Showing 51001 words to 54000 words out of 81932 words

Chapter 18 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf



Ammi kuwa da Rayhana cikin kad'uwa da tsantsar Happy suka nufi gaban Meenarl d'in.

Ita kuwa Meenarl tana ganin Ammi ta saki Ummin ta cikin kaunar k'anwar mahaifin nata ta
rugume Ammin baki na rawa tace.
"Ammi na ina Hamma Jabeer na Ammi ina yake ban ganshi ba."

Ita kam Ammi sai dariya take da hamdala shi kuwa Ramadan cikin had'a fuska da yanayin fushi
yace.
"Bodd'in Bappa wato ni bakiyi kewa taba?."

tana jin muryan Yaya Ramadan d'in nata ta juya gunshi cikin murna da salon su na wasan d'an
Goggo da y'ar kawu ta mik'a mishi hannu suka tafa tare da cewa.
"Kai Yaya Ramadan ai kasan Hamma Jabeer na shima yana sona."

Ita kuwa Rayhana ture baki tayi cikin kaunar k'anwar tata tace.
"Ai dama ni na sani Bodd'i ni da Hamma Sani baki wani damu da muba."

Da sauri ta saki hannun Ramadan ta rugume Rayhana cikin fara'a tace

"Anty Rayhana inason ku wallahi duk da bansan Hamma Sani ba ina son shi a raina."

Gaba d'aya haka suka cika da tsantsar farin ciki da murna.
Nafeesat kuwa ta bushe a tsaye.

Abdul kuwa Barrister Lawan yace a dakashi har sai ya fad'i wanda ta saceta tunda shi yace ba
shi ya kawo ta garin Kaduna ba.

Cikin azaba da rad'ad'i Abdul yace.
"Wallahi ni ba satota nayi ba d'an uwanane ya satota shi ya kawota gidan mu san ina ya
samota ba yace matarsa ce kuma wallahi zai kasheni in ban maidata gida ba kuyi hak'uri zan
kirashi zai zo."

Cikin tsawa Captain Garba yace.
"Maza kirashi ."

Jiki na rawa ya zaro wayarsa dake cikin aljihun wonddon shi ya kira General,
Wanda a lokacin ya fito office nashi kenan zai koma cikin Kaduna,
kamar bazai amsa kiran ba sai kuma ya d'an zaro woyar a aljihun yinifon d'in nashi ,
ganin Abdul ne ke kiranshi ya d'an yi mamaki sai kuma ya d'aga kiran tare da cewa .
"Uhum."

Shi kuwa Abdul cikin kuka da tsoro yace.
"Hamma Aliyu zasu kasheni sun kamani sun k'wace Meenarl wai yarsu ce sun saceta Hamma
Aliyu kazo karsu kasheni su kashe Meenarl."

Cikin tsananin fushi da hatsala yace.
"Kai banza kamin bayani su waye ne? kuma a ina suke? a ina suka samu Meenarl d'in? yanzu
kuma ina? banza kayi min bayani."

Cikin tsoro yayiwa General bayani da kwotoncen gidan,
su kuwa Captain Garba tuni sun cika gidan da sojojin da y'an sanda,
suna shirin cin uban wannan Hamma Aliyun da Abdul ke kiran.

Shi kuwa General cikin zafi da fushi ya kalli yaranshi dake binshi a baya yace.
"Tafiya Kaduna zamuyi Ku fito da sauri."

Binshi a baya sukayi cikin gudu suka shishshiga motacin nasu sannan suka nufi cikin Kaduna .

Shi kam General gaba d'aya a hatsale yake hakan yasa ya gane kwotoncen Abdul amman sam
bai tuno da cewar wannan gidan da akayi mashi kwotoncen d'in gidan su Captain Sani bane har
suka shiga shiga cikin gidan.

Dai-dai lokacin Captain Sani kuma ya fito harabar gidan.
A dai-dai lokacin kuma General Aliyu Abubakar Rumoh ya bud'e motarsa cikin cikar haiba da
sura ya fito,

Tsayuwar motar tasace taja hankalin mutanen wurin baki d'aya,
Ramadan da Rayhana kam wani irin farin ciki ne mara adadi ya rufesu yayin da Ammi kuwa tuni
ta zuba mai ido fuska cike da k'ollah sai kirjinta dake harbawa.

