Showing 39001 words to 42000 words out of 81932 words

Chapter 14 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf

nasara ba toh na sunk'uru zamuyi mishi,
yadda na rab'a uwarsa da ubanshi haka zan rabashi da ko wacce y'a mace."

Ido Abdul ya zuba mata cikin murmushi farin ciki baki na rawa yace.
"Mama kin gama min komai wallahi."

Sai kuma ya d'anyi shiru sannan yace.

"Amman kar a hanashi Aure gaba d'aya in yaso adai rabashi da Meenal d'in kawai."

Zama tayi gefen shi cikin rashin imani tace.

"Dama ko Aliyu bayyi ma haka ba inason in hanashi aure inko ban hanashi auren ba toh zan
hanashi haihuwa bare kuma yazo ya maka wannan abin."

Cikin mamaki yace.
"Toh Mama me ya miki?."

Jinjina kai tayi sannan tace .
"Na tsane shi ne,
sabida ai kasan dai gidan nan na Abban Aliyun ne ba gidan Daddyn ku bane? Toh tun kafin a
haifi Aliyu naso in zubar da cikin sa yafi sau biyar ina bawa Ammin Aliyu maganin tana sha kai
harda allura nasa an mata cikin dabara amman da yake wannan Aliyun taurin Kaine dashi
kamar shaid'an tun yana cikin uwarsa shi gardama yake min wallahi sai cikin sa yak'i zubewa."
Cikin mamaki yace.
"Toh Mama meyasa kike son hana matar Abba haihuwa? tunda naga ita ba kishiyar ki bace?."

Tsaki taja tare da cewa.
"Kaima banza ne naga alama ka fara zama irin yayan ka Amir da k'anwar ka Nafeesat,
raguwar zuciya gareku ko toh,
abin da yasa nake tsoron kar matar Abban ta haihu sabida kar ya samu Magaji kaga in baida
yaro da zaran ya mutu Daddy kune zai gajesa kaga d'en duk dukuyarshi ta zama tawa nida Ku
y'ay'ana,
toh amman don jaraba da taurin kai saida wannan jarabebben d'an nasu Aliyu yazo duniya
gashi ya fito d'an namiji ta yadda duk zai kwakwashe gadon,
toh shine yanzu banson Aliyu ya haihuwa tunda ko ubanshi ya mutu ya gaji dukiyar toh in baida
y'ay'an dole kune zaku gajeshi daga nan dukiya ta zama tamu,
kaga dama shi Daddyn Ku ba abin da yake dashi yana nan kamar b'eran masallaci fak'aru alal
larurati kawai."

Ido ya ware cikin jin hud'ubar shaid'aniyar uwarsa,
cikin zak'uwa yace. "toh Mama ya kikayi ki rab'a iyayen Hamma Aliyu?."

Murmushi tayi cikin yarda da kanta tace.
"Yanzu kan zan tafi gidan boka mai gobe da nisa dan ya fara min aiki a wannan rana sai gaba
zan baka labarin yadda na rabasu a sauk'ak'e."

Ido ya zura mata tare da mik'ewa yana tafiyar yan kaciya yasa hannun ya d'an dago jallabiyar
sa karta fameshi,
Ita kuwa mayafinta ta yafa sannan suka fito parlour anan ya tsaya itako ta wuce gidan bokan
nata Wanda yake can cikin k'auyen Zaria kauyen ma a bayan garin.

Tana zuwa ta samu gidan a cike da mata anata bin layi gidan boka ya zama tamkar asibiti,
Itace bata samu shi gaba sai goshin maggariba tana shiga bokan ya kalleta cikin yin shu'umin

dariya yace.
"Hajia zulai a gidan lallai mugunta ta motso."
Zatayi magana yayi maza yace.
"Kiyi shiru nasan meke tafe dake amman kinsan sharad'in aiki na dole yau nine matsayi mijin ki
kuma kinsan abinda zamu aikata."

Kai ta jinjina tareda cewa.
"Ba dai buk'atata zata biya ba?."

Cikin zare ido yace .
"Sai dai in ban miki wonka ba."

