Showing 3001 words to 6000 words out of 81932 words
Chapter 2 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf
Jaligo a hankali yace,
"Canma garin fulanine "
forko babban lokal gmt esu ya kafawa ido *Gembu* ya fad'i
tare da sake cusa kai cikin babban lardinsu can qasa gefen yaga *Membila*
daga qasan shi kuwa sai sunayen rigar fulanine dake zagaye da dutsen membilan cikin sa'a
yayi tozali da *Rumoh* garin mai cike da Fulani makiyaya ga dutsen membila daya zagaye su
yayi musu qawanya daga bayan su kad'an kuma kokin membila ne zagaye dasu,
sai babbar gadar da akayi daga saman garin nasu gadar babban sai dai ta kata koce yayin da
rigar Rumoh ta kasan ce a bakin gaba bayan garin kuwa dutsen membila ne d'aya kasan ce
farin ciki ga d'aukacin al'ummar wurin ya kuma kasan ce abin ziyartar turawa da baqaqen mu ta
yadda ya zama lardin wurin ya zama babbar hanyace konce kan dutsen hanya mai salon tafiyar
maciji yayin da qasan kuma kogine gefen kuma tabki ne mai girma gaske can daga saman su
kuma forres iya ganin mai kallo,
garin Rumoh kenan da Aliyu ya gama binci ke a cikin Sa,
dukda bai gamsuba Amman ya gudurta tafiya cikin kwana nan biyu masu zuwa yashirya tafiya
tun kan hutun shi ya qare!..
Haka Aliyu yayi ta shiryer-shiryen shi shi kad'ai ba tare da neman shawaran kowa ba sai Baba
da yacewa an turashi taraba wani bincike.
Daga manya shi biyu kuma a wurin aiki an bashi pars na tsawon 2 weeks.
Yau jummah tun safe Sani ya had'a kan sojojin da zasuwa Aliyu rakiyi Wanda an hadasu da
sabbin Hilux dan sanin hanyar da zasu dosa hilux 6 da sojojin 27 aka had'a sukayi sammako
tun sanyin safiya suka nufi hanyar Adamawa Yola,
yayin da shiko Aliyu da Sani jirgi zasubi zuwa cikin Adamawa dan babu na Taraba,
sai na Kaduna 2 Yola suka samu hakan yasa sai dai su diro jihar Adamawa daganan su ma
tawagar sojojin dake ta howa a motocin sun iso daga Yolo sai su kama hanyar Taraba da mota.
Su sun tashi tun safe,
suko sai 4 na yamma jirgisu ya tashi zuwa Yola.
4:25 pm jirginsu yayi diran mikiya cikin..!!!!!!
By
Garkuwar Fulani
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*BANDIRAWO* pg 3β£
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*pure moment of life writers*
P.m.l.w
jirginsu ya dira cikin International
Airport na Yola,
bayan d'an wani lkcin matafiyan suka rinqa fitowa d'aya bayan d'aya,
cikin sanyi General Aliyu ya zuro qafarsa tare da shaqar iskar garin Adamawa Yola ,
Sani na biye dashi a bayan shi cikin salon shi na murtuqe fuska suka sauqo yayin da
Airport din ya ke cike da sojoji maqil,
domin ko ya samu tarba daqa shugaban sojoji na jihar Adamawa tare da tarban fadawan
masarautar Sarki Muhammad barkind'o,
don karramawa ga jarumin dake sadaukar da ransa domin baiwa qasarsa kariya.
Kai tsaye daga Airport din cikin Yola suka nufa domin kai gaisuwa ga Sarki Muhammad,
daga nan kuwa barrack suka dawo inda nanma suka gaisa sama-sama daga nan suka fito suka
kama hanyar Taraba.
Tafiya suke cikin gudu dan su samu su isa da wuri
tunda Yola 2 Taraba tafiyar awa 3 ne
bare su suna tsula gudu,
uwa uba kuma su duk inda suka biya basu hanya ake,
shi yasa 9:00 pm suna cikin birnin Taraba jaligo ja gari na baba Abasu.
