Showing 54001 words to 57000 words out of 81932 words
Chapter 19 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf
wasu sabbin iyaye wai natane me ya had'a Taraba da Kaduna me
ya had'a babarbare da ba fillatani tinda yasan Alhaji Ibrahim su barebari ne.
Tsaki ya ja da tuna wad'an nan abubawan,
cikin tsawa da hatsala yace.
"Kai Captain Sani zonan."
Shiko Captain Sani ido kawai ya zaro d'an tabbas yasan ya shiga tsaka mai wuya sannan duk
ta inda ya motsa shine shi kuwa yasan lallai anyi aure kan aure,
ciki bin umurni ya matso inda General d'in ke tsaye ya coge sai kad'an yar k'aramar bindigarsa
yakeyi.
Ita kuwa Ummi jin sautin muryar General ya k'ara tsananta bugawar zuciyar ta tana tuno woni
sautin murya irin na General sak hawaye ne ya k'ara wonke fuskarta tuno tun tana k'arama
rebonta da jin wannan muryar.
Ammi kuwa cikin kuka ta d'ago fuskarta tana kallon fuskar d'an nata cikin kuka ta rik'o hannun
Rayhana tare da cewa.
"Rayhana kalli fuskar d'an uwanku ji muryarsa ki kalleshi da kyau Rayhana dan komai nashi na
mahaifinku ne ba abinda ya rabashi da Abbanku,
farinshi tsawonshi fuskarsa muryarsa gashi kanshi sajenshi fushinsa komai nashi na
mahaifinmu ne."
Ido Rayhana ta zuba mishi cikin kuka tace.
"Ammi kenan Ramadan ma da Abban mu yake kama?."
Kai ta gyad'a mata cikin kukan.
Shi kuwa General Captain Sani na zuwa gaban shi ya juya cikin fad'a ya kalli Captain Garba da
muryar bada umurni yace.
"Kai Captain Garbage maza kwashi wad'an nan zugar sojojin da ka kwaso kayi woje dasu."
"Yes sir" Captain Garba yace tare da juyawa ya kalli sojojin yace.
"Ku shiga mu tafi."
Shi kuwa Captain Sani kai kawai ya sunkuyar cikin goga k'afarshi a k'asa,
shiko Dr ido ya tsurawa General ganin yadda ya murtuk'e duk annurin fuskarsa ya bace,
sannan ga Meenarl da ya ganin ta wani Sha jinjin jikinta ta nitsu a gaban shi tana wasa da
yatsunta,
a d'aya gefen kuma hankalishi ya tafi kan Amminshi goggon shi k'anwar Daddyn shi kenan can
kuma ga Ummi dake kuka tana kallon fuskar General d'in.
Shi kuwa General lips enshi na k'asa ya kamo ya matse lokacin da yaga sojojin duk sun tafi sai
shi da Abdul sai mutanen gidan,
cikin tsuke fuska ya kalli Captain Sani da yayi k'asa da kanshi rai a bace yace.
"Captain!."
Shiru Sani yayi dan a wannan yana yin fuskar General yana bashi tsoro ,
shiko General jin bai amsa mishi ba ya hatsala shi cikin zafi ya ware hannu shi ya zabga mishi
wani gigiceccen mari.
Cikin zafin Marin Captain ya d'aga kai murya a d'an sake yace.
"Na'am."
Meenarl ya nuna tare da cewa.
"Wannan wacece a gare ka ? kuma me had'inta da zuriyar Ku? me ya had'ata da yayanka Dr
Jabeer? asani nadai Ku musulmaine ni kuma musulmi ne! amman kaji Dr yana cewe Meenarl
matarsa ce? me ya had'a Taraba da Kaduna? meya maida matataaah matar Dr Jabeer?."
shi kam Captain Sani ya rasa bakin magana sai kai yake juyawa,
hakan ya hatsala General yasa shi ya rink'a zuba mishi maruka yana.
"Ina magana kana jina kayi shiru ko wani munafurcin ka koyo."
Barrister Lawan kuwa dashi da Abba da sauri suka zo Abba ne ya kamo Captain Sani shiko
Barrister cikin fushi da b'acin rai yace.