Hajia Aysha kuwa mahaifiyar Meenarl Ummi kenan,
ganin Aliyu ya razanata ya cika mata zuciya da zulumi dan tunda yake zuwa basu tana kad'uwa
ba,
Ido ta zuba mai tana kallon kwayar idanun shi dai-dai lokacin...



By
*Garkuwar Fulani*

By
*Garkuwar Fulani*



*BANDIRAWO* page

4⃣1⃣to4⃣2⃣

Na
*Aysha Ali Garkuwa*







*La shakkah Moh Allah wuju furd'ata wallahi Moh Allah seini b'uri sembe innu adamajo suna
d'um*



Lokacin da ya fito ya tsaya fuska a murtuk'e,
shi kuwa Abdul yana ganin shi ya mik'e cikin wahala ya nufeshi tare da cewa.

"Hamma Aliyu zasu kasheni zasu tafi da Meenarl."

Alhaji Ibrahim kuwa ido ya zubawa Aliyu cikin mamaki tare da cewa.
"Kana nufin shine ya sacemin yar tawa?."
Shi kuwa Barrister Lawan cikin tsantsar hatsala ya kalli tarin sojojin dake gabansu yace.
"Maza Ku juya kuje ku canzawa wannan d'an banzan kamannin Ku sumar min dashi asume
nakeso ku fita dashi daga cikin gidan nan."

Juyawa ya kuma yi a hatsale ya kalli Captain Sani da yake tsaye cikin kullewar kai da cushewar
tunani ya zama tamkar wani soko,
ido yake bin Meenar da Rayhana yana zaro ido woje shi baima lura da oganshi da ke tsaye ba
cikin murtuk'e fuska.
Tsawa Barrister ya buga mai cikin takaici yace.
"Kai Sani tsayuwa kayi yanzu nake so ku koyawa wancan hankali.

Su kuwa sauran zugar sojojin da yan sandan gaba d'aya cikin zafin nama da hatsala suka nufi
inda General yake tsaye ya hard'e hannuyen shi a k'irji ya koma ya jingina da jikin motarsa tare
da hard'e kafafunshi ya coge cikin isa.

Shi kam Abba shiru kawai yayi yana kallon yadda sojojin suka nufi General d'in da gudu,
shiko Barrister Lawan cikin fushi yake basu umurnin su bugeshi sai sun sumar dashi.

Suko sojojin da sukazo da General sun san duk masu nufo kansu d'in yaran General d'in.

Ita kuwa Ammi hannu tasa ta dafe k'irjin ta fuska cike da k'olloh gaba d'aya jikinta na rawa,
Shiko Ramadan wurin General d'in shima ya nufa Rayhana kuwa Ammi ta matso cikin rawar
murya tace.
" Ammi kin ganshi ko kinga Hamma Haiydar d'in ko."

Itako Meenarl gaban Umminta ta koma tana kallon yadda Ummin ke juya kai tare da kad'uwa.

Gaba d'aya sojojin suna zuwa gaban shi suka yi wani irin tsayuwa a tare cikin mugun tsoro suka
d'ad'd'aga hannu suka sara mashi tare da buga k'afafunsu a k'asa,
ji kake rib-rib suna "yes sir ".

Mamaki ne ya rufe Barrister ganin duk sunje suna saramishi sun k'ame k'am sun tsaya a gaban
shi cikin yana yin suna jira ya basu umurni su aikata.

Shi kuwa Captain Sani da Captain Garba sai ido suka tsurawa juna cikin tsoro,
Barrister kuwa ganin Sani na tsaye gim yasashi hatsala cikin fushi ya juya gun Sani da Garba
yace.
" wai shi waye shi da Ku sojoji bazaku aikin ku a kanshi ba ko shi yafi k'arfin doka shine fa ya
sace Amina,

shiwaye a k'asarnan?."

Cikin yin k'asa da murya Garba yace.
"Shine Brgdl General Aliyu Abubakar Umar Rumoh soja mai kula da rund'unar sojojin na k'asa
baki d'aya."

Tsaki Barrister yaja cikin takaici yace.
"Wannan mai halin sace yayan mutane shine wai aka bawa wakilcin tsaron wannan k'asa
tamu?,
an bashi daman aikata b'arna son ranshi,
yaro ne aka d'auki wannan matsayi aka bashi ba dole ya maida mata abinda yaga dama ba,
tunda ya samu dama ga k'uruciya ga matsayi ga kud'i ga kyau ga rashin mafad'i dan wannan da
ganin shi zaiyi taurin kai da izzah."