Barrack din suka wuce tare da tarbar mutanen jihar
a barrack din ya diro sauran sojojin yayinda ya fita shida captain Sani suka wuce jummu hotel
dakin Sani na qasan nashi ,
shi kad'ai ya tare a dakinshi daga shi sai tunanin shi da ya cika mar rayuwa wonka ya samu
danyi sannan yazo ya kwanta tare da jawo laptop enshi ya fara aiyukan shi tare da banda
umurni ga sojojin da suke qarqashin sa,
haka dai baiyi bacci ba har zuwa 12:30: Am sannan ya d'an rumtsa.
Kashe gari suna idar da sallah suka kammala shirin su suka kama hanyar Gembu,
Tafiya mai dad'i hanya mai cike da abin al'ajibi hanya mai tarin abin sha'awa hanyar da duk
fad'in qasarmu ta Nigeria bamu da irinta
hanya mai cike da tsirrei da qoramu da koguna da lambuna tare da sanyi mai dad'in ji yanayi
mai sanya sanyi a zuciyar bani Adama
hanyar Gembu 2 Membila kenan.
Shi kam Aliyu zaune yake a bayan yayinda yake tsurawa dajin ido mamaki
yake ganin yadda fulani sukawa dajin qawanya duk inda ya cillah idonshi dabbobi yake gani bila
adadin sai mata masu fasa cikin dajin da qoren nono da ka shigo sashin wurin zakaga banbanci
matan wurin da sauran matan sauran jihohinmu wannan ba shati fadi bane
matan Gembu sunyi zarrar da tasa sunka doke matan kamaru ma
Kyawun halitta haiba cikar zati uwa uba tsafta duk wanda yasan matan Gembu ya sansu tamkar
larabawa suke
fararene tas masu yalwar gashi suna da sura ta haqiqa.
10:00 Am
Suna cikin garin Membila daga nan
Aliyu ya tsaya tare da tara yaran shi cikin sanyi,
ya tsura musu ido d'aya bayan d'aya
da salon bada umurni yace.
"Sani daga nan su Garba zasu tsaya ni da kaine zamu qarisa cikin dajin domin saimun ga
yanayin wurin sannan mu shigo baki d'aya".
Cikin bin umurnin suka sassara mai tare da qamewa daga nan,
ya jaqoran cesu zuwa tantin sojin dake kula da dajin Membila sabida yawan kashe fulanin
wurin da akeyi.
Sai da ya tabbatar ya sama musu duk abin buqata,
sannan suka wuce shida Sani.
Tafiya ma budin ilimi taken Mahmoud Nagudu,
Tafe suke Sani na mishi hiran yanayin wurin tare da nuna mai tsirrai masu ban sha'awa,
shi kam Aliyu bin hanyar yake da ido cikin mamaki tabbas hanyar Membila abin kallone da bada
mamaki,
tafiyar suke Sani tun yana surutu har yayi shiru.
Cikin sanyi ya kalli Aliyu tare da cewa "Oga inaga daga kan dutsen nan hanyar ta tsaya ba ci
gaba sai waccar hanyar da muka wuce".
Kai ya d'an juya tare da cewa ka zagaya bayan dutsen nan ta gefen dama akwai y'ar qaramar
hanya tabin shanu sai mubi ta wurin"
Haka suka kutsa cikin dajin yayinda suke ta ratsa tsaunuka wani wurin badan Hilux bane da
bazai fitaba.
Wasa-wasa sukayi yawo cikin tsaunu kan duk ya zagaye rigar Fulani dake ta wurin baiga rigar
Rumoh ba,
gashi da zaran sun tsaya a wasu rigan dan sunyi tabbaya sai su samu ba maza sai mata matan
ma yara dan mazan sun tafi kiwo matan ko sun tafi tallar nono shiyasa sai yara suko da yaran
sun gansu da yinifon din sojojin da bindiga a hannusu sai su gudu.
A hakan har d'imuwa ta fara dibarsu cikin jarumta Aliyu yacewa sani
" Muyi gaba gancan wani ma ki yayin".
suna zuwa gunshi daga d'an nesa dashi sukayi parking sannan suka fito tare da cire rugunan
jikinsu suka bar best sannan suka qarisa gunshi cikin sanyi dan gudun kar ya tsorita Aliyu yai
gyaran murya tare da cewa.
