da
faɗin.
“Abba wace alfarma ce wannan?”.
Zama Abba ya gyara kana yace.
“Tajudden Nasan al'aƙarka da kai da Mamana alaƙace data kasance mai tsabta cike da
tsarkakekke zuƙata, irin hasken nan dake haskaka juna wanda aka gina saboda Allah kasan irin
ƙaddarar dake bibbiyar rayuwar Mamana?”.
Cikin wani irin yanayi mai gauraye da zaƙuwar jin ƙarshen mgnar ya jinjina kai. Tare da
sunkuyar da kansa ƙasa Muryarsa cike da sanyin da ƙasan sa farin cikine yace.
“Sosai ma Abba na sani”.
Cikin damuwa da rauni Abba yace.
“N.....!
Littafin nan dai na kuɗine ki biya ki karanta cikin aminci 1k ne 0661110170 GTBank Aisha Aliyu
Garkuwa.
*BY*
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/13, 1:34 PM] Leematu: ✈️
*INDA RAI*
*BOOK ONE PAGE 11*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
*Littafin INDA RAI na kiɗine wannan free pages ne mukeyi kuma suna gab da ƙarewa, 1k ne
kacal kuɗin samur karanta littafin ki saya ki karanta cikin aminci. 0661110170 GTBank Aisha
Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276. Mutanen kasar
Niger kuma 1000fc ne jaka ɗaya kenan rak zaku tura Kuɗin karanta littafin +22790899076 ita
zakuyiwa magana*
“Nasan cewa tana fuskantar matsala akan Aure, amma itama ya kamata ace ta gyara niyarta,
banason in matsa mata saboda banason tayi tunanin na takura mata akan matsalar rashin
Aure, bana kuma jin daɗin zamanta haka babu aure abin yana min ciwo yana hanani bacci
Tajuddeen, domin mutane laifina suke gani, faɗi ake na barta tana abinda takeso ta hau babbar
mota taje aiki tana zirya a gari ba aure”.
Cikin tausaya Taj