Showing 66001 words to 69000 words out of 80879 words
Chapter 23 - Inda Rai B1 True Books Available Rubutawa Aisha Aliyu Garkuwa .pdf
hannu ya ɗaga tare da dakatar da Uncle Jibril kana ya kalli Taj da cewa.
“Taj me nake ji?,Me Meymey take faɗa?, Tajuddeen me nake ji?,”.
Shi kuwa Taj har zuwa lokacin ya kasa magana sai jujjuya kansa yake yayin da lips ɗin sa ke
rawa kana Idanunsa sun kada sunyi jawur Araunane ya juya ya kalli Ummey jin tana cewa.
“Kayi magana Afif shirunka awannan lokacin zai iya yi mana cutar da har abada baza ku warke
ba. Tajuddeen ka buɗe bakinka kayi In-kari akan abinda nake da yaƙinin baza ka aikata shiba”.
Araunane ya runtse idanunsa ya kasa magana kwata-kwata bazai iya magana ba dan da zaran
ya buɗe baki da niyar zaiyi magana sai yaji tamkar zare ake sawa ana tsuke bakinsa saboda
nauyi da zuciyarsa tayi masa.
Cikin tsananin fushi Yah Abana ya ɗaga hannu tare da tsinka masa mari akan kumatunsa kana
yace.
“Ba magana nake maka ba? kayi shiru kana kallona?”.
Sake risinar da kansa ƙasa yayi sam ba zai iya magana ba sai dai atake fuskarsa ta rine tayi ja
jijiyoyin jikinsa suka tashi lokaci ɗaya jikinsa ya sake rikicewa da karkarwa wani irin kiɗima da
ɗimuwa yake ciki wanda tunda yake a iya tsawon rayuwarsa bai taɓa riskar kansa aciki ba,
kana nadama mai tarin yawa ta rufe mishi dukkan jiki da zuciya.
Hajiya Babba ce ta miƙe kana ta ƙarasa gaban Yah Abana tare da risinawa tace.
“Dan Allah na roƙeka dan darajar Annabi kada ka yanke hukunci cikin fushi. ka fini sanin waye
Tajuddeen wani ma zai bada shaida akansa, bare kuma kai kada kayi gaggawan yanke hukunci
akansa kai masa uzuri sannan ka bashi dama”.
Cikin sauri Ummu Aryaan ta taso, ganin abinda take sonyi yasa Aryaan sa hannu da niyyar
riketa ahanzarce ta buge hannunsa kana ta tsugunna gefen Yah Abana tare da cewa.
“Kada ka manta cewa Tajuddeen bai taɓa kare kansa ba tun yana Karami Tajuddeen bai iya
musu ba koba shi ya aikata abuba, kamar yadda ko baya son abu baya musu in ka sashi haka
yake aikata shi. Baya iya musu bare ya kare kansa sam bai iya In-kari ba dan Allah dan darajar
Annabi ka riƙa maimaita Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun za'a samu bakin zaren”. Ummey kam wani irin sassayan kuka take cikin rauni da miƙa lamuranta zuwa ga Ubangiji
mabuwayi gagara misali tace.
‘“Taj kayi magana kayi magana”.
Baki ɗaya haka falon ya ruɗe ko wannensu na cikin tashin hankali da Alihini saɓanin Aryaan
Kabeer Mom Amal...
Uncle Jibril kuwa gyaran murya yayi cikin nutsuwa yace.
“Kuyi haƙuri kuyi shiru duk abinda yayi tsanani yana tare da sauƙi ”.
Jin haka yasa suka shiga maimaita Kalmar Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun yayin da muryoyin su
keyin ƙasa...
Meymer kam rarrafowa gaban Mahaifinta tayi cikin matsanancin kuka tace.
“Abba Yah Afif yaci amanata Abba ka aura min Yah Afif na zauna aƙarƙashinsa duk da ba sona
yakeyi ba, na bishi nayi mishi biyayya dan nagartasa da ban zaci zai iya aikata wannan
ƙazantan ba.
Yah Afif ya rasa yarinyar da zai nema yana lalatawa sai yarinyar da ya ajiye agabana na riƙe?,
Yarinyar marainiya du-du-du ƴar shekara sha uku”.
Cikin wani irin azabebben bugun zuciya Taj ya runtse idanunsa kalaman Meymer na barazanar
toshe masa ji cikin matsanancin kuka da sarƙewar murya ta cigaba da cewa.