Kai ta jinjina tare da cewa.
" na yarda"
Dariya yayi tare da cewa.
"Toh a wannan Daren zan tura aljana kasalau ta zuba mishi kasala da sanyi mai tsanani da
zazzab'i ta yadda bazai iya yin nafilfilin daya saba yi da karatu k'ura'ani da azkar da yake duk
sai ya kasa yi kafin mu samu nasara a kanshi."

*Wa iyazubillah ya Allah ka tsare mana imanin mu hak'ik'a wannan abu ya yawa ita a cikin
matan wannan zamini*


Shi kuwa General bayan anyi sallan ishah ne ya koma kan 3str ya konta,
Captain Sani ne ya kalleshi cikin kula yace.
"Sir ya kamata mu koma cikin Kaduna ko?."
Kai ya jinjina tare da rumtse idonshi ,
can kuma sai ya mik'e tare da rarumo..

By
*Garkuwar Fulani*

*BANDIRAWO* page

2⃣9⃣to3⃣0⃣

Na
*Aysha Ali Garkuwa*


*MOH ALLAH HOINANI WALAH KO SAKLATA D'UM*

*Wannan shafi nakune Ku kad'ai Anuty Kausar (Kausar m hassan) & Maryam S bello msb tare

da Jannart Lamod y'ar gatar Garkuwar Fulani*


Pml
Key d'in motar sa ya d'auka tare da ficewa yana cewa Captain.
"Kai tashi mu tafi "
mik'ewa yayi tare da binshi a baya suna fita harabar ajiye motocin ya mik'a mishi key d'in
sannan Captain ya bud'e mishi marfin motar ,
shiga yayi ya zauna tare da lumshe idonshi sannan ya jingina da jikin kuje ran kamar maiyin
bacci,
shiko Captain jiniyar motar ya tayar cikin tsuwa da shaidawa mazauna wurin General zai fita,
hannu Aliyu ya d'aga mishi tare da cewa.
"Ya isa bance ka gayya toh min kowa ba,
mu tafi kawai."

Shiru Captain yayi tare da figan motar suka fito a guje,
suka kama hanyar Kaduna.

Ita kuwa Meenal ranar kusan a parlour ta wuni tare da Abba ita ta shiga kitchen tayi musu girki
irin namu na fulanin daji wanda yasha man shanu,
Abba na tafiya masallaci ita kuma ta koma cikin bedroom tare da rufe k'ofar,
kai tsaye toilet ta shige tare da yin wonka tare da al'wala tana ,
fita ta d'an zauna gaban mirror gashin ta kawai ta d'an tace sannan ta tubke gashin sai kuma ta
murza d'an turaren humran da Anuty Aysha ta bata,
man baki ta d'an shafawa pink lips d'in ,
ras ta fito gonin sha'awa nan ma ba kolliya tayiba ,
wota y'ar doguwar riga ta dauka mai laushi da sulb'i rigar bakace mai dan tsukekken k'ugu sai
dan gajeren wondo mai taushi tasa tare da zura rigar sannan ta yane kanta da gyalen rigar ras
fuskarta ta fito cikin tarhan wanda dama ta iyashi ras dan Hamma Jabeer ya koya mata kasan
cewar irin kayayyakin yake saya mata yana kuma cewa suna mata kyau, sallah tayi sannan ta d'auko k'ura'ani mai girma ta rink'a karatu cikin muryar ta mai dad'in
sauraro,
har zuwa wani lokaci sannan ta rufe tare da jero addu'oin Azkar tare da shafe jikin ta,
cikin dan k'arfin guiwar da jin tsoron da takeji ya regu ta koma kan gado ,
konciya tayi tare da yin shiru tana fidda numfashin a hankali
tana cikin hakan taji motsin mutun a parlour,
shiru ta k'ara yi ko zata ji anyi magana tsorone ya fara diro mata jin anyi shiru ba magana gashi
tasan in Abba ne zayyi gyaran murya inko General ne yana shigowa zai nufi cikin bedroom d'in
inko yaji a rufe ne toh zai fara kiran.
"Meenarl "
"Meenarl"
kanta ta kuma mannawa jikin pillow tare da yin zuru-zuru da ido,
tsoro ne ya kuma rufeta jin karan k'iran woya wanda ta shaida karar na woyar Abdul ne,

tsore ne ya rufeta a take gaba d'aya jikin ta ya fara rawa,
shi kuwa Abdul da yake lellek'a cikin gidan har ya samu ya shigo parlour nasu ya fara k'ok'arin
zare key d'in k'ofar tasu jin karan k'ira ya shigo woyarsa ya sashi fita a firgice cikin sauri gudun
kar wani ya ganshi ,
ta bayan windowta ya koma tare da amsa k'iran ganin Mama ce cikin rad'a yace.
"Mama har yanzu baki dawo ba? kinsan fa Daddy zaiyi fad'a."

