Showing 60001 words to 63000 words out of 81932 words
Chapter 21 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf
jin zafin rabuwa da ita yana kuma tuhamar kanshi da jin zafin d'an indai yace bazai rabu
da ita bama bayyi mata adalci ba, sannan ya zaiyi da amanarta da Bappa ya bashi,
hannu shi dake rik'e da towel d'in k'ugun nashi ya d'an daga tare da kife hannun kan mararshi ,
har lau dai idanun shi na kan fuskarta matse marar tasa yayi tare da rumtse ido a hankali yace.
"Minalin Hamma Haiydar,
lafiya tayiwa Hamman ki tsad'a Minalin Hamma!
ciwo ya min illah! ciwo ya kama ni a inda ya zamar dani nida babu kad'an ne babban cinmu ,
Minali na na cutu,
na samu k'arin ciwo a kan damuwar da rayuwata ke ciki na rasa mahaifiya ta tun ina karami
yanzu kuwa ciwo zai rabani da amanata."
Ita kam Meenarl tuni sai hawaye ke bin fuskar ta cikin raunin zuciya ta rink'a zubda k'ollah tana
shafa mararshi inda ya kife hannun shi,
tana kuma kallon fuskar sa jin yadda wurin ya fara tauri da zafi yasa ta d'an matse wurin da d'an
k'arfi.
Zillo General yayi cikin dauriya ya rik'e wurin a sunkuye ya isa bakin gado zama yayi cikin fidda
numfashin wahala.
Matsoshi tayi cikin sanyi ta zauna gefen shi tare da cewa.
"Hamma kayi hak'uri muje asibiti."
Kai ya juya cikin cije lips ya koma ya konta a rigingine tare da yin mik'a yana mai rumtse idanun
shi.
ita kuwa sai k'ollah ke bin fuskar ta,
tasa hannu tana shafa mishi kan marar tashi a hankali tana d'an danna wurin.
ido kawai ya tsura mata cikin sanyi ya jawo hannu ta kan jikinshi ya kontar da ita suna fuskarta
juna murmushi k'arfin hali yayi tare da cewa.
"Minali Hamma,
Hamman kifa bashi da wani amfani a gareki banban cina da macecce kad'an ne ya rigada na
gama mutuwa."
Ido ta zaro cikin tsoro tare da bud'e baki cikin kuka tace.
"A,a
a a Hamma Haiydar bazaka mutuba."
Sai kuma kawai ta fashi da kuka tanayi tana shafa sajen fuskar sa.
Lips enshi ya cije tare da mirgina ta ya kontar da ita kan pillow,
cikin sanyi ya yunk'ura yayi mata rumfa da k'irjin shi cikin sanyi yasa bakin shi kan fuskarta yana
hura mata iska.
ita kuwa sai kukan take tana sheshshek'a k'asa-k'asa .
Idon shi ya tsura cikin nata a hankali ya manna bakin shi da nata harcenshi yasa ya rink'a lasar
lips enta yana kallon fuskarta.
Shiru tayi tare da lumshe ido tasa hannu cikin suman kanshi.
Shi kuwa ganin yadda tayi shirun ne ya d'an yi murmushi a hankali ranshi ke fad'a mishi ,
"Meenarl matar lafiyeyyene."
A zahiri kuwa lips d'inta na k'asa ya d'an kamo tare da d'an cizawa.
Cikin duniyar nitsuwar da ta tafin taji zafin ya ratsata.
Cikin tsoro tayi zillo tare da tureshi tana yarfa hannu da zaro ido woje.
Shi kuwa General yadda tayi likimon da yadda ta zaro idon ne ya bashi dariya abinda General
bai fiye yiba kenan.
Dariya ya rink'a yi a hankali tare da nunata dariya yake cikin danne mararshi dake mai ciwo a fili
ta zaro idon shi kuwa abin ya bashi dariya da ta nitsu tanaso ya murjeta dataji sab'anin haka ta
wani zoro ido.
Ita kuwa baki ta tura tare da kaimai bugu tana.
"Allah ko Hamma Haiydar sai na rama wallahi zan rama."
dariya ya kumayi cikin d'aga mata gira yace.
"Zo zo ki gani Minali."
tureshi tayi tare da matsoshi tana cewa.
"Maranka zan danna."