"Akuma *BANDIRAWO*, noi layde e dabbaji men"
Sannu dan uwa ya daji da dabbobin mu"
Cikin mamaki ya juya gunsa tare da yin magana cikin fillanci yace .
"Ra ga Allah Surbajo toi yiftu d'on Mi hetayi on"
Kai d'an Saurayi ina kuka fito ban ganeku ba"
Daga nan kuma sukaci gaba da magana cikin fillanci yayinda Sani ko ya bushe a tsaye mamaki
yake wai ase dama General Aliyu ya iya fillanci ji yadda ya juye kamar cikin su yake rayuwa shi
kam sai murmushi yake dan tabbas Aliyu ya burgeshi ase akwai masu adana yarensu dan irin
wannan ranar.
Suko Aliyu zuwa yanzu d'an fullo har ya masoshi tare da rik'o hannushi ya miqa mai sanda cikin
fillanci yace.
"Ko zakayi kiwo?"
Ba kin shi kawai ya d'an motsa alamar murmushi sannan yace .
"Yanzu dai tabbaya muke sai wani jiqon in na kuma zuwa sai muyi kiwon ko".
Ido ya tsurawa fuskar Aliyu tare da cewa.
" kai ko bakayi fillanci ba wlh zatinka ke muna kai asalin ba fulatanine gaba da baya,
dan haka ba matsala menene tabbayar?".
Ajiyar zuciya ya d'an sauqe tare da yamutsa fuska yace .
"Rigar Rumoh nake nema".
Cikin tsoron ya zare ido tare da ja baya gani da nunashi yana fad'in.
" kodai kune mutannen birnin nan da kuke zuwa kuna korar mutanen rigar Rumoh! kuna kashe
su! kuna kama musu yan matan su! kuna tafiya dasu birnin! sannan Ku sace musu
shanayensu! da raqumansu! kuna zalum tarsu?".
Sani ne ya buga mai tsawa cikin fad'a yace.
"Shi wannan mai gaskiya me baya aiki sai na gaskiya shi ba mugu bane shi mai taimakon
wanda aka zalum tame".
Cikin tsoron yace "ya zanyi na yarda?".
Qara matsoshi yayi tare da cewa.
" Shin kana jin General Aliyu Muhammad Umar Rumoh?
shin kasan shine shuga ban kare haqqin makiyaya dake cikin fad'in wannan qasa tamu da suke
cikin dazuzzuka da tsaunuka? shin ko kasan shine soja na forko d'aya rasa cikin dajin Sambisa
ya kuwa ci nasara?".
Shiru yayi tare dayin murmushi ya matso kusa da Aliyu a hankali yace.
"BANDIRAWO ka makaran kana can kana baiwa wasu sashuka na qasarmu ranka dan ka
karesu yayinda masu b'arnar sukazo tushenka suka tarwatsa mutanen ciki suka koresu suna
kashe na kashewa suka qona na qonawa".
Cikin tafasan zuciya Aliyu ya rumtse idonshi tare da cewa.
" Muje ka kaimu Rigar Rumoh na gani".
Shiru yayi tare da siyayar da hawaye ya kamo hannun Aliyu cikin takaici yace.
*Bandirawo* a inda muke tsayennan cikin asalin rigar Rumoh ce ai an dad'e da watsa rigar
Rumoh ta zama wurin kiwonmu yau kimanin shakaru 4 kenan da y'an ta adda suka hana rigar
zaman lafiya sabida suka watsasu,
Kaga wadan can rigogin dake kusama
kullum cikin baraza na ake musu kan dole subar nan ".
Jikin jijiyar bishiyan da suke qasanta Aliyu ya zauna tare da dafe kanshi har zuwa d'an wani
likaci sannan kuma ya miqe tare da cewa Sani.
" Shi kenan na rasa ma dafa na rasa ma dosa mu tafi Sani zan qare rayuwa ta ba farin ciki".
Cikin sanyi da tausaya mai Sani ya miqe tare da cewa"oga kaqa yamma tayi kuma ba zamu
gane hanyar ba mu roqi Gainako ya rakamu".