Shi kam Sani baki ya sake cikin mamaki da rashin ganewa yace.
"Daddy General me yayi muku?."

Cikin tsawa Barrister yace.
"Shine ya sace Amina yar uwarka banza mara tunani kana tare dashi baka San ya sacema yar
uwa ba."

Ido ya sake fiddawa cikin rud'u yace.
"Daddy ina Aminan take?."

Zuwa yanzu Barrister ya gama hatsala cikin fushi ya yarfawa d'anshi Captain Sani wani irin
gigiceccen mari tare da janyo hanna yenshi fiii har zuwa gaban Meenarl dake tsaye gaban
Ummi,
cikin nuna Meernal d'in Daddy yace.
"Sani ga Aminan gatanan itace Aminar itace yar uwarka da muke ta nema itace yar d'an uwana
Ibrahim wacce take Gembu Membila."

Kai Captain Sani ya rink'a juyawa cikin zama wani soko yace.
"Daddy wannan itace Amina yar uwata?."

Kai Daddy ya gyad'a mai tare da kallon Meenarl wacce ta tsurawa Sani da Daddyn ido fuska
cike da alamun tabbaya,
shiko Barrister cikin kula yace.
"Amina ga d'an uwanki Sani wannan shine Hamma Sanin naki."

Ido suka tsurawa juna cikin mamaki shiko Sani tsoro da firgicin me zai faru anan gaba kad'an,
naunauyan
ajiyar zuciya ya sauk'e ido cike firgici baki na rawa yace.
"Daddy kenan Amina itace Bodd'in Bappa sannan itace Meenarl matar ogana General Aliyu

Abubakar Umar Rumoh?,
Daddy ya akayi haka ta kasance ina mafita? sannan kuma Amina itace watar Hamma Jabeer
na? Daddy kaina kulle na rasa tinanina kamin bayani."

Ido Daddy ya tsura mai cikin jin haushin d'an nashi yace.
"Sani kana nufin dama kasan inda Amina take har kana cewa matar oganka ne?."

Kai ya gyad'a tare da cewa.
"Ehh Daddy nansata muna tare da ita tun randa aka d'aura aurenta da General."

A hatsale Daddy ya rink'a yarfawa Captain Sani maruka masu zafi da gigitarwa har sai da
hankali mutanen wurin kab ya dawo garesu.
Sannan Barrister yace.
"Ashe baka da imanin d'an uwana da taka yar uwar da d'an uwanka kana sane Ibrahim har
ciwon zuciya ya kamashi sakamakon batan wannan yarin yar sannan kana ganin halin da d'an
uwanka ke ciki.
amman wai kana cemin kuna tare wuri d'aya ka barmu cikin rud'u har kuma kana cemin matar
ogan kace ita,
waye aura masa ita su waye masu aurar da ita a duniyar nan bayan mu,
ya sato yarinya yazo yana cema matarsa ce."

Dafe fuska yayi cikin rawan murya yace.
"Daddy ka manta ni bansa Amina ba ban tab'a zuwa garin da takeba kuma ko pictures d'in ta
tun nayarin tane na sani."
Mari Daddy ya kuma watsa mishi cikin nunashi da yatsa yace.
"Kalli fuska Rayhana ka kalli fuska Amina ko makaho in yashafa yasan yan uwane ,
Amman da yake kai kifeffen mutum ne mai karamar basira ka kasa gano hakan ,
sannan inma baka gane da kamannin su ba ,
Ina pictures d'in Amina da aka baku d'an nemota suma duk basu ganar da kai ita bace?."

Kai yaci gaba da juyawa tare da cewa.
"Daddy wallahi tallahi ban tab'a lura da kamannin Rayhana da Amina ba sai yanzu da ka fad'a,
batu pictures d'inta kuma wallahi tallahi Daddy ban kalli pictures d'in ba d'an muna fita na bawa
General su a hannushi kuma shima wallahi bai gansuba d'an a hannun Captain Garba ya
dank'a hotunan."

