Showing 63001 words to 66000 words out of 81932 words

Chapter 22 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf

ki bani in bashi.",

Cikin sauri ta had'e farin zuman a cikin ruwan d'umin sana ta d'an sa zam-zam ta jujjuya cikin
kula ta mik'awa General tare da cewa karb'i kasha."

Gaba d'aya jikin shi rawa yake ya k'asa karb'a sai Ramadan ne ya karb'a ya saka mishi a baki.
shi kuma yayi bisimillah sannan ya shanye.

Ajiye k'oriyar Ramadan yayi tare da tsura mishi idanun jin yadda yake sauk'e ajiyan zuciya a kai
akai sai zufa a take tuni ya rink'a atishawa a jere har sau 7 sanna ya rink'a fad'in .
"Alhamhadullih."

Rayhana kam sai mumurshi takeyi tana kallon yadda lokacin d'aya jikin shi ya bar b'ari shiko
Ramadan da Bappa suma ,
hamdalan sukayi ,
Inna kuwa sai mik'a mishi zuman tayi zallan farar Zuma wanda tana cikin sak'arta ma tace.
"Karb'i ka rink'a lasa."

Ido ya tsura mata ita da Bappa sannan yasa hannu shi kan mararshi da dazun nan yake da
tauri kamar dutse sai gashi yanzu-yanzu wurin yayi normal.

Karb'a yayi yasa yatsarshi tare da laso zuman,
murmushi yayi ciki sanyi yace.
"Ramadan daga Yau kai ba Dr bane,
Bappa ne babban doctor mu kaji wallahi gaba d'aya yanzu ba abinda ke min ciwo Alhamhadullih
yau naji sauk'i."

Dariya Ramadan yayi tare da cewa.
"Alhamhadullih B'iyaye na."


Kamar wasa rahanar ubangiji yawane da ita tuni General yaji shi garau,
Inna da Rayhana suka shiga cikin gida suka kawo musu abinci,
Bappa kam tasa Aliyu yayi a gaba kamar yaro sai da ya bashi abinci yaci cikin kulawa shiko
General yaji dad'in abincin dan yasha man shanu,
Inna kuwa ruwan Lipton ta had'a mishi ta bashi,
gaba d'aya suna zaune a d'akin Bappan,
cikin tura baki Ramadan yace.
"Wallahi na lura yanzu Hamma Haiydar kawai kuke so ni kun wani shareni."

Dariya sukayi gaba d'ayansu shiko General Murmushi yayi cikin k'aunar d'an uwan nashi cikin
murmushi ya d'an bugi kafad'an shi yana.
"Ai kai d'an gatan Ammi ne ni ba masu sona sai Bappa da Inna ."

Haka sukaci abinci suna raha.

Bayan sun nitsu ne a daren Ramadan ya kalli Bappa cikin nitsuwa ya bashi labarin abinda ya
faru baki d'aya.

Sannan yaci gaba da cewa.
"Bappa meyasa lokacin da ka had'a auren Bodd'i da Hamma Haiydar ba kayi tunanin wani abu
zai iya faruwa ba? Bappa baka ji tsoron Habba Aliyu ba?."



Shiru Bappa yayi tare da komawa ya zauna ya jingina jikin gini
yanata tunani a hankali yace.
" kusan tun bayan tafiyan Bodd'i kullum cikin tunani nake
Harga Allah nayi iya tunani na dazaiyi akan masu son cutar da ita dan na kareta amma babu
mafita sai yadda nayin, koda ace nayiwa ALIYU kwatancan mahaifin ta dan ya kaita badole
bane yazama inya kaita yakaita lafiya ba dan komi na iya faruwa kasancewar Bodd'i mace ce
wacca ta amsa mace, gashi kuma ALIYU namiji kuma shed'an yana iya samishi wani abu
tunda shima mutum ne babu Wanda ya wuce jarabawar ubangiji."

Ajiyan zuciya ya sauk'e tare daci gaba da cewa.