Kai ya juya cikin dariyar yace.
"Kashe Hammanki zakiyi ko."
Sai ya kuma nuna mata lips enshi yace.
"Zoki rama anan."
A hankali ta matsoshi tare da zama kan cinyarshi suna fuskantar juna,
lips enta tasa da nufin kamo nashi ta ciza ,
sai kuma tayi ajiyar zuciya tare da sakewa a jikinshi jin ya manne bak'in shi da nata ya zira
harshensa cikin bakinta tare da d'aga mata gira d'aya alamar ki rama.
Ina shiru tayi tana jin yadda yake sauk'e mata kasala da salonshi..
A parlour kuwa Dr Jabeer mik'ewa yayi lokacin dayaji sautin dariya General cikin zafin abun ya
kalli Ramadan da Captain Sani yace.
"Sani mu zamu tafi ."
Ramadan kuwa kallonshi yayi cikin girmamawa yace.
"Hamma Jabeer Ammi kam su Daddy sun hanata zuwa ko ? bazata zo taga halin da Hamma
Haiydar ke cikiba."
Tsaki ya d'an ja k'asa-k'asa tare da cewa.
"Ba shine yake wannan dariyar ba? ko ciwon dariya yake yi?."
Shiru sukayi gaba d'aya d'an sun fahimci Hamma Jabeer a hatsale yake,
Ita kuwa Rayhana kallon shi tayi cikin had'a fuska tace.
"Hamma Jabeer inka koma ka cewa Ammi ni dai wallahi in bata zoba banzan koma Adamawa
ba."
Harara ya cilla mata tare da cewa.
"Bodd'iiiii,
Bodd'iii".
Shi kam Abba ido ya zura musu.
shi kuwa Captain Sani hankali shi na kan Nafeesat yana nuna mata pic d'in Ammi a phone
nashi.
A cikin bedroom d'in kuwa.
wani irin zafi da takaici ne ya tokari k'ahon zuciyar General jin muryan Dr Jabeer cikin sanyi ya
zame bakin shi a cikin nata ,
cikin had'e fuska ya tsura mata ido a fili yake zaton yadda take mak'ale mishi haka take
mak'alewa Dr Jabeer ko?,
a take sai zazzab'i ya fara rufeshi sai sanyi da ya fara ji cikin cushewar voice yace.
" Meenarl ke da waye kika zo?."
idonta a lumshe ta konto kanshi.
Cikin zafi ya tureta tare da buga mata tsawa yace.
"Ke dawa kika zo?."
Ido ta tsura mishi baki na rawa tace.
"Hamma Jabeer nane fa."
Tureta ya kumayi tare da sauk'owa k'asa baki na rawa ya nunata da yatsa yace.
"Ehh ai nasan nakine ba sai kince min ke da Hamma Jabeer dinki bane,
nasan shi naki ne,
d'an haka tashi tashi ki bishi me ya kawoki gareni?."
Gaba d'aya ya juya fad'a yake har muryanshi na rawa kamar zaiyi kuka ga zafin zazzab'i yana
zura rigarshi tare da cewa.
"Ni ban damu ba karki sake zuwa gareni Allah ne gatana ,
Ammi nama ta gujeni,
Meenarl kema ki tafi gun Jabeer,
karki sake zuwa gidan nan tunda iyayenki basa sona tun ina k'arami suka rabani da maifiya ta
duk family naku bakwa sona,
Insha Allah zan shirya Na tafi Gembu zanje Membila zan koma wurin Bappa zanje na gaya
mishi a manar daya bani tafi karfina zan taho dashi na nuna mishi inda kike."
Ita kam Meenarl kuka kawai take tana cewa.
"Hamma Haiydar ina zakaje?."
Tsawa ya buga mata tare da zaro key d'in motarsa,
yace.
"Ban sanina ki tashi kibi Jabeer din naki kije ya maida ki gun iyayen ki."
Parlour ya fito itama biyo shi tayi a baya suna fitow ya kalli Ramadan da Rayhana yace.
"Ramadan ku taso mu tafi."
Ba musu suka mik'e tare da cewa.
"Abba bari muje?."
Shima General Abban ya kalla tare da cewa.
"Abba zamu fita."
Shi kuwa Dr Jabeer hannun Meenarl ya kamo tare da cewa.