Tsaki ta d'an ja tare da cewa.
"In ya dawo kace mishi naje gidan Hajia ta zan kwana sai gobe zan dawo bata jin dad'i ne."

Fuska a had'e yace.
"Toh shike nan ai, ki gaishe ta."

"Toh" kawai tace tare da katse k'iran ta shiga d'an bukkan bokan ,
tana shiga ya mik'a mata hannu tare da cewa .
"Zo mu fara aikin mu dan sai mun fara namu kafin aljana kasalau ta fara nata aikin,
cikin d'auke war imani da rashin tsoron Allah Mama ta matso kusa da wannan k'azamin bokan
suka rink'a aikata k'azamin aiki mai matuk'ar muni da bala'i,
yayin da shaid'an yake mata hud'ubar zakiyi nasara.

Shi kuwa Abdul tunda sukayi magana da Mama har zai koma parlour sai ya jiyo karan tsayuwa
motar General,
hakan yasa sai ya juya cikin sauri da ware k'afa ya koma part din Mama yayin da Nafeesat ko
take part din Anuty Aysha..

Ita kuwa Meenal tuni tsoron ta ya dawo sai numfashi take a hankali,
Shi ko General suna isa ya fito ya nufi cikin gidan ,
yayin da Captain Sani ko ya nufi part d'in Abdul.

Yana shiga cikin gidan yaji gidan shiru ba motsin kowa haka tasa ya wuce cikin sanyi kai tsaye
ya wuce parlour Abba,
sallamah yayi tare da cewa.
" Abba kayi bacci ne?."

Ido Abba ya bud'e jin muryar d'an nashi cikin kula yace.
"Haiydar ka dawo ne? shigo mana."

Shiga yayi tare da zaunawa kusa da Abban a hankali yace
"Ehh Abba yanzu na dawo,
naga gidan shiru duk har kunyi bacci."

Cikin kula yace .
"Toh tashi kake ka shiga sai da safe ko."

"Toh" yace tare da mik'ewa yana.
"Sai da safe.".

Yana fitowa parlour bakin k'ofar bedroom d'in yaje ya tsaya tare da murd'a k'ofar gim,
yaji k'ofar a rufe ,
"Meenarl "
Ya kirata cikin d'aga murya wanda cikin tsoron ta jiyo k'iran kamar a mafarki a hankali ta tashi
zaune,
Shi kuwa a hatsale ya kuma watsa mata kira.
"Meenarl"
"Meenarl".

Da sauri ta mik'e tana zuwa ta murd'a key d'in k'ofar ,
shiko tun kafin ta k'arisa murd'a key d'in ya tura kofarda d'an k'arfi,
cikin rashin sa'a k'ofar ta dawo ta buge mata kai saida ta koma baya-baya zata fad'i,
cikin jin zafin ya fame mata goshinta ta juya ta zauna kan gado tare da dafe kan nata tana .
" wayyo kaina ni kam naga ta kaina."

Tsaki ya ja tare da tab'e baki a fad'ace yace.
"Wallahi kin fiye rakin banza da wofi,
sannan kinji ina k'iran ki kowa na jina kekuma kin wani b'ingire kina bacci."

Shiru tayi tare da zuba mishi ido fuska na zubda k'ollah,
bawai dan zafin buguwar bane zafin rashin tausayin da yake goda matanne ya sata kuka.