“Yah Afif bai taɓa kallona matsayin matar Aurensa ba, duk tsawon zaman da mukayi dashi
watanni kusan takwas kenan yanzu in ƙarya nake mishi gashi nan ya faɗa, wlh ko yatsata bai
taɓa riƙewa da sunan muyi zaman aureba ashe duk yana shareni ne dan ya samu Laylah a
kusa”. Cikin Mamaki Uncle Jibril ya zuba mata ido ganin tayi shiru ta kife kanta ajikin kujera tana
cigaba da kuka.
A hankali ya gyara zamansa cikin sanyin murya mai haɗe da tausayin ƴar tasa yace.
“Kiyi shiru Mamana kukan nan ya isa haka”.
Momy Meymer kuwa cikin wani irin yanayi take kallon Meymer kallo irin na tuhuma da son
fahimtar wani abu cikin takaici ta buga mata tsawa tare da cewa.
“Dan Allah rufe min baki,
kike ta maimaita magana ɗaya kamar kin samu karatun Alkur'ani ko karatun Alqur'ani ba kya
maimaita shi haka kamar yanda kike ta maimaita Yah Afif yamin kaza Yah yamin kaza ki rufe
min baki ki kuma bace min da gani”.
Kallonta Uncle Jibril yau kana yace.
“Ya za'a yi ki tayiwa Mamana tsawa? Ki barta bana so kada ki sake yi mata tsawa ki bari taji da
abu ɗaya”.
Jin abinda ya faɗa yasa tayi Ƙwaffa...
Yah Abana kuwa idanunsa sun sake jajur tamkar zasuyi aman wuta kallon Taj yayi kana yace.
“Tajudden ka tashi agana kada ka sake zuwa gabana har sai ka tabbatar kana da abinda zaka
faɗa min bana son ganinka bana son zargin da ake ya tabbata akan ka.
Ka sani in dai zargin da ake ya tabbata akan ka Tajuddeen baka da amfani arayuwata”.
Runtse Idanu Ummey tayi kana muryanta na rawa tace.
“Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun”.
Ta ƙare maganar tare da fita ta nufi ɗakinta.
Taj kam jikinsa rawa yake so yake ya miƙe yabi bayan Ummey ganin yanda ta fita amma ya
kasa.
Mikewa Yah Yusuf yayi kana ta tallafe sa ya ɗaga sa kallon yanda jikinsa yake rawa yayi kana
ya riƙe sa suka nufi sashen Ummey...
A nan cikin falon kuwa Yah Hafiz ne ya juya ya kalli Meymey Muryarsa dashe yace.
“Meymey dan Allah dan darajar Annabi kada ki sake faɗan irin wannan kalaman akan
Tajuddeen”.
Sabon kuka ta fashe dashi kana cikin gaskiyar abinda take gani shine dai-dai tace.
“Yah Hafiz abinda ya aikata nake faɗa idan bai aikata ba bazan faɗa ba”.
Laylah kam kuka take...
Taj da Yah Yusuf kuwa suna shiga Falon Ummey suka sameta zaune gaban 3sitter ta jingina
kanta da jiki tana shesh-sheƙan kuka yayin da Zakiyya ke gefenta itama kuka take cikin
damuwar ganin halin da Mahaifiyarta ke ciki tace.
“Ummey menene ki faɗa min Meyafaru?”.
murya can ƙasan maƙoshi sukayi sallama jin sallamarsu yasa ta ɗago kai ganin Taj da Yah
Yusuf yasa tayi saurin miƙewa kana ta matsa gabansa muryanta na rawa kana hawaye na zuba
daga Idanunta tace.
“Ko wani lokaci a kowani yanayi baka iya In-kari kan abinda ya shafe ka baka iya musu adai
wannan lokacin muddin baka buɗe baki kayi In-kari ba sannan kayi abinda zai tsarkake kanka
daga idon Mahaifinka ba, zaka ja mana baƙin cikin da zamu dawwama aciki Afif ka buɗi baki
kayi magana”. Kansa kawai ya girgiza saboda bazai iya ba ya sani haka Allah ya haliccesa Allah yasani bazai
iya ba.
Kuka Ummey ta fashe dashi mai tsuma zuciya tafi kowa sanin wanene Taj ciki da waje haka
zalika tafi kowa sanin Wanene Malam wannan dalili yasa ta sake fashe da kuka.
Ganin yanda take kuka yasa Taj zubewa akan gwiwoyinsa ya rasa ya zaiyi kana ya rasa mai zai
ce.
Cikin sanyi da disashewar murya tace.
“In dai baza kayi magana ba, ka cutar dani Tajuddeen adai wannan karon idan har ba kayi
magana ba ka gama cutar dani ka cutar da kanka”.
