Showing 15001 words to 18000 words out of 81932 words

Chapter 6 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf

yasa ya manta bai murd'a key d'in ba

haka suka fita suka tafi.
A parlour suka tarar da Mama tare da Abdul tana d'uma mishi hannu qato dashi,
wucewa yayi kamar bai gansu ba a ranshi kuwa zafi yakeji shi bai tab'a samun irin wannan
kulan ba shi ya rasa wannan gatan a rayuwar sa.

Suna fita daga cikin parlour General Aliyu yaji muryar....


By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 1⃣1⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Pure moment of life writers


*Dedication 2 Haermeebraeh & One luv and Maryam S bello (MSB)*

*Masoyan BANDIRAWO kuyi haquri da wannan page d'in jiya da yau duk baqi nakeyi amman
insha Allah gobe zan mana page 2*


Gaban Mama ya tsaya cikin murtuqe fuska da yamutsa fuska tare da tsura mata ido cikin
tsantsar zafi,
Abdul kam a hankali ya rinqa ja da baya cikin tsoro yana kauda kai,
Ita ma kanta Mama tabbas Aliyu yana mata korjini tana jin wani iri in ta ganshi ya koma kamar
zaki.

Ita kuwa Meenal sai kuka takeyi cikin sanyi da tsoro ga wani irin riqo da Aliyu ya mata gashi
ganin yadda ya juyen ya qara firgitata sai numfashi take ja cikin tsoro da qamqame jikin ta.


Cikin muryar gargad'i da daqilewar voice yace.

"Wlh daga yau ko kallon banza aka kuma yi mata, Hmmmm."

Sai kuma ya cike lips enshi cikin murtuqe fuska.

Cikin qarfin hali Mama tace,
"Hmmm zaka had'iye mune ? ko me zakayi mana? aikin banza ka kwaso karuwa ka kawo mana
gidan Aure gidan sunan wallahi ko yanzu sai in dakata inga me zakayi?."

Turata yayi gaban Mama cikin murtuqe fuska yace.
"Gata wallahi gata magoji ya goda aga abin da zanyi."

Shiru sukayi sai tsilli-tsilli suke da ido.

Hannun ta ya kuma ja tare da matso Abdul cikin watsa mai harara yace.
"Duk randa ka kuma tab'ata ko mugun kallo kayi mata wallahi sai na karya ka."

Ya Amir kam da Nafeesat sai murmushi suke ganin yadda Abdul ke zare ido cikin tsoro.

Daddy kam mamaki ne da dariya da kuma tabbayoyi ne a zuciyar sa,
shin ita wannan wacece? me had'inta da Aliyun ? ita y'ar waye?.

Haka ya sake ido da baki yana kallon yadda General yake jan hannun ta,
itako tana biye dashi parlour suka shiga yana shiga ya maida qofar ya rufe,
ita kuwa hannun ta ya yarfa tare da watsa mata harara ya kuma qara tsare fuska cikin fad'a
yace.
"Waya baki damar bud'e qofar parlour nanma ? bare kuma har ki fita tsakiyar gida ?,
dan tsabar iskanci da raini nace karki fita shine kika fita ko!?"

Kai take juyawa cikin tsoro da zubda hawaye baki na rawa tace.
"a a tsuntsune fa naga zai mutu."

Ido ya zaro cikin zafi ya d'aga hannushi zai yarfa mata mari dan in ba bugeta yayiba bazata
nitsuba,
dan tsabar raini wai ai tsuntsu zata tai maka mari mai zafi ya d'ago zai zuba mata,
sai kuma ya tsaya yatsura mata ido ganin yadda ta,
rumtse idon ta tare dasa hannu ta kama kanta 🙆🏻�gaba d'aya jikin ta sai rawa yake sai
numfashi take fuzga da qarfi cikin azaban tsoro.