Matsosu gainako yayi ganin suna tafiya dan Aliyu ya muna baya buqata.
da sauri yasha gaban sa cikin sanyi da jin son shi yace.
"Bandirawo kalli kan dutsen can da wancan qoraman".
Ido ya tsurawa dutsen da saman qoraman sai wani irin farin hayawi ke tashi tuni wurin ya fara
rufewa da hayaqin sai duhu ya fara qaruwa".
Maganar Gainako ta kuma katseshi cikin fillanci dai har yanzu yace.
" kaga wannan yanayin shi muke kira da *Labbare* yanayin ne da yake sauqa da zaran yamma
tayi dashi muke kwana sai kuma gari ya waye yake fara tafiya da zaran labbare ya sauqa ko
dabbobinmu basu fiye gani sosaiba kuma sanyine ke ratsa ko ina sannan tanan baku da hanya
fita sai ta bayan dutsen inko nan zakubi dole sai kun kwana a nan kafin ku samu fita sabida
yanzu duk ta inda zakubi zaki hadu da hayaqin labbare da kuma makiyaya sun taso kiwo".
Ido Sani ya dan kuma warewa ganin a take wurin ya fara wani irin yanayin duhu da sanyi mai
tsananin gaske.
Shi kam Aliyu duk bai ganiba don baijin komai
Amman gani tako ina dabobine ke faso dajin na fita yasa dole yabi hanyar zagayen yayin da
Gainako ke binsu a baya tare da sakin wani irin ihu irin na makiyaye da dabobnsu,
aiko sai ga dabobin sun biyishi a baya.
Cikin d'aga sauti yace.
"BANDIRAWO Ku biyoni zan nuna muku hanya".
Jin haka yasa suka rinqa bin shi a baya da motar su.
Tafiya mai dan nisa sukayi
Sai gasu sun fito ta bayan wata rigar Fulani mai matuqar kyau da tsari rigace mai zagaye da
ni'imomi da korayen tsirrei ta bayan rigar shukoki ne masu matuqar kyau daga gaban rigar
kuma wata koramace mai ruwan garai-garai ke gudana sai dutsen dake gaban qoramar gaba
d'aya wurin sai ya banda wani kalan qamshi da ni'imah.
Gainako tsayuwa yayi tare da ajiye sand'ar kiwonsa a wani fili mai farin yashi dake gaban
qoramar sannan ya juya gunsu dai-dai lkcin wani farin dottijo ya fito cikin wani gida daga dukkan
alamu gidane sai dai yanayin gidane mai zagaye da katanqar manyan duwatsu,
kai tsaye gunsu dottijon ya nufo cikin sanyi da tsura musu ido tare da murmushi
cikin sanyi yace.
(" Surbajo waru d'o")
"D'an saurayi zo nan"
Cikin sanyi suka matsoshi Sani ne ya gaida shi shiko Aliyu kawai bin shi da ido yake .
Cikin sanyi ya juya tare da cewa su biyo shi.
Shi kam Aliyu bin shi kawai yake cike da mamaki inane nan kuma Gainako ya kawosu.
Suna shiga tsakiyar gidan
dottijon yace
"Badd'i waru an e Inna waziri"
Badd'i kizo keda Inna waziri kuzo da madara da ruwa munyi baqi".
dai-dai lkcin wata Yar budurwa mai kimanin shekaru 16 ta fito daga cikin wata bukka riqe da
gwaryya a hannuta kanta a qasa tafiya take cikin kula da qoryar karta subuce ta fad'o ta fashe,
tazo dai-dai kan Aliyu da yake sunkuye yana qoqarin kwance but din qafafunshi qoryar tai
qasa......
*Wasa farin girki masu karu yanzu muka fara shiga cikin labarin muje zuwa*
By
Garkuwar Fulani
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*BANDIRAWO* page 4β£
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
Pure moment of life writers
P.m.l.w
*Dedicated 2 Ummee pinky & Becky Tika tare da Hanan smart*
Ta fad'a gefen shi lokaci d'aya ya d'ago kanshi cikin sauri don jin d'umin madarar shanun da ya
ratsashi gashi duk ya watsumar a jikinshi har izuwa fuskar sa.