Ta ƙare maganar tana zama kan kujera.
Yusuf kuwa ganin bazai yi magana ba yasa ya Daga shi suka fita direct mota suka shiga
ahankali Yah Yusuf ya kallesa kana yace.
“Ina muka nufa?”.
Shiru Taj yayi saboda bazai iya magana sai wani irin karkarwa da lips ɗinsa keyi duk da yana
taune su maganganun Meymey basu zauna a ransaba ko kaɗan ganin alamun fushi da fusatar
Yah Abana ne ya hautsina mishi lissafi.
Bayan sun danyi nisa da tafiyar Yah Yusuf ya sake kallo sai tare da cewa.
“Afif ina zamuje?,Ko dai in kai ka gidan Addawa ne?”.
Kai ya gyada masa kana kai tsaye ya juya akalar Motar zuwa gidan Addawa...
A can falon Yah Abana kuwa kallonsu yayi cikin Muryarsa dake ƙunshe da tarin damuwa ya
kallesu kana yace.
“Ku tashi ku tafi”.
Cikin mutuwar jiki kowa ya watse da zullumin dake ransa Momyn Meymer kuwa side ɗin
Ummey ta nufa.
Meymey kuma hannun Laylah ta riƙe suka fita suna fita tashiga motarta suka wuce gida.
Acan gidan Addawa kuma cikin tsananin tashin hankali take sauraren bayanan da Yah Yusuf ke
mata baki ɗaya ilahirin jikinta rawa yake kana hawaye na zuba mata tamkar an buɗe famfo
tsoronta kuwa sake hau-hawa yake nan take firgici ya bayyana ƙarara asaman fuskarta Babu
kalmar da take maimaitawa face Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un tana mai cigaba da cewa.
“Ya Allah ka tsare wannan bawan naka da abinda ake zargin sa da aikatawa”.
Sosai suka riƙa tausan Taj kan yace wani abu amma ina kasa magana...
Jin kiran sallar maghariba ne yasa suka tashi suka tafi masallaci sukayi sallah masallacin
unguwar su Addawa ranan agidan Addawa ya kwana anan falonta ita kanta har zuwa lokacin
bai buɗi baki ya mata magana ba.
Washe gari da Asbah bayan an idar da Sallah yana shiga Falon ya sameta tana waya wanda
bisa duk kan alamu da Ummey ce jin tana cewa.
“A gidana ya kwana gashi nan kuma tunda yazo bai ce min komai ba haka zalika baiyi magana
ba”.
Ganin shigowar yasa tayi saurin cewa.
“Yawwa gashinan ya dawo yanzu”.
Sai kuma ta matsa kusa dashi kana tace.
“Tajuddeen ga Ummey ka nan,tana son magana da kai”.
Ahankali ya gyaɗa mata kai kana ya zauna tare da karɓan wayar ya manna akunnensa cikin
wata iriyar murya mai cike da tsananin sanyi da rauni wanda har ta bawa Ummey tsoro yayi
sallama da damuwa atare da ita tace.
“Lafiyarka kuwa Tajuddeen?".
Cikin sanyayyar murya ya gyada mata kai kamar yana gabanta kana yace.
“Lafiya lau Ummey ”.
Cikin jin ƙai irin na uwa da ɗanta ɗan ma mafi soyuwa azuciyar ta girgiza kai tare da faɗin.
“Tajuddeen Me zaka iya cewa?, Tajuddeen ka buɗe baki kayi magana ”.
Idanunsa ya lumshe kana ya taune lips ɗin sa na ƙasa tare da cewa.
“Kiyi haƙuri Ummey bazan iya ba”.
Wani irin kuka ne yazo mata cikin zubda hawaye tace.
“Tajuddeen ba zaka iya bafa kake ce min?.
Kasan abinda ake tuhumar ka dashi kuwa?,kasan me ake tuhumar ka dashi Tajuddeen? Kasan
cewa duk mutumin daya taɓa Aure mace ko Namiji hukuncin haddi kisa ake yanke masa
Tajuddeen shine kake cemin baza ka iya magana ba?”.
Kansa ya jinjina yana mai jin tausayinta akasan ransa yace.
“Kiyi haƙuri Ummey bazan iya ba kiyi haƙuri, gwara ma a kashenin kawai kowa ma ya huta”.
Ya ƙare maganar zucin yana miƙawa Addawa wayar suka ci-gaba da magana.
Ganin ya miƙe yasa tayi saurin cewa.
“Ina zaka je?”.
Ahankali ya motsa laɓɓansa tare da faɗin.