"Aura mishi ita danayi itace mafita dan koba komi ina yiwa yaron kyakkyawan zato, hakan
yasa komi yazo cikin sauki, aure darajane dashi mai girma wanda insha Allah adalilin auren
zata iya gamuwa da mahaifinta,
Sannan kuma ni nasan Bodd'i yarinyace mai biyayya nasan zata yiwa Aliyu biyeyyah zata
kuma yi hak'uri zama dashi na kuwa san Bodd'i bata da musu ko gardama,
adalilin haka ina sakaran sake haduwa da ita cikin farin ciki da zuriyya dayyiba,
tun a lokacin kuma na lura da Aliyu yana cikin damuwa a rayuwar sa duk da bai gaya min ba
amman na lura yana buk'atar mai shiga rayuwarsa dan tausaya mishi."

Shiru yayi tare da kamo hannu General yaci gaba da cewa.

"Aliyu sana din had'a ka da Bodd'i da nayi ya jazama matsaloli ,
sannan kuma yayi sana d'in had'uwar ka da mahaifiyar ka da k'annen ka,
sai rashin fahimta dake tsananin yayun mahaifiyar ku da mahaifin ku,
Ni kuwa Insha Allah gobe goben nan zamu wuce tare daku da Inna waziri zanje Insha Allah za
dai-dai ta tsakanin su Ammin ku zata koma gidan Abban ku."

Shiru Inna tayi tare da cewa .
"Tabbas su Alhaji Ibrahim basu kyauta ba ai ko dan rik'e musu yarsu da kayi da a mana da zusu
bar maka ita a matsayin matar ka kuma tunda shi Sani ya gaya musu Bappa ya d'aura muku

Aure ko mu bamu isa da ita bane?."



Cikin sanyi Bappa yace.
"Batun auren su kuwa wannan hurumin bana kowa bane tunda aurene akayi a kan Aure kuma
wannan matsalar a kawai maslahar ta cikin addinin mu na musulunci dan addininmi bai regemu
da duhun komai ba."


Cikin sanyi General yace.

"Bappa me yasa Baku gayawa iyayen Bodd'i aura min ita kumayi ba?."

Kai ya jinji na cikin nadaman abin yace.
"Wannan shine kuskuren da nayi dana yarda nabi shawarar mahaifiyar Bodd'i ita kuwa tace a
fad'i hakan ne dan tana ga kar mijin ta yaga banyiwa yarshi adalci ba ko na aurar da ita ga
wanda ban sani ba,
amman ni nasan nayi kuskure ka gafar ceni."

Kai ya juya tare da cewa.
"Bappa baka yimin komai ba,
kuma Insha Allah gobe iwar haka muna jihar Kaduna."


Haka suka kwana cikin tsantsar farin ciki, da k'aunar juna.

washe gari da sassafe suka kama hanyar Kaduna,
tafiya kuwa tayi kyau General ke jan motar sai Ramadan a gefen shi Bappa da Inna da
Rayhana kuwa suna baya.

11:00 pm dai-dai General ya kutsa hancin motarsu cikin Jaji yayinda gaba d'aya sun cika da
gajiya,
bayan sun shiga Ramadan ya jido musu ledodin kayan cima da General ya lodo musu,
ya kawo musu Inna da Rayhana d'aki d'aya suka shiga suna shiga ko ruwan basu shaba suka
konta idanun cike da bacci jiki dauke da gajiya.

Ramadan ma tuni ya b'ingire yana bacci Bappa kuwa saida yayi nafilfilinshi sannan ya konta.

Shi kuwa General wonka yaje yayi sannan yazo ya konta tare da k'ura'ani a hannu shi karatu ya
rink'a yi cikin sanyin saiti,
jin bacci na fin k'arfinshi yasa yarufe karatun tare ajiye kura'anin,
sannan ya koma ya konta,

cikin hamdala ya matse mararshi tare da cewa.
"Alhamhadullih yau gani lafiya ta lau ba ciwo har na manta na tab'a ciwon ma."

Ido ya rumtse da k'arfi tare da matse cinyoyin sa cikin ranshi yace.
"Allah ka yaye min wannan raunin shawa'an da ke damuna dan tabbas yaji sauk'i amman
kuzarin shi da saura.

Haka yayi ta Addu'a.
Washe gari bayan sunyi wonka Rayhana tayi musu girke-girke sukaci suka sha sannan suka
nufi cikin kaduna.

Abba kuwa shima da Daddy bayan sun gaba shawarwarin su ,
Captain Sani ya dauke su ya nufi gidan Alhaji Ibrahim dasu.

