Showing 21001 words to 24000 words out of 81932 words

Chapter 8 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf

mik'e tare da cewa.
"Anty Aysha zan tafi lokacin sallah yayi."

Cikin kula tace.
"Toh muyi sallan a nan mana sai muci abinci in yaso sai ki tafi ,
wota k'il ko zakiyi bacci ne."

Murmushi tayi sannan Anty Aysha ta ce mata .
"Muje ciki kiyi al'wala."
Murmushi kawai tayi tare da binta a baya.

Bayan sunyi sallah ne suka zauna suka d'anci abinci suna d'an hira,
kafin su ankara har 3:13 pm tayi ganin haka ta mik'e cikin sauri tana cewa .

"Kai bari in tafi ."

Nafeesat ce ta kuma tsaida ta a dole tayi sallah bayan sun idar suka kuma shiga kitchen tare
suna shiga kitchen d'in itama ta zage suna ta aiki tare dan tana son gane kan kayayya kin aikin
ba laifi kuwa ta fara ganewa gashi Anty Aysha na janta a jiki Nafeesat kuwa duk abinda zasuyi

sai tayi mata bayanin yadda ake sarra fashi,
dad'i sosai takeji a wannan d'an taraiyar da sukayi dan ta d'auki darusa da yawa ta fara gane
komai bugu da k'ari dama ta iya girki kam tsab.

Suna cikin kitchen d'in har zuwa 5 dai-dai zuwa lokacin kuwa sun kammala komai.

*Mutan Katsina kuwa*

har sun iso cikin gida
A gajiye Abba ya zauna a parlour part d'in nasu,
yayin da suka wuce babban parlour gidan kuwa ba kowa dan Mama da Abdul sun fita yawon
mugun tarsu ya Amir kuwa da Daddy basu dawo gida ba tukun.


Captain Sani ne yaje ya kawo musu ruwan sanyi tare da zama gefen Abba yana .
"Abba sannu."

"Yau wa Sani sannu kai ma dan ai kaine mai tuk'in ka fimu gajiya."

Shi kuwa General wucewa yayi cikin bedroom yana shiga yayi shiru a nufin shi ya saurara ko
tana cikin toilet d'in,
shiru ba motsi hakan yasa ya matso jikin k'ofar a hankali ya dan buga k'ofar ,
shiru ba motsi tsaki ya d'an ja sanna ya murd'a marfin tare da d'an lek'awa,
wayam ba kowa ganin haka yasashi juyawa cikin tsuke fuska kitchen ya shiga nan ma bata ciki
ganin hakan yasa ya fito a fusace kai tsaye tsakiyar babban parlour yaje ya tsaya tare da
tsurawa tsakiyar parlour ido cikin d'aga murya tare da tsuke fuska ya fara aika mata kira.

*"MEENAL"*
sai kuma ya d'anyi shiru tare da k'ara had'e fuska dan yasan yanzu Mama zata zo tayi rashin
mutuncin nata.

Jin shiru bata amsa ba yasa ya fara antaya mata kira ba k'ak'k'auta wa a jere- a Jere.

*"Meenal"*

*"Meenahhl*"

*"Meenahhhl*"

Abba da Captain dama tun yadda suka ga ya fita a fusace suka bishi da ido sannan kuma suka
jiyoshi yana ta rabka k'ira,

Sai suka mik'e tare da biyo bayan shi ganin ya tsaya ya coge yasa suka tsaya suma tare da

zuba mai ido,
fitan su yayi dai-dai da fitowar Meenal d'in daga cikin kitchen d'in cikin tsoro da rawan jiki ta nufi
gunshi tana mai kallon yadda ya tsuke fuska tana zuwa sai ta tsaya gaban shi tayi k'asa da kai
tana fidda numfashin tsoro,
Anty Aysha da Nafeesat ko na biye da ita a baya ,
dai-dai lokacin ya Amir da Daddy suka shigo,
suna shiga sai ga Mama da d'an kanzagin ta Abdul.

Duk tsayuwa sukayi cirko-cirko suna kallon yadda ya tsareta a gaba yana hukun tata da ido.

Ya Amir ne cikin mamaki yace.
"Daddy kalli Abba a gidanmu yau."