“Gida”.
Yana fita sai ga Abu Hashim yazo bayan motar ya shiga yana zama wayarsa na ringing yana
dubawa yaga Sunan Ishmah na yawo wayar iska mai zafi ya furzar yasan ta kira ne su gaisa
kamar yanda suka saba ko wacce safiya kuma yanaji bazai taɓa iya bari bai amsa kiranta ba
picking call ɗin yayi ya manna akunnensa ya shiru.
Daga ɗaya bangaren cikin sanyayyar murya mai cike da nutsuwa tace.
“Barka da Safiya Taj".
Ahankali yace.
“Hmmm”.
Cikin bugawar zuciya mai gauraye da jin alamun yana cikin damuwa tace.
“Ya Salam Taj me yake damunka?”.
Ahankali ya sake cewa.
“Hmmmm”.
Still da damuwa afuskarta tace.
“Dan Allah Taj na roƙeka kayi min magana in samu salama”.
Sai alokacin ya ɗan cije lips ɗin sa murya can ƙasan maƙoshi yace.
“Me kika ji”.
Tana jujjuya kai tayi saurin cewa.
“Taj muryanka ta faɗa min baka cikin nutsuwa da kwanciyar hankali muryanka na tattare da
damuwa meke faruwa? Jikina ya jiyo min alamun kana cikin damuwa. Me yasamu Laylah”.
Sai alokacin yaji wani irin zafi da zugi azuciyarsa tunaninsa ya tafi kan Laylah dagaske ne
kenan?,ciki ne da ita, to idan ya bari aka kashe shi waye zai kula da rayuwar Laylah, Ya
Ummeeyshi zataji, waye zai meyewa Ishmah gurbinsa?”.
Asanyaye ya furzar da iska mai zafi jin Ishmah na kiransa a hankali yace.
“Ba abinda ya samu Laylah Ma'eesha”.
Itama cikin sanyi tace.
“Toh yanzu meye ne matsalar”.
Ahankali ya sake runtse idanunsa tare da faɗin.
“Kiyi min Addu'a Ma'eshaa”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“In sha Allah zanyi, to amman addu'ar me zan maka?”.
Tsintar kansa yayi da cewa.
“Kiyi min Addu'a Allah ya bani ikon cinye Jarrabawar dake kutso kai cikin rayuwata”.
Cikin gamsuwa tace.
“In sha Allahu zan yi maka addu'a yanzu ma ina kan sallaya bari nayi maka addu'a”.
Kai ya gyada tare da katse kiran.
Da kallo tabi wayar jin ya katse yasa ta sake tabbarwa yana cikin matsala.
Bisa kan sallaya tayi sujjada tare da cewa.
“Ya Allah ka kare wannan bawan naka, ka tsare wannan bawan naka daga sharrin masu sharri,
ka ɗaukaka darajarsa ka kare mutuncinsa ka hanasa ta ɓewa ka yalwata duniyarsa da lahirar
da farin ciki ka bashi ikon cinye Jarrabawarsa”.
Haka dai tayi ta mishi addu'oi...
Taj kuwa dai-dai lokacin ya shiga ya samu Meymey na zaune kan 3sitter Laylah na gefenta tana
bata tea wani irin kallo ta bishi dashi.
Ahankali ya girgiza kansa kana ya saki Murmushi wanda yafi kuka ciwo Murmushin da yake
nuna zallan Jarumtakarsa wanda yake nuna rashin nasarar maƙiyansa a kansa Murmushin
dake nuni da alamar Fahimtar abinda ke ranta.
A hankali ya wuceta ya nufi bedroom ɗinsa yana shiga ya kwanta saboda yanda yake jin
tsananin ciwon kai da yanda yake sarawa kwanciya yayi ya rasa mai zai tuna a duniya
arayuwar ya rasa abinda zai tuna ranan haka ya yini aɗaki, ko jami'in Sallah agida yake yi tunda
ya shiga ɗakin bai fito ba sai washe gari da safe ya fito. Yana fitowa ya tsaya atsakiyar falon kana ya ɗan ɗaga sautin muryan sa da bai fita yace.
“Laylah!, Laylah!!, Laylah!!!”.
Cikin yanayin tsoro da firgita ta fito da sauri ta tsaya gefensa baki ɗaya ilahirin jikinta na
karkarwa matsawa kusa da ita yayi tayi saurin ja da baya Muryarsa asanyaye yace.
“Laylah ki tsaya ba abinda zan miki”.
Kai ta shiga jujjuya masa amma ba tace komai ba.
Yana sauƙe ajiyar zuciya yace.
