Showing 30001 words to 33000 words out of 81932 words

Chapter 11 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf

a hankali sai hawaye dake
tsiyaya a idonta kuma idon suna lumshe alamun ta farfad'o amman bata dawo hayya cin taba,
ajiyan zuciya ya sauk'e tare jingina kanshi a jikin ta,
Shiru yayi tare da tsura mata ido ganin gaba d'aya Abdul ya kumbura mata fuska tayi jajir gashi
duk jikin ta jini cikin tsoro da far gaba ya rumtse idon shi tare da kad'a kai,
gaba d'aya ya rasa abinda yake tunawa bere yasan abin da zaiyi mata,
Mik'e yayi ya fito Parlor cikin sanyi yana k'iran .
"Aysha."
Shiru ya tsaya ganin bata nan,
hakan yasa ya fitoh babban parlour nasu yana k'iran Anty Ayshan ,
Mama ne ta d'ago jajayen ida nunta cikin tsantsar k'iyeyya da tsanar Aliyu tace.
"Lallai ka dafawa kanka abinci wahala da bak'in ciki da k'uncin rayuwa kuma wallahi sai ka
kwashe saka makon wannan aikin da kayi min."

Bai kula taba bare ya kalle ta sai tafiyar shi yayi yana k'iran Aysha,
Abba ne ya kalle shi cikin tsoro yace.
" kai Haiydar zo nan."
Kanshi a sunkuye ya dawo gaban Abban shi cikin sanyi ya zauna gaban shi,
Ido Abba ya tsura mai ciki tuhuma yace.
"Haiydar anya kuwa kai mutum ne ? anya kuwa kana da zuciyar tausayi ? anya ko Haiydar kana
tsoron aika ta kisan kai ? shin ka manta nan ba fagen yak'i kakeba ? kana sane d'an uwanka ka
kashe? wannan wanne irin rashin imani ne?."

Kanshi a sunku ye yace.
Abba kuyi hakuri kai da Daddy Ku gafar ceni ."

A fusashe Abba ya rink'a zuba mai maruka tare da sakin kuka yana marinshi da tureshi yana
kuka yana cewa.
"D'an, d'an uwana ka kashe a gaban mu wai kuma kana cewa muyi hak'uri kai wanne irin zuciya
ne da kai mugun zuciya ko?."

Kai kawai yake juyawa tare da rawan murya yace .
"Abba ban kashe shiba ni hukun ci na d'auka a kanshi Abba kasan abinda Abdul yayi kuwa?."

Sai kuma ya mik'e cikin sauri,
Part nasu ya shiga yana zuwa ya ruggumo Meenal a jikin shi ya fitoh da ita yana zuwa kan 3 str
ya kontar da ita yayin da Abdul ke shimfi d'e a k'asan 3 str,
cikin rawar murya Aliyu ya kalli Abba da Daddy yace.
"Abba kuga abinda Abdul yayiwa y'ar mutane ga yadda ya sauya mata kamannni haddin ta
yaso ketawa ganin tak'i bashi fad'in kai yasa ya rink'a dukan ta kamar zai halla kata yaci zara
finta yaso ya keta haddin Aure dana shariyar musulmai yaci zarafin mace mai rauni,
amman dan na d'auki mataki kan laifin daya aikata shine gaba d'aya kuka k'asa ganin illar
abinda yaso aika tawa,
ita baku ga halin da yasa ta a cikiba ko dan ita ba y'arku bace Abba yanzu da Nafeesat aka
yiwa haka ya zakaji wanne matakin zaka d'auka kalli fa yadda ya fasa mata kai ."

Gaskiya dai koya take d'aya ce dai kuma a fili take,
gaba d'aya sai jikin su ya mutu sukayi shiru dan tabbas da y'arsu aka yiwa haka hak'ik'a suma
zasuyi abinda Aliyu ya aika ta.
Ya Amir ne yayi magana cikin sanyi yace.
"Wannan zaman baida amfanin mu tafi asibiti dasu yafi."

Kai Aliyu ya girgiza tare da cewa .
"Kar akai Abdul asibiti."
A fusace Mama tace.
"ai dole kace kar a kai kashi asibiti mugun uban mugaye wato a barshi ya mutu toh wallahi
alhak'in mutuwar sa a kan wuyan ka, banza mai zuciyar fir'auna."