Daddy kam da sauri ya k'arisa gaban d'an uwan shi cikin k'aunar juna suka gaisa ya Amir ma ya
iso tare da gaida shi .

Nafeesat ce ta k'arisa gaban General d'in cikin tsoro murya na rawa tace.
"Ayyahhhhh Hamma Aliyu kayi hak'uri wallahi muna kitchen ne muna taya Anty Aysha aiki."

Kai ya d'an dago ya kalleta ,
ganin yadda ya cilla mata wani irin kallo yasa tayi k'asa da kanta cikin sanyi ta juya gun Abba,
gai dashi tayi cikin sanyi taci gaba da cewa.
"Ayyahh Abba kacewa Hamma Aliyu ya rink'a barin Meenal tana zuwa muna zama gashi muna
taya Anty Aysha aiki kaga dama aiki ya mata yawa kuma Meenal zata ji dad'in zaman mu zamu
d'ebe mata kewa."

Kai Abba ya jinjina cikin sanyi yace .
"Ba damuwa insha Allah zai barta."

Nafeesat kam sai dariya tayi tare da jawo hannun Meenal cikin raha tana cewa.
"Meenal kizo ga Abban mu shine Baban Hamma Aliyu dama yana Katsina yaune yazo."

Gaban Abban suka tsaya cikin sanyi ta d'an durk'usa a hakali tace.
"Sannu da hanya Abba ."

Cikin fara'a Abba yayi maza yace.
"Taso Meenal ni mahaifi ne a gareki ni ba surki bane a gunki,
ki d'auken kamar mahaifin ki,
Allah ya muku al'barka."

Cikin jin dad'i tace.
" Amin Abba ."
Itama Anty Aysha ta matso tare da gaida Abba cikin happy ya amsa tare da cewa.

"Aysha kema kinga kin samu y'ar uwa ko,
Ke Meenal ai zakina zuwa kina taya Aysha aikin ko?."

Murmushi sukayi baki d'aya sannan suka amsa da cewa.
"Ehh Abba."

Shiko Abdul duk maganar da akeyi idon shi na kan Meenal gaba d'aya ya zauce a kanta sai
binta da ido yake baki a sake kamar soko tunda Nafeesat taja hanunta zasuje gaban Abba,
yabi k'ugunta da ido har yana lasan lips d'inshi ganin yadda gaba d'aya take tafiya cikin wani
salo a ranshi yake jin ya samu garab'asa har gida a hankali yace.
"Nagode Hamma Aliyu ka kawo min ganima nima dole na d'ana."

Ita kuwa Mama wani irin tsuke fuska tayi cikin salon rashin mutun ci da bak'in cikin dawowar
k'anin mijin nata,
sannan ga tsanar Aysha da Meenal da take ji cikin bak'ar magana ta kalli Aysha tace.
"ai in mace nason ta samu,
masu taya ta aiki haihuwa zatayi in ta isa ke kina nan baki da aiki sai ci sai k'aton kashi banza
mai maceccen zuciya."

Sai ta kuma juyawa kan Meenal cikin gyatsine tace.
"Lallai karuwan ci ya fara samun lasisi tunda har ubban korton naki zai baki wurin zama,
ko da yake ba bak'on abu bane ai shima ubban zaman banzan yakeyi a katsinan,
uwar ma waya san ko yanzu haka tana *TAPA* jigon y'an iska."

Wayyo General Aliyu gaba d'aya ya kejin jinin sa na tafasa zuciyar sa na soyuwa ji yake kamar
zai had'iyi zuciya ya mutu gaba d'aya jikinshi har b'ari yake cikin fushi ya nufi gaban Maman."

Abba ne ya kirashi cikin d'aga murya yace.
"Kai Haiydar zo nan banson jin koma daga bakin ka."

ai ya k'asa magana sai juyowa yayi ya rab'a gefen Abban kai tsaye bedroom ya wuce ya kasa
zama ko tsayuwa sai zirga-zirga yake ranshi na tafasa.