Shima General kai tsaye gidan Alhaji Ibrahim d'in ya nufa dasu dan a cewarsa lokacin da yaje
ya jajubo maganar auren Abban shi bai sanina haka kuwa zai warware abin ba tare da sanin
Abba .

Motarsu General nayin Parking sai ga Motarsu.....



By
*Garkuwar Fulani*


*BANDIRAWO* page

4⃣9⃣to5⃣0⃣

*Na*
*Aysha Ali Garkuwa*






*Wannan shafi d'uggu ruggum d'in shi nakine ke kad'ai Khaleesat Haiydar Allah bar zumunci da
k'aunah ina al'fahari dake, MI YID'I MASIN KHALEESAT*

Dr Jabeer shima yayi parking,
Ido Aliyu ya tsurawa motar Dr Jabeer d'in cikin takaici,
Meenarl ya haggo zaune a gefen Jabeer daga dukkan alamu tare suka fita kuma yanzu sunka
dawo tsaki ya jaa cikin murtuk'e fuska yayi shiru yana matse siteri,
Bappa kuwa da Inna da Rayhana shiru sukayi dan basu san me yasa shi jan tsaki ba kuma ya
tsuke fuska ya k'i ya bud'e musu motar,
Shiko Ramadan shima kallon motarsu Meenarl d'in yake tare da son fitowa dan sauri yake
yayiwa Meenarl albishir da zuwan su Bappa.

Ita kuwa Meenarl shiru tayi tana kallon Hamma Jabeer d'in nata da ya rik'o hannun ta yana
murza yan yatsunta cikin wani salon ya k'ara juyowa gareta suna fuskar tar juna cikin sanyi
yace.
"Bodd'i na ina sonki inason kasan cewa tare da ke inason farin cikin ki,
me yasa kike k'untatawa kanki akan Aliyu ai da ya damu dake yadda kika damu dashi da bazai
iya korarki ba,
Bodd'i nifa d'an uwan kine na jini ki dawo da zuciyar ki gareni zan soki zan kula dake zan
riritaki."


Shiru tayi fuskar ta na cike da k'ollah tace.
"Hamma Jabeer,
Ni ina tausayawa Hamma Haiydar bashi da lafiya kullum dere baya bacci kuma ba mai taimaka
mishi sai ni."

Sai hawaye shar-shar a fuskarta tana juya kai.

Shiru Dr Jabeer yayi zuciyar shi cike da k'aunar ta yasa hannu ya tallabe hab'arta k'ara matsota
yayi tare dasa hannun shi ya share mata k'ollah.


Shi kuwa General da k'arfi ya rumtse idanun shi cikin k'ara matse siterin yana mai juya kai.

Ganin haka yasa Ramadan dannan pin d'in bud'e motar sannan ya bud'e ya fito tare da bud'e
wa su Bappa da Inna suma suka fito,
shima kainshi a sunkuye ya bud'e ya fito cikin tsuke fuska.

Suna fitowa ,
Meenarl ta wore ido cikin tsananin mamaki da farin ciki cikin sauri ta fito tare da yin gudu tana
zuwa ta rugume Inna cikin kewar juna Inna ta rugumeta Bappa kam sai murmushi.

Ita kuwa Meenarl sai hawayen farin ciki,
sai ta kuma sake Innar tayi cikin gida da gudu tana.
"Ummi! Ummi ina kike ? Ummi ga Bappa na da Inna ya Ramadan ya kawo minsu."

Su kuwa bin bayan ta sukayi suna dariya a babban parlour suka tarar da mutanen gidan baki
d'aya,
cikin farin ciki da k'aunar juna suka gaggaisa.

Shiru Bappa yayi ganin Aliyu bai shigo ba cikin kula ya kalli Ramadan dake gefen Ammin su
yace.
"Kai Ramadan ina Aliyu ."

"Yana woje yace shi bazai shigoba tunda masu gidan basa so."

Cikin girma Bappa yace.
"Shima ai nan gidan sune."

Sai kuma ya mik'e ya fita yana zuwa kai hannun shi ya kamo yayi cikin gida dashi suna shiga
parlour.