Alhj Ibrahim ne ya rik'e hannun Barrister sanda ya d'aga hannu zai kuma yarfawa Sani mari
cikin damuwa da kullewar kai yace.
"Yaya Lawan barshi haka wannan magana akwai rikici a cikin ta dole mu barshi ya mana bayani
a hankali."

Ita kam Meenarl sai ido take zarewa cikin mamaki ,
Ammi kuwa kuka kawai takeyi jin wani rikicin da ya had'e da d'anta da yar d'an uwanta ido take

rumtsewa jin mugayen furucin da yayanta Lawan ke yiwa d'an nata sai kuka take tare da
sheshshek'a Rayhana na share mata k'ollah itama fuskarta cike da hawaye ,
Ita kuwa Ummi mahaifiyar Meenarl kuka takeyi tare da nuna General tana.
"Wayyo Innata ina kike zoki ga wata fuska mai cike da kamannin fuskar da kike begen ganin
tsawon shekaru."

Ammi kuwa zuwa yanzu ta durk'usa har k'asa tana fidda sautin kula mai cike da k'unan rai.


Shi kuwa General cikin tsuke fuska ya d'aga hannu tare da yiwa zugar sojojin alama su bashi
hanya,
a take suka yi layi tare da sara mishi.

Taku d'aya yayi zuwa biyu yaci karo da Ramadan dake nufoshi cikin tsuke fuska ya tab'e baki
tare da ci gaba da tafiyan ,
shiko Ramadan binshi yayi a baya cikin sanyi kamar rad'a yake cewa.
"Hamma Haiydar ni d'an uwanka ne! ni jinin kane! kalli can gacen mahaifiyarmu! da yar uwarmu
Rayhana! Hamma Haiydar ina mahaifinmu? Hamma Haiydar nida Rayhana muna begen
mahaifinmu."

Shiru yayi cikin son yaji abinda yaron ke fad'a da kyau d'an bai jishi da kyauba.

Shi kuwa Ramadan matsoshi yayi cikin sanyi zayyi magana kenan,
ita kuwa Meenarl ta juyo garesu,
cikin mamaki ta nufu gaban General cikin d'an d'aga murya tace.
"Hamma Haiydar kazo?."

Ido kawai ya tsura mata cikin mutuwar jiki dan kamannin Rayhana da Meenarl din ga
maganganun wanna yaron da suke tsananin kama dashi.

Tana isa inda yake hannu shi ta kamo cikin happy tace.
"Hamma Haiydar zo zokaga mamana da babana ga zuriyata baki d'aya Hamma Haiydar ashe
Captain Sani Yaya nane d'an uwanane shi shine Hamma Sani na k'anin Hamma Jabeer d'ina
gacan goggona k'anwar mahaifi na ga Yaya Ramadan da Anty Rayhana."

Su Alhaji Ibrahim da Barrister kam da Hajia Amina binsu da ido sukeyi cike da mamaki.

Dai-dai lokacin Dr Jabeer yayiwa harabar gidan diran mikiya cikin wani irin yanayi yayi parking,
marfin motar ya bud'e tare da fita da sauri tin kafin ya k'arisa fitowa yake kiran Meenarl yana.
"Bodd'i na inaki ne bangan ki Bodd'i na Hamma Jabeer naki ne ke kiranki."


Gaba d'aya hankalin su ya koma kanshi ,

ita kuwa Meenarl cikin tsananin happy ta sake hannu Aliyu tare da yin tsalle da gudu ta nufi inda
Dr Jabeer yake ,
tana zuwa ta mik'a mishi hannu ,
shima hannun ya mik'a mata tafin hannun su suka had'e wuri guda Dr Jabeer d'in yasa
yatsunshi ya rumtse nata da k'arfi lokacin d'aya kuma suka yi..

Shi kuwa General idonshi ya rumtse da k'arfi......


By
*Garkuwar Fulani*


*BANDIRAWO* page

4⃣3⃣to4⃣4⃣

Na
*Aysha Ali Garkuwa*





*Wannan shafi sadaukar wane ga mahaifiyar y'ar uwarmu (Feedo Deedo y'ar ficika) Allah ya
jik'an Ummah Allahu yasa ta huta muko in tamu tazo Allah yasa mu cika da imani*




*Resa tum! mara tum! heb'a tum! seya tum!*



*Happy birthday 2 youuu my lovely Sadnaf Allah ya k'aro shekaru masu albarka*





Sai ya kuma bud'e idon nashi ya tsurawa Meenarl da Dr Jabeer d'in ido.