Ita kuwa Mama dariya tayi cikin jin dad'i sannan ta juya tare da jan hannun Abdul suka tafi.
Ya Amir kuwa da Daddy hak'uri sukayi ta bawa Abba shi ko Abba murmushi kawai yayi tare da
jansu Abban da ya Amir d'in yana mai basu labarin yadda akayi auren General da Meenal,
fatan alkhairi sukayi tare da sanya albarka .

Anty Aysha kuwa hannun Meenal taja tare da cewa Nafeesat.
"Ku zomuje mu sharewa Abba d'akin shi."

D'akin Abba na cikin part d'in Aliyu Amman inya zo yawan ci a parlour yake zama,
gashi yanzu ko General ya tare a parlour koya za'ayi ne rai?.

Shara sukayi tare da goge mai komai sannan suka fito tare da bawa Meenal hak'uri da halin
Mama.


Shiko General da k'er ya samu ya sarrafa zuciyar sa,
sannan ya watsa ruwan tare da yin alwala sannan ya fito suka tafi masallaci.
basu dawoba saida sukayi ishah.

Suna dawowa Daddy yasa kab suka zauna a babban parlour yayin da Meenal da Anty Aysha
da Nafeesat suka shirya musu abinci, tsarin gidan kenan duk tare suke had'uwa a parlour suci
abinci.

Ita kuwa Mama ta samu damar yi musu cin fuska kenan.

Shi kam General a cike yake tab ya k'asa cin abincin dan shi dama In dai ba Abban shine yazo
ba bai zama a cikin,
sai harara yake cillawah Meenal itako tana kauda kai.


Hira sosai Abba yayi tayi da Daddy tareda Ya Amir da kuma Nafeesat da Meenal a parlour nasu
shi kuwa General so yake ya keb'e da Bodd'i ya casata dan koma menene itace ta jaza masu
da tabi dokar sa ai hakan bazai faruba,
shi yasa yace shi bacci zaiyi.

Hakan yasa suka watse hirar tasu Abba ya nufi d'akin shi,
Suma su Daddy duk suka tafi part nasu.

Suna fita ya rufe k'ofar sannan da sauri yabi bayan Meenal d'in yana cije lips d'in shi,
yana shiga cikin bedroom d'in..........


By
Garkuwar Fulani

*BANDIRAWO* pg 1⃣5⃣ to 1⃣6⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*



Pure moment of life writers

Gaban ta yaje ya tsaya,
ya tsare ta da ido yana matso ta,
itako tana ja da baya har ta zauna gefen gado,
k'afar sa d'aya ya dago ya taka gefen ta cikin fad'a yace.
"Ke ba a isa dake bako? duk abin da kika ga dama shi zakiyi ko ?
toh wallahi ni zanyi maganin rashin kunyar ki sai anyi magana kiyi ta zaro ido kamar tsohuwar
mayyah."

Ita kam sunkuyar da kai tayi tare da zubda k'ollah cikin sheshshek'ar kuka .

Ranshi ne ya k'ara b'aci ganin shi ba abin da ya mata kuma ta sashi a gaba tana kuka dan
muna furci.

Cikin fad'a ya damk'o hannun ta cikin masifa ya mik'ar da ita cikin k'uluwa ya nunata da d'an
yatsa sannan tare da tsare ta da ido yace.
"Wallahi ki had'iye kukan ki maza rufe min bakin me nayi miki da kike min koke-koken muna
furci kin iya rashin kunya kuma kice kar ayi miki magana ."

Kai ta rink'a juyawa cikin son had'iye kukan amman ta kasa sai hawaye shar-shar .

Tsawa ya kuma buga mata cikin k'ara matse hannun ta yace.
"Ki had'iye kukan ki da wahayen ki muna fuka yanzu me nayi miki?."

Cikin kukan ta d'an d'ago ta kalleshi tana girgiza kai,
baki na rawa cikin kukan tace.
"Kayi hak'uri ka gafar ceni."
Sai kuma kukan ya kufce mata kuka mai cike da k'unan zuciya kukan take har kamar numfashi
ta zai d'auke gaba d'aya jikin ta sai bari yake da ker take cewa.
"Kayi hak'uri bana son fad'a ina tsoron tsawa kaina na juyawa."

