Showing 66001 words to 69000 words out of 81932 words
Chapter 23 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf
zaiyi magana kenan Captain Sani ya shigo parlour cikin sanyi yace.
"Daddy ga Abban su Ramadan yazo tare da d'an uwan shi."
Cikin kula Alhaji Ibrahim yace.
"Maza je ka shigo dasu kace su iso."
"Toh" Captain yace tare da juyawa ya taho da su.
Bappa kuwa haka kawai yake jin wani irin farin ciki mara adadi Inna kuwa da Ummi mahaifiyar
Meenarl sai zuk'atan su ke harbawa da sauri-sauri.
Shi kuwa General Captain Sani ya watsawa harara dan ya naga shine yayi shishshigin kawo
Abban shi gidan,
Ramadan kuwa sai murmushi yakeyi.
Suna shigowa parlon Captain Sani ne a gaba sai Abba dake binshi a baya.
Inna ce ta mik'e tsaye cikin tsananin mamaki da d'an rud'ewa gaba d'aya jikin ta sai rawa yake
yi cikin firgici ta nuna Abban Aliyu baki na rawa tace.
" *WAZIRI* Kaine nake gani ko kamace? Bappa waziri juyo ka gani ga waziri da Usmanu."
Cikin sauri Bappa ya juya tare da sauk'e k'wayan idanun shi kan fuskokin ya ranshi da suka
bace masu dere d'aya yau kimanin shekara 38 kenan."
Bappa kam ba abinda yake cewa sai.
"Alhamhadullih ala kulli halin,
Allah na godema da wannan rahawa da kayi min na godewa Allah daya bani aron rai da damar
sake sa yarana a k'wayan idanuna."
Abban Aliyu da Daddyn Nafeesat kuwa,
gaba d'aya jikin su rawa yake kamar mazari kai tsaye gaban Bappa suka durk'ushe kamar yara
kuka sosai sukayi cikin kewar iyayen sun.
Inna kuwa gani take kamar mafarki takeyi shi yasa ta matsosu tare da rik'e Hanna yensu tana.
"Alhamhadullih Abubakar Usman nagode wa Allah ."
Barrister Lawan ne yayi magana cikin rud'ewa yace.
"Bappa su waye wad'an nan din a gareka ? ka sansu ne?."
Aliyu ma kai ya jinjina cikin zubawa Bappa ido.
Ajiyan zuciya Bappa ya sauk'e tare da nuna Abban Aliyu da Daddyn Nafeesat yace.
"Lawan wadan nan da kake gani yaranane na jinina nine mahaifinmu su
Inna waziri itace uwarsu mahaifiyar su wannan mai kama da Aliyun shine d'anta Wazirin da
kukeji ina kiranta dashi ,
wadan nan sune yayun Aysha mahaifiyar Bodd'i ,
yayunta uwa d'aya uba d'aya ,
sun bar rigarmu ne a wani deren munwayi gari babusu ba labarin su munyi nema har muka
kareya daga bisani muka fauwalawa Allah tare da saka ran watarana zamu gana,
lokacin da suka bar gida Aysha tana k'arama ,
ashe Aliyu jika nane ban sanina."
Wannan abin al'ajibin ya saka farin ciki a zuk'atan su baki d'ayansu. "
Ummi da Ammi kam sai murmushi sukayi..
Sun zauna sun tattauna sosai sannan daga bisani .
Bappa yace .
"Toh a maida auren Abban Aliyu da Ammi."
Barrister Lawan da Alhaji Ibrahim ne suka kalli juna cikin son nemawa k'anwarsu enci sukace.
"Bappa bamuk'i maganar kaba amman a bari sai gobe in munyi shawara."
Kai Aliyu ya dago tare da zuba musu ido zuciyar shi cike da tsanar su,
ya za'ayi ana son maida auren Ammin shi sukuma suna dojewa.
Cikin hatsala ya mik'e su Aliyun a goshi yace.