"Kai wanne irin tantirin ne? dame kake gadara? da zakazo har gidan da kasace musu yarsu
sannan kana dukan d'an gidan shin matsayin hauka ne dan kai General ne sai ka taka wanda
make so dan rashin tarbiya toh ka sani da Barrister Lawan kake ja ba sai na gaya maka ba duk
mara gaskiyar k'asran tsoro yake a had'a shari arsa da ni bare kai da na kamaka dumu-dumu
kasace min yar d'an uwana".
Daga nan cikin b'acin rai Abba ya jawo hannun Meenarl tare da nunata yace.
"General Aliyu wannan y'atace nine ubanta mahaifi."
Sai kuma juya yanuna Ummi tare da cigaba da cewa.
"Gacan maihaifi yarta,
inda kaje ka sace min y'ata kuwa gidan kakanninta ne ma haifan Aisha."
Cikin fushin ya bawa General labarin yadda ya auri Aisha da kuma sanadin zaman Meenarl a
can sannan ya karishe maganar da cewa.
" kuma na aurawa Jabeer ita yanzu a matsayin matarsa take."
Kai General ya rink'a juyawa tare da bugawa Captain Sani tsawa yace.
"Kai Sani Meenarl wacece a gareni????."
sannan ya kamo hannun Meenarl ya fizgota....
*Kuyi da wannan hak'uri sisters da nayi niyar yin mai yawa so inada wani uzurine*
By
*Garkuwar Fulani*
*BANDIRAWO* page
4⃣5⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
*Moh Allah hokki b'uri moh baba hokku*
*Masu tabba yata menene ma,anar BANDIRAWO? toh ga ma'anar BANDIRAWO na nufun
D'AN UWA ko Y'AR UWA duk yana d'aukar ma'anar BANDIRAWON*
Kusa dashi cikin tsawa yace.
"Meenarl dai matata tace! kuma matar auren sunnah aure na halal kuma da waliyinta wanda
shine madadin uba a gareta kuma aurene da aka d'aura da shaidu kuma ga Sani wanda ya
kasance d'aya daga cikin manyan shaidun,
batun y'ar kuce jikar Bappa ce ni duk bansan da wannan zancen ba,
dan amanarta aka bani Bappa ya bani amanarta cikin k'arfin guiwa da yak'inin zan rik'e amanar
shi yasa ya aura min ita."
Captain Sani ya kuma fuzgowa cikin hatsala yace.
"Shin Sani kurma ka zama ne ko ka manta lokacin da ka mik'a kudin sadikin Meenarl da hannun
ka?."
Kai Captain ya rink'a juyawa cikin sanyi ya kalli General yace.
"Kayi hak'uri oga tabbas ban manta ba tabbas lillahi ni shaida ne kan aurenka da Meenal."
Sai kuma ya juya gun Daddyn shi tare da kallon Abban Meenarl d'in yace.
"Daddy kuyi hak'uri wallahi tabbas General ba sace Meenarl yayiba aura masa ita Bappa yayi
kuma aure na suna bisa koyarwan Annabin mu,
Daddy kune kukayi kuskure kune kuka d'aura aure akan aure Daddy General Aliyu ba mutumin
banza bane kamar yadda kuke zaton ba,
Daddy ka tuna alkhairan General a kaina,
Daddy kasan General mai mutunci ne a gareni."
Shiru Captain yayi tare da tsurawa iyayen nashi ido cikin fahimtar wa,
amnan ina sunyi nisa bazasu gane ba,
Shiko Dr Jabeer cikin tafasan zuciya ya kamo hannun Meenarl ya fizgota jikin shi cikin tsawa da
harzuk'a yace.
"Kuji zancen banza maganar wofi General zaifi ma kyau kaja motarka kabar gidan nan,
dan fad'a kake cikin rashin gaskiya dan Bodd'i tawace matata ce,
in kai a sama ka sameta ni tun tana yar Babynta nake rainonta."
Hannu shi ya d'aura kan k'ahon zuciyarshi tare dacigaba da cewa.
"Meenarl da kake fad'i itace bugun zuciya ta tun tana k'arama nake dakon sonta a zuciya ta
k'anwata ce matata ce."
Daddy ne ya kalli General a fusace yace.