Ammi da ta zubawa k'ofar shigan ido tana ganin shi ta rink'a sauk'e ajiyar zuciya tare da tsura
mishi ida wasu hawaye masu zafi suka kwaranyo mata cikin rawan murya tace.
"Haiydar."

Shi kuwa General Kanshi a sunkuye yabi Bappa dake rik'e da hannu shi ,
gaban Ammin yaje ya ajiye shi sannan ya zauna gefen shi cikin kula yace.
"Aliyu ga mahaifiyar ka gata a kusa da kai gata a gaban ka."

Shiru Aliyu yayi tare da tsurawa yatsun k'afafun ta idanu lokacin d'aya yaji wani irin karayan
zuciya gaba d'aya sai yaji zuciyar shi ta raunata.

Ita kuwa Ammi hannu tasa ta jawo kanshi ta d'aura kan cinyarta yayinda kan Ramadan yake
kan d'aya cinyar Rayhana kuwa ta rakub'e a jikinta,
cikin sanyi ta d'aura hannun ta kan tsakiyar kan Aliyu baki na rawa tace.
"Aliyu Haiydar ina sonka d'ana ina tunako ako wacce rana ban tab'a yin sallah na idar ba tare
da nayi maka Addu'a ba Ammin ka tana sonka kaine farin ciki na
Nagode wa Allah daya kare min kai."

Shi kam General manna kanshi yayi da jikin Ammin kamar mai tsoron kar a saceta a hankali yaji
hawaye masu zafi irin hawaye da yake ji a duk randa bagen mahaifiyar shi ya dame shi,
ita kam Ammi fad'ar farin cikin ta bazai yiwu ba,
General kuwa zuciyar shi cike da k'aunar mahaifiyar shi a d'aya gefen kuwa har cikin ranshi
yake jin zafi da haushin yayun mahaifiyar tashi dan su suka mishi Katanga da ita tun yana
k'arami suka mai dashi marayan dole.

Bappa ne ya gyara zama cikin halin girma ya kalli Barrister Lawan da Alhaji Ibrahim sannan ya

kalli mahaifi yarsu a hankali yace.

"Wannan shine babban kuskuren da mutanen mu sukayi a wanna zamanin, aiki da zuciya fushi
da tunzura a duk inda aka samu saki ya gifta a tsakanin ma'aurata,
mata kin forko da za d'auka shine hak'uri sai kuma a duba darajan Aure sannan a koma a duba
makomar yaran dake tsakanin dan gujewa aikin dana sani,
babu wani riba cikin yin fushi dan anyi saki a reba uwa da d'an ta domin ko a shariyance yara
suna gefen uwane har sai sun shekara 7 yanzu kai Lawan ribar me ka samu daka reba y'ar
uwarka da d'anta kalli hawaye dake bin fuskar ta,
kalli illar rebesun da kukayi yasa Aliyu ya rayuda Bodd'i tsawon lokacin Amman baisan y'ar
uwarsa bace itama bata sani ba,
kuna ne manta a can gefen bakusan tana kusa da kuba."

Shiru sukayi baki d'ayansu dan tabbas gaskiya Bappa ke gaya musu,
gaba d'aya zuk'atan su sun cika da nadama,
Barrister kuwa har cikin ranshi yake jin kunyar y'ar uwarshi.

Haka Bappa yayi ta musu nasiha da fad'a da nuna musu illar yin fushi dan an saki y'ar uwarka
kace zaka rebata da yaran ta.


Gaba d'aya sun maida hankali kan Bappa shi kuwa cikin girma ya sake gyara zama tare da yin
gyaran murya yace.

"Ibrahim wai ka d'aura auren Aminatu da Jabeer."

Cikin sunkuyar da kai Alhaji Ibrahim yace.
"Ehh Bappa na d'aura musu Aure ."

"Yaushe ka d'aura musu auren?."

"Bayan munje Membila lokacin da kukace an saceta toh damuka dawone da wata 1 na d'aura
musu auren tunda shi Jabeer yana sonta."

Kai Bappa ya jinjina cikin kafeshi da ido yace.
"A lokacin kana da yak'inin Aminatu tana rayene? a lokacin kana da yak'inin zata dawo ne?
kasan inda take a wanna lokacin ne?.