"Ni na bar muku y'arku,
Inma nine bakwaso a cikin zuciyar ku,
sannan yadda kuke ganin zaku hana Ammi na komawa gidan Abba na toh,
Shima yana iya d'auke mahaifiyar Meenarl tunda k'anwar sace,
sannan kuma zamu dauke Ramadan da Rayhana tunda yaran shine ,
ni kuwa a karan kaina ni Aliyu zan dauke Ammi na tunda mahaifiya tace,
Ku Kurik'e zuciyar ku muma mu rik'e tamu zuciyar."
Yana kaiwa nan ya fice yana cewa,
"kuyi tunani da kyau."
Yana fita ya figi motarsa yayi gida.
Barrister Lawan kuwa shiru yayi yana tunanin a zahiri fa Aliyu zai iya tsanarsu ya dauki gaba
dasu ,
tuno hakan yasa shi yarda a take a wurin aka d'aura auren Ammi da Abba ,
Barrister yayi haka ne dan Samar da fahimta,
sannan batun Meenarl kuwa,
Sukace tunda shida bak'in shi yace ya hakura shike nan.
A ranar Abban Aliyu ya dauki matarshi da iyayenshi da su Ramadan ya koma dasu cikin gidan
shi.
Gidan su Aliyu ya cika da farin ciki da wolwola sai dai sam Aliyu baya sake wa da Ammin shi.
Meenarl kuwa tunda General ya fita take ta kuka DR Jabeer yayi iya yinshi tak'i sai cewa take.
"Hamma Haiydar bashi da lafiya wallahi inajin tausayin shi."
Captain Sani ne ya kalli d'an uwanshi cikin sanyi yace.
"Hamma Jabeer wallahi tausayin shine jigon so da zaran tausayin ya zauna toh akwai so
maitarin yawa,
inka yarda ka meyarwa Hamma Haiydar matarsa shi take tausayawa ni nasan irin zaman da su
kayi."
Washe gari da dare
Wannan magana ta Captain ita tasa Dr Jabeer karaya ganin tun jiya take kuka tak'i ko cin abinci
haka ta wuni har zuwa yanzu na d'arfe 9 na dare gaba d'aya ta tsanan ta damuwan ,
hakan yasa Dr ya yankewa kanshi hukunci yanzu zai kaita gun Aliyu shi zai hakura da ita zai
bar mishi ita,
ko dan hadisin nan da ya horemu da mu sowa yan uwanmu abin da zamu sowa kanmu.
Haka yasa ya kalleta cikin sanyi yace.
"Muje en kaiki."
Haka kuwa ta biyoshi suka taho gidan su General d'in.
Shi kuwa General a dai-dai lokacin ya sallami Ammin shi ya fito da nufin wucewa cikin Jaji.
A bak'in get ya tsaya ganin motar Dr Jabeer na shigowa,
fitowa yayi ganin Dr Jabeer d'in ya fito rik'e da hannun Meenarl kai tsaye gaban General d'in ya
tsaya cikin sanyi ya kamo hannun Meenarl ya had'a dana Aliyu cikin karfin guiwa da zuciya
yace.
"D'an uwana ga matar ka ni na bar maka ita har a bada dan na gane cewa a kanka Meenarl
tasan so."
Shiru General yayi cikin mutuwan jiki ya k'asa ko magana,
Shi kuwa Dr sai murmushi yayi tare da cewa.
"Fatana zaka bani auren Rayhana."
Shima Aliyu sai murmushi yayi,
tare da cewa "uhummm."
Daga nan shikam Dr Jabeer ya shige cikin gida gun goggonshi Ammi,
Shi kuwa General hannun Meenarl yajawo tare da cewa.
"Minalin Hamma Haiydar zomu tafi Jaji a can zamu kwana."
Sai kuma ya jawota jikin shi tare manna...