Ido kawai ya tsura mata cikin mamakin ganin yadda gaba d'aya ta rud'e tana kukan cikin
cushewar numfashi da k'unan zuciya gaba d'aya ta ke d'an layin jin kanta na juyawa."

Cikin ta kaici ya kuma watsa mata tsawa.
"Kada Allah yasa kiso tsawan wato ke gaki mai iya fidda kai ko ji muna furci toh wallahi ki kiyaye
ni ko na fasa miki kan naki da tsawan."

yana rufe baki ya hanka d'ata gefe ya juya ya nufi gaban durowa.

Ita kuwa hannu tasa ta kama kanta cikin firgici da tsoro kukan da take ne ya cusa numfashin ta
sai jiri a take sai duhu ya rufe mata ido sai ga jiri yu-yuh yana d'ibar ta.

Blanket ya zaro tare da juyowa zai d'auki pillow,

Ido ya tsura mata yana tsaye ba tare daya matso ta ba ganin tayi tangal-tangal zata fad'i yasa
ya d'an matso ta cikin rashin sa'a kafin ya isoma ta fad'i k'asa kanta ya buga jikin gado ta kuma
sulewa k'asa a take goshin ta yayi wani irin k'aton k'ulu sai wani irin kuka ta kuma saki cikin
marayan murya da rauni tana.
"Wayyo Allah na wayyo Bappa na kaina zai tsage."

Zamewa yayi ya zauna gefen ta cikin sanyi ya jawo ta jikin shi cikin d'an daga murya yace.
"Ke hauka ne a kanki zaki kashe kanki ko? yanzu fisabilillahi me nayi miki? ."

Ita dai ba magana sai k'anmk'ame hannushi da tayi cikin mancewa da waye ne a kusa da ita
dan azabar ciwon da kanta keyi,
zaman yayi tare da jingina da jikin gadon,
tallabe kan nata yayi ya d'aura kan cinyar sa ido ya tsurawa k'ulun dake goshin ta ido ya rumtse
cikin jan tsaki,
tafin hannun shi ya bud'e a hankali ya d'aura kan k'ulun sannan ya danna da k'arfi yana
murzawa .

Mik'a tayi cikin jin wani irin azaba dake ratsa kanta hannu bibbiyu tasa ta zagoyo k'ungunshi
tare da k'amk'ameshi tana murza kanta kan cinyar sa.

Jin yada ta cikuiku yeshi gaba d'aya ta mak'aleshi tana turmusa shi ,
lokaci d'aya jikin shi ya rink' bari a hankali yaji wani irin sanyi na shigarshi duk ta inda hudan
gashi jikin shi yake,
fata idon shi na sama suka fara wani irin motsawa lokaci d'aya sanyi mai tsanani ya rufe shi
jikin shi sai kerba yake,
cikin jin sanyin ya fara zamewa a hankali har ya konta kan chainis carpet d'in dake gaban gadon
cikin rawan sanyin ya jawo pillow ya d'ora kanshi ,
ita kuwa jin ya dena murza mata wurin dake ciwon sai ta rink'a sauk'e ajiyar zuciya tare da mirgi
nowa tayi pillow da damtsen hannushi,
lokaci d'aya baccin azaba
ya kwashe ta,
Shi kuwa. Sanyin ne ya rufe shi tuk'uru cikin rawan sanyin ya yawo blanket d'in da ya d'auko
sannan ya woreshi ya rufe su tare da k'ara matso ta yana dan rumtse idon shi.

A haka cikin wannan yana yin bacin wani irin bak'on yanayin ya saceshi,
baccin suke cikin blanket d'aya tunda suka konta suka fara baccin suka mak'ale cikin blanket
d'in.


4:49 Am General ya bud'e ido cikin sanyi tare yin mik'a da yin Addu'ar tashi daga bacci,
motsin shi ne ya tasheta cikin sanyi ta bud'e ido,
aiko sai sukayi ido cikin ido,

a firgice ta mik'e cikin rawan jiki da tsoro,
kan gado ta haura tare da yin k'asa da kai tana dafe da goshin ta cikin jin zogi.