Tsaki yaja da qarfi sannan ya koma kan kujera ya zauna ya lumshe ido tare da damqe hanna
yenshi yana kad'a qafa,
ita kuwa jin shiru bata ji sauqan marin ba yasa ta bud'e idon ta a hankali kan kujeran da yake ta
tsurawa ido tana kallon yadda jikin shi ke bari kamar mazari sai ta qara takure wa jikin 2str tana
mai zubda qollah,

Can dai ya bud'e idon a hankali sannan ya sunkuya yana kunce igiyar takalmin but d'inshi hatta
hannushi sai rawa yake dan an tsoka noshi kuma bai samu ya huce ba yana zare takal man ya
d'an kalle ta da gefen ido cikin tab'e baki ya miqe cikin fushi ya nufi bakin qofar da ake buga
musu a hatsele ya bud'e,
A fusashe ya......


*kuyi haquri my lovely fans na wlh naso yau nayi typing 2 page so baqi nayi yanzu ko na dage
zan mana ko 1 page ne mai Reed More 3 toh Wallahi tallahi banji shauqi shiko typing dole sai
da nitsuwa da shauqi da kuzari toh yau jikina a mace kuyi haquri insha Allah gobe zan mana 2
pages Ngd*

By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 🔟
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Pure moment of life writers

*Wannan shafi Sa daukar wane ga duk masoyan wannan littafi na BANDIRAWO Ngd da
qaunarku gareni*




Daddy na ki ranshi
tsayuwa yayi ba tare da ya juyoba,
shiko Daddy da sauri ya qaraso inda yake yayin da Captain Sani kuma yayi gaba,
gefen General d'in Daddy ya tsaya tare da kallon shi cikin tausayi da sanyi yace.
"Aliyu anya ko a kwana kinnan kana zuwa gun Abban ka."

Shiru bai bashi amsa ba sai ci gaba da tafiya da yake yi a hankali a zahiri da bad'iri Daddy yake
sauraro amman kuma bai bashi amsa ba sai tsuke fuska da ya qara yi,
shiko Daddy ba tare da ya damu da rashin amsar saba yaci gaba da magana dan inda sabo ya
saba dama yasan bazai bashi amsa ba a hakan yaci gaba da cewa.
"Aliyu kayi qoqarin a satin nan kaje gun Abban ka,
sabida ko jiya naje gunsa bai da lafiya ciwon sugarnshi ya tashi sannan hawan jinin sa ya qara
hawa ."

Shiru yayi kawai suna tafiya a hankali shiko Daddy ba tare da damuwa ba yaci gaba da cewa.
"Aliyu kayi qoqarin ka canza rayuwar ka mana ka samawa kanka farin ciki ka tayani roqar
Abban ka ya dawo gidan nan kaji ko Aliyu inason d'an uwana ya kasan ce kusa dani."

Kai ya d'an d'ago dai-dai lokacin da suka isa gaban motar.
Ajiyar zuciya ya sauqe cikin yace .
"Hmmm ."

Daga nan kuma yace.
"Daddy aini Abba ke gudu zama da nine baiso ya barni tun yarin ta na rayu ni d'aya a part namu
tamkar maye,
sai yanzu kuma ince ya dawo kuma ni d'in dai ina gidan ai ni d'inne da basa so."

Kafa d'anshi Daddy ya dafa cikin kula yace.
"Kaje ka duba Abban ka Aliyu!."

"Toh" kawai yace tare da shiga mota suka tafi.

Shiko Daddy ido ya rumtse yana mai jin zafin yadda d'an qanin nashi ya tashi cikin kad'aici da
maraici tamkar maraya al'halin iyaye yenshi na raye,
shine ya kamata ya lura dashi shiko Allah bai bashi mata ta gariba,
gashi sana din rashin gata daya tashi a ciki yasa ya taso mai tsaurin ra'ayi gashi tun asali dama
shi miskili ne ga rayuwar kad'aici ta qara sashi ganin rashin gatan da qaunar iyaye da yake ciki,
murmushi ya d'an yi tune yadda yake tsare fuska cikin qin yarda da kowa shi tunda iyayen shi
suka bashi yake ganin kowa ma baya son shi,
sai dai kuma duk da haka yana mutun ta Daddy kuma muddin ya mishi magana kan abu toh
yakan bi shawarar sa.