Shi kuwa toilet ya shige tare da jallabiyarsa a hannu yana shiga ya d'an watsa ruwa tare da yin
alwala sannan ya zura rigar ya fito tare da d'an k'ara min towel a hannushi yana goge suman
kanshi,
yana fitowa gaban mirror ya tsaya tare da murza towel din a kanshi sannan ya d'an shafa mai a
jikin shi sama-sama sai kuma turarukan da ya feshe illah hirin ikinshi dashi gaba d'aya d'akin ya
d'ebi wani irin k'amshin mai dad'in shak'a.

ita kuwa Meenal har yanzu zaune take tana kuka k'asa-k'asa ga hawaye cur-cur suna zuba
daga dukkan alama bacci take ji amman kukan ya hanata tayi baccin ,
ta cikin mirror ya tsura mata ido tare da tsuke fuska a ranshi ko yana Mamaki yadda kuka baya
mata wuya yanzu inta ga dama sai ta hanashi bacci da wannan kukan,
tsaki ya d'an ja tare da sa hannu ya tatsi maganin ta na shafawa a goshin,
cikin kauda kai yaje bakin gado ya tsaya a gaban ta,
a hankali yasa hannu ya d'an d'ago fuskar ta sannan ya d'an matso maganin tare da
sunkuyowa yana murza yatsun sa biyu kan goshin nata,
kan nata ta janye tare da komawa tsakiyar gadon tana yarfa hannu tare da cewa.
"Shiihhhi wallahi zafi."

Bai kula taba sai haurawa kan gadon yayi tare dasa hannu ya jawo nata da nufin ta matso ya
shafa mata,
ita kuwa cikin jin d'an zogin maganin ta zame ta konta tare dasa hannu ta kare goshin nata.

Shi kuwa yunk'ura yayi da niyar ya sauk'a ya barta da ciwon ta dai-dai sanda yasa guiwar sa zai
tsalla kata ya sauk'e k'afafun shi,
a dai-dai lokacin a take yaji wani irin sanyi ya ratsa shi wanda gaba d'aya tsikar jikin shi ta
mimmik'e wata iriyar muguwar kasala ta rufe shi ta yadda hatta lips d'in shi yaji sun mishi nauyi
a take jikinshi ya fara wani irin rawa da tsuma cikin kasala mai tarin yawa,
ya zame kan gadon ya konta jiki na rawa konciyar yayi a hargitse k'irjin shi zuwa cikin shi ya kifa
kan pillow sannan yasa hannushi d'aya ya zagayo k'irjin ta k'afafun shi kuwa suna kan nata
k'afafun,
ido ya lumshe cikin kasalan da sanyi tare da jin tsinkewar zuciya ,
hannushi yake son janyewa ya kasa kuma sai kawai rawan sanyin daya fara yana ta duk'unk'u
newa.

Ita kuwa Meenal jin yadda ya matseta yasa ta tattaro k'arfin ta zata yunk'ura hakan yasa ta
zame kan pillow sai gashi shima ya mirgino tare da had'e k'irjin su wurin d'aya,
tsoro ne ya rufeta jin yadda yake numfashin da fizga kai ta d'an d'ago ta kalleshi cikin tsoro tace.
"Me haka Hamma haiydar?."

Cikin sanyin murya ya fara magana.
"shhhhh Meenarl sanyi nakeji rufeni rufemin jikina."

Ido ta zaro cikin Mamaki ganin yanzu yanzu lafiyar sa lau sai gashi yanzu kuma sai rawan
sanyin yake yi.

Yunk'uri tayi zata zare jikin ta daga gareshi ,
sai kuma taji ya k'ara shigewa jikin ta yana.
"Shhhhhhhihhh sanyi nake ji Meenarl zazzab'i shhhihh kija blanket ki rufe ni."

Cikin tausayi tasa hannu ta janyo blanket d'in ta rufe shi ,
shiko sai k'ara shigewa jikin ta yake yi yana murza k'afafun shi a jikin ta cikin kasalan ya rink'a
tura hannayen shi yana mik'a da had'e su cikin blanket d'in.

Ita kam Meenal ba abinda take yi sai cewai .
"(Isa ) sannu" .

Lokaci d'aya zazzab'i mai zafi ya rufeshi gaba d'aya jikin shi sai wani irin tiriri yakeyi jikin yayi
zafi tamkar wuta.

A haka yayi ta rawan sanyi da dunk'u lewa cikin jikin ta.

Haka ya kwana cikin wahala da kasala da zazzab'i da tsinke war zuciya,
shine bai samu sa'ida ba sai da iskar asuba ta fara kad'awa tana ratsa ko ina.