“Yau ba kije school bane?”.
Kai ta gyaɗa cikin tarin tsoro tace.
“Malam yace in daina zuwa school”.
Cikin matsanancin tsoro da firgita ta kai karshen maganar.
Da mamaki yace.
“Yah Abana da kansa ya faɗi haka?”.
Kai ta gyada masa.
“To saboda me?”.
Ya tambaya yana kallonta murya na rawa tace.
“Yace wai kar inje a gane ina da ciki in zubar mishi da darajar sunansa da gidansa”.
lip ɗin sa na ƙasa ya cija da ƙarfi tare da juyawa ya fita.
Yana fita yayi kiciɓis da motar Amal tana shiga...
Yana fita ya wuce asibiti da nufin ko zai iya aiki koda yaje yaji bazai iya aikiba ji yake to mai zai
yi daga can ya wuce gidansu Ummey kai tsaye falonta ya wuce yana shiga ya samu falon shiru
sai Aunty Maryam da
Rashida,Rashida na ganinsa tayi saurin cewa.
“Taj".
Cikin sanyi ya amsa mata kana ya zauna gefenta itama Aunty Maryam zama tayi gefensa ta
zamana sun saka shi a tsakiya.
Ummey kuwa jin an kira sunansa ne yasa ta fito daga bedroom bisa duk kan alamu walaha tayi
hannunta riƙe da Carbi zama tayi aƙasa agabansa tace.
“Afif”.
Idanunsa da suka jikkata da dimuwa da tsantsar tashin hankali ya ɗago ya kalleta kana har
zuwa lokacin suna nan Ja-ja-jur ahankali tace
“Afif na roƙeka ka yakice wannan ɗabi'a taka ka raba bakinka da wannan nauyin, ka cire
wannan zurfin cikin, ka kare kanka Tajudden al'amarin nan fa Babba ne kada ka ɗauke shi da
wasa lamarine da zai ruguza duk kan wani farin cikinmu”.
Ahankali ya juya ya kalli Rashida da tun kiran sunansa bata sake cewa komai ba sai kuka.
Aunty Maryam kam zamewa tayi ta kifa kanta jikin kushin ta zubda hawaye.
Ahankali ya zame ya zauna gefen Ummey har gwiwoyinsu na gugan juna ahankali ya ɗaga
tafukan hannayensa ya daura kan haɓarta ya shiga share mata hawaye.
Cikin sanyi tace.
“Ba abinda zaka min ka share min hawayena wadda ya wuce ka buɗi baki kayi magana ka fadi
abinda yake zahiri ka fadi abinda yake gaskiya, sannan ka fadi abinda yake tsakaninka da
Ubangiji ka kuma fadi abinda ka sani akan cikin Laylah”.
Runtse idanunsa yayi yana jin tausayinta aƙasan ransa Ummey kam cikin tarin tausayin sa da
kuma jin kai ta cigaba da cewa.
“Ni ban sani ba Yah Abananka bai sani ba daga kai sai Allah ne kuka sani, dole sai ka buɗi
baki kayi mgna ne zamu sani ka samu ka kuɓuta da kan ka Tajuddeen”...
Sake runtse idanunsa yayi jin yanda ƙahon zuciyarsa ke harbawa cikin sanyayyan murya yace.
“Kiyi haƙuri Ummey bazan iya ba ban san me zanceba”.
Cikin sauri da matsanancin tausayinsa Rashida ta ɗago kai tare da cewa.
“Afif zurfin cikin ka zai ja mana bala'i kayi magana dole ka fito kayi magana kayi In-kari”.
Ahankali ya subkuyar da kansa ƙasa Ummey kam tafin hannunta tasa ta tallafo fuskarsa kana
ta riƙe haɓarsa dai-dai gemunsa tace.
“Ka kalli Idona ka faɗa min me gaskiyar abinda Meymey ta faɗa”.
Cikin yanayin dashi kansa bai sani baya kalleta araunane yace.
“Ummey nima ban sani ba”.
Idanunta na tsatstsafo da ruwan hawaye tace.
“Kamarya baka sani ba?,ka faɗa min gaskiyar abinda Meymey ta faɗa kai kayiwa Laylah ciki?”.
Kansa ya sunkuyar tare da cewa.
“Ummey i don't know bansan abinda zan ceba”.
Yanda yayi maganar ne zai nuna daga ainihin ƙoƙon zuciyarsa yake fita”....
Daga Page 15 zan gama free pages in dai Kinga littafin INDA RAI a wani group ɗin ba group
ɗina na littafin ba to na satane kika karanta.