Ajiyar zuciya Alhaji Ibrahim ya sauk'e tare da jin saurin tabbayoyin Bappa sai kai kawai yake
gyad'a wa tare da cewa.
" a a,
bani da sanin wannan Bappa."

Gyaran murya Bappa ya kumayi sannan ya kallesu baki d'ayansu tare da cewa.

"Lawan ana d'aura Aure da babu ne? ana d'aura Aure da wanda ba san inda take ba?."

Cikin goge zufa Barrister yace.
"A a tabbas ba,a d'aura auren da babu matar ,
Amman nima wallahi Ibrahim bai gaya minba sai kawai cemin yayi ya d'aura musu aure."

Cikin ilimi Bappa yaci gaba da cewa.
"A cikin rashin sani kukayi aure a kan Aure! toh cikin wadan nan auraki biyun wanene ya zauna
wanda akayi da fari ko na biyu?."

Dr Jabeer kam tuni tabbayoyin Bappa ke tsinke mishi hanjin cikin shi sai ido yake bi Bappa da
shi,
shi kuwa Aliyu jinsu kawai yake dan ya gama yanke hukun ci a ranshi shi dai Ammin shine zai
tafi da ita.


Cikin sanyi Barrister yace.
"Na farin dai tunda shi na biyun kan na farin aka daura shi ."

Murmushi Bappa yayi tare da cewa.

" toh zab'i yana gun Amina ita zata zab'i wanda take so a cikin su dan haka shariya ta bata
dama,
zancen gaskiya kuma Aliyu ni na aura mishi Amina Aure bisa koyarwan addinin mu ga sadakin
Amina a hannuna ko sisi ban tab'aba,
kuma ko a wancan lokacin Aliyu bashi yace yana son Amina ba nine na rok'eshi dan sirar da
mutun cin ta."

Sai ya kuma juyawa gun Aliyu yace.
"Dan haka Aliyu in baka sonta ka saketa ga sadakin ka sai a maida maka,
inko kana sonta saita zab'a a cikin Ku duk wanda tace bata sonshi sai a maida mishi sadakin
shi ."

Gaba d'aya su yarda da maganar Bappa dan gaskiya ce.

Barrister ne ya kalli Meenarl cikin sanyin jiki yace.
"Meenarl wa kike so a cikin su in Aliyu kike so ki fad'i shima d'an uwanki ne."

Ita kam Meenarl sai kawai ta juya kan Dr Jabeer tana kallon shi ido cikin ido fuska cike da
k'ollah ta k'asa magana sai kuka an kad'a an rawa tayi magana ta k'asa sai kallon Dr da takeyi
tana kuka.

Shi kuwa Aliyu ba k'ara min hatsala yayi ba ganin yadda take kallon Dr Jabeer tana kuka cikin
cije lips enshi yace.
"Ni banzan rabata da d'an uwanta ba dan nasan zafi da ciwon dake cin zuciyar wanda aka raba
da d'an uwanshi dan haka ni zan barwa Jabeer ita ,
dan shiyafi cancanta da ita kuma shi ya tashi cikin farin ciki dan haka niko banzan zo rana tsaka
na rabashi da farin cikin da ya rayu a cikiba ,
niko dama bansan menene farin ciki ko dad'in d'an uwa ba dan haka haka ni zan bar mishi ita."

General yana maganar ne da iya gaskiyar sa dan a can cikin ransa yana jin zafin yadda
Minalinshi ke kallon Jabeer tana kuka shi kuma ko inda yake bata kallah ba a d'aya gefen
zuciyar sa kuma yana tuna cewa shifa har yanzu lafiyarsa nada rauni.

Shi kuwa Dr Jabeer cikin tsantsar farin ciki da jin k'aunar General d'in yace.
"Nagode d'an uwana Allah ya bar zumunci da k'aunar juna."

Ita kuwa Meenarl zuciyar ta cushewa tayi sai wani irin sautin kuka ta saki cikin tsurawa Jabeer
d'in ido.

General kuwa ganin duk sunyi shiru ne ya kara b'ata mishi rai a zuciyar shi yace.
"Ai dama su ba sona suke yiba."

Bappa kuwa ido ya tsurawa General dan ya gano Aliyu yaudaran kanshi yake yi.

Bappa ya bud'e baki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login