By
*Garkuwar Fulani*
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*BANDIRAWO* page
5β£1β£to5β£2β£
*Na*
*Aysha Ali Garkuwa*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*Wannan shafi naki ne ke kad'an Fiddausi sodangi Allah ya bar zumunci*
*Hak'ik'a mai sonka shike kawo maka goron gayyata da nufin kaje muhallin sa tare da baka
kulawa da karramawa ta mussam man tabbas nasan kuna k'aunata k'uggiyoyin da kuka nemi
da na kasance a cikin ku , ku sani bazan mantaku ba kuma har kullum a duk inda nake kuna
raina Garkuwar Fulani takuce kamar yadda kuke nawa INA k'aunarku ν ½νΈν ½νΈν Ύν΄ν Ύν΄ ina al'fahari
daku ina kuma mai kyau tata zaton zakuyi min uzurin da kekyawan fahimta na rashin karb'ar
goron gayyatar ku gareni. ina k'aunarku inamai al'fahari daku ν ½νΈν ½νΈν Ύν΄*
Manna ta a k'irjin shi yana sauk'e ayijar zuciya,
ita kuwa Meenarl tureshi tayi tare da janye jikinta daga gareshi cikin had'e fuska ta tura bak'in
tare da juyawa tayi bak'in gate d'in da nufin zata fita gidan.
Ganin haka yasa General yin sassanyan numfashin tare da binta a baya cikin sanyin murya
yace.
"Minalin Hamma Haiydar ,
fushi kikayi da Hamman ki ne?."
Shiru bata kula shi ba sai ci gaba da tafiyarta tayi tana zubda k'ollah.
Matsota ya kumayi cikin kula ya mik'a hannu da nufin jawota jikin shi ,
da sauri ta kauce tare da k'ara saurin tafiyar tata.
Shi kuwa General gabanta ya sha tare da tsura mata ido fuska a tsuke yace.
"Tun da bakya son ganina zoki koma gun Dr Jabeer ai shi kina son kasan cewa tare da shi."
Cikin fushi da kukan da ya kufce mata tare da ci gaba da tafi yar tace.
"Ehh zan tafi d'in nima zan tafi gidan mu shi ma Hamma Jabeer ai bayada zuciya ne ina jinka ai
jiya kace ba ruwan ka da ni harda cewa su Abba su rik'e zuriyar su kuma ku rik'e taku dan haka
nima bazan je gidan kuba."
Kamar wasa yaga tuk'uru tafiya take har ta fita harabar gidan ta mik'e kan titin tana tafi yar ta ga
uguwar shiru kowa na cikin gidan shi sai haske da ya gauraye kan titin ganin haka yasa shi
juyawa cikin gidan cikin motar shi ya shiga tare da jan motar a hankali ya fito tare da bin bayan
ta.
Bappa dake cikin masallancin k'ofar gidan kuwa murmushi yayi tare da binsu da ido.
Shi kuwa tafiya yake a hankali har yaje gab da ita sai kuma ya tsaya tare da bud'e mata marfin
motar ,
tsuke baki ta kumayi k'ollah na bin hab'arta sai tafiyarta take kamar ma bata ganshi ba.
Shi kuwa k'ara binta yayi a hankali har ya iso gefen ta sannan ya kuma bud'e mata motar,
nan ma juyawa tayi tare da tsuke baki ta tura shi ta d'anashi sama kamar k'arin kunama.
Shi kam General haka kawai yake jin shauk'in yana yin da suke cikin sai murmushi yake yi tare
da shafa sajen shi.
Matsota ya kumayi da motar,
Amman sai ta kauce tayi gaba da sauri.
a hankali Meenarl ta fara juyo sautin kukan kare yana dumfaro inda take,
gaba d'aya sai ta kame jikin ta dan harga Allah tana da tsoron kare a rayuwar ta gashi titin
uguwar shiru kamar ba mutane .
shi kuwa General binta ya kumayi tare da tsayuwa a gaban ta ya bud'e murfi tare da tsura mata
ido cikin karya wuya.
Share shi tayi tare da d'aga k'afar ta taku d'aya tayi a nabiyun ta d'ago kanta cikin zare ido dan
haggo karnu ka har guda 4 sun nufo kan titin da taken cikin gudu da haushi,
ido ta zaro tare da juyawa ta kalli Hamma Haiydar d'in nata,
ganin haik'an k'adaran kanta zasuyi yasa ta juyo cikin tsoro da fushi ta shige cikin motar tare da
jawo marfin ta rufe gim.
Shi kam General kai ya sunkuyar tare da sauk'e ajiyan zuciya ya figi motar a guje,
tafiya yake kamar bai san da ita a cikin moton ba ,
ita kuwa tura baki tayi da had'a fuska ga yunwar dake k'wak'wular hanjin ta sai kawai tayi luf a
jikin sit d'in tana zubda k'ollah.
a haka cikin lokacin kad'an suka isa cikin Jaji kai tsaye gidan shi ya nufa dasu.