"Mu tafi a banza zaki tsaya kina kuka."
janta yayi ya fice.
shi
kuwa Captain Sani kallo yabi General dashi ganin yadda yake watsa mishi harara,
harce General ya juya cikin fillanci yace.
"Abba zamuje mu kwana a Jaji da kanne nah."
Murmushi Abba yayi tare da cewa.
"Toh saida safe kenan,
Amman ko zaku meda Rayhana gun Ammin ku ne,
shi kuwa Ramadan zai kula da kai."
Kai kawai ya gyad'a mai tare da ficewa.
Kai tsaye Jaji suka zo suna shiga cikin gidan nashi suka samu mai aikin a parlour ,
cikin mamaki suka kalli juna.
Shi kuwa General fuska a had'e ya kalleta tare da cewa.
"K'anne nane kin tsaya kina kallon su kije ki kawo musu abinci."
.
Kai Rayhana ta rink'a juyawa cikin tuhuma tace.
"Hamma Aliyu wannan kuma wacece? kuma me takeyi? A gidan nan."
Baki ya tab'e tare da cewa .
"Shara da jiran gidan take yi."
Harara Ramadan yayi mata tare da kallon yayan nashi yace.
"Gaskiya Hamma tabar gidan nan bai daceba ka zauna da ita."
Ido ya lumshe cikin sanyin zazzab'i yace.
"Toh ka salla meta tunda baka son zaman ta a nand'in."
Ido ta zaro cikin tsoron kar a rabata da aikinta zatayi magana
Ramadan yace.
"Kiyi hak'uri zaki bar gidan nan kam ki shirya da safe zan salla meki."
zata kuma yi magana General yace.
"Fita a daga nan gobe da safe zai salla mekin hakan da yace banson musu."
Haka ta fita ranta a bace tana jin zafin su ramadan.
Shi kuwa General ya biye musu ne d'an ya lura kamar zargin shi da ita su ke son d'arsuwan
musu ,
sannan kuma yana son duk wani abinda zaiyi ya sasu Happy.
Ramadan kam tare ya kwana da General a kan gadon shi yayin da Rayhana ke d'aya d'akin ,
shi kuwa General mamaki yake d'an ciwon shi tun juya yake reguwa d'an jiyama bai mishi
kamar na kullum ba bugu da k'ari kuma da asuba yana jin wani yanayi da ke bashi mamaki,
sai kuma gashi yau kam zazzab'i ne ma kawai ke damun shi,
a d'aya sashin zuciyar shi kuwa,
Meenarl yake son yak'i cewa haka ya kwana cikin tunani ,
da k'udirin washe gari zai wuce Taraba d'an gaba d'aya hankalin shi ya koma wurin Bappa .
Haka kuwa. Akayi da asuban fari ya shirya tsab shida k'annen shi , sannan suka sallami mai
aikin suka ja gidan suka rufe,
sannan
suka d'auki hanyar Taraba Rayhana da Ramadan zuciyar su k'al da farin ciki dan suna matukar
kaunan wannan garin.
Captain Sani kuwa suna fita ya kalli Abba cikin tank'waushe k'afafun yayi k'asa da kanshi tare
da cewa.
"Abba Hamma Haiydar ya rasa farin ciki da kulawar mahaifiya tun yana k'arami,
hakan tasa ya rayu kamar maraya ko yaushe fuskarsa cike take da maraici,
hak'ik'a nasan iyayena basu kyauta ba ,
Amman baya ta wuce yanzu mu gyara gaba,
Abba ka maida auren Ammi ka dawo da itakan 'ya'yan ta,
wannan ne kawai zamuyi musa farin ciki a zuciyar. Hamma Haiydar a dawo da Ammin shi kusa
dashi."
Kai kawai Abba ke gyad'a wa cikin gamsuwa da shawarar Captain ya kuma yarda da shawarar ,
sannan yace.
"Insha Allah gobe zan gayawa d'an uwana kuma jibi ko gata zamuyi shiri muje gidan ku,
zanje na nemi gafarar Barrister Lawan da Alhaji Ibrahim da Fatima ta dawo kan yaran ta."
Sosai Captain yaji dad'i dan yana son ya bawa General mamaki ,
ya kuma yi niyar dawo mar da farin cikin sa AMMIN shi.