Shi ko Aliyu a Jaji yayi kwana 4 ranar jummah da yamma yake ta shirin komawa cikin Kaduna
da zugar yan rakiyar sa.

Ita kuwa Meenal tun randa suka tafi batayi gigin yin girki ba sai fruits kawai take sha wanda aka
loda mata a firic Yau tun da safe take tajin zaman d'akin ya isheta gani take an binne mata

rayuwa ace mutun bazai ga ko idon rana ba.


Bayan Anyi sallan la'asar ne Abdul kuma ya shigo gida cikin takai ci ya kalli Mama dake zaune
a parlour bayan ya zauna gefen ta cikin bacin rai yace .
"Wallahi Mama ni nama rasa me zanyi wa wannan Hamma Aliyu wallahi qofar zan balla kamar
yadda ya balla min hannu mugun banza duk horonsu na sojoji yake zuwa ya sauqe a kaina."

Fuska Mama ta tsuke cikin takaici tace.
"Wallahi ko yanzu zaman da nake a nan mamaki nake dan naje gefen window bedroom d'in shi
wallahi naji motsin mutun tsoro na Allah kar dai Aliyu ya fara tsafi ne da cire kan mutane".

Ido ya zaro cikin kad'uwa da d'an dariya yace.
" Haba dai Mama cire kai kuma? tsafi kuma? Hamma Aliyu d'in?,
a a kam Hajia sai dai in karuwar shi ya kawo ta zauna zaman daduro."

Ido ta tsura mai tare da cewa.
"Ehh haka nefa wallahi kai Abdul kanka na jaa kai kaga ka gane,
toh wallahi muje mu balla qofar."

Miqewa sukayi a nufin zasu je cikin d'akin sai sukaji motsin ana bud'e qofar hakan yasa suka
tsaya.

Ita ko Meenal ta window bedroom taga irin qananan tsuntsayen nan wanda ake cewa caccangi
so tana son tsuntsayen tun a Membila ganin yana d'an firewa da ker yasa ta fita don ta taima
ka mai.


Tana fita shiko tsuntsun ya zagoyo ta qofar aiko yana firewa a hankali,
aiko tai ta binshi a baya tana ta son kama shi tana ta faman murmushi.


Mama kam da Abdul baki da ido duka suka sake suna mamaki lokaci d'aya kuma sai ga Ya
Amir da Aysha Nafeesat na biye dasu a baya Daddy da yanzu ya shigo shima sai ido kawai
yake binta dashi.

Itako ko a jikin ta don bata ma san akwai mutane a wurin ba,
ganin bata ko kula suba yasa cikin qufula Mama ta qarisa gunta cikin bala'i da zafi ta yarfa mata
wani irin gigiceccen mari.

Cikin tsoro ta dafe fuska jiki na bari tuni hawaye ya fara zuba sai tsoro da ya bayyana a fuskar
ta,
Abdul ne ya matso cikin tsura mata ido da kallon qirjin ta har yana lasan lips enshi murya a

sokan ce yace.

"Ke qaramar karuwa yanzu ke ayanzun kinnan har kin iya biyo ingarman namiji kamar Hamma
Aliyu har gida?
lallai ka ruwanci ya zama abin da ya zama."

Mama ce ta kuma ture ta cikin masifa tace.
"Yau zakici ubanki zaki gane kinzo ka ruwanci shima ai nandin ba gidan ubanshi bane kuma
nan ba gidan karuwai bane."


Nafeesat ce ta matso cikin tausayin yarin yar da tagani wacce bazata wuce sa'arta ba,
murya na rawa tace.
"Ayyah Mama zaton fa zunubi ko daya ya kasan ce gaskiya,
daga ganin ta kawai Ku bita da qazafin zina Mama kunfa san hukuncin maiyi wa wasu qazafin
zina a musulun ce kalle tafa mai kyau da ita".