Harara ya cillah mata cikin murtuqe fuska lokaci d'aya ya had'e gira sama da qasa yana mai
binta da wani irin mugun kalloh,
duk jikin sa sai d'iga yake tal-tal da nono.
Ita kuma Bodd'i qasa tayi da kai sai kerma da jikinta keyi kar-kar hatta numfashin ta sai da ya
sauya salon harbawan da yake,
cikin tsananin tsoro yana yin General Aliyu baki na rawa ta rinqa d'an ja da baya cikin sanyi
tace.
*"Wad'u muyal BANDIRAWO* kayi haquri dan uwa".
Cikin murtuqe fuska ya kuma watsa mata wani mugun kallo da yanayin jin haushin abinda tai
mai yaja wani irin ajiyar zuciya tare da jan d'an gajeren tsaki dan haqiqa kunyar dottijon nan yaji
ba dan shiba da zai zuba mata mari kam ai ita ba makauniya bace.
Itako tuni ta jabaya gun dottijon cikin fillanci tace.
"Bappa bari na kawo musu wani nono"
To yace tare da cewa.
"Ki kula fa karki sake zubda Wanda zaki kawon."
Kai ta gyad'a mai tare da juyawa cikin sanyi ta komai cikin gidan.
Shiko General cikin sanyi da d'an rad'ad'in zafin madarar ya kalli dottijon cikin fillanci yace.
"Bappa ni yanzu zan d'an watsa ruwa a jikina don na cire wannan kayan".
Toh yace tare da miqewa yana fad'in .
" Toh bari naje na sa a kawoma ruwan d'umi dan sanyin zaima yawa gashi labbare ya fara
sauqa ga sanyin magriba ga sanyin yanayin damina."
Kai ya jinjina tare da miqewa cikin sanyi yace.
"A a Bappa ba matsala zanyi ko da mai sanyin ."
Cikin fahimtarwa dottijon yace .
" kai Surbajo mufa sanyinmu ba irin naku bane bazaka iyaba don baka sababa."
Cikin dan murmushi yace.
"Toh ai jikina ba irin naka banne Bappa nifa jinina a tsinke yake ba kamar naka daya fara bacci
ba."
Dariya yayi sosai tare da cewa.
"Toh asheko Yau zaka san sanyin Gembu da Membila ya banbanta da na wuraren da ka saba
zuwa a dai cikin wannan qasa tamu kam."
A haka ya muna mai wasu randu nan tab'o guda 3 manya suna jere rabinsu duk an binnesu
cikin qasa sai samansu kad'an gaba d'aya jikin su sai naso yake da fidda damshin sanyi,
wata qorya ya d'ago daga gefen randar cikin murmushi ya bud'e randar,
da sauri General ya matso cikin sha'awa
yakarb'i y'ar qaramar qoryar yana juya ruwan cikin,
ruwane fari tas har yana wani garai-garai daga tsaye mutun na iya ganin fuskar sa da zanen
qasan randar,
d'iba yayi ya cika qoryar sannan ya d'aga cikin fillanci yace.
"(Bappa hato gad'a sudu mai woni)
Bappa ina toilet d'in yake?."
da hannu ya muna mai cikin murmushi da binshi da ido,
she ko shiga yayi cikin sauri don maqariba ta qarato.
Cikin sakin fuska Bappa ya kalli Captain Sani cikin hausar sa da take d'an fita yace .
"Surbajo tashi inkai ka d'akin ku."
Miqewa yayi tare da cewa.
"Toh Bappa bari na d'auko jakar kayan mu a mota."
Bayan ya dawo Bappa ya nufi wani d'an dakin bukka Wanda yake shatin kobo shi dai yana
binshi a baya cikin bin tsohon da ido tsohone fari tas mai kyawun fata da gashi sannan da ka
ganshi kaga mutun mai sanyin hankali da nitsuwa.
Suna shiga cikin d'akin Sani ya dire jakar General cikin mamaki ya sake baki tare da bin d'akin
da ido,
Komai na d'akin tsaf yake sai qamshi yakeyi ba