Tsaki yaja tare da cewa .
"Oho ba dole,
in kuna so kuje asibitin ayi ta yad'e farar jikin shi kullum safe da yamma daga nan su nak'asa
miki d'a ni wallahi ba ruwana."

"Allah ya fika aniyar ka ta koma kanka."
Mama ta fad'i cikin tsana.

Shi kuwa Aliyu sake daukar Meenal yayi ya maida ta dak'i ya kwantar da ita sannan ya koma
kitchen d'in su ya bud'e fridge ya d'auko goran zam-zam mai sanyi,
Parlon ya dawo inda ya samu Abdul ya farfad'o sai jujjuya kai yake cikin wahala dan abi yafi
gaban kuka bare hawaye.

Gefen shi ya zauna cikin kula yace.
"D'azu na d'auki hukunci ne a kanka a matsayina na Jami en tsaro mai kare al'ummar k'asar sa,
ban hukun taka dan mugunta ko san kaiba na hukun taka kan kaso ka cutar da yarinyar da bata

san komai ba kuma na tsaya matane na d'auka mata fansa dan nine kad'ai dalilin zuwan ta
garin nan sannan dan nine madadin Uwa da uba a gareta kuma amanarta aka bani,
yanzu kuma zan jinya ceka a matsayi ka na d'an uwana jinina,
sannan ita kuwa zanci gaba da kula da ita da kawar da duk wani abin da zai cutar da ita a
matsayin ta na wacce aka bani amanarta kuma y'ar k'asata kuma mace mai rauni,
ka kiyaye gaba ko kallon kirki banson kayi mata bare kallon banza bare ta kai ga kayi niyar
cutar da ita ,
In kuwa kak'i ka goda hmmm zanyi abin da yafi haka."

Shi kam Abdul kai yake juyawa cikin wani irin numfashi da nishi sai zare ido yake da damk'e
hannushi zufa na keto mai tako ina.

Shiko General k'ara matsoshi yayi cikin sanyi ya bud'e marfin robar zam-zam d'in sannan ya
saiti inda ya tsulala mishi mayin gyadan ya rink'a zuba mashi zam-zam mai sanyin.

Hak'ik'a zam- zama rahama ne,
a take Abdul yaji wani irin sanyi na ratsa shi zafin na reguwa sanyin yake ji har cikin ranshi,
gaba d'aya kuma k'unan ya fara komawa dan da har ya fara tasowa,
(Zam-zam kenan maganin k'unan wutane duk tsananin sa koda ya tashi matuk'ar aka sa
zam-zam insha Allah zai koma kuma duk zafin da k'unan ya keyi ana zuba zam-zam sanyi
zaiyi),
duk cure-curen da Abdul keyi a take ya lafa sai ajiyan zuciya yake sauk'ewa lokaci d'aya baccin
sauk'i ya k'washeshi.

Mik'ewa Aliyu yayi cikin ajiye robar zam-zam d'in a gaban Mama yace.
Gashi a rink'a bashi yana sha kuma ya rink'a amfanin dashi insha Allah nan da 1 week zai
samu sauk'i".

Harara ta watsa mai shiko bai kulata ba ya wuce part din su .

Har yanzu Meenal a konce take cikin zubda k'ollah ganin kamar bacci take yasa ya shiga toilet
al'wala yayi dan jin an fara k'iraye-k'irayen sallah yana fita masallaci ya wuce tare dasu Abba da
ya Amir.


Ita kuwa Meenal yana fita,
ta fara motsi cikin tsoro ta fara kuka tana k'iran.
"Hamma Aliyu kazo d'an uwanka zai kashe ni zai keta min haddi."

Anty Aysha ce ta shigo da gudu jin kukan nata gashi ta ga fitar Aliyun,
tana shiga bakin gadon ta zauna cikin sanyi ta dafa kanta tace.
"Meenal kiyi shiru ki kontar da hankalin ki Hamma Aliyu yazo ya ceceki,
har abada Abdul bazai sake gigin yi miki komai ba bud'e idonki ki gani nice Anty Aysha ce a

kusa da ke."

cikin kukan ta bud'e ,
tana ganin Anty Aysha ta k'ara sakin kuka murya na rawa tace.
"Anty Aysha kaina wuyana guiwata duk ciwo suke min."