Ture ta Mama ta kuma yi sannan ta yarfawa Meenal wani wawan mari har saida tayi
tanggal-tanggal kamar zata fad'i.

Dai-dai lokacin General Aliyu yayiwa parlour diran mikiya ganin suna tsaye cirko-cirko gaba
d'ayan su,
ga Meenal kuma a tsakiyar su sai kuka take yi cikin sheshsheqa.

Su duka basuma san ya shigo ba sai da Mamata d'aga hannu zata kuma yarfa mata wani
marin,
ita kam ido ta rumtse cikin tsoro .
Shiko Aliyu cikin. daga burya da zafi yace.

*" Meenal* ."

Jin muryar shi yasa gaba d'aya suka juyo inda yaken,
ita kuwa cikin tsoro da gudu ta juya da gudu tayi kanshi tana zuwa ta tsaya bayan shi tana kuka
me cin rai.

Hannun ta General Aliyu ya kamo cikin takun isa da fushi cikin yanayin gargad'i ya yawota
har......


By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 1⃣2⃣

Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Pure moment of life writer


*Wannan shafi naku matan GARKO group GARKUWAR Fulani na gaida ku a duk inda kuke
ina qaunar Ku ina al'fahari daku*



Ya juya ya koma kan kujeran ya zauna,
Captain Sani dake bakin qofar ganin yadda yake a murtuqe yasa ya shigo cikin sanyi,
can gefen Meenal ya dire Trolley da ya shigo dashi tare da qatuwar jaka sannan ya zauna
gaban ta kad'an,
ita kuwa Meenal ganin shi yasa ta d'an sake tare da share hawayen ta,
shiko General ko inda suke bai kuma kollo ba.

A hankali ya bud'e trolleyn cikin sanyi yace.
"Meenal ga kayan ki."

Shiru tayi tare da tsurawa kayan ido.
D'inku nane masu kyau na zamani na gani na fad'a sannan ga dogayen riguna zubin larabawa
sai kuma riguna da siket yar kanti sabbin zubi sannan ga hijabai manya masu kyau sai su onthis
nata masu laushi da tashi sannan d'aya jakar kuma takal mane a ciki masu kyau sai mayuka da
turaruka su shampoo dai kala-kala sai man gashi da dai sauran kayan buqata na matan
zamani,
ido ta kuma tsurawa yan d'inku nan da aka mata masu kyau lokaci d'aya taji sanyi a ranta zata
cire wannan riga mai dogon hannu,
a hankali ta bud'e baki tace.
"Na gode."

Ido ya qifta mata cikin rad'a da alama da ido yace.
"Oga ne ya saya miki shi zakiyi wa godiya."

Kai ta juya ta kalleshi ganin baya ko kallon inda suke yasa ta juya cikin sanyi ta kad'a kai a
hankali tace.
"Zaiyi fad'a."

Kai ya girgiza mata tare da cewa.
"Kije kimai godiya."

Yana fad'in haka ya miqe tare da cewa.
"Oga bari naje na watsa ruwa."
Baiyi magana ba kuma bai bud'e ko idon shiba.

Shi dai Sani yayi gaba abin shi,
Ita kuwa cikin sanyi ta matso gunshi a hankali tace.
"( mi yetti masin) na (gode sosai,)
Allah ya saka."

Bai kula taba sai miqewa da yayi ya shige cikin bedroom d'in kai tsaye ya wuce toilet ruwa ya
d'an watsa da sauri-sauri sannan yayi al'walah yana fita ya kimtsa sannan ya fesa turare mai
sanyi da qamshi sannan ya fito,
a parlour ya same ta zaune tana ta ninke kayan fita yayi ya nufi masallah ci,
a qofar fitan ya had'u da Nafeesat dake shirin shiga part d'in nasu tana ganin shi tai sauri ta
matsa baki na rawa tace.
"Hamma Aliyu zanje gun Meenal ne."
tsaki ya d'an ja cikin tsuke fuska yace.
"Na tabba yeki ne da zaki tsaya min surutu kamar parrot."