Yana yin parking ya fito tare da yin mik'a sannan ya bud'e baya ya sunkuye tare da jawo laptop
enshi sannan ya koma gaba ya dauko phones enshi,
sai kuma ya rufe k'ofofin tare da zaga yawa gunta bud'e motar yayi ba tare da yayi magana ba,
Ita ma shiru tayi sannan ta fito ,
tana fita ya rufe motar sannan ya mik'e ya nufi cikin gidan,
da fari kamar ta tsaya so sai kuma taga gaba d'aya harabar wurin cike yake da sojojin ,
hakan yasa ta bishi a baya,
a parlour ta riskeshi yana since igiyoyin takalmin shi,
ita kuwa sai ta koma gefen ta tsaya cikin fara kuka kasa-kasa dan harga Allah yunwa takeji,
Shi kuma yana cire takal man ya mik'e tare da balle beld'in k'ugunshi ,
ya zame wondon kakin dake jikin shi,
sai kuma ya fara balle boturan rigarshi,
yana gamawa ya zare rigar ya bar bocs da bes sannan ya had'e su a hannun shi ya wuce cikin
bedroom.
Yana zuwa kai tsaye toilet ya shige cikin sauk'e ajiyan zuciya yayi wonkan shi pes tare da murje
jikin shi da sabulai masu k'amshin gaske, towel ya d'aura a k'ugunshi tare da rataye d'an k'ara
min towel d'in a kafad'an shi
yana fitowa gaban dressing mirror ya tsaya ,
hannu yasa ya rink'a murje jikin shi da mai tare da feshe duk sashin jikin shi da turaruka masu
sanyin k'amshi da sanyaya zuciya gaba d'aya d'akin ya d'auki wani irin k'amshi da sanyin A,C.
Ita kuwa Meenarl zuwa yanzu ta gama iya dauri yarta sai kawai ta saki kuka mai k'arfi tare da
yarfa hannu tana d'an dire k'afafun ta tare da cewa.
"Wayyo Allah na! wayyo Bappa na! ni dai wallahi yunwa nike ji kirjina ciwo wayyooo."
Kai General ya d'ago cikin tab'e baki ya ajiye rigar baccin sa d'aya zaro sannan ya fito parlour
yana gyara d'aurin towel d'in dake kan k'ugun shi.
Yana zuwa gaban ta ya tsaya tare da Sa hannu ya jawota gare shi,
itako sai yarfa hannu take tana d'an dukan k'irjin shi tare da cewa.
"Ni dai ka maidani gun Ummi na wallahi ni gun Bappa na zaka kaini ni yunwa nikeji."
Fizgota jikin shi yayi da k'arfi sannan ya matsota a jikin shi cikin had'e fuska yace.
*"Meenarl* ki nitsu ki tsaya me kike so?."
Cikin kuka tace.
"Ni yunwa nake ji jiri nake ji k'irjina ciwo."
Kai ya juya tare da Jan tsaki a ranshi yace.
"Ba ga irinta nan ba RAMADAN YA KORE MIN MAI AIKI,
yanzu ya zanyi."
Ita kuwa jin yaja mata tsaki yasa ta tureshi ta koma kan kujera ta zauna taci gaba da kukan.
Ajiyar zuciya ya sauk'e tare da jawo phone enshi ,
Captain Garba ya kira tare da bashi umurnin ya somo mishi d'an abin da zaici.
Cikin k'ank'anin lokacin sai ga Captain Garba da aiken ogan nashi.
Yana karb'a ya juya tare da rufe k'ofar gaban ta yazo ya ajiye mata ledodin sannan ya mik'e tare
da shigewa kitchen pilet da cup ya d'auko,
yana zuwa ya wore ledan wanda kaji ne a ciki wanda sunsha kayan had'i sai k'amshi yake tashi
,
kan pilet din ya baje mata shi sannan ya d'auki cop d'in ya tuttula mata juice mai sanyi,
sai ya tura mata su gaban ta cikin murtuk'e fuska yace.