ITA KUWA Meenarl tunda suka dawo ta k'asa ta tsare so take tayi fushi da Hamma Haiydar d'in
nata amman tausayin shi nacin zuciyar ta,
Abban ta da Barrister da Dr Jabeer kuwa abinyana damun su Ammi kuwa tunda Meenarl ta
gaya mata halinda General ke rayuwar in dere yayi ,
ta dage tuk'uru tanayiwa d'an ta addu'a da nema mishi sauk'i da kariyar ubangiji kuka take tana
kai kukanta gun mahaliccin mu tana kuka tana yiwa d'an ta addu,a.
Tafiya mabud'in ilimi General Aliyu kam tuni yabar jihar haduna ya nausa Taraba ,
A cikin *Mayo balwa* sukayi sallan magariba sannan sukaci gaba da tafiya,
gudu Aliyu yake kamar zai fire d'an so yake a yau dinnan su isa rigarsu Bappa tuk'in yake da
sauri a lokacin da suke cikin Membila dan zuwa yanzu mararsa da zazzab'i ga sanyin ciwon da
yake ji d'in ga sanyin garin Mambila tuni ya fara karkarwa,
ganin haka yasa Ramadan ya karb'i tuk'in dai-dai lokacin da suke za gayawa bayan dutsen
mambila d'in.
9:47 pm dai-dai Ramadan yayi parking a k'ofar gidan Bappa cikin rawan sanyi ya kalli General
dake ta karkarwa yana damk'e da mararshi.
Rayhana kuwa kai tsaye cikin gida ta nufa tana zuwa,
Bappa na ganin ta ya mik'e cikin tsantsar farin ciki ya mik'e tare da yin woje yana cewa.
"Muta nen Kaduna kai sannun ku da hanya wannan tafi yan deren cikin deren kuka shigo
wannan lardi Allah ya k'ara karewa."
"Amin" tace.
tare da zauma a gefen Inna dake ta faman yi mata sannan .
Bappa kuwa yana fita ya nufi inda motarsu ke tsaye cikin mamaki ya kalli Ramadan tare da
haska wanda ke koncen yana rawan sanyi.
cikin firgici da kad'uwa da mamaki da farin farin ciki yace.
"Aliyuuuu,
Alhamhadullih Aliyuuu dama nasan tabbas! tabbas wata rana zaka dawo wannan rigar tamu."
Sai kuma ya kalli Ramadan cikin kad'uwa yace.
"Ramadan meya sameshi ? kama shi mu shiga cikin gida."
Bayan sun kontar dashi kan katifar Bappa Ramadan ya d'ebo magungunan shi zai bashi .
Cikin fahimta Bappa ya matse matar tashi kai ya juya cikin sanyi yace.
"Ramadan ciwon Aliyu bana asibiti bane wannan ciwon kura'ani ne da add'a maganin shi."
K'ara damk'o wurin Bappa yayi tare da matsewa da k'arfi.
cikin wani irin.....
*Allah Yau da k'er nayi typing d'inga*
By
*GARKUWAR FULANI*
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*BANDIRAWO*
page
4β£8β£
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*Fulb'e BANDIRAB'E am mi hofni on*
Zafin da sanyin zazzab'i General ya k'ara dunk'ulewa tare da kamo hannun Bappa ya rik'e
murya na rawa yace.
"Bappa marata zata tsinke! sanyi zai kasheni! Bappa kaina kamar zai fashe!."
Cikin tausayawa Bappa ya shafa kanshi tare da girgiza mishi kai yace.
"Insha Allah yanzu zaka rebu da wannan ciwon In Allah ya yarda zaka samu waraka a jinyarka
da zanyi maka yanzu."
Kai Bappa ya d'ago ya kalli Ramadan cikin shak'uwar dake tsaka ninsu da yaron yace.
"Ramadan tashi kaje cikin gida,
kace Inna Waziri ta baka zam-zam da ganyen magariya sannan ta baka da farar zumanan ta
had'oma da ruwan d'umi."
Cikin sauri Ramadan ya mik'e tare da cewa.
" toh."
Yana shiga cikin gidan d'akin Inna ya shiga cikin sauri ya shaida mata aiken Bappa.
Rayhana najin haka ta mik'e tare da cewa.
"Jikin Hamma Haiydar ko? ."