Kai kawai take juya mashi tare da rab'awa gefen shi ta wuce cikin parlour tana murmushi a
ranta tace .
"Nagode dai da baka hanani shiga ba."

Shiko fita yayi ba tare daya kuma sauraron taba.

Tana shiga cikin sanyi ta isa kusa da ita gefenta,
ta zauna a hankali tace.
"Meenal kina da kyau."

Murmushi tayi tace.
"Na gode."

Kallon ta ta kuma yi tace.
"Wallahi naji ina sonki kinmin kyau gaki da gashi,
dama nazo ne inbaki haquri da abinda Mama tayi miki kiyi haquri insha Allah bazata sake ba."

Murmushi ta kumayi tana mai tattara kayan tace.
"Ba komai ya wuce me sunan ki kekuma?."

dariya tayi sannan tace.
" Ni sunana Nafeesat kinga daga yau mun zama qawaye ko ga Anty Aysha ma tace tana sonki
kin zama qanwar ta wai zaki na zuwa kina taya ta hira ko."

"Ehh mana zanje nima ina sonta ."

ganin tana tattara kayan ne yasa itama ta miqe tana tayata tana ta mata hira suna shiga cikin
d'akin ita ta shirya mata kayan sannan suka fara tattara daga ciki har parlour har zuwa cikin
kitchen duk suka gyara ko ina suna gama moping aka kira sallah,
al'walah sukayi sannan sukayi sallah suna idarwa Meenal ta shiga wonka riqe da gorar
shampoo ita kuwa Nafeesat sai ta zab'a mata kayan sawa ,
tana fita ta shirya tsab abinta sannan sukayi ihsha parlour suka koma Nafeesat taje cikin gida ta
karbi sitirecan Anty Aysha tana zuwa ta zauna kan kujera cikin fara'a tace ,
"Allah ko in na ja miki gashin kin nan zaizo har gadon bayan ki gashi mai sulb'i."

Ita dai Meenal sai murmushi lokaci d'aya ta gyara gashin nan yayi tsab ya miqe sai sheqi yakeyi
da qamshi daga nan kuma tace.
"Meenal muje cikin gida ."

Kai ta jinjina a hankali tace.
"a a bacci nake ji."
murmushi tare da cewa .
"Hmm toh bari in tafi sai da safe."

"Na gode BANDIRAWO am
Na gode y'ar uwa ta."

Tace mata lokacin da take fita .

Toh kawai tace ta fita,
tana fita shiko General ya shigo Captain Sani na biye dashi a baya riqe da leda a hannun shi .

a parlour suka zauna suka d'an ci abin ci itako tana cikin bedroom d'in tayi konci yarta tana
jinsu can kuma bacci ya fara d'ibarta kafin woni lokacin tayi bacci dan sanyin AC dake ratsata .

Su kuwa suna gamawa Sani ya miqe tare da cewa .
"Sai da safe oga."

Kai ya d'an dago cikin sanyi yace.
"Gobe fa zamuje katsina ka shirya dan da wurin zamuje mu dawo."

Toh yace tare da fita a ranshi yana jin dadi dan harga Allah yana son yaga Ogan nashi na zuwa
gun mahaifin nashi.

Abba mahaifin Aliyu tunda ya rabu da mahaifiyar Aliyu Ammi bai sake zaman Kaduna na
tsawon wata d'aya ba sai dai ya kan d'an zo yaga halin da Aliyun ke ciki kuma har yau bai kuma

Aure ba ya koma can yana rayuwa shi d'aya kamar wandda akayiwa sihiri da zaman kadunan,
shiko Aliyu yakan dan je kad'an-kadan in Daddy ya nace mai da yaje d'in.

Captain Sani na fita ya miqe ya nufi bedroom en bai kalli ko ta inda take ba ya bud'e durowar ya
zaro blanket sannan ya matso bakin gadon kanshi a gefen yasa hannu da nufin ya d'auki pillow,
da sauri ya d'an juyo jin hannun shi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login