"Ina fatan dai kasan nan ba gidan ubanka bane ? so don haka ka b'ace min da gani yaro ba
tarbiya ancema yarinya yarmuce ka tsaya kana zuba mana rashin kunya."
Abba ne ya kalli General cikin takaici yace.
"Aliyu Meenarl y'atace kuma nine ubanta kuma ni zan aurar da ita nike da hakk'in zab'a mata
miji."
Sannan ya juyo ya kamo hannun Meenarl ya rik'e tare da cewa.
"Y'ata zomu tafi."
Janta yayi suka nufi cikin gida ita kuwa Meenarl sai juyowa tayi tana.
"Abba Hamma Haiydar baida lfy fa Abba d'an Allah Ku kaishi asibiti,
Hamma Sani kai kasan baida lafiya dan Allah ka gayawa Abban shi akaishi asibiti."
Sai kuwa ta juya gun Dr Jabeer dake binsu a baya tace.
"Ayyah Hamma Jabeer ka duba Hamma Haiydar wallahi baya da lafiya."
Ammi kuwa zuwa yanzu sautin kukanta ya cika wurin ita kuwa Ummi baki na rawa ta tsaya
gaban mijinta da yarta cikin sanyi tace.
"Wallahi Abban Bodd'i,
Aliyu mijin Bodd'i ne tabbas aurenta Bappa ya d'aura kubi abin nan a hankali."
A take fuskar Abba tayi jazir dan b'acin rai a fusace yace.
"Toh ya sakar min yata yaje ya rubuta mata takardar sakinta yaron da bansan iyayenshi bane
zan bashi auren y'ata waya san asalin shi tunda iya sanina ba a gaban iyayen shi yake ba."
Da k'arfi General ya rumtse ida nunshi cikin tarin bak'in ciki gaba d'aya ranshi ya gama b'aci da
zafin furucin da Alhaji Ibrahim da Barrister ke mishi,
lips enshi ya ciza cikin tafasar zuciya ya juya tare da damk'e hannu shi yace.
"Ni dai ba shege bane! ina da asalina! ina da ubana! kuma ni musulmi! ne kuma ni ba tantiri
bane! kamar yadda kuke fad'an! kuma ni ba b'arawo bane! bare na sace muku yarku! ga d'anku
Sani shi shaida ne a kaina! ba saceta nayiba!,
Meenarl kema kina sane ba saceki nayi ba?! Bappa da kanshi ya dan k'amin hannu ki a cikin
nawa!, dan Allah
Barrister karka sake cemin bani da asali! ina da Ubana! kuma ya raine ni! Uwata kuwa mutuwa
ce ta rebani da ita!!."
Zuwa yanzu nufashin Sa ya fara fizga cikin zafin rai ya fizgo hannun Abdul murya na carkewa
ya nuna Abdul tare da cewa.
"Ko a nan wurin ina da d'an UWA! gashi nan ba gidan marayu na rayuba! Captain Sani kai
kasan hakan!!!."
Cikin zafi da cushewar zuciya ya bud'e motarsa tare dasa Abdul a ciki shima ya zagaya ya
shiga ma zaunin direba cikin zafi ya fizge hannu shi da Ramadan ke rik'e dashi yana kuka
kamar yaro cikin kukan yake cewa.
"Hamma Haiydar kana da UWA mahaifiyar ka bata rasuba tana raye Hamma Haiydar ba Abdul
kadai bane d'an uwan ka a nan nima d'an uwanka ne ga Rayhana ma y'ar uwarka ce Hamma
Aliyuuu ga Ammin mu tana raye Hamma Haiydar Meenarl d'in kanta y'ar uwarka ce."
Ina General tuni ya rufe motar ya figi motar a guje yayi woje k'iris ya rege ya taka mai gadin su
gaba d'aya inda nunshi sun makan ce zuciyar sa ta cushe ba abin da yake cewa sai.
"Ammi na Meenarl Ammi na Meenarl itace ta fara cireni a halin da nake ciki na rashin ki,
itanma rashin ki ya jazamin rashin ta."
gudu yake kamar zai tashi sama.
Shi kuwa Ramadan ganin General ya fita ya sashi sakin kuka kamar yaro cikin kukan yazo ya
durk'usa gaban Abba da Hamma Jabeer sai ya saki wani irin kuka cikin muryar kuka yace.