Kanta ta shafa cikin tausayawa tace.
" bari in had'a miki ruwan zafi kiyi wonka insha Allah zai bari."

Ruwan ta had'a mata mai zafi sannan ta dawo cikin d'akin cikin kula tace.
"Meenal tashi kije kiyi wonkan ko."

Cikin k'arfin hali ta yunk'ura tare da cije lips d'inta ta mik'e ta tsaya.
tana tsayuwa wan ta saki wani irin k'ara tare da yin k'asa zata fad'i tana.
"Wayyo guiwata."
da sauri Anty Aysha ta taimaka mata tare da rik'e ta gam sannan tace.
"Sannu Meenal Allah zai saka miki,
daure muje kinji ko?."

Kai ta gyad'a mata sannan cikin d'ink'isawa da taima kon Anty Aysha taje tayi wonka ta canza
mata kaya sallah ma sai a zaune tayi dan k'afar ta cije ga kanta dake sarawa tana idar da sallah
Anty Aysha ta kawo mata abinci,
amman sam ta k'asa cin tana zaunen sai kanta ke tsuke ga guiwar dake mata zogi,
suna cikin haka General ya shigo tare da Captain Sani samun ta a zaunen yasa Captain Sani
farin ciki shi kuwa General sai cewa yayi.
"Kici abinci kafin doctor yazo ."

Kai ta girgiza cikin zubda k'ollah tace.
"a a ni bana son wani doctor yazo sabida su sai suce sai sunmin allura wallahi ni bana so."

Tsuke fuska yayi tare da cewa .
"Toh a haka zaki zauna da ciwon.?"

"A a ni dai a barni zai worke."

"Toh kici abincin in bakya son Dr yazo."

Kai ta karya cikin sanyi gonin tausayi tace.
"Toh kacewa Dr kar yazo."

Murmushi Captain Sani yayi tare da zaro phone d'in shi ya k'ira doctor Jabeer cikin sanyi yace.
"Broz ka bar zuwan ma kawai dama kaima kace baka jin dad'i kuma matar ogan ma tace ita
batason allura."

Toh kawai Dr Jabeer yace sannan ya katse k'iran.

Ita kuwa Meenal cikin zubda k'ollah ta d'an cin abinci sannan tace bacci takeji .

Cikin tsurawa Aysha ido tace.
"Anty Aysha zan konta."

Matso ta tayi tare da talla fa mata ta d'aga ta amman sun k'asa dan yanzu k'afar ta k'ara tsani
gashi yanzu a k'asa dirsham take d'azu kuma a kan gado take.

Ido Aliyu ya zuba musu ganin sun tsaya suna haki ita kuwa Meenal sai hawaye take da cike
lips d'inta,
cikin sanyi yace.
"Aysha barta bazaki iya ba."

Ita kam Aysha sai ta koma gefe tana kallon Meenal Captain ma ido ya zuba musu.

Shiko General matsota yayi tare da sunku yowa zai d'aga ta.

Ganin haka yasa Aysha da Captain suka fice suna cewa.
"sai fa safe,"

Ita kam Meenal ido ta tsura mai ganin ya d'aga ta cid'ac kan gadon ya kontar da ita ba tare
d'aya kalli fuskar ta ba sai tsuke fuska da ya k'ara yi,
blanket yaja ya d'an rufeta sannan ya juya ya shiga toilet zai d'an watsa ruwa.

Ita kuwa Meenal tana konciya ta lumshe idon sai bacci ,
tana fara baccin sai ta fara ganin abinda ya faru da rana cikin mafar ki,
a firgice ta rink'a kuka cikin mafarkin tana .
"Hamma Haiydar zai kashe ni."

Yana jin muryar ta ya jawo towel da sauri ya d'aura jikin shi har tsuma yake ya fito,
yana zuwa ya sun kuyo kanta cikin d'aga murya yace.
"Ke ki nitsu ba komai ki bud'e idon ki ba abin da zai sameki ganin anan."

Idon ta bud'e a firgice sai zazza resu takeyi tuni zufa tafara tsatstsafo mata,
sai binshi da ido tayi shi kuwa juyawa yayi tare da cewa.
"Kiyi baccin ki insha Allah ba abida zai same ki."