Kai kawai ya gyad'a mata tare da karb'an goron zam-zam din da sauran abubuwan ita kuwa
Rayhana ta karb'i akoshin zuman,
sanan Innan ta kallesu cikin kulawa tace.
"Ku kai da sauri bari in d'ebo ruwan d'umin zan kawo."
"Toh kiyi sauri Inna." Rayhana ta fad'a lokacin d suke fito tsakiyar gidan.
Ita kuma Inna ta nufi kitchen d'in su har zasu fita,
suka d'an tsaya cikin had'e fuska Ramadan ya kalli Lari kishiyar Innan dake musu tsaki tare da
cewa.
"Muna fukai kunzo ko kai wannan yaron na tsani ganin fuskar ka."
A hatsale Ramadan yace.
"Wallahi ki rik'e mugayen furucin ki ni ba Inna da Bappa bane wallahi sab'a miki zanyi in kin
saba fad'in mugun zance toh ki kiyayeni ina gab da casaki banza kawai mai bak'in baki."
Shiru tayi d'an har ga Allah tana shayin Ramadan da kuma jin tsanarsa dan fuskar sa na tuna
mata 'ya'yan Inna da tayiwa mugun baki suka watse suka bar garin."
Ita kuwa Inna cikin sanyin ta tace.
"Ramadan ku tafi kuje Bappa na jiran Ku."
Juyawa sukayi suka tafi,
ita kuwa ta shiga kitchen d'in ta d'ebo ruwan d'umin ta bisu a baya.
Suna shiga d'akin Bappan ,
Ramadan ya mik'a mishi goran zam-zam d'in tare da y'ar k'aramar k'oriya tare da k'anyen
magariyar ,
karb'a yayi da sauri ya tsiyayi zam-zam d'in cikin k'oriyar sannan ya d'auko ganyen magariyar
k'waya bakwai sannan ya zauna dirsham tare da tonk'oshe k'afafun shin cikin nitsuwa da cikar
tajwidi tare da tauhidi ya fara karanto addu'oi irin su,
Ayatulkirsiyu Qulhuwa Falak'i Nasi amanarrasulu tare da had'e yatul shifa baki d'aya yana tofi a
cikin ruwan zam-zam d'in .
Sannan ya kalli General d'in dake rawan sanyi kar-kar har hak'oranshi na bugan juna yasa
hannu ya damk'e cikin shi.
Cikin sanyi Bappa ya juya gefen Ramadan dake ta gyara rufewa General jiki da blanket cikin
tausayin su yace.
"Ramadan taima ka mishi ya zauna yasha ruwan zam-zam d'in nan."
"Toh" yace tare da yunk'urowa ya tallab'o Aliyu cikin dauriya General d'in ya zauna tare da
cewa.
"Zan iya fa ba sai an d'agani ba."
Mik'a mishi y'ar k'oriyar Bappa yayi tare da cewa.
"Kasha tare da bisimillah."
Kai ya gyad'a yayi bisimillah sannan ya k'afa kai ya shanye kab.
Yana ajiye k'oriyar a hankali ya fara yin gyatsa yana mai rik'e cikin sa sai gyatsan yakeyi ba
k'ak'k'au tawa tuni ya rink'a jin bugun zuciyar shi ya tsanan ta sai tsinke wan zuciya a hankali
rawan jikin shi ya k'aru amman kuma ya kasa konciya sai cikin shi d'aya damk'e da k'arfi yana
wani irin mik'a cikin juya kai ya damk'e hannun Bappa da hannu shi d'aya yace. "Bappa cikina marata zata fashe Bappa kaina na juyawa,
Bappa cikina."
Inna da yanzu ta shigo cikin mamakin ganin Aliyu ta matsoshi tare da cewa.
"Aliyu gadanga k'usar yak'i kaine,
Aliyu ina Bodd'i na ina take?."
Kai ya murza cikin zafi yace.
"Inna Bodd'i tana wurin iyayen ta Inna ga Ramadan shine shaida na bar Bodd'i gaban iyayen ta
na barta cikin lafiya na meda amanar da Bappa ya bani."
Fuska a karye Bappa yace.
"Habba Inna waziri ki barshi mana yaji da ciwon shi yanzu ki had'a min zuman nan da ruwan
d'umin