A hankali ya fara jin sauk'i sai kuma kasalan dake damun shi,
ido ya bud'e tare da kallon yadda suke konce cikin jikin juna ita kam Meenal baccin take cikin
mak'aleshi,
ido ya tsura mata ganin yadda ta d'aura kanta kan k'irjin shi ta mirgina k'afafun ta kuma tsakiyar
cinyoyin shi yayin da gaba d'aya rigarta ta tartare ta dawo har kan cikin ta sai d'an gajeren
wonddon dake jikin ta hatta cibiyarta a fili take daga sama kuma ta matse mai k'irjin sa da nata,
shi ma en duk jallabiyarsa ta nad'e cinyoyin shi kab a woje fatarta na gogarta sa sai hannunta
d'aya akan cikin shi.
Shiru yayi yana mai jin sauran kasalan a jikin shi so yake ya mirgina ta k'asa ya kasa sai murza
k'afafun shi yakeyi,
ita kuwa motsin shine ya sata ta d'ago kanta cikin bacci ta kife kanta kan nashi kan bakin ta
dai-dai kan nashi ta woni tsuke bakin ta tura shi ,
bakin shi ya bud'e cikin sanyi da nufin ya tasheta,
aiko sai ga lips d'in ta cikin bakin shi
ido ya lumshe cikin janye numfashi ya d'an kamo lips d'anta na k'asa ya d'an ciza,
cikin tsoro da firgita tasa hannu ta tallabe kanshi tareda janye bakin ta,
ido ta tsura mishi cikin tura baki tace.
" wallahi ba kyau yin mugunta."

Ido kawai ya tsura mata a ranshi ta bashi dariya amman sai kawai ya d'an kamo lips d'inshi ya
fara tsotsa,
ita kuwa cikin kiciniyar tashi takeyi daga kanshi,
shi kuwa ya matseta da hannu d'aya sai ya kuma tura d'aya hannu tsaka nin cinyoyin su yana
lalubo jallabiyar sa a nufin shi ya jawo ya rufe cinyoyin shi karta ganshi a hakan
ita kuwa ido ta zaro jin yanata tura hannushi a tsaka ninsu,
shiko ya samu ya jawo ya rufe jikin shi sannan ya d'auke hannushi a kanta,
jin ya sake tan yasa ta mirgina ta konta ta bashi baya tare da tura mishi k'ugunta,
Robar gajeren wonddon dake jikin ta ya tsurawa ido ganin yadda hips d'anta ya ciki a ciki har
wonddon ya matseta,
Ido ya lumshe tare da sa hannushi kan k'ugunta yatsun shi biyu yasa ya kamo roban sanna ya
sake,
pet ya fetta mata shi tare da jawo duguwar rigarta yana rufe mata cinyoyin ta,
Ita kam tsalle tayi tare da dirowa kasa tana shafa inda ya fetta mata roban,
shi kuwa cikin kauda kai ya mik'e yaje yayi al'wala sannan ya fito ya nufi masallaci,
itama alwalan tayi tana ta mota sannan tazo tayi sallan.

Sune basu bar masallacin ba sai 7 dai-dai ya shigo cikin gidan shida Abban shi a parlour suka
same ta ta shirya musu abin shan tea ,
Abba ta gaida tare da bashi tea d'in,

shi kuwa General sai ta kalleshi sai tayi saurin sunkuyar da kanta,
a haka har suka gama shan tea d'in Abba ya mik'e ya nufi parlour shi,
itama Abban na tafiya ta mik'e tayi cikin bedroom ensure,
Shima mik'ewa yayi cikin zafin nama yabi bayan ta,
suna shiga yayi kanta tare da matse....


Ramadan kuwa shida Rayhana tun jiya suna dawowa gida cikin tsere suka nufi part din Ammin
suna shiga suka sameta da bak'in hakan yasa dole suka koma part din Ramadan suka rink'a
magana kan wannan mutumin da suka gani,
jira sauk'e bak'in su tafi suko bak'in sai tara harda rebi suka tafi,
Wanda tuni su Rayhana anyi bacci,
haka yasa Ramadan yana fitowa masallaci sallan Asuba,
kai tsaye d'akin Ammi ya wuce,
bayan ya gaida ta cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login