Shi kuwa Dr Jabeer jawo hannun Meenarl yayi suka d'an sunkuyo sai yasa hannu shi ya d'an ja

k'afan wondoshi ya d'an nad'e tare da cire takalmin k'afar,
itama cire takalmin tayi sannan ta d'an janye siket d'in ta sama kad'an ta rik'e da hannu d'aya,
matsota Dr Jabber ya kumayi tare da manna k'afarsa da tata k'afar suka dai-dai ta yatsun
k'afafun nasu,
hannuta da yake cikin nashi ya kara rumtsewa tare da juyowa suka kalli juna murmushi yayi
cikin wasa da kulawa da yanayin da suka saba duk randa suka had'u sai sunyi haka sannan su
nad'e k'afa d'ad'd'aya sama kad'an sai su d'an yi taku biyu zuwa uku cikin sigar wasa da
shak'uwa.
Ita ma murmushi tayi tare da cewa.
"Hamma Jabeer inka fad'i sweet lede-leda zaka seyo min."
kai ya gyad'a mata sannan cikin wasa suka d'aga k'afafun nasu a tare sukayi taku d'aya ana
biyu suka dire tare da sauk'e ajiyan zuciya sai kuma ya juyo gareta ya mik'a mata hannun suka
tafa tare da yin murmushi.

Wannan itace d'abi'ar Dr Jabeer ko ince al'ada matuk'ar suka had'u sai sunyi wannan abin dan
Dr tuk'uru yake biyewa Meenarl ya zama kamar abokin wasanta na yarinta.

Suna yin hakan sai ta kuma jawo hannu shi da k'arfi har kamar zai fad'o kanta cikin tura baki da
salon wasa tace.
"Zo nan Hamma Jabeer zo muje ku gaisa da Hamma Haiydar."

Dariya Dr yayi tare da cewa.
"Wayyo Bodd'in Bappa kinyi k'arfi har zaki kada Hammanki a k'asa."

Sai kuma ya kalleta yadda take janshi tana ta dariya har dimful dinta dake tsakiyar d'an
gemunta yana lotsewa.
kallon ta Dr yayi cikin kula da tsantsar farin ciki yace.
"Har wani Hamma Haiydar kika samu bayan mu duk bamu isheki bane?."

Ita dai janshi tayi har zuwa gaban General wanda ke tsaye tamkar an dasashi ko ido ya kasa
k'eftawa mamaki cike a ranshi "ashe dama Meenarl tana dariya haka? ashe tana da surutu?
ashe ita mai faram-faram ce? ,
kenan shine ya maidata shiru-shiru kenan shine ya cika zasuyar ta da tsoro ta zama ko yaushe
a firgice take.


Su Barrister kuwa da Abba ido suka zubawa General da Ramadan dake tsaye gefen shi kamar
su ta k'ara fitowa ras.

Shiko Dr Jabeer yana zuwa cikin happy da yanayin godiya da jinjina ya mik'awa General hannu
suka gaisa shi a zatonsa General ne ya gano mishi Meenarl d'in,
shiko Aliyu hannun kawai ya bashi cikin sakewar jiki yake binsu da kallo yana sauraron abinda

Dr yake fad'i.
" A gaskiya General Aliyu bani da baking yi maka godiya ko nuna farin cikina a gareka ba
abinda zance da kai saidai ince Jxkllahu bil jannah nagode ka gano min matata farin cikina."

Ido ya kuma fitarwa woje baki cikin sanyi yace.
"Matar ka? matarka kuma?."

Hannun Meenarl Dr Jabeer ya kuma jawowa cikin yanayin farin ciki yace.
"Eh matata ce kuma k'anwa tace jinina ce ita kuma tintini an d'aura mana aure da ita."


Cikin murtuk'e fuska da b'acin rai ai shi a ganin shi wannan ma ai rainin hankali ne tunda dai shi
yasan Meenarl aurenta aka d'aura mai kuma mahaifinta ne ya auramai ita kuma a can taraba
cikin dajin gembu Membila iyayenta fulanin daji masu kiwon shanu ma zauna cikin riga,
sannan ya kuma za ace ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login