"Ammi kiyi hak'uri ki gafar ceni nasan abinda zan fad'i zai b'ata miki rai yau zan gayawa su
Abba gaskiya."
Cikin kukan Ammi ta mik'ewa tazo gaban su cikin juya kai tace.
"A a Ramadan a a."
Kai ya juya cikin zubda k'olloh yace.
"Daddy kun ganin ko Abba kalli yadda y'ar uwarku ke kuka da zubda k'ollah kalli har kamar
numfashin ta zai yanke,
Daddy shin kasan waye General Aliyu ? Abba,General Aliyu Yaya nane d'an Ammi nane shine
d'anta na fari wanda ta haifa a gidan Abban mu shine d'an da kuka rabashi da uwarshi tun yana
d'an shekara 4 zuwa 5 gashi da kunnen Ku kunji yana fad'in mahaifi yarshi ta rasu alhalin gata a
gaban shi Amman bai ganeta ba kun rab'a UWA da d'anta dan laifin Abban mu ya saketa."
Ammi kam sai kawai ta yi cikin gida tana kuka cur-cur da hawaye,
shi kuwa Dr Jabeer cikin b'acin rai da tarin tausayin Ammin nashi yabi bayan ta.
Daga nan gaba d'aya suka shige cikin gidan,
A babban parlour Dr Jabeer ya samu Ammi tana zaune kan 1 str tana zubda k'ollah yana zuwa
gaban ta ya durk'usa cikin tsura mata ido yasa hannun shi ya goge mata k'ollah baki na rawa
yace.
"Ammi ke k'anwace ga mahaifi na Amman duk wani gata da UWA keyiwa d'anta ke kinyi minshi
tabbas ni nasan kina da wani d'an mai suna Aliyu Ammi wai da gaskene General Aliyu shine
d'an uwana Aliyu da kike fad'a min?."
Hannun Dr Jabeer ta rik'e murya na rawa tace.
"Jabeer General Aliyu d'an uwanka ne ka tuna fuskarsa ka kalli fuskar Ramadan."
Cikin sanyin jiki Abba da Daddy suka zauna jiki a mace Abba kam sai juya kai yake yi.
Captain Sani kuwa Kuka yake kamar ba soja ba tamkar yaro k'arami yana juya kai ya kalli
Meenarl yace.
"Habba ashe Hamma Haiydar d'an uwana ne jinina ne shi Meenarl ashe ke jinin Hamma Aliyu
ne shi yasa mukeyiwa juna wani irin kauna ashe kula da kauna da Jana a jiki da Hamma
Haiydar yakeyi ni d'an uwanshi ne shi yasa."
Gaban Daddy ya rarrafa yaje cikin kukan yace.
"Daddy General Aliyu akan Meenarl ya kusan nak'asa wannan d'an uwana nashi duk da su
basa son shi amman General shi maison y'an uwanshi ne,
Abba kune sana din sa General cikin kad'aici a rayuwar sa,
kullum sai yayi kukan rashin mahaifiyar shi ashe kune kuka maida shi maraya,
kalli ratar dake tsaka nina da General amman ba tare d'aya duba matsayin shiba ya jani jikin sa
Daddy kasan cewa a mata kan soja Aliyu yana mataki na 8 niko ina mata ki na 3 shi General ni
Captain amman ya zabeni a matsayin mai kasan cewa tare da shi."
A haka cikin kuka Captain Sani ya basu labarin tun zuwan su Gembu Membila har abinda ya
faru tsakanin Abdul da Meenarl har yadda Mama ke cuszuganawa General d'in da yadda yayi ta
lura da Meenarl da bata kariya har zuwa kan ciwon da yake kwana dashi.
ya k'ara da cewa.
"General bashi da kowa ba wanda yasan halin da yake ciki nima Meenarl ce ta gaya min sai
kuma lura dashi da nakeyi."
Ramadan ne ya mik'e cikin kuka yace.
"Ammi kiyi hak'uri Daddy Ku gafar ceni nagode da kulawar ku nasan zafin abinda Abban mu
yayiwa Yar uwarku ne yasa kuka k'i yafe mishi,
toh ni kam da Rayhana mun yace mishi kuma ni zan tafi gun mahaifi na da d'an uwana zanje na
kula dashi zanje na jinyacesa zanje na d'ebe mai kewa zanje in cireshi cikin kadaici zanje na
gaya mishi Ammin shi tana raye kuma tana sonshi."