Ita dai a firgice take shiyasa sai binshi da ido takeyi.

Shiko 3qtr da bes ya d'auka ya fita parlour a can ya kimtsa sannan ya koma cikin bedroom ,

fuska ya tab'e ganin ta kuma komawa bacci.

Parlour ya dawo ya zauna yana shan tea saiga Captain Sani ya shigo da ledan magunguna dan
yaje yayiwa Dr Jabeer bayani ciwon nata shine ya bashi magungunan ya kawo mata,
yana bashi magungunan ya juya ya tafi,
shiko yaci gaba da shan tea d'in,.

Ita kuwa Meenal Abdul d'in ta kuma gani cikin farki cikin tsoro ta fara tirje-tirje tare da sakin ihu
tana k'iran Hamma Aliyuuuuuuuu.

A firgice General ya nufi cikin d'akin yana shiga yaja wani irin dogon tsaki ganin baccin take
tana kuma ihu da tirje-tirje,
kanta ya matso cikin fad'a yace.
"Ke da Allah kin toshe min kunne ya isa haka kin zauna kina ta zunduba ihu cikin dare."

ai ita batama san yana yiba kukan take tana.
"Wayyo Bappa na Hamma Aliyu ya cuceni ya kawoni inda za'a keta min haddi d'an uwanshi zai
kashe ni wayyo Hamma Haiydar Abdul zai kashe ni."

Ganin tuk'uru tara mashi jama'a zatayi yasa ya sunkuyar yo kanta tare da d'an d'aka mata mari .

aiko cikin gigita ta saki k'ara tare da mik'ewa a firgice da kid'ima zata gudu ta hanka d'ashi har
saida ya fad'a kan gadon,
ta juya zata gudun ne yasa hannu ya kamo hannu ta ya fizgota jikin shi da k'arfi cikin maida
numfashi ya ruggume ta cikin faffad'an k'irjin shi sannan ya kuma......


By
*Garkuwar Fulani*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 2⃣3⃣to2⃣4⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*Kinkid'i kankad'a d'amoni na d'amoni gidd'o mo fina laramo, gaid'omo fina sukoyo ladde Allah
yamad'um, 💃🏻 shakka wala ν ΌνΌ² yoriki tenete ki b'ibb'e sammete b'end'uki yamete ki d'oidi
yalete...........*

Pml

Matseta da kyau tare komawa jikin kan gadon ya jingina ,
ita kuwa sai tuttureshi takeyi tana fizge kanta ganin tak'i nitsuwa ne yasa shi,
k'ara matseta gam a jikin shi kanshi ya sunkuyar dai-dai kunne ta a hankali ya fara hura mata
iska a kunne tare dasa hannu shi d'aya yana shafa bayan ta zuwa kanta ,
jikinta tad'an saki tare da murza kanta,
shi kuwa cikin muryar lallashi ya fara magana a hankali.
" Meenal ! Meenal kiyi shiru ki nitsu gani gaki Hamma Haiydar ne a kusa dake ba Abdul bane
gani nazo ina kusa dake Abdul bazai cutar da keba."

Shiru tayi cikin sauk'e numfashi da lumshe idon a hankali ta k'ara sakewa a jikin shi hannu ta
tasa ta zagayo k'ugunshi ta rik'eshi gam ,
Ido ya lumshe tare da shafa bayan ta ya gyara mata konci yarta a jikin nashi ,
ita kuwa kanta ta kuma murzawa a tsakanin wuyanshi da kafad'ar sa bakin ta na dai-dai kunne
shi cikin sanyi ta fara magana.
"Hamma Haiydar ka maida ni gun Bappa na."

"Me yasa kike so in maida ki gun Bappan?."

cikin baccin da ya fara d'ibar ta tace.
"Hamma Haiydar Abdul zai kashe ni ina tsoron shi ."

Gyara konciyan sa yayi tare da tallab'e kanta cikin sanyi yace.
"Gani a kusa dake ba abin da Abdul zai miki bazan sake barin wani abu ya cutar da keba kinji
ko Minalin Hamma Haiydar?."

Kai ta gyad'a tare da lumshe ido cikin gigin baccin ta rink'a k'iran shi.
"Hamma Haiydar!"