Shi kuwa a kunya ce ya mik'e zaune hannun shi da tayi pillow dashi ya d'ago tare da yarfa
hannun dan yayi tsami ya tara jini mik'ewa yayi tare da suke fuska da jan wani irin dogon tsaki
sannan ya watsa mata harara ya wuce toilet.

Wanka yayi a gaggauce dan kar jam'i ya wucesa yana fita ya fesa turare tare da ficewa
masallaci.


7 dai-dai suka shigo cikin gidan a parlour su ya zauna da Abban shi suna d'an hira sama-sama,
Captain Sani ya shigo shima ya zauna cikin girmamawa ya gaida Abba sannan ya kalli General
cikin Sanyi yace.
"Oga Uncle Ibrahim na baida lafiya ciwon zuciyar sa ya tashi tun jiya,
so yanzu ina son inje in duba shi kafin ka gama shirin tunda yau zamu koma cikin Jaji."

"Sai ka dawo ka gaida shi."
General ya bashi amsa a gajar ce.

Abba ne ya kalleshi cikin sanyi yace.
"Sani ciwon zuciya kuma? tun yaushe yake tare dashi? kuma meke tayar mai da ciwon?."

Kai Sani ya jinjina cikin sanyi da tausayawa yace.

Abba Uncle Ibrahim ya kanmu da ciwon zuciya ne a a dalilin b'atan yarshi tilo da yake da ita."

Cikin kula General yace .
"Y'ar Sa kuma ? ta b'ata kuma? b'ata kamar babyn roba? a ina ta b'ata?."

Ajiyar zuciya ya sauk'e cikin sanyi ya fara basu labari.

*"Alhaji Ibrahim mai dala* babban d'an binciken ma adannan cikin kasane Allah ya bashi duniya
mai tarin yawa Amman sai ya rasa haihuwa mafaifin Sani kuma yayan shine so rashin haihuwar
yasa d'an uwanshi ya bashi d'anshi a haka ya reni Captain Sani cikin gata da kulawar matar sa
Hajia Amina mace mai mutunci suna zaune a haka.
wata rana Alhji Ibrahim ya tafi jihar Taraba wani binci ke cikin dutsen Membila Toh a can Allah
ya had'a shi da wasu Fulani masu mutunci ,
so zamane na tsawon shekara yayi a wurin da fari yaje da Hajia Amina toh yanayin wurin yasa
ta k'asa zama ta dawo nan Kaduna,. Shiko yaci gaba da zaman can ,
Mutanen da yake tare dasu masu mutunci da y'ar su mace d'aya mai suna Aysha ,
lokaci d'aya Allah ya had'a jinin Ibrahim da Aysha,

suko iyayen Aysha ganin mutun cinsa yasa suka aura mai ita.

cikin sa'a anayin auren ta samu ciki bayan watanni 9 ta haifi ya mace ,
a wannan lokacin kuma Alhaji Ibrahim ya gaba aikin shi so sai ya nemi tafi da matar sa Aysha,
toh fa a nan iyayen ta suka k'i amin cewa abu kamar wasa ya zama gaske sunce ai sunsan inya
tafi da Aysha sun rebu kenan sai dai ya barta a nan tunda itace kad'ai ta rege musu,
a haka sukayi ta jani'in jaka har yarinya tayi wata 11 toh sai ga Aysha da wani cikin yayin da
Hajia Amina ko take ta farin cikin sun samu yara a gidan su,
Ibrahim yaso ya taho da matarsa amman sun hana sunce sai dai in zai bar musu yarshi inyaso
ya tafi da Aysha tunda sun san albarka cin y'arsa zai ke zuwa da Aysha suna ganin yarsu suna ,
a dole ya yarda ganin ai ga wani cikin a jikin Aysha
haka ya taho da Aysha da ciki ita kuwa babyn suka barta gun kakannin ta bayan sun dawo ba
jimawa cikin Aysha ya b'are daga nan kuma bata kuma ko batan wata ba Alhaji Ibrahim ya
shiga damuwa matuka toh amman yazaiyi.

Haka Y'ar shi take rayuwa a rigar fulanin toh kwanaki da yaje dan dubata dashi da Aysha sai
suka samu wai wasu yan birnin sun taho da ita kuma suma basu sansu ba,
anyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login