Daddy kam shiru yayi cikin kuny'ar uwar tashi shiko Abba tuni sai k'ollah yake dan dama
Barrister ya fishi zafi.
Ita kuwa Meenarl tuni ta koma jikin Hajia Amina ta rakub'e sai sautin kukanta dake tashi,
Dr Jabeer kuwa hannun Ammi ya rik'e cikin lallashi yace.
"Ammi kibar kuka insha Allah farin cikin ya dawo gareki."
Ummi kuwa kuka take tana maison kara ganin fuskar General sai yanzu ta gano dalilin da yasa
take son Ramadan ashe kama take ganin yanayi da d'an uwanta amman sai yau taga kamar da
tafi na Ramadan d'in,
cikin kukan ta bawa Alhaji Ibrahim labarin yadda sukayi da Bappan ta kuma fad'i dalilinta na
hana Bappa ya gaya mishi.
Ramadan kam juyawa yayi ya mik'a wa Rayhana hannu cikin sanyi yace.
"Rayhana muje ga d'an uwanmu yana buk'armu a kusa dashi."
Hannu ta mik'a mishi suke nufi woje Captain Sani ma mik'ewa yayi cikin share k'ollah a fuskar
shi yace.
"Daddy nima zan bi su Ramadan zanje gun Hamma Haiydar."
Shiru iyayen nasu sukayi har suka fita basuyi ko motsiba.
Kai tsaye gidan su General suka nufa,
suna zuwa bak'in k'ofar get d'in Captain Sani yayi ta dannan hon Amman shiru mai gadin ya
lek'a sai ya koma ya share su cikin hatsala Captain ya fito yazo inda yake yace.
"Sajen ka bud'e min get."
Cikin girmamawa Sajen din yace.
"Oga yace kar a sake barinka ka shiga gidan nan."
Kai ya kad'a cikin tausayi dan yasan yau ba mai tausar General d'in ,
su Ramadan kuma da ya gaya musu cewa sukayi .
"Mu banza mubar k'ofar gidan nan ba wallahi anan zamuyi ta zama har sanda zai fito."
Haka kuwa suka coge a k'ofar gidan har zuwa dare in lokacin sallah yayi suyi sallah a
masallacin k'ofar gidan.
Ita kuwa Meenarl Dr Jabeer ya tare a gidan yana ta cikata da salon wasan d'aya saba tuni ta
sake suna ta hira da dariya Ammi kuwa yayunta sunyi ta lallashin ta duk da hakan,
ita kam Ammi har yanzu hankali ta na kan d'an ta.
10:00 pm Meenarl dake zauna gaban Hajia Amina da Ammin ,
tayi wani irin razana cikin zaro ido ta dafe kirji gaba d'aya jikin ta na rawa tace.
"Momy Hamma Haiydar wallahi daga yanzu ciwon shi ke tashi."
Shiru Ammi tayi tare da sunkuyar da kanta k'ollah na zuba.
Hajia Amina ce tace.
"Insha Allah yau zai samu sauk'e kinga Dr Ramadan yana can gun shi."
Ita dai kife kanta tayi cikin cinyoyin ta.
Shi kuwa General Aliyu tunda ya figi mota ya fito gidan su Meenarl ko idanun shi basa ganin
cikin ikon Allah ya kawosu gidan lafiya,
yana yin parking ya bud'e mota ya nufi cikin gida yayin da Abdul kuwa ke binshi a baya cikin
tausayawa hak'ik'a yau zuciyar shi ta cika da tausayin d'an uwan nashi a fili yace,
"Hamma Aliyu Allah ya kawo ma farin ciki a rayuwar ka."
Shi kuwa General yana shiga gidan kai tsaye part ensu ya nufa a parlour su ya zame cikin
kuncin rayuwar ya kife kanshi kan kujera ya rink'a kiran.
"Ammi! Ammi! Abba! Abba! me yasa baku tuna makomata ba gashi a yau an wayi gari ana
shirin shegan tani,
Ammi na me nayi mik'a ni kuwa da kika manta ni,