"Sauk'o kici a cici kawai mai kukan yunwa."
Tura baki tayi tare da sauk'owa k'asa ta zauna cikin share k'ollah ta fara tsakuran naman
gefe-gefe tana cin tana d'an shan juice d'in,
shi kuwa phones enshi da laptop nashi ya tattara zai mik'e kenan ta ture pilet d'in tare da mik'e
wa tana tura baki tace.
"Hamma ya isheni wonka nake son yi kuma girjina yana min ciwo."
Pilet d'in ya kalla sannan ya d'ago kanshi tare da tab'e baki yace.
"Ai dama ba yunwar kike jiba mai jin yunwa harda kukan ne zai cakalkali abinci yace ya
k'oshi."
A hankali tace.
"Zanyi wonka fa."
Juyawa yayi ya shige cikin bedroom yana.
"Toh zoki hau kaina kiyi wonkan!."
Kai ta kad'a tare da tattare pilet din ta kaisu kitchen sannan ta shige cikin bedroom d'in,
shi kuwa dama yana shiga kan gado ya haura tare da watsa laptop enshi da phones nashi a
gefenshi shi kuma yayi rigingine ya had'e tafin Hanna yenshi yayi pillow dasu gaba d'aya k'irjin
shi a woje sai towel dake k'ugunshi.
Ita kuwa tana shiga bata kalleshi bama ta shige toilet d'in cikin jin bacci ta zare doguwar rigar
dake jikin ta sannan fesa wonkan ta,
sannan ta kalli. towel d'in dake wurin d'an k'ara mine gashi ita kuma bata son maida rigar da ta
cire yanzu,
shiru tayi tare da jawo d'an bireziyar da ta cire wanda kab Momy ce take saya mata su duk da
dai ita ba sakawa take yiba asalima yau ta fara sakawa dan ya bata sha'awa,
mak'alashi tayi da k'er sannan ta d'aura towel d'in kan k'irjin ta kai ta sunkuyar ganin bai kai
guiwarta ba,
amman sai ta yi k'asa da kanta sannan ta fito ,
gaban mirror taje ta d'auki man shafawarshi ta shafe jikin ta sannan ta koma kan turaru kanshi
ta rink'a feshesu a jikin ta tana lumshe ido,
shiru yayi yana kallon yadda take feshe turarukan fees,
saida taji kanshi ya isheta sannan ta je gaban shi a bak'in gadon cikin sanyin bacci da sanyin
AC ta kalleshi tare da cewa.
"Bacci nake ji ina zan konta ?."
Lumshe ido yayi tare da nuna mata gefen shi.
Ita kuma sai tsuke baki tayi tare da cewa.
"Ni wurin nan ya min kad'an gashi duk ka ajiye tarka cen woyoyin ka."
Shiru yayi tare da bud'e idanun shi a hankali ya tsurawa fuskar ta ido,
sai ya kuma nuna mata kan k'irjin shi murya a kasalan ce yace.
"Tunda ke giwace uwar birgima zo ki hau kaina ki konta tunda nan duka bazai isheki ba."
Hannu ta fara yarfawa tana d'an buga k'afa tace.
"Ni dai bacci zanyi gashi k'irjin yana ciwo."
Haka ta rink'a mita har kusan 12 ganin hanashi bacci zatayi ya sashi mik'o hannu a hankali ya
jawota jikin shi kan k'irjin shi ya kifata,
hannu yasa a tsakiyar bayan ta ya rink'a shafawa a hankali murya can k'asa yace.
"Dere yayi Minali kiyi baccin ki kinji ko."
Kanta ta rink'a juyawa tare da murza k'afafun ta a kan nashi har tana shirin zame mishi towel
d'in jikin shi cikin jin bacci tace.
"Hamma kirjina wallahi kirjina ciwo yake min numfashi na yana tafiya."
"Dama kina da ciwon k'irjin ne?."
"A a ni Yau na fara jin ciwon."
Hannun shi ya cusa cikin towel d'in jikin nata a hankali ya cusa yatsun shi biyu ya kamo robar
bireziyar nata sannan ya sake shi pet a bayan ta cikin rad'a yace.
"Yaushe kika fara saka wannan abun?."