"Na'am ."

"Hamma Haiydar."

"Na'am Minalin Hamma."

Sake k'iran shi tayi a karo na 3,
Murmushi ya d'anyi cikin sanyi yace .
"Na'am ."
Haka tayi ta ki ranshi yana amsa mata har bacci ya d'ebesu baki d'aya.......


4:40 Am General ya farka cikin sanyi ya bud'e idonshi,

cikin kunya da tsuke fuska ya zameta gefen shi sannan ya mik'e yana tab'e fuska,
al'wala yayi sannan ya nufi masallaci
ita kuwa yana fita bada jimawa ba ta farka cikin tsoro ta sauk'o kan gadon ,
sai kuma ta saki k'ara tare da dafe gini ta tsaya dn azaba gaba d'aya k'afar ta rik'e tayi zafi
amman bai kai na jiya ba sai dai goshin ta ne kam k'ara kumbura ma yayi,
cikin dauriya da dafe gini ta d'ink'isa ta shiga toilet,
tana shiga ruwan zafi ta had'a mai zafi sosai sannan ta dunk'ule d'an kwalin ta ta rink'a
tsomawa cikin ruwan zafin tana d'an dannawa kan guiwar tata sai rumtse ido take dan zafi
amman a haka ta daure taci gaba da gasa guiwar har ta daina jin zafin,
goshinta ta goda gasawa amman ta kasa sabida zafin shi yafi na guiwar dan shi goshin kusan
sau 4 yana goruwa,
haka ta bari tayi wonka fuskar ta ko sai sabulu ta d'an shafa,
tana fita dogon wondo tasa d'an tsukekke sannan ta zura duguwar riga yar cas da ita ,
kan sallaya ta tsaya bayan ta zura hijabi a jikin ta,
sallan tayi cikin wahala dan in tayi sujjada kamar ta kurma ihu,
haka dai tayi sallan sannan tayi fara karatun azkar ,
tana shafawa ta koma bakin gado ta konta, cikin jin ciwon kai d'in sai hawaye da ke bin fuskar
ta.


Dr Jabeer kuwa tun wunin jiya yake cikin fargaba da tsinkewar zuciya ya kasa samun sukuni
gaba d'aya hankalin shi ya koma kan Aminan shi ,
a haka ya wuni cikin far gaba ko abinci ya kasa ci ,
dere nayi wani sanyin zazzab'i ya fara ratsa shi hakan yasa da wuri ya konta bayan yayiwa
Uncle saida safe ,
konci yayi amman ya kasa bacci,
daya rumtse idon shi sai ,
Fuskar Meenal yake gani cikin halin damuwa ga zazzab'i ga rashin konciyar hankali haka tasa
ya mik'e yayi al'wala ya fara nafilfili yana nemawa Meenal d'in shi tsari daga dukkan abin
cutarwa tsakanin mutum da aljan'
haka ya kwana kan k'afafun shi har sai 4:42 ya tafi masallaci ,
Bayan anyi sallan Asuba an idar Alhaji Ibrahim ya shaidawa liman akwai d'aurin auren da za'ayi
,
hakan yasa liman ya tsaida mutane daga fita masallaci ya shaida musu akwai d'aurin aure
yanzu nan,
Shi kuwa Dr Jabeer labarin d'aurin auren ya sama mashi kuzari kad'an tunda yau za'a malla
kamishi Amina a matsayi matar sa shiko yayi alk'awarin jiran ta koba dad'e koba jima zai jirata
kuma yanzu ya fara k'aunar ta da nemota dan gani yake duk jami'an tsaron nan na banza ne ba
gano mai ita zasuyi ba.
Cikin sanyin safiya da sa'ar dake ciki aka d'aura auren Amina Ibrahim mai dala (Meenal ) tare
da Doctor Jabeer Muhammad kan sada ki dubu 50 tare da shaidawar dubban al'ummah dake
rayuwa a ugguwar tasu da kuma yawun Malam Salisu Abduljalal limamin masallaci kenan ...

Bayan sun koma gida,.
hajia Aysha tare da Hajia Amina basu yi mamaki abinda ya faruwan ba dan sun san Alhaji
Ibrahim mai dala kaifi d'aya ne in yace ehh tofa ehh